Showing 207001 words to 210000 words out of 227321 words

Chapter 70 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1562



Ya fada ba tare da ya kalleni ba sai kofar tsohon gate din gidansu Mama yake kallo.

 So fada min kin cika idda ko da saura?

 Na cika

Na amsa bayan shiru ya dade da shiga tsakaninmu. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleni yana murmushi mai taushi.

 I miss you so much, irin yadda ba zan iya fassarawa ba, shiyasa ban kira ki ba i just need to see your innocent face

Na yi murmushi kadan domin ban san me zan fada ba, i miss him too but not like i use to do.

 Noor

Ya kira sunana na dago na kalleshi cikin ido.

 How are you Noor?

The way da yayi min tambaya muryarsa so low, kuma ina kallon tsakiyar idonsa ne, sai kawai na ji hawaye ya taru a idona, abubuwan da na manta suka dawo min.

 You're not alright i know, kina jin kin tsani rayuwarki kin tsani maza? Kina ji kina ganin kowa azzalumi

Na daga mishi kai.

 Yes ana samun haka a mata da maza ko da yaushe akwai bata gari, kuma dace ana yinsa ne idan an dage da addu'a mutanen da baka saka ran za su gujeka ko su cutar da kai ba su suke yi, baki da tabbacin kirkin kowa ni ma karki sheda ni

 Indai har Zafeer zai iya kyamata ya kushe ni, ya wulakanta ni kuma ya sake ni, to kowa zai iya

 Yeah, da zan baki shawara ki yarda da kin koma makaranta islamiya da boko cigaba da karatu you can meet new friends damuwa zata rage miki, ki aje soyayya a gafe auren ma ki dan daga masa kafa

Na share hawayena ina mamakin yadda yake cankar duk abun da yake raina da kuma kudina.

 Wannan shi ne plan dinta, ni ban shiryawa aure ko soyayya ba

 Haka ya kamata, karki sake bari wani yayi breaking heart dinki, and ke ma karki sake breaking heart din kowa

 Ni ban taba breaking heart din kowa ba, Zafeer ne, shi ma kuma yanzu na gane hi deserve it

Yayi murmushi mai sauti.

 You have no idea i feel lokacin da kika auri Zafeer baki fada min ba, you break my heart into piece, don't try that again

Na dube shi.

 Kareem are you hare because you love me?

 No, I'm here because you need me, I'm your best friend remember? Kuma ba miki alkwari zan kasance da ke a kowane kalar hali?

Na daga mishi kai.

 Good please smile my princess kin hade rai

Yayi min alamar murmushin da hannunsa, sai gani ina murmushi kamar ba ni ba. Daga nan hira ta canja salo ya dauko min labarin tiyatar da aka yi masa, kamin ya tambaye ni wace makaranta nake son shiga.

 Sa'adatu Rimi akwai yan unguwar nan da suke can

 No karki duba yan unguwarku da suke can, wani lokacin makarantar da kawayenka suka yi yawa zai iya sakawa ki kasa maida hankali, zan duba miki wata makaranta mai kyau private school kin ji?

 Amman...

 No amman ki bar komai a hannuna, as your best zan duba miki komai zan kula da komai

 Kareem wayo

Na lankwafe kai a shagwabe na ce.

 Wayo kake min Kareem kana min duk wannan saboda kana so na!

 Idan ina kin ki ai ba zan tsaya a nan ba ko? Ke ce dai kike min wayo ki cinye min kudi idan buduwarta ta ji ki sai ta yake ki

 Wacece ka yi budurwa ne?

Ya gyara rayuwarsa with seriousness ya amsa min da amsar da bata min dadi ba kuma ban tsammata ba.

 Ina da wanda nake so a yanzu Noor, she's my new girlfriend

 Da gaske?

 Nawa zaki ba ni idan na miki karya? Lokacin da kika yi breaking heart dina lokacin ne Allah ya ba ni wata

 Wasa dai kake Kareem, to a ina take?

 Zaki ganta soon

Kamar hadin baki aka kira wayarsa yana dagawa na ji yace

 Baby... Okay na sani kawai ina jin zolaya ne yau, ya aka yi?

Na ji wani abu na rashin dadi ya ziyarce ni, okay na ji ya amsa da shi sannan ya sauke wayar ya kalleni.

 Zan tafi akwai abun da kike so?

 Cewa ta yi ka zo tana son ganinka?

Na tambaya abun da be kamata na tambaya ba domin be shafe ni, murmushi yayi ba tare da ya amsa min ya sake tambayar abun da nake so.

 Ni bana son komai, amman dai mata ba su da tabbaci ka yi taka tsantsan kai ma

 Zan yi Bestyna

Ya amsa ni, ko ina ruwana a cikin lamarinsa oho shi ma fa da gani zai iya cin amana domin gashi nan daga rabuwarmu har yayi sabuwar budurwa.

 Ko Safeena ce?

Na tambaye shi yayinda ya bude motarsa zai shiga, domin maganar ci na take na kasa hadewa kai kace bana da damuwar da ya kamata na damu da ita. Ya rufe motar ya juyo ya kalleni.

 In har mata za su kare a duniyar nan, ya rage sauran Safeena kadai to zan yafe aure ne ba zan taba aurenta ba, yana daga cikin godiyar da nake yi ma Allah kuma nake tuna Momyna ina jindadi, na hana ni auren Safeena da ta yi, na ga alfanun hakan yanzu, kuma na gane ba dukan abun da kake so alheri a gareka ba

 Amman ita new girlfriend dinka ta san kana da Safeena? Kuma zata rika maka shi? Ko zaka bar shi gurin Safeena?

Na fada ina yatsina fuska.

 Safeena ta yi accident Noor, mijinta ya sake ta ta tuka kanta sai dai kamin ta bar garin Kano ma ta yi hadari, kuma yaron ya rasu, ita kuma har yanzu tana asibiti kuma kashin bayanta ya samu matsala, bata iya tashi

Na rufe baki da sauri tsoron Allah na kara kamani.

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, ita kuma haka rayuwa ta yi da ita?

 Ta cancanci fiye da haka karki ji tausayinta, matar nan tana daga cikin mutanen da suka nesanta ki da farinciki, na tabbatar halin da take ciki yanzu somin tabu ne mai wuyar yana nan zuwa, kowa yayi da kyau zai ga da kyau, masu mummunar karshe su ne ba su tsaya sun kyautata rayuwarsu ba

 Amman shi Abdull din yana ina? Meyasa ya sake ta? Da ya hakura ya zauna da ita ai halinsu daya

 Ba ni da labarinsa

Ya amaa yana sauke ajiyar zuciya sannan ya sake bude motar ya shiga, ya dauko katinsa ya ba ni.

 Ki kira ni, a tunani yanzu kamar ina da hurumin kiran wayarki ko?

 Ina da number a kaina

Ya kalleni yayi murmushi ni ma na mayar masa, sannan na daga masa hannu na yi masa bye bye as my best friend, domin ni ban shiryawa saurara kowa ba a yanzu, ko da ace ma na shirya shi ai ya riga da ya samu wanda yake kauna a yanzu, oh maza masu abun mamaki kamar ba shi na fada min bayan ni ba zai sake son wata ba, yau shi ne yake ffada min ya samu wacce yake so.

 Daman da gani shi ma ba son kwarai yake min ba azzalumi, haka yayi breaking heart din Safeena shiysa yake bibiyar rayuwarsa, shi ma da yanzu ya sake ni

Na fashe da kuka.

 Gaba daya maza babu na kirki, shiyasa ma na daina soyayyar na huta

Na share hawayena domin babu dalilin kukan, kokarin goge numbersa nake dake cikin kaina kawai haushinsa nake ji ba zan iya kira ko yin chat da shi ba, ba shi kadai ba mazan duniyar ma gaba daya haushi suke ba ni. Sai da dare nake labartawa Mama yadda muka yi da Kareem na neman a bar masa ragamar komai na karatuna.

 Ni wannan abu na ku yana daure min kai, Kareem din nan idan har son ki yake ai ya ci ace ya nuna, tun kamin aurenki na farko yake bibiyar rayuwarki, kika yi aure ya kika fito ya dawo kike sake kika fito ya dawo, yanzu kuma ya sake dawowa, na rasa gane inda ya dosa, ki yi taka tsantsan da shi, kuma ki fada masa na ce aa domin ba aurenki yake ba balle yace hakkinki yana kansa, kuma ba ba haihuwarki yayi ba balle na ce ubanki ne. Na san yayi iya kokarinsa hidima da Nabil kadai abun a yaba masa ne, Allah ya saka masa da alheri amman ke na dauke masa

Abun da Mama ta fada ni ma shi nake ganin ya dace, ni dai a yanzu bana bukatar wani abu nasa ya tafi can su karasa ta new girlfriend dinsa, kuma mama tana da gaskiya meyasa yake min duk wannan bayan ya san yana da wacce yake so.

 Wa'alaikumussalam

Na ji Mama ta amsa waya, har tana fadar

 Toh Allah yasa lafiya dai

A take na tattara hankalina na maida gurinta.

 Toh gobe zam shigo In sha Allahu

Ta sauke wayar.

 Mama waye?

 Daga kotu ne aka kira ni wai na zo gobe Kotu tana son ganina

 Amman lafiya

 Taya zan sani? Wata kila wani abun ne ya taso, ta bangaren Alhaji, domin tun da aka shiga kotun nan be taba zuwa ba, kuma ba a taba zama ba, kullum da kalar uzurin da lauyansa yake bayarwa

 Sai idan na je sai mu ji

 Allah yasa mu ji alheri to

 Ameen

 Sun ce na zo da wani nawa

 To ki je da ni kawai Mama

 A cikin manya na suke nufi ba ke ba

 Ni dai gaskiya Mama sai na biki hankalina ba zai kwanta ba idan ba mu je tare ba, a yanzu ke ce kawata ni ce kawarki ni gaskiya sai na biki na san me zai faru?

Mama ta tabe baki tana kallon yadda nake zuba mata shagwaba.

 Kyaji da shi, kawunki ba zai bari ba

 Tun yanzu idan zaki fada masa Mama ki ce masa sun ce azo da ni

 Ban iya karya ba

Na bata fuska haka na yi ta maga magiya har ta gaji ta tashi ta bar min dakin. Washe gari da wuri Mama ta shirya shirin tafiya kotu, kamar na san zata je da ni ni ma na tashi na shirya na shafa mai da powder na zauna ina ta kallonta.
Ban san me ta fadawa Kawu ba, ya aminta a tafi da ni ji na yi tace na tashi mu tafi, a take na fito da hijab dina dake boye a bayana na saka ina ta zumudi muka kama hanya.

Kusan wannan ne karon farko da kafata ta taka kotu, gabana sai faduwa yake ashe ko da baka da laifi tsoro kake ji. A bangaren rigistira muka shiga muka zauna domin mun iso ne tun kamin alkalin ya shigo, wai ance kotu bata jira sai dai a jirata. Da na gaji da zaman ne na fito waje domin zama a gurin da na hango wasu suna zama wasu kuma suna cikin kotun suna jiran isowar alkali. Kamar daga sama na ji an kira sunana.

 Noor...

Na kalli saitin da sunan yake fitowa sai na yi arba da ustazun nan da Kareem ya hana ni tsayuwa da shi yana sanye, nuna shi na yi ina kokarin tuna sunansa.



KAREEM POV.

Driving yake yana murmushi sauyin yanayi da ya gani a fuskar masoyiyarsa Noor a lokacin da ya fada matana yana da wanda yake so, bata iya rike kanta ba kuma ya ji dadin haka. Ya gama karantarta ya san tsare tsarenta shiyasa be fada mata ko nuna mata soyayya ta kawo shi ba, kuma ya goya mata baya akan kudurinta duk kuwa da yana jin kamar ba zai iya jurewa ba.

Sai dai a yanzu bakin zaren lamarin yake nema dole, ya tafi mata a yadda take so. Harabar gidansu ya faka ya bude motar ya fito yana murmushi, ya nufi main door ya murda ya bude ya shiga, kanwarsa Khadija dake rike da plate din kankana ta amsa masa sallamar da yayi.

 Wa'alaikumussalam Big Bro

 Little Sis ya kike?

 Lafiya kalau, Big Bro yau nishadi kake ji da adama

Ta fada tana kallonsa, ya fadada murmushinsa.

 Me kika gani?

 Da na kira ka ka ce min Baby

 To me ai, you're baby, kuma ina kusa da girlfriend dita ne kawai ina son na saka ta kishi ne, shiyasa na fadi haka

Ta wara ido.

 Big Bro da gaske? Ina take ina kuka hadu? Wacece ita?

 Zaki santa soon

 Yaushe, da wuri za ayi auren?

 Haka nake fata, kawai ta cika kafiya ne, amman dai na fita wayo ai

Ta yi dariya.

 Hajiya na ciki ita tace a kira ka

 Okay

Ya saka fork ya dauki yankan kankana daya da take sha ya kai bakinsa sannan ya nufi dakin Step mother dinsa yana tauna kankanar.
 Kin manta ni ko? Sunana Salees. Me kike yi a nan?

 Na zo kotu ne

Na fada da dan kunya.

 Gurin me? Kashe aure? Sharia kike da wani?

 Aa ni aurena ya mutu ai, ba aurena ba

 Auren da kika yi har ya mutu kuma?

Kunya ta kama ni na masa alama da ya rage murya.

 Ashe ka san na yi aure

 Na sani mana, last zuwan da na yi an fada min kin yi aure

Na yi shiru mutane sai kallonmu suke even though basa jin abun da muke tattauna.

 Me kike yi a nan?

 Ba komai

Ai da kunya na fadi cewar Mama ne take son kashe aure bayan kuma ni nawa auren ya mutu.

 Kai me ya kawo ka kotun?

Yayi murmushi kawai ya wuce ciki da kallona na bi shi na yi zaton cikin kotun zai shiga sai na ga ya zagaya ta wani gafen ya bi ta wata hanya. Ni kuma na juya na koma gurin da su Mama suke na zauna, babu jimawa aka shigo kiran Mama tare da kawu sai muka dunguma har ni muka bi dan aiken har chamber Alkali ashe daki ne a gefen kotun har da ac da carpet. Mama ta fara shiga sannan Kawu ni ce ta uku, wa zan gani a kujerar dake dakin mai dauke da tebur da takardu ba Salees ba?

 Ranka ya dade ga mu

Mama ta fada ni kam na sakar masa ido kamar tv daman Alkali ne, shi kam be yarda ya kalleni ba. Sai magana yake da Mama cikin girmamawa.

 Mama abokin shari'ar wanda zan iya kira da mijinki ya aiko da sako ta hannuna yana son na hannata miki

Ya dauko wata takardar ya mikawa Mama ta karba ta bude. Alhamdullahi na ji ta fada tana sauke ajiyar zuciya, ashe saki ne a ciki ban fahimta ba sai da Kawu ya karba ya karanta.

 Miye abun godiya a saki?

 Yace ba zai iya ja dake akan abun da yake fa ikon aikawa a take ba, domin shi sanannen mutum ne baya son abun da zai janyo ka ce na ce

 Da haka ya aikata tun farko ai da ba mu kai ga zuwa nan ba, mun gode ranka ya dade

Kunya ta kara rufe ni a lokacin da ya kalleni zai ce ni da Mama ba ma zaman aure kenan domin shi be san other side of the Story ba.

 Sannu Noor

Yanayin yadda yayi min maganar sai ka dauka lokacin ne farkon haduwarmu a kotun.

 Ina kwana

 Lafiya kalau

Mama ta kalleni.

 Kun san juna ne?

Kamin na yi magana yayi murmushi ya ce.

 Zan shiga kotu Mama a sauka lafiya

Muka mike tsaye a tare shi ya kwankwasa kofar kotun ma'aikatan suka zo da gudu ni kuma na bi bayan su Mama muka fice. A napep Kawu sai fada yake yi ma Mama akan abun da ya faru ita ce bata ce uffan ba balle kuma da zai iya daukewa da mari.

Sai da muka isa gida sannan Mama take tambayar ina na san Alkalin na labarta, yayi so na amman be taba fada min shi Alkali ba ne kawai yace min aikin gobnati yake yi, kuma ban samu damar tsayawa na yi zance da shi yadda ya dace ba balle ya fayyace min komai, ko a lokacin bana son zuwa saboda tsananinsa na son sai na saka Hijab ga wa'azi sama da kasa, gashi idan ya zo be wani dadewa sosai, kamar mai tsoron mutane haka yake amman yanzu na gane dalilin.

Da yamma liss aka aiko kirana zuciyata ta raya min ko dai Kareem ko abokin Yaya ko kuma Salees, na fito sanye da hijab sai na samu Salees din a mota zauna ganina ya saka shi fitowa ya jingina da motar yana murmushi fararen tufafin dake jikinsa sun kara masa kyau. Yadda yake da kurciya ba kace Alkali ba ne ashe akwai yara alkalai.

 Hajiya Noor

 Ranka ya dade

Na fada ina murmushi.

 Ya kike ya gida

 Lafiya Kalau, ya Kotu ashe kai Alkali ne ko?

Yayi murmushi, ni ma murmushin na yi a karo na biyu na kalli gurin da na ji karar rufe mota. Kareem na gani fuska a hade kamar be taba murmushi ba har tsoro ya ba ni. A take nawa murmushin ya gushe, da kai yayi min alama da na wuce cikin gida. Ba ko musu kamar yayi magani sai kuwa na juya da sauri na shige cikin gidan na bar Salees a tsaye.

Ina shiga dakin Mama na zube mata a kasa na fashe da kukan shagwaba.

 Me ya faru?

 Kareem ya ce na wuce gida, kuma na dawo din na bar Salees a waje

 Waye kuma Salees ke dai har yanzu ba ki bar janyo mana maza kala kala ba ko?

 Wannan Alkalin ne fa shi ne Salees

Mama ta rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login