Showing 24001 words to 27000 words out of 227321 words

Chapter 9 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1502

busar da iskar bakinsa ya rufe ido ya bude ya girgiza kai. Sai kuma ya bude motar ya dauko wayarsa ya rufe. Number Safeena yayi dialing ya kai a kunnensa. Wayar ta yi ringing har ta gaji bata daga ba. Ya sake cika bakinsa da iska ya koma cikin motar ya zauna.

 Noor karki sake yi ma wani karyar kin san ni, kuma ki daina bin motane any how ko kin san su ko baki san su ba

Ta daga mishi kai a hankali cike da natsuwa.

 Kuma ki rika jin maganar iyayenki kin ji?

Nan ma ta daga mishi kai.

 Ka yi hakuri, ba zan sake ba daga yau ba zaka sake ganina ba

Ta fada tana hawaye sai kuma ya ji babu dadi.

 No ba wai bana son zuwanki ba ne, kawai bana son ki saka kanki a matsala ne, kin ga iyayenki suna miki duka da fada, kuma kin ga yanzu kin samu rauni saboda haka

 Na fahimta...

Ta amsa masa murya a sanyaye hakan sai ya kara masa raunin tausayinta dake zuciyarsa.

 Me kike son ki ci?

Ta girgiza kai, ta bude motar ta fita.

Sai shi ma ya bude ya fita ya wuce gaba ta bi bayansa.



NOOR POV.

Babu kowa a office din, mutunen dazun da ban san waye ba yayi tafiyarsa. Kareem da kansa yaja min kujera na zauna sannan ya zauna a kujerar dake facing din tawa.

 Baki sha'awar cin komai? Ko kuma na miki takeaway

Na girgiza masa kai, ji nake bana sha'awar komai nasa a yanzu.

 Noor

Ya kira sunana a hankali a lokacin da na dago kai sai na tarar ni yake kallo.

 Kin sa na ji babu dadi, maganar da na yi ce ta bata miki rai?

Nan ma na amsa masa da kai. Yanzu kam gaba daya hankalina ya koma gida gurin mahaifiya hukuncin da zan karba idan na koma shi ya tsaya min a rai.

 Ina tunanin gida ne, yau Mama sai ya sake karya min hannun babu wadda zai cece ni

Na fada hawaye na sauko min, domin a lokacin ne na gane kuskuren da na aikata na biyo matar har nan.

 Ko zamu tafi tare da Saurayin na ki sai mu bata hakuri mu yi mata bayani? Bana son ta dake ki?

Magana yake min kamar wadda ya damu da ni da gaske. Na girgiza masa kai ina kallon hannuna da aka daure.

 I'm sorry haka kaddara take wani lokaci, ba ma iya kauce mata

 Ni kaddara ce marar kyau a gidanmu, shiyasa ni ce mai laifi kullum, shiyasa Babana...

Na samu kaina da fadar haka, sai kuma na yi shiru domin be kamata na fadi ciwona a inda babu magani ba. Wani abun da ban yi zato ba, shi ne tashin hankalin da na gani a fuskar Kareem a lokacin da yake kallona, damuwa da tausayi sun bayyana karara a fuskarsa. Na sauke kaina kasa tare da saukowar ruwan hawaye.

 A duk lokacin da kika ji kina bukatar wani abu ki zo gurina kofata a bude take, ko gobe idan wani ya tambaye ki miye alakarmu ki fada masa abun da yayi daidai da ra'ayinki, karki ji haufi

Ban ce masa komai ba, kuma ban dago ba hawaye kuma ba su fasa min zuba ba. Ta gilashin dake window na lura da Magariba ta yi saboda duhun da ya fara shigowa. Yunkuri yayi sai mike tsaye sai aka turo kofar office din aka shigo bayan ya kwankwasa.

 Ranka ya dade wai wani ne yake nemanka, sunanshi Zafeer

 Shigo da shi

Sai ya koma ya zauna da kyau bayan ya amsa, sannan ya kalleni.

 Share hawayenki kar ya ga kina kuka

Na share hawayen na maida hankalina da dubana gurin kofar shigowa. Babu jimawa Zafeer ya shigo dakin yana kallon hannuna hankalinsa ya kara tashi.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Baby Noor me ya same ki?

Na yi shiru wani sabon hawaye ya cika min ido ni da ban saba hawaye sosai ba. Kareem yana masa bayani amman Zafeer ko kallon inda yake be yi ba, da alama daga bakina yake son jin karin bayanin.

 Wata mata ce tace na kawo ta nan...

Na fada masa gaskiyar yadda komai ya faru. Sai dai a yadda na lura gaskiyar tawa ta masa Waci domin kuwa rufe ni yayi da fada abun da be saba ba.

 Me yasa zaki yi haka? Wa kike son ki burge? Me kike nema a gurina da baki samu ba har zaki kwadayin wani ya zama saurayinki? Ita din me kika mata da zata ji Miki ciwo a hannu haka? Saboda me? Daga makaranta sai ki tsallake ki zo nan yanzu matar nan idan cin mutane take sai ta cinye ki

Wani irin fada yake min da tsawa kamar ba Zafeer dina ba. Lallai na yarda ni sokuwa ce kuma an aikata babban laifi. Ta cikin ruwan hawaye na ke ganin Kareem ya mike tsaye yana fada.

 Haba Malam daga zuwanka sai ka rufe ta da fada, ta ki yarda na kaita gida saboda tana tsoron fada, tace a kiraka saboda tana tunanin zata samu sauki a gurinka sai kuma ka rufe da fada babu sauraren Uzuri, yarinya ce fa bata kai matsayin da kuke tunanin ta banbance daidai da akasin haka ba kuma babu wadda baya kuskure

Zafeer ya kalleshi.

 Ai kai ka banbance daidai, tun da kana tsaye aka ji mata a hannun, sai yanzu zaka ce bana sauraren uzuri, uzurin me zaka ba ni?

Kareem ya nuna shi da tsaya.

 Tsaya matsayinka ka kula da kalamanka, wata kila ba dan yarinyar nan ba, da baka da alfarmar shigowa office din nan, so respect yourself

 Gaskiya ne, kai ya kamata ka fara respecting kanka ai, kamin ka ni, babu ruwanka da yarinyar nan babu ruwanka da ni, baka san abun da ke tsakaninmu ba

Zafeer ya fada. Kareem ya kalleni ya kalleshi sai kuma ya dauke kai. sannan sannan ya kalleni a fusace.

 Mu tafi

Na wuce da sauri ya biyo bayana, haka ya saka ni a gaba har muka isa titi. Ya tari Napep ya shiga sannan ni ma na shiga, gaba daya a rikice nake, yadda na ga ran Zafeer ya bace ya saka hankali kara tashi, shi kenan da yake goyon baya baya son bacin raina balle kuma Baba ko Mama ya ransu yake a yanzu.

 Noor

Na kalleshi.

 Me yasa kika ce mutumen nan Saurayinki ne?

Na yi shiru domin ba ni da wata hujja da zata gamsar da shi, indai har Hujjar dazun da na bashi labarin komai be gamsar da shi ba ban san me zai kare kaina sa shi ba.

 Saboda yana da kudi?

Zuciyata ta buga da karfi, Zafeer ya fara lissafin da ban taba yi ba, ya zarge ni da abun da ban yi tunani ba. Sauke murya yayi kasa sosai kamar marar lafiya.

 Zan yi kudin In Shaa Allah Noor zan gina miki irin gidan da kike so, da irin tsarin da kike so, zan wadata ki da komai, zan maida ke sarauniya na maida ke abar kwatance, ki kara hakuri ki kara min lokaci kin ji?

 Ba saboda haka ba ne, ni dai kawai na yi ne saboda na firgita matar

Ina jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya kalleni a raunace.

 Dan Allah karki sake, rai na ya bace yau saboda abun da kika yi, ban jidadi ba kin saka na raina kaina, kuma kin saka na miki wani kallo da be kamata ba, Baby Noor ki zama mai sauraren maganar iyayenki kin ji? Ki zama mai bari idan aka hana ki, mai yi idan aka ce ki yi kin ji Baby na

Na daga mishi kai har lokacin jin nake kamar ba Zafeer dina ba ne, Mai Napep din ya juyo ya kalleni.

 Lafiya?

Zafeer ya tambaya be ce komai ba ya juya ya cigaba da tukinsa.

 Kin san inda matar nan take?

 Ban santa ba

Na amsa ina share hawayena. Zafeer yayi kwafa.

 Zafeer ka yi hakuri ba zan sake ba

Na fada murya na rawa, sai yayi min ya girgiza min kai. Be sake ce min komai ba har sai da muka fita Napep din ya sallami mai Napep din a lokacin duhu ya fara sosai sai dak hasken wutar nepa da ya haska unguwar ya taimaka mana.

 Ina sonki Noor Allah ya saka min sonki fiye da yadda kike tunani, kuma na san kina so na kema, dan Allah karki bari shedan yayi nasara akanki, karki biyewa kyale kyalen zamani, with time ni ma zan yi miki komai

Muna tafe yana fada min haka, ban iya furta komai ba har muka doshi gida, zuciyata kuma ta doshi bugawa kamar wadda azali ke kiranta. Daga nesa muka hango mota fake a kofar gidanmu, ni dai daga inda nake Ina iya shaidar Kareem ne tsaye a tare da Baba, domin akwai wutar nepa a unguwar, kuma na gane tufafin jikinsa na yau da motarsa sai dai abun da suke tattauna ne ban sani ba. Na kalli Zafeer sai na ga yanayinsa ya sauya kamar be ji dadin haka ba, ni dai da mamaki na karasa gurin faduwar gabana yana karuwa, hakan ya saka ni rage tafiyar da nake Zafeer ya kalleni.

 Muje zan masa bayani zai fahimta ba zai miki komai ba

Kamar Kareem ya san abun da Zafeer yake fada sai na ji ya ce.

 Noor karaso nan, na yi magana da Baba na masa bayanin komai, kuma ya fahimta daman shi ne makasudin da ya saka na yi rigaku zuwa

Na kalli Zafeer har sai da yayi min alama da na tafi sannan na tafi ina rike da hannuna.

 Allah dai ya tsare babu karaya ai

Cewar Baba da far'arsa kamar ba shi ba. Zafeer ya gaishe shi, Baba ya amsa.

 Ashe kai ta kira...

Zafeer ya risina.

 Eh ayi Hakuri dan Allah Baba

 Babu komai, Allah kyau gaba Ai shi Alhaji yayi min bayanin komai

Zafeer ya kalleshi ya kalleni.

 Shiga gida Noor

Na nufi kofar gidan kamar yadda ya bukata na shige cikin gidan. Sai dai ban isa a inda Mama take zaune ba kamar tana jirana, Yaya Nabill ma dake kusa da ita ina iya karantar yadda yake cika yana batsewa.

 Idan na tsira daga dukan Baba Mama fa?

Na tambayi Kaina...
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -8


Daga Yaya har Mama babu wanda ya ce da ni shigo ki zauna ko kuma juya ki koma. Ina tsaye a gurin na kasa kuka na kasa magana har Baba ya shigo.

 Shiga ciki ki zauna mana, ai duk abun da kike ba laifin ki ba ne uwarki ce ta ke goya miki baya, baki da matsala ke

Cewar Baba sannan ya wuce ni ya shiga cikin gidan. Mama kamar tana jiransa ta ce.

 Daman ai kullum ni ce ice mai dadin hawa, nan gana Noor ko kisan kai ta yi ni zaka dorawa laifi, duk abun da kowa zai aikata kaina zai dawo, shin ni kadai nake da hakkin tarbiyantar da ita? Kai ba Uba ba ne?

 Saboda ina uba sai aka ce na zauna gida na kula da yara? Tarbiya ai ta uwace no Cewa aka yi na fita na nemo, ke zaki kula da gida dan haka dole duk abun da yara suka yi na ce laifin ki ne

Mama ta yi shiru na san kuma ba dan ta rasa abun cewa ba sai dan tana gudun fadan yayi nisa.

 Ni na gaji da halin yarinyar nan, tun da aka haife ta cikin wahala nake, kar taje nan gaba ta dauko min abun magana tun da har ta gane bibiyar maza a inda suke, daga bige hannu da kai ban san inda za'a tsaya ba, ko yanzu Allah kadai ya san gaskiyar abun da ya faru, kar taje ta dauko min abun kunya na kasa fita cikin jama'a, zan fadawa yaron idan ya shirya fito ayi auren daman ni dai ba wani abu na aje ba, balle na ce zan dauka na kai masa, ko zane daya Allah ya hore masa ya kawo a hada ya da tabarma ayi musu aure su je can su karata, ke dai ba iya tarbiyarta kike ba tun rana karama balle kuma yanzu da take kara girma

A fusace Mama ta mike tsaye sai ganin na yi bulalar wayar wuta ta fado a jikinta.

 Wai Malam tunanin kake abun da N???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?oor take dadi yake min? Ko kuma ganin kake ni nake zaunawa na tsara mata shirirtar da zata je ta yi a waje? Daga Islamiya fa ta bar yar'uwarta ta tafi gurin yawon shiririta, a can idan kasheta za'ayi an dade ba'ayi ba, kuma kamar Noor ace ta san ta tsame kafa ta bi wata su tafi restaurant, kanen ubanta ne a can ko na uwarta, babu sanarwa babu neman izinin kowa

Baba ya rike gemu.

 Toh.... Ai ga irinta nan a gabansu kike fada min magana son ranki kina min tsawa saboda kin isa, ai tarbiyarce suke kallo suna dauka

 Tarbiyar ce, idan baka Gamsu da ita ba Malam ka auro wata uwar ta zo ta ba su wata tarbiyar, daman ai ka saba aure aure

Yau kai na ga dabam, Baba ce take fadawa Baba magana cikin bacin rai abun da bata taba ba a gaban idona. Baba kamar yana jira sai ya nufe ta yana nuna kansa.

 Ni kike cewa na saba aure aure...?

Ya Nabil dake zaune yayi hanzarin mikewa tsaye ya tare Mama ya shiga tsakiyarmu.

 Toh ko dukana zaka yi? Nace dukana zaka yi?

 Ba dukanka zan yi ba Baba amman ba zan zuba ido ina kallo ka daki Mama ba a gaban idonmu, Baba abun da kake babu dadi wani abun ba laifinta ba ne amman sai ka dora mata laifi komai aka yi a gidan nan cewa kake laifinta ne, ta ina yanzu laifin Noor ya shafe ta? Baba be kamata ace a gaban idonmu ka doke Mama ba wani abun ai ka daga mata kafa ko dan mu

 Ayyy haka ne, lallai Nabil wuyanka yayi kwari, yanzu ni zaka zauna ka tsarawa magana haka son ranka? Ashe kai ma baka da mutunci toh sai ka doke ni na san ka girma marar mutunci, saboda ina talaka kake raina ni?

Mama ta ja Nabil gefe ta tura shi.

 Fita can waje idan ya fita sai ka dawo...

Tana rufe baki Baba ya dauke ta da mari.

 Ya fita sai na fita ya dawo wato ga mahaukaci ko? Ga mahaukaci na hauka

 Baba...

Ya Nabil ya zaburo da karfi yana hakki har sai da Mama ta rike shi.

 Kul kul kul ko yanka ni ubanka yayi ka kai hannu ka dake shi ban yafe maka ba Nabil, karka kuskura zuciya ta debeka ka aikata abu makamancin wannan

Sai kuma ya fashe da kuka Mama ma ta saka kuka.

 Fice ka bar min gida, karka sake kwana min a gida daga yau, kuma kar a sake ba shi abincin gidana

Baba ya fada yana nuna masa kofar waje. Ni kam na yi tsaye kamar hoto ina kallon drama da ake a cikin gidanmu, na san halin Baba na dukan Mama ko fada mata magana marar dadi, domin mahaifina irin mazajen nan ne da ba su girmama matansu sun maida matansu kamar ba yi, shiyasa duk auren da yayi babu mai dadewa suke fita su bar Mama. Sai dai abun da ban saba gani ba shi ne mayar da martani na magana da Mama ta yi a yau, da kuma yunkurin da Ya Nabil yayi, duk kuma saboda ni ne. Baba ne ya fara ficewa daga gidan sannan Yaya ya nufo kofar fita sai na jinin jikina na matsa jikin gini sosai gabana na faduwa hawaye na ta zirya a fuskata. Ashe dai ban tsira ba domin yana kawowa kusa da ni ya dauke ni da mari mai bala'in zafi da radadi har sai da na taune halshena. Kuma yaja ya tsaya a gabana, jira yake na yi kuka ko na kalleshi ko kuma na furta wani abun yayi min duka. Ban yarda na daga ido ba balle na kalleshi ban bar wata kalma ta fito daga bakina ba, kuma kuma ban yunkurin yin motsi ba har ya gaji da tsayin yayi ficewarsa.

Sannan na dago kai na kalli na kalli cikin gidanmu, Mama na jiyo tana fadin.

 Kin yi nasara an kuri dan'uwanki ga dakinsa can sai ki share ki zauna, ba ke kadai na haifa ba amman ke kika saka ni ciwon kai da ciwon zuciya kullum, girmanki ya kai ace kina da wayo da hankali amman yayi miki nisa, baki bar ni da bakincikin ubanki ba, ba ki bar ni da bakincikin neman abun da zan aurar dake da abun da zamu ci ba, wani kike lalabowa kina yafa min, kullum nuna miki ake amman sai ki rufe ido bako duban daidai na gaji da halinki Noor


Na durkusa daga inda nake tsaye ina son na bata hakuri na kasa magana. Gurin da muke aje kayan wanke wanke ta nufa tana juyowa na ga wuka a hannunta, domin tabbatarwa sai ta nufi suminti ta koda wuyar sannan ta juyo ta kalleni.

 Kin ga wuka nan na koda, yau sai na kwantar da ke na yanka, na gaji da halinki yau din ba zaki kwana da rai ba...!

Yanayin da na samu kaina a lokacin da Mama da nuna ni da wukar tana furucin da ya dursaso da tashin hankalina a kusa ya wuce misali. Ashe har na gundurar da Mama haka, rashin jin magana ta ya kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login