Showing 138001 words to 141000 words out of 227321 words

Chapter 47 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1513

har take tambayar su basa samun sukuni ne tun safe suke fita kuma basa dawowa sai dare yayi sosai, na yi mata karya da cewar yanayin aikin ne yanxu a haka. Sai da ta kwashe kwana biyu a gidan sai a rana ta uku suka hadu kasancewar weekend ne, babu aiki kuma ita take girma mana abun karyawa a yanzu, na jidadin ganinta da yayi burina ya fahimci ba ni nake girkin ba a yanzu ya rika ci saboda kar yar'uwata ta zargi wani abu.

Sun gaisa cikin mutunci yayi mata ya gida ya mutanen gidan duk ta amsa da lafiyarsu kalau. A ranar ni da ita da shi duk a dinning muka yi breakfast ina ta Jefa masa hira sai ya ga dama yake amsawa, arziki na daya be fadi wata maganar marar dadi ba, har muka gama. Sai da zai tashi yake tambayar wa zai girka abinci a yau.

 Hana zata girka ai ita take girkawa a kullum yanzu

 Me za a girka?

 Me kake so?

Na tambaye shi sai ya kalleta.

 Kin iya dambu?

 Babu abincin da Hana bata iya ba, ta fi ni kokari ita bata jin wahalar aiki da girki ma

 Sai na ci na ji zan tabbatar

Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamar dai bakar magana kuma kamar a bakin gaskiyarsa kenan. Na yi murmushi

 Shikenan sai ta baka mamaki kuwa

Ya kalleta kadan ya dauke kai.

 Za mu gani

Na yi dariya ita kuma ta yi murmushi. Sai da ya bar dinning sannan take fada min next time zata zuba nata abincin ta ci a dakinta.

 Why?

 Ni dai kawai na fi jin sakewa, ki bar ni na ci a dakina ku kuma ku ci a falo

 Shikenan ba dole ai sai rai na so

Na fada mata ina dariya. Ya ci abun da ya girka da rana saboda a gida ya wuni, be yaba ba amman kuma be isa yace be yi dadi ba domin kowa ya ci dambu a ranar ya san yayi dadi. Da haka dai har ya gaji ya fara yabawa idan ta yi girki, wani lokacin har cewa yake a sake yin jiyar jiya. Sannu a hankali ya fara sakewa da ita ita ta dan sake da shi har sukan zauna su yi hira a falo. A gaba ranar yake tambayar makaranta ta fada masa ta kare amman bata cigaba gaba ba saboda tana jin Baba ba zai aminta ba.

 Indai haka ne sai mu rike ki a nan a saka ki a makaranta, ga makarantu masu kyau a nan, kuma da ganinki zaki yi kokari ba kamar Noor ba

Na kalleshi da sauri ina hade rai irin na wasa, jin yana shigar mata a yau, domin idan yana wasa da ita nuna yake na fita iya komai alhalin ya san kuma ta fi ni.

 Yau kuma?

Yayi saurin kai hannu ya taba ni.

 Ke wasa nake, ta ina zata fi Mamata kokari, kawai ina dan zuga ta ne kar ta ji babu dadi

Muka yi dariya dukanmu. After magariba ya fita titi zagayawa, ni kuma na yi dawo falon na zauna inda Hana take cin abinci.

 Noor gaskiya yanzu kam kin dace, yadda kuke rayuwa da Abdull abun ya burgeni Allah yasa hakan ya dore

 Ameen

Na amsa ina hamma, domin tun da na shiga wata na hudu nake ta yawan bachin dare, da zarar an yi magariba zan fara jin bachi sosai. Sai bayan sallah isha'i ya dawo tare da tsarabar suya. Hana ta dauko katon plate aka zube kamin kowa ya kai hannu ni har na kai baki tare da albasa da tumatir. Sai da ya ci yanka biyu sannan ya kalli Hana ya ce.

 Ci mana

Sai ta mike tsaye.

 Bari na dauko plate a saka min

 Kamar ya? Ki saka hannu mu ci a tare, hana karki zama bakauya yar zaria mana

Muka kwashe da dariya daman kowa ya san yan zaria bayin kanawa ne.

 Ni dai zan fi jindadi na ci ni kadai

 Wallahi ba zan zuba ba, idan ba zaki zo ki saka hannu mu ci tare ba sai dai ki hakura ci

Jin yayi rantsuwa cikin zafin rai ya saka ni ma na yi mata magana sai ta dawo fa zauna ta saka hannu muka fara ci a tare dukanmu, har hira ta biyo baya yana fada min gurin wani basakkwacce mutumen yabo ya siyo suyar nan. A take kuwa Hana ta saka santi.

 Har na tuna da wani kilishi da Mama ta ba ni da naje mata bankwana tace daga Sokoto aka zo da shi a local government Dange, Dangin kilishi

Muka saka dariya har sai da na sarke, ita kanta sai daga baya ta gane santi ta yi. Na jidadin yadda Abdull yake kula Hana, da farko na yi zaton wulakanci ne zai biyo bayan zuwanta gidan, sai gashi har da ni ya canja min na samu sassauci, na yadda yake mu'amala da ni daga samun cikin. Sai dai kuma a duk tsawon lokacin Abdull baya kai hannunsa balle jikinsa a nawa, zamu kwana a gado daya mu tashi amman ba zai ma bari ko a kafadarsa na kwanta ba.

Na yi masa uzurin wannan saboda na san baya son cikin, wata kila yana hora ni ne har yanzu. Ta dayan bangaren kuma bana mamakin kaurace min da yayi, musamman a yan kwanakin nan da nake yawan farkawa tsakar dare na ga baya nan amman ina jin motsin ruwa a bandaki, wata kila yana biyawa kansa b*ka*ta ne saboda ya kaurace min gaba daya.

Ranar da Hana da cika wata biyu da sati biyu a gidan ta fara min zancen komawarta gida, saboda Baba ya matsa ta dawo, kullum ya kira waya fada yake mata, bata dawo ba. Sai tace masa ban ji sauki ba, da muka kai shi makura sai ya rufe mu da masifa daga ni da har ita yana ta zaginmu a waya.

Washe gari friday kamar kowace jumma'a ya shirya cikin manya kaya na malam bahaushe yana ta kamshi, yana tsaka da saka agogo na ce.

 My Soul jiya Hana ta yi min zacen tafiya gida

Ya juyo ya kalleni.

 Tafiya gida kamar ya?

 Gida dai wai tana son ta koma saboda na fara jin sauki, kuma Baba ma ya matsa gaskiya Saboda Umma take yi ma sana'a

 Aa ba yanzu ba, ta bari sai kin haihu tukuna, idan zaki koma gida sai ku koma tare, ko ma ku yi zamanku a nan gaba daya

 Baba ba zai yarda ba, yayi ta mana fada jiya fa sosai saboda dawowarta, wai taje ta zauna

 Toh wai idan ta koma me zata masa ne?

 Babu fa kawai tana yi ma Umma talla ne ina tunanin Umma ke zugawa ta dawo, saboda sana'arta

 Ki yi magana da ita ta yi hakuri ta zauna a har sai kin isa haihuwa mana

Zan yi magana ya riga

 Bari na yi mata magana

Ya juya ya fita, sai na sauka daga kan gadon na bi bayansa. A falo muka same ta zaune tana rike da remote. Abdull ya fara mata magana sai ta nuna masa ita bata da matsalar zama, matsalar ta Baba ce sai ya aminta.

 Fada min gaskiya ko dai saurayinki ne ya matsa ki dawo

 Hana bata da saurayi for now

Na amsa sai ya wara ido yana tsokanarta.

 Taya tsaleliyar budurwa irinki, ace bata da saurayi duk kyaun nan na ki

Ta rufe ido tana jin kunya. Sai yayi murmushi ya ce.

 Zan kira shi na yi magana da shi, wata kila yana jin nauyi na ne shiyasa be taba kirana yayi min magana ba, idan ma ta kama na rika saka masa wani abu a account da za a rika bawa Umma madadin kudin tallarki zan yi haka, daga nan ma sai ya aiko mana da takardunki a sama miki makaranta ki samu ko nce ko diploma

Ni da ita muka kwalo ido waje ta taso da gudu ta rumgume tana tsalle tana murna, ta duka kasa tana masa godiya. Ni ma na masa godiyar ina jin kamar Allah ya amsa addu'a ta ne ya sauya masa yar rayuwar da ya fara na wulakanta. Domin kyautatawa yar'uwa ta jini kamar kyautata min ne. Be ce komai ba sai kallonta yake yana murmushi har ta dauki karamar wayarta ta kira Mama ta shiga dakinta tana fada mata.

 Kanwarki ta fi ki kyau Noor, ko wani friend dina da ya zo ranar ya ganta sai da yace yana da kyau

Ya fada min kai tsaye, ba tare da fargabar komai ba na yi murmushi, ai jindadi ne a yabawa dan'uwanka a gabanka.

 Tana da kyau, kuma ita tana da jiki ba kamar ba

Ya mike tsaye yana lalaba aljihunsa.

 Ba wani jiki da ita sosai ba, ta dai fiki cika ne kawai. Zan tafi sai na dawo

 Allah ya tsare, ka siyo min rake idan zaka dawo

 Toh

Na raka shi har waje sannan na dawo cikin gidan. Ina jin hana tana ihu da murna kamar zata fasa gidan dan murna, na zauna kan kujera ina murmushi yau kuma ta zama kamar ni da hauka. Kamar jira ake na zauna sai na dan abun da ke cikina yayi motsi, ban taba ji ba sai ranar na bude rigar da sauri na kalli cikin, sai ya sake yin motsi da sauri. Hawayen farinciki ya cika idona na kai hannu na shafa cikin ina jin sanyi a cikin raina.



It's 500

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660






https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0


KAREEM POV.


Dagowa yayi daga rubutun da yake a diary ya kalli Safeena dake zaune gabansa fuska a murtuke kamar an mata mutuwa.

 I thought na fada maki bana bukatar sake ganinki?

A take ta yi murmushi.

 Ta ina zaka so ganina ka samu sabuwar mace? Ka ba ni mamaki Kareem, ashe zaka iya bude zuciyarka wata ta shiga not just zuciyarka jikinka ma zaka iya hadawa da ita?

 For the very last time ko ki fita ko na saka security su fitar da ke

Wannan karon dariya ta yi.

 Ashe zaka iya wulakanta ni saboda wata banzar bazara, me ta fi kwarewa akai? Karamar yarinyar kamar Noor zata dauke maka hankali

 Karki sake zaginta, tana gidan mijinki tana zaman aure noor ba karuwa ba ce, ta san mutumcin aurenta

Ta runtse ido kadan ta tauna halshenta.

 Ni da kai ne ba mu san darajar aure ba kenan? Da rarrashi na zo gurin amman na lura gaba daya ta canja maka tunani akaina ta canja maka kwakwalwa, shikenan

Ta mike tsaye.

 Daman na zo nan ne na ji, cikin dake jikinta na mijina ne ko naka?

Kareem ya watsa mata wani mugun kallo.

 Ita fa ba fasika ba ce

 Kawai dai na tambaya ne, saboda na sani kamar yadda ita ma ta san cewa dan da na haifa yanzu naka ne

Ya kalleta without blinking try to connect his heart with his brain.

 You're stupid...

Ta yi murmushi

 Yau har na kai haka? Lallai Kareem kai ba dan goyo ba ne, cikin kanen lokaci ka canja min, gaba daya yarinyar nan ta dauke maka hankali, haka mijina yanzu ba shi da lokaci na

 Daman mijinki be taba lokacinki ba, dan haka karki zargi Noor, idan ya koma garin da yake manta ki yake yana can yana sha'aninsa kina na ki

 Muna na mu dai

Ta gyara masa tana kallon idonsa cikin bakin rai.

 Me yarinyar nan ta tare miki ne wai? Baki da magana sai na ta

Ta zagayo Inda yake yana ganin hakan ya mike tsaye.

 saboda ita ta kwace min kai, a rayuwa kai ne kadai mutumen da zaka nesanta da ni, azabar son ka ta azabtar da ni na kasa hakuri da kai, da ba haka kake ba, amman zuwan yarinyar gaba daya ka sauya min kuma ka kwashe sirrinmu gaba daya ka fada mata, har tana yakata da shi, baka jin kunyar mu'alama da mata har biyu? Bayan karyar da ka yi min akan Yusura?

 Ban taba hada shimfida da Noor ba, kuma ba zan taba ba har abada, indai har sai ta kazantacciyar hanya zan samu Noor, to ina rokon Allah ya hana min ita har abada, kuma aure take a yanzu bana fatan ya mutu, fatana ta samu kwanciyar hankali a ko'ina zata kasancewa?

Ta dan matsa baya.

 Baka taba kaiwa jikinta ba? To me ya dauke hankalinka ka fada mata sirrinmu? Ba na mu'alama kadai ba wai har na haihuwar da muka yi?

 What? You're not serious? Taya za fada mata abun da ba ayi ba?

Ta matso kusa da shi tana kallon wayar idonsa.

 Miye ba a ayi ba a ciki? Haihuwa ko alaka?

 Na ji na fada mata alaka, amman yaushe muka haihuwa balle na fada mata?

 Yanzu kuma kokarin wasa kake da hankalina?

 Wane irin wasa da hankali? Karya kika mata cewar mun haihu ne? Idan ma kin yi haka to kin yi akan aurenki ne kina kashe kanki ne, domin Noor baki ba linzami ce

Ta kalli gefe sannan ta sake kallonsa.

 Taya zan fada mata sirrina? Kai ka fada mata, shiyasa da ta zo gidana ta fada min magana son ranta

Ya fisgota ya rike cinyar hannunta.

 Stop talking about Noor, yaushe muk haihu? Are you out of your mind?

Ta fisge hannunta.

 Ai na fada maka tun ina da ciki ko? A asibitin nan aka karbi haihuwa danka, kuma Wallahi jininka ne! Au kenan baka yarda ba da na fada maka? Ka dauka karya nake?

Kareem ya daka mata tsawa.

 Yaushe rabon da na yi wani abu da ke? Akwai dai abun da kike kokarin yi Safeena

 Babu abun da nake kokarin yi, ni ba zan iya cutar da kai ba, amman an da na haifa yanzu Wallahi naka ne, last haduwar da muka yi na samu cikin, sati biyu na kara akan lokacin da nake period a satin Abdull ya dawo, yana barin garin nan naje aka min test aka ce ina da ciki dan sati uku, yaron da na haifa yanzu idan aka kalleshi kallon kurilla za a san cewar danka ne, idan baka yarda zan kawo shi ka gwada jininsa

He lost his temper when he was saying.

 Baki da hankali Safeena? Taya zaki aje ciki i mean taya zaki haihu? Dan Haram ne Safeena kuma ki dauka ki kawai mijinki? Ina da aure da yaya safeena kina da aure da yaya taya zaki yi haka?

Ya fadi zaune yana rufe bakinsa.

 I don't believe you?

 Na kawo maka yaron ka auna?

Ya kalleta.

 Idan gaskiya me ye hujjarki na aikata haka?

Ta risina a gabansa.

 So so ne, Kareem ina kaunarka ba zan iya zubarwa ba, ko da ba zan same ka ba zan so aje jininka, kuma waya sani ko nan gaba mu kasance ma'aurata

 Ina zamu kai zunubin Safeena? Ga na zina ga na daukar alhaki? Mu dauki alhakin yaron mu dauki na mijinki? Why how? Why why why Safeena why?

 Ni ma bayan na haihu na yi tunanin be kamata mu yi haka ba, amman komai ai ya riga da ya faru, kuma ba a kanmu farau ba, suna nan da yawa yaran da ba na iyayensu ba

Ya kalleta babu alamar wasa ya ce.

 Je ki dauko yaron

Ta mike tsaye ta dauki jakarta ta fice daga office din. Fuskarsa ya shafa yana jin gumi na karyo masa, daman da ta fada masa tana dauke da cikinsa gaskiya ta fada? Ya dauka tana masa wasa ne ko barazana shiyasa ta dawo asibitin. Kuma tun bayan rabuwa da ita be sake bincikarta komai ba saboda yana tunanin ya yanke alaka da ita.
Ya mike tsaye yana jin kamar baya iya numfashi.

 I can't believe this ba gaskiya ba ne, Kareem

Ya fadawa kansa yana nufar windows din ya rika gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Juyowa yayi da karfi ya dauki keys dinsa ya fice daga restaurant din gaba daya. Gurin aikinsa ya koma, ya kira waya ya sanar mata inda yake, a can Safeena ta kai masa yaron mai cike da koshin lafiya mai jiki da haske gwanin sha'awa. Tun da Safeena ta aje yaron yana kallonsa gabansa na faduwa domin ya ga kamaninsa a fuskar yaron, ta dayan gefen kuma yana kama da Safeena.
Be ce mata komai ya fita office din, babu jiwa ya dawo sanye da safar hannu ya debi jinin yaron a syringe.

 Idan har abun da kika fada ya tabbata Safeena kin cutar da ni, kin cutar da kanki kuma kin cutar da yaron nan

Ta kalli yadda yake kuka bayan Kareem ya dauki jininsa ta ce.

 Abu ne da zamu iya ajewa, mijina be sani ba, matarka bata sani ba, to mu bar shi a boye mana, sirrinmu ne ai

Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din. Tun tana jiran dawowarsa har ta gaji ta tashi ta fita. Be bar asibitin ba sai da ya debi nashi ya hada ya kai laboratory suka auna masa. He wait they sai da aka hada results aka ba shi. Tsoron abun da zai gani ya saka shi kasa duba takardar har ya shiga motarsa.

Ta zauna a motar na tsawon awa daya yana tunanin yadda rayuwa zata kasance masa a yanzu, idan har ta tabbata dansa ne, idan a gurin wasu ba abun kunya ba ne shi a gurinsa abun kunya ne. Daker ya ja motar ya fice daga asibitin, be yi nisa ba ya faka gefe titi ya kai hannu ya dauki result din ya duba. Booom..... Zuciyarsa ta buga da karfi, gaskiya Safeena ta fada, dansa ne jininsa ne.

 Why Safeena Why?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login