Showing 15001 words to 18000 words out of 227321 words

Chapter 6 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1501

na dire saboda muryar lallai wannan mutumen mai saukin kaine sosai mai jin maganar mata.

 Mu je mota ka karbo mata sako, Noor Allah ya tsare gaba

Ya karasa yana kallona.

 Ameen

Na amsa sannan na shige cikin gida ina jin kaina kamar wata sarauniya a yau.
https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx


Assalamu Alaikum...
Ina talata muku
KHADEEJA CANDY STORE >?p?=?L?
Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo.

''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -5


KAREEM POV.

After ya mika masa tsarabar Noor ya bude motar ya shiga sai Nabil ya rage tsawonsa yana bashi hakuri.

 Ranka ya dade dan Allah ka yi hakuri, Wallahi ba zan sake bijirewa umarninka ba, kuma idan wani abun marar dadi Noor ta yi maka da ya saka ya kanye wannan hukuncin dan Allah ka yi hakuri

Kareem ya kirga 10k ya mike masa.

 Noor bata min komai ba, kuma a yanzu ina jin hakan da na yi yayi daidai domin be kamata na baka umarni ka saba ba, ba wai na koreka ba ne noo zaka zauna ne a gida har Monday

 Toh ranka ya dade

Har Kareem yaja gambo zai rufe motar sai kuma ya kalli Nabil

 Shekarar kanwarka nawa?

 Wannan watan zata yi 15

 Fresh one, shiyasa kanta be tsaya ba, tashen balaga take

Ya fada a ransa a zahiri kuma sai ya sake tambayar Nabil.

 Kai kuma fa?

 19 ranka ya dade

 Okay, amman tana karatu?

 Bata karatu gaskiya, bata son makaranta

 Why?

 Haka nan kawai bata son karatun, kanwarta da kusan suke tawaye tana karatu sosai amman ita bata son makaranta

 Kuma aka zuba mata ido? Baku tsoron future dinta ya lalace?

 Toh ya za'ayi ranka ya dade ai ka ga yadda take, Baba ne kawai zai iya da ita shi kuma karatun ba damuwarsa yayi ba

 Allah ya kyauta

 Ameen mun gode

Ya rufe motar ya juya, ya fice daga unguwar. Ba gida ya nufa kai tsaye ba restaurant dinsa ya sake komawa a gurin yayi sallah La'asar yana fitowa Masallacin abokinsa Hafiz na fakawa kusa da motarsa, Kareem ya karasa gurinsa ya mika masa hannu suka gaisa.

 Dazun na ga motarka, na so mu yi magana amman ban san fitarka ba

Kareem yayi murmushi tunawa da Noor.

 Wata bakuwa na yi mai kiriniya ita ta saka ni zuwa nan kuma na kaita gida

 Bakuwa?

Hafiz ya tambaya domin be taba jin abokinsa yayi zancen wata mace ba bayan Safeena da matarsa, ko siblings dinsa iyakarsa da su gaisuwa, sai kuma fada idan sun yi ba daidai ba.

 Yeah wani yaro na ne, da yake aiki nan ya zo duba ni sai ya zo da kanwarsa to kanwarsa ce rikitacciya

Yana maganar yana murmushi maganarsa da ita yake tunawa a lokacin da take fada masa abincin restaurant dinsa yayi tsada.

 Kuma ka kawo ta nan ka kaita gida? Ko dai...

Kareem yayi hanzarin katse shi yana girgiza kai

 Noo kai yarinya ce irin fresh yaran nan yanzu take girma, kuma ni bayan Safeena babu kowa a raina

Hafiz yaja tsaki jin ya ambaci sunan matar da ya fi tsana a duniya fiye da kowa, matar da ta sauya dabi'u da mu'amalar amininsa zuwa wani dabam da ba shi ba.

 Ya jikinka?

 Alhamdullahi na ji sauki sosai

 Amman baka shiga aiki ba yau, domin na shiga ban same ka ba, na tambaya aka ce baka shigo ba

 Na shiga da yamman nan na kai Noor na mata treatment

 Wace Noor me ya faru?

 Yarinyar da nake baka labari yanzu ita ce Noor, Yusura ce ta buga mata abu akai kan ya fashe jini ya zuba shi ne a kaita asibiti

Da mamaki Hafiz yake kallon abokin nasa.

 Yusura ta fasa mata kai kace fa? How?

Kareem ya dan tabe baki yana jingina da motar Hafiz.

 Yusura tace wai ta fada mata magana ne, amman ita yarinyar tace Yusura kishinta take saboda ta ga kyakkyawar budurwa

Yana maganar yana dariya, Hafiz ma yayi dariya.

 And she got lucky ka kaita asibiti

 Daman wa zai kaita asibiti ba ni ba, matata fa ta fasa mata kai, a asibitin ma tambayoyi take min har da na banza wai ance ina zubar da ciki

Hafiz ya tintsire da dariya.

 Kirikiri?

 Wallahi a gida ma haka ta gama ba ni labari wai restaurant dina yana da tsadar abinci, amman bata san ni ne mai restaurant din ba sai daga baya

 Zan so ganin yarinyar nan

 You better not babu ruwanta take zata fara maka maganar da ta zo bakinta, kuma ka san kai ba irina ba ne zaka iya fusata, amman labarin cikin nan ya ba ni mamaki

 Kareem kenan, ka yi kaurin suna kowa ya san kwarewarka akan iya aiki da daukar komai babu wasa, so dole makiya za su nemi hanyar da za su yada wani abun kyama game da kai

 Toh ai ni taimako kawai nake, bana cirewa sai wanda na san akwai matsala, amman masu cikin shige ni bana zubarwa

 Duk yadda zaka yi ba zaka gujewa mutane ba, wata ma cikin banza zata dauko ta zo tace maka mai matsala ne ka burke mata ta zubar

 Aa sai na yi bincike nake yi ai, ni ba shashasha ba ne irin Noor

Hafiz da sai a lokacin ya rufe motarsa ya kalli Kareem.

 Muje ka bani labarin yarinyar nan there is something special about her...

Kareem ya jera da abokinsa suna tafiya ya zuba hannayensa duka biyu aljihu. Har suka isa office labarin abun da Noor ta yi masa yake ma Hafiz, and Hafiz was so excited domin ya dade yana jiran irin wannan labarin daga gurin abokinsa.

 Amman be dace mahaifi ya furtawa yarsa haka ba, ko da daga ita sai shi ne balle kuma har a gaban wani

Hafiz ya fada bayan ya zauna. Kareem ya daga kafadunsa.

 Ni ma shi na gani, irin haka ke sa yaro ya lalace, ni ma ban jidadi ba balle kuma ita, amman tace min ita ai ta saba, duk sai ta ba ni tausayi Wallahi, gata karamar yarinya she's just 14 no 15 this month

 Kasan fa wasu iyayen idan talauci ya halbo su ido rufewa yake

 Baka da kirki Barrister amman fa akwai alamar haka, domin daga ganin gidan nan da unguwar ma ka san suna fama da talauci ko'ina kwata

Ya fada yana ciro wayarsa dake ringing ya duba, ganin sunan Safeena ya saka shi dan shakkun dagawa a gaban Hafiz domin ya san ba karamin abu ba ne su yi fada saboda kiran, but babu yadda zai yi dole ya daga domin ba zai tana iya rejecting kiran Safeena ba kuma ba zai ga kiranta ya kasa dagawa ba.

 Hello...

 Kareem guess what?

Safeena ta fada daga dayan bangaren.

 Ina guest's House dinka

 Safeena i thought mun yi magana idan mijinki yana nan ba zamu ga juna ba? Dazun nan ma ba mun yi maganar nan ba?

 Na kasa rike kaina ne, kuma i have surprised for you shiyasa na zo, kawai magana za mu yi

 Shi ke nan gani nan zuwa

Ya amsa da kamar yanayin damuwa, sannan ya sauke wayar.

 Yanzu baka ko jin kunya barina zaka yi a nan ka tafi ka gurinta

Cewar Hafiz cike da takaici. Kareem yayi murmushi.

 Kamar baka san tsakanina da Safeena ba? Tana son ganina and i can't say No

 Ka ji tsoron Allah Kareem, kana mu'alama da matar aure macen har da yayanta hakkin ai sai ya maka yawa

 Shiyasa na ce idan mijinta yana gari ba zamu rika ganin juna ba

 Yanzu idan wani ya kwanta da matarka ya zaka ji? Amman kai kana yi ma matar wani?

 If wani ya aikata matata haka, kashe shi zan yi, ba zan iya jurar komai ba, ko da kuwa Yusura ce da bana so balle ace wadda nake so

 Amman kake aikatawa matar wani? Idan kuka mutum a wannan halin kace me? Waya sani ma ko ita ma tana tare da Ex dinta

 Ex dinta yana can kasar waje, ba dan an cilasta mata aurena ba, da yanzu tana can tare da shi suna rayuwa ni ma da yanzu da Safeena nake rayuwa, amman ya zamu yi kaddarar mu ta zo a haka

 Ka yi sabon Allah kace kaddararka ce a haka? Kareem ka raina wayon mutane Wallahi

Kareem ya busar da iskar bakinsa.

 Wai da duk wannan abun why not ta kashe auren ka aureta?

Kareem ya girgiza kai da sauri saying no to Hafiz question.

 Har abada, ba zan iya aurenta ba, idan ta fito gidan mijinta wa zai rike mata yayanta? Ni dai yadda nake da kishin nan kasan ba zan iya rike yayan wani ba, kuma...

Yayi shiru.

 Kuma me? Ba zaka aureta ba saboda kana jin ba da kai kadai take tare ba?

 Da ni kadai take tare a yanzu na sani, amman daga lokacin da zan aureta ba ni da wannan tabbacin, what after na aureta ta koma tana mu'amala da tsohon mijinta kuma? Ko wani? Daga lokacin da na fara kaiwa jikin Safeena sai aka tsinke igiyar aminci a tsakanina da ita, for now na san ni kadai ne, amman idan na aureta ba zan samu aminci ba

 Kenan haka zamu yi ta zama har bada?

 Not har a bada, ina fatar canjin

 A hakan?

Hafiz ya tambaya yana masa wani kallo. Kareem yayi dariya grabbing his phone ya mike tsaye ya fice daga office din.

 Allah ka tsare mana imaninmu ka tsare mu da auren mata irin Safeena

Ya fada yana juyawa ya bi kofar office din da kallo. Kareem na shiga motarsa ya dauki hanyar gidansa da ya gina da kansa saboda Safeena da kuma irin tsarin da take so, sai dai kaddarar rayuwa bata ba su damar zama ma'aurata ba, sai suka zama ma'aikatan aikata zunubi. Yana yin horn mai gadi ya bude masa gate sai ya shiga ya faka motarsa, yana ganin motarta ya tabbatar tana gidan kamar yadda ta fada masa. Ya bude motar ya fito ya nufi kofar falon ya saka key ya murda ta bude ya shiga. Yanayin arba da ita sai murmushi ya baibaiye fuskarsa ta taso da sauri tana kamshi turare mai karfi ta rumgume shi.

 I miss you so much

Ta fada tana shafa fuskarsa, bakinta ya sumbanta ya rike bayanta.

 I miss you too, kwana biyun nan da baki kusa kamar na yi hauka

Ta yi dariyar jindadi.

 Ba ga matarka ba?

 Matata ai kin san once in a month ne, amman ke kullum ne, kin san yadda nake sonki ai

Ta sake yin murmushi ya kai bakinsa cikin nata, sun dauki lokaci a haka kamin ya cire bakinsa.

 Yau kam ba zamu wuce nan ba, Safeena ina son ki rika jin maganata, na fada miki idan mijinki yana nan ba zamu rika haduwa ba

 Na sani, yanzu kawai na zo maka da abun mamaki ne kuma abun Farinciki

 Surprised din me ne?

Ya tambaya yana kokarin raba jikinsa da nata, sai ta yi baya ta nufi jakarta ta bude ta dauko abu sannan ta boye a bayanta.

 Rufe idonka

Ya rufe idon yana murmushi har sai da ya ji matsowarta kusa da shi ta ce ya bude sannan ya bude. Yana yin arba da surprised din sai murmushin dake fuskarsa ya gushe, mamaki ya koma masa tashin hankali.

 Innalilillahi Wa'inna Ilaihirraji'un

Ya furta har sau biyu sannan ya karbi PT scrip din yana dubawa.

 Me hakan yake nufi?

 Ciki mana Kareem, kai fa likita ne

Ta fada cikin tsananin farinciki, da tsammanin shi ma farincikin zai yi. A take ya ji gaba daya tsigar jikinsa tana tashi.

 Cikin waye Safeena?

 Cikin Kareem, mijina shekaranjiya ya dawo ai ba za ace na yi cikin tsakanin jiya zuwa yau ba, kuma tun da liyin ya nuna sosai that's mean cikin ya dade, kasan for the whole 3 months muna tare, I'm happy Kareem zan haifi anka...

Ta kai hannunsa ta taba fuskarsa tana murmushin jindadi sai ya buge mata hannaye ya fadi zaune ya shafa kansa ya mike tsaye ya sake komawa ya zauna.

 Me ya faru? Wannan abun Farinciki ne a tsakaninmu Kareem

Ta nufeshi ta rika shi sai ya kauce daga rikon.

 Baki da hankali Safeena baki da hankali, miye abun farinciki a nan? Kina da aure ki yi ciki da wani a waje kuma ki ce abun farinciki?

 Saboda naka ne Kareem, duka yara uku da na haifa na Abdull be, ina son na haihu da kai, ka san yadda nake sonka...

Ya aje PT din trying to calm himself down.

 Na sani, amman ban da ciki, wannan kuma mun wuce gona da iri ba zamu iya rumgumar abun da ya biyo baya ba

Ta kalli cikin idonsa hawaye na cika idonta.

 Me kake nufi?

 Zamu zubar Safeena ba zamu taba haihuwa a tsakaninmu ba har abada, babu wannan

Ya matsa zai taba ta sai ta matsa baya tana kallonsa.

 Me kake nufi kenan?

 Zubar zamu yi, ba zam iya wannan ba Safeena ba mu wuce gona da iri ba

 Na yi mamakin jin wannan kalamar daga bakinka, ban yi zaton haka ba, ni ina son cikin idan kai baka so ni ban daina kaunarka

 Ni ma ban daina kaunarki ba, amman ba zamu yi cikin banza ba, kuma da igiyar aure akanki

 Ba zan iya zubarwa ba Kareem, ba zan iya ba

 Safeena na san muna son juna amman...

 Ba zan zubar ba Kareem ka daina magiya...

Ya tsaya yana kallonta da mamaki.

 Shi ke nan ki aje cikin, ni kuma zan tsinke duk wata alaka tsakanina da ke

Yana furta haka ya nufi kofar fita falon ransa a bace.

 Kana wasa da mace Kareem

Ta fada masa cikin fushi sai ya juyo ya kalleta.

 Ke kuma kina wasa da rayuwarki...

Ya juya Fuuu ya fice daga falon ya barta tsaye cike da mamaki.




NOOR POV.

Sai da Yaya ya fara aje ledodi sannan ya ciro dubu goma cif ya mikawa Baba.

 Gashi yace a siya mata magana

Baba ya karbi kudin da sauri ya kirga sannan ya saka aljihu ya mike tsaye be kula abun da ke cikin ledodin ba yayi ficewarsa ba tare da ya ba ni ko sisi ba, balle kuma Mama. Da kadan yake jira tace yayi rufeta da masifa, ni kam ban yi hanzarin tana komai ba har sai da na dan jira na ji ko Yaya zai yi fada amman ga dukan alamu damuwa ta hana shi cewa komai. Hana ta janyo ledodin da fara budewa daman tuni kamshi ya kara cika mana hanci.

 Nidai bari na bude idan ba za ku bude ba

Na kai hannu na taba leda daya sai Mama ta buge min hannu, ina kokarin juyowa na kalleta ta dauke ni da mari har sai da yatsanta ya fada min ido, zan yi ihu ta rufe ni da duka iyakar karfinta.

 Shiyasa ubanki kullum yake kuka dake, halinki ya fara isata, na gaji da ke Noor na gaji da halinki sakaryar yarinya dakikiya marar hankali da bata san ciwon kanta ba, yar iska gantalalliya, kullum haka kike ke babu ranar da za ki gayu

Daker Yaya ya kawace a hannun Mama ina kuka sosai. Ba zan iya fadar dalilinta na duka ba, iyakar abun da zan iya shaida shi ne ranta a bace yake tun shigowata har zamana, wata kila Baba ne yayi mata ba daidai ba, dalilina ko kuma wani abun ne ya faru kamin dawowata.

 Babu abun da zaki ci a cikin nan, wannan Mugun kwadayin da rawar kai sai ya zama ajalinki matukar baki daina ba, yar iskar yarinya da bata gudun abun magana

Na mike tsaye ina kuka har bada iya gani saboda hawayen da suka min zuba. Ji nayi an kwashe min kafafuwa na fadi kasa ribbbb gurin da na ji rauni a dazun ya sake buguwa har na yanzu ya fi na dazun radadi da zurfi.

 Mama dan Allah ki yi hakuri, ki yi hakuri Mama dan Allah ki yafe mata

Shi ne abun da na ji Hana na fada Yaya kuma yana rikon Mama.


Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -6


Duka sosai Mama tayi min tun tana dukana tana zagina har ta kai tana dukana tana kuka kamar yadda nake kuka. Hana ma kuka take saboda ta ga ina kuka daman haka take duk fitinarmu da ita idan wani abu ya bata min rai ko ya saka ni kuka ita tana shiga damuwa sosai, wani lokacin har ta kan fi ni ma saboda Mama tana cewa ni ban san ciwon kaina ba, sai dai wani ya sanin min. Na rarrafa na tashi zaune ina jin tsiyayar ruwan da na tabbatar na jini ne a kaina.

 Mama yanzu me ye amfanin haka? Gashi yanzu kin ji mata rauni a raunin da ta ji, yanzu kuma a koma jinya ana neman na magani Baba kuma ba badawa zai yi ba kin san tun da kudin nan suka kai hannunsa ba zai bada su ba, kuma halin nan ba dainawa zata yi miye amfanin dukan?

Bana ganin fuskar kowa saboda kuka, sai dai zan iya shaidar muryar Yaya Nabil ne mai maganar cikin yanayin damuwa.

 Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un

Shi ne abun da nake ta jin Mama na maimaita cikin kuka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login