Showing 222001 words to 225000 words out of 227321 words

Chapter 75 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1548

rumgume ni a tsayen da yake yana shafa kaina.

 Addu'a suke da bukata a yanzu, ba kukanki ba, kuma yanzu komai ya wuce I'm right here My Love

Na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya. Sai ya duko yana taba fuskata.

 Haba yan matana, haba uwargidan Kareem kuma amarya, daga ke babu kari, haba yar tilon Mama, kanwar Nabil, duk ke kadai ehen ga ki kuma yar gatan mijinta, mai son ganin bacin ran Kareem ya taba Noor, haba ta Kareem bada kanki a asare ki je ki cewa Mama ya fadi, haba autar mata....

Na kalleshi ina murmushi, duk wani abun da Kareem zai yi ya kwatar min da hankali ya san shi kuma yayi kuma yayi nasara domin mun ci abincin da ya girka min cikin farinciki da kaunar juna. Ya wancin aikin gidan shi yake yi ya dauke min nauyi abubuwa da yawa tun da muka yi auren balle kuma a yanzu da nake dauke da babynsa.

Wannan cikin ya zo a dabam ba kamar cikina na farko ba ina fama da yawan rigima abun da be kamata na damu da shi na kan damu, abun da babu ruwana ma sai na shiga, na tabbatar da a gidan haya muke wata kila da yanzu an koramu ni da mijina. Cikina na wata tara mun fito daga family house dinsu Kareem na rika masa magiyar ya bar ni na ga Safeena idan dai tana garin nan.

Ba dan ya so ba ya tafi da ni gidansu Abdull kuma gidansu Safeena a yanzu, kamin a bude masa gate yake fadar ba lallai a bar mu mu ganta ba, ba lallai idan ta san mu ne ta yarda ta fito ba. Ni mna na raya wannan a zuciyata sai dai ta inda muka taki sa'a muna shiga bangaren uwargidan wanda a nan ne ake rikon Safeena sai muka same ta harabar gidan zaune a well-chair tana kallon motarmu.

Gabana ya fadi na ji kamar bana bukatar ganinta kamar yadda Kareem ya fada da farko, sai dai kuma mun riga da mun zo, har Kareem ya bude min mota.

 Zan tsaya a nan, karki dade

Ya jingina da motar fuskarsa na kallon gate din gidan. Ni kuma na taka ta tulelen cikina na karasa kusa da ita na tsaya ina kallonta tana kallona, can kuma sai ta yi murmushi.

 Na san kin yi nasara Noor baki bukatar nuna min, kin raba ni da wanda nake kauna, kin raba ni da aurena, kin juyar da mutumen da yake tsananin kaunata zuwa makiyi na, yanzu miye dalilin zuwanki? Rayuwata kike nema ko me? Ko kin zo nan ne, saboda ki fada min kin yi nasara a rayuwa? Kin zo ne saboda ki fada min kin auri Kareem har kin samu ciki da shi?

Na girgiza mata kai ina kallonta ita din abar tausayi ce a yanzu me yasa bata tausayin kanta? Kusan rabin fuskarta zuwa habarta na bangaren hagu ya bar mata tabon wuta alamar kone da aka yi aka warke.

 Ban zo nan saboda na nuna miki na yi nasara ba, zan fada miki na yi nasara ne idan muka shiga aljanna ni da Kareem. Na zo nan ne saboda na tunatar da ke abun da kika manta, mutum baya iya canja abun da Allah ya kaddara zai faru ga bawansa, dabara da wayo basa sauya kaddara, kuma ba zaka saka wani a bakinciki kai kuma ka yi tsammanin zaka dauwama a farinciki ba, ta kika kone nawa iyayen ke ina naki iyayen suke a yanzu? Da kika so raba ni da rayuwa ke ya taki rayuwar take a yanzu? Annabi Muhammad S A W ya fada, imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan'uwansa abun da ya so ga kansa, ina imaninki ya tafi Safeena? Abun da kika yi nufi da ni, za ki so ya faru da ke?

Ta dauke kai tana hawaye.

 Ni na yi nufin bawa zuciyata abun da take so ne kawai, kamar yadda kika yi jarabawa ta ce son Kareem, amman kin raba ni da shi, go home and celebrate

Na juya na kalli Kareem dake tsaye fuskarsa tana wani gafen baya kallon gurin da muke tsaye, sannan na juyo na kalleta.

 Kamin mu yi aure, ba zan iya cewa ina son Kareem ba, ko da ina son shi to ni ban sani ba, amman da kaddara ta yi nufin hadamu sai abubuwa suka faru, daga karshe kuma sai ya zama abokin rayuwata. Amman Safeena namiji be yi tsadar da za a kashe rai saboda shi ba, namiji be yi tsadar da za a haihu ba tare da aure da shi ba. Kin yi sikar mutuwar mahaifin da be miki komai ba, da yar'uwar dake cike da buruka, Allah ya isa ban yafe miki ba...

Na juya na nufi motar Kareem ina kuka, sai na ji ta kira sunana.

 Noor... Ki yi hakuri dan Allah

Na juyo na kalleta sai ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Na juya na cigaba da tafiya ba tare da na ce mata komai ba. Ina isa Kareem ya rumgume ni.

 Na fada miki baki bukatar zuwa, ba ki ji ba

Ya bude min mota na shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga, ya juya motar muka fice daga gidan. Hannuna daya ya rike yana tukin yana kallona har muka isa gida

 Wani abu ta fada miki ne?

Na girgiza masa kai, ya fita motar ya bude min na fito ya rikani muka shiga falon ya zaunar da ni a kujera, sannan ya shiga kitchen ya dauko min ruwa kaina ya rika sai ba ni ruwan a baki sai na saka hannu na karba na aje na mike tsaye na bude masa hannayena.

 Ina son ka Kareem

Ya rumgume yana shafa bayana.

 Ni na dade da mutuwa a sonki Beb Allah ya sauke ki lafiya

 Ameen

Addu'ar da yake min kenan a kullum, ni ma nake yi ma kaina mahaifita ma take min. Hakan kuma ya taimaka min sosai haihuwar ta zo min da sauki, na haihu ba tare da na sha wahala sosai kamar haihuwa ta farko na haihu daga ni sai likitana a gida. Shi ya wanke ni ya gyara min jiki ya wanke jariri ya kwantar da ni sannan ya kira iyaye ya sanar da su.

Jaririn ya dauko yayi masa huduba ya rada masa sunan mahaifina sannan ya saka min shi a hannuna na fara ba shi nono da be da ruwa a lokacin domin ruwan Nono be kawo da wuri ba. Ina rumgume da ana mijina yana rumgume yana min sannu da kissing. Na kalleshi hawaye fal a ido na ce.

 Wannan yana da rai

Ya sunbance ni.

 Haka zaki yi ta haifo mana masu rai da yardar Allah har sai kin gaji

Ya sumbanci yaron ya karbe shi daga hannuna yana kallona cike da kauna, bakinsa ya miko min muka sunbanci juna be cire ba har sai da ya ji alamar shigowar mutane a gidan. Kan kace kwabo yan'uwansa da nawa sun suka gidan kowa sai murna yake. Yaransa da sai daukin babyn suke kamar za su cinye shi.

Duk yadda Mama ta so a bar ni na koma gida ganin kamar haihuwar fari ce Kareem be yarda ba, yace kamin yanzu na taba haihu Mama ta bar masa matarsa kawai shi dai zai fi kwanciyar hankali idan ina gidan. A yanzu ne na san yadda uwa take ji idan mace ta haihuwa hidimar jego da jariri sai yanzu nake samu domin wacan haihuwa ta zo ne ba a yadda aka yi zato ba.

Wannan kuma ta zo a lokacin da ya dace cikin so da kaunar miji ga yan'uwa miji da yaya masu son new babyna da muka yi masa alkunya da RAYID.
An ci an sha an wadata da komai a ranar sunan RAYID, kawayena har na nesa sai da suka zo, a ranar sunan ne kawata Zainab dake da yara biyu a yanzu take fada min Zafeer ya rabu da matarsa, shekara daya bayan mun rabu, na sha mamaki domin ban dauka zai iya sakinta ba.

 Amman ya saketa Zainab?

Na tambaya ina juyar da fuskata mai min kwalliya tana shafa min jan baki.

 Hmmm ta dai sake shi, ke kina ganin zai iya sakinta ne? Ance fa tun da kika fita babu zaman lafiya baya jindadinta abububuwa take masa na rashin jindadi, kuma kamfanin mahaifinta ma da aka saka shi suka cire shi, daman ni na san za a cire shi ai, saboda za su yi tunanin be da amana, indai har zai iya cin amanarta ya aureki ba tare da ta sani ba, to zai iya yin komai ma

 Hmm ai maza haka suke da cin amana

Mai mini kwalliya ta fada ni kam sai na yi karaf na ce.

 Wasu dai ban da nawa

Sai duk suka saka dariya Zainab ta kai min dudu a baya.

 Wato Noor ban da Kareem

 Aa ban da shi gaskiya, Kareem dan albarka ne rabin rayuwata, bawan Allah mai son farincikin matarsa

Mun yi wunin sunan cikin farinciki an yi hotuna???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? a gurin da Kareem ya saka ayi decoration da sunan RAYID, na yi ta zuba zinarina ana min hotuna cikin shiga kala kala. Wani kuma aka yi mana tare da Kareem wani tare da yaransa as family picture.

Sati daya da yin taron sunan ina zaune falo dattijiwar dake yi ma baby wanka ta kawo min kunun ganye bayan ta gama gyara min yarona, na karba cup din ina kallon Kareem dake rumgume da ansa yana daukata hoto a waya.

 Ya aka yi? Tun dazun kike kallona karki cinye ni

Na yi murmushi da ya bayyana hakora na, tsohuwar ma ta yi dariya, na shanye kunun na mika mata kofi ta nufi kitchen sai na amsa masa murya kasa kasa.

 Cinye ka zan yi

Be ce min komai ba sai ta da aje cup din ta fito ta yi mana sallama ta fice, sannan ya taso daga inda yake zaune ya dawo kusa da ni yana saka min fuskarsa a cikina yana cizon cikin.

 Aya gani cinye

Na buge masa kai na ja masa kunne ina dariya.

 Idan na fara rama cizo da kwantar da kake min a gidan nan Hubby ba zaka iya da ni ba

Ya aje babyn ya fara kokawar cire min riga.

 Bari na cije ki inda zaki fi jindadin ramawa

 Dan Allah ka bari Haba Kareem Haba Kareem

Ya zare ido.

 Haba Kareem? Wato Kareem ko?

 Mantawa na yi Wallahi haba Hubby haba haba.... Hahahahahahah

Dariya ta ci karfina saboda cakulkulin da yake min, ya riko ni muka fada kan carpet din dake kasa, ni da shi muna dariya.




*** *** ***

Married is sweet when you meet the right person, sai ya mantar da kai damuwa da duk wani hali da ka taba kasancewar a rayuwa. Na yarda da wani abu a rayuwa, ba zaka cutar da wani ba, kuma ka yi tsammanin rayuwa zata tafi maka daidai, ba zaka zalinci wani kuma ka ce zaka ga daidai ba a rayuwarka.

Kuma na yarda dukan tsanani yana tare da sauki, na yarda riba mai hakuri tana da yawa, na yarda addu'a maganin dukan wata musiba ce ta rayuwa, haka ma na yarda dukan wanda Allah ke yi ma fada baya fada. Idan kuma Allah yace kai ne to kai be babu makawa babu wanda ya isa ya sauya wannan? Hausawa suka ce matar mutum kabarinsa, shi ma yarda, domin duk mazajen da nake aure ban zauna ba sai a gurin Kareem, ba su iya rikon ba, sai shi, zuciya bata natsu ba sai da ta kai ga wanda aka hallicceta domin shi.

Aure yayi albarka domin shuka ta yi yabanya, kan na maida shekara bakwai a gidan mijina na sauke masa yara biyu mata bayan RAYID, sai na hada su da nasa yaran na rike kamar yayana. Ni ma dai ashe zan girma, zan yi hankali zan zama abar misali a gurin wasu, ashe dai ni ma zan yi hankali na zama uwa, sai dai na kasa girma a gurin mijina a kullum yarinya yake ganina, ni kuwa na yi ta yarintata musamman akan shimfidarsa.

Na tashi daga TA KI ZAMAN AURE zuwa tana dakin mijinta yaranta, daman mutane ne ba su fahimci kaddara ba, idan mace ta fito sai ayi gulma suna manta su ma iyayen matan ne, wasu kuma iyayen basa fahimta kamar Mama kamin ta sauya, wani kyaun kuma an baro shi ne tun gurin haihuwa, kamar dai yadda iyeye suka ta yi min baki da farko, ko da yake kaddarar kowa dabam, saboda wata ta dace a farin farko ko na biyu, ba shi yake nufi wata zata dace ba, kuma saboda wata bata dace ba ba shi yake nufin ke ba zaki dace ba. Rayuwar aure akwai dadi, akwai daci, akwai farinciki wani lokacin kuma akan samu tsabani da bakinciki, manufar abun dai aure ibada ce, ribar tana a gurin Allah ne.

Babu macen da zata kashe aurenta saboda tana jindadin zaman gidansu, babu kuma macen da zata ki zaman auren saboda dadin zaman gidansu, mace bata sakin kanta mace yar sunna bata gudun sunna. Kar wahalar gidan auren wata ya saka ki cire rai daga samun mijin na gari, kar rayuwar auren wata ta burgeki ta saka ki dogon buri, just pray and hope for the best.


Kaddara mai sauya labari, a yanzu an bude min wani sabon shafi na farinciki ni da mahaifiyata a gidan nata sabon mijina. Dan'uwana ma a yanzu baya kasar a makarantar da yayi karatu suka dauke shi karantarwa bayan yayi masters, suka ba shi muhalli sai ya dauki amaryarsa Mariya da dansa aya suka koma can sai idan sun kawo mana ziyara ko kuma mu din mun tafi.




KAREEM POV.

 Okay Daddy, daman dai saboda na ga yara ne, amman tun da ka saka baki zan barta ta tafi

 Hakan ya fi

Ya sauke wayar sannan ya bude motar ya fita, ya shiga cikin gidan da babu kowa a yau sai matarsa yaran duka suna family house gurin Hajiya Hassana. Kamshi turare ne ya fara yi masa lale marhabun a lokacin da ya saka kafarsa a falon. Noor dake saukowa ta zo da gudu ta tarbe shi sai ya rumgume ta ya cije hancinta.

 Saboda na ce ba zaki je ba kika hada ni da Daddy ko?

Ta sake shi ta fara rawa tana rauyasa.

 Idan ba haka na yi maka ba ba zaka bar ni na tafi ba

Murmushi yayi ya rikota ta dawo jikinsa cike da so da kauna yake kallonta.

 Bana son ki yi nisa da ni ne ko kadan, kin riga kin shanye min zuciya ko aiki naje Allah Allah nake na dawo na ga fuskar yar budurwar nan tawa

Ta yi murmushi, shi ma murmushin yake yana kallonta kamar zai cinyeta, yana son ta wannan abu ne da kowa ya sani, yana son farincikinta wannan kuma wani aiki ne da ya rataya a wuyansa. A cikin abubuwan da yayi mata alkawari akwai mutuntawa, akwai farinciki, akwai riritawa, akwai gata, akwai soyayya? Kusan ya cika kowane amman har yanzu zuciyarsa bata gamsar da shi Noor ta wadatu da farincikinsa ba.

A kullum yana neman hanyar da zai faranta mata yake. Domin shi na shi farincikin ya cika ya samu matar da yake so yake kaunar matar dake mantar da shi damuwa matar idan ya kalleta sai farinciki da nishadi su kama shi, matar da kamshinta ke fitinarshi, matar da zuciyarsa ke marari, gashi ta haifa masa kyawawan yara, kuma ta hada da na shi ta rike kamar nata, shi kam yanzu me ya rage masa? Sai yi ma Allah godiya.

 Mu je ki raka ni

Ya fada yana jan lebenta.

 Ina?

Ta tambaya a shagwabe, domin mace shagwababbiya ce a gurin mijinta no matter how old she's balle kuma ita da take matashiyarta.

 Gurin yaran Hafiz zan kai musu na su kayan ne

Ta sunbance shi sannan ta sake shi ta shiga ciki ta dauko mayafinta suka fita tare. Har gobe har jibi idan za su fita ko suka dawo shi yake bude mata mota ta fita ko ta shiga, yaransa har sun koya idan za a fita da ita su yi ta rigen rigen bude mata front seat. Suna tafe suna hira har suka isa gidansu Aisha sai da yayi sallama aka sanar mata sannan ya shiga ciki ya gaisa da ita Noor ma gaisa da ita Aisha na amsa mata sama sama, Kareem ya saka aka shigar musu da abinci da kayan tea da kayan kwadayi irin na yara, ya bawa yaran kudi suna ta murna daman ya bawa kansa a duk lokacin da yayi siyayar gidansa zai yi na yaran abokinsa Hafiz.

Daga gidan suka wuce gurin Iyayen Hafiz su ma yayi musu alheri ya ba su na su siyayyar suna ta saka masa albarka da Noor har ya fito. A mota take masa ta yin tafiya kauyen tare da shi.

 Aa ki tafi yanzu ke kadai ni ki bar ni da yarana idan mun dawo Ummara sai mu tafi da su can

 Ni na tafi kauye ku, ku tafi ummara kenan?

 Eh mana ba kin nace sai kin tafi kauye ba?

 Amman ni ma ai ina son na tafi

 Last year baki tafi ba?

 Ina son na sake zuwa

Ta turo baki gaba, hannunsa ya kai ya ja bakin.

 Ba za a da ke ba, ni dai zan tafi da yarana mu yi addu'a sabon restaurants din da zamu bude a Kaduna da Abuja da Sokoto da Lagos ya zama babban kuma ya karbu kamar na Kano

 Idan babu ni addu'ar ba zata karbu ba

Ya saka dariya.

 Tashi zaki yi ki rike ta?

 Tsab kuwa yadda na rike maka zuciya ba

Yayi dariya sosai ya riko hannunta.

 Ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login