Showing 45001 words to 48000 words out of 227321 words

Chapter 16 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1555

da yata, ai Annabi S. A. W ma cewa yayi idan wadda kuka yarda da addininsa da mu'alamarsa ya zo son yarku to ku aura masa, addinin musulunci ya bawa iyaye damar zabar wa ?a?ansu mazajen aure, daman can ni ban wani yarda da tarbiyar yaron nan ba, waya sani ma ko zuwa yayi ya hure mata kunne ta bishi su gudu?

 Zafeer din Baba?

Na furta da kaina kuka yana cin karfina. Sai ya zabura ya tashi zaune.

 Zafeer din fa, ko ubanki ne shi ko kanen uwarki ne? Dan'adam babu abun da ba zai iya aikatawa ba ai, ke kuma kwakwalwar kifi ce dake gaki sokuwa sai ya tsara miki ki yarda ki hau ki bi, to daga yau sai yau kar ya sake sallamawa ki fita, ke ban ma yafe miki ba ki kula shi ko a hanya, ban yafe miki ba wata magana ta sake shiga tsakaninki da shi

Mama ta tashi tsaye dukan kirji.

 Malam kana lafiya kuwa? Wane irin abu ne wannan? Saboda wani ya bullo ya nuna yana son Noor cikin kankanen lokaci ya siye bakinka da zuciyarka da dukiyar da baka san hallaci ko haramcinta ba zaka yarda ka rusa soyayya da baiko shekara uku dake tsakanin yaran nan? Duk irin iya shegen da Noor take haka Zafeer ya ganta yace yana so sai kuma ka shiga tsakani yanzu da yake hararo gaba? Haba Malam kar ka yi abun kunya mana kar kasa hakki ya bibiyemu

Baba ya mike tsaye ya dauke Mama da mari.

 Duk wata doka da zan saka a cikin gidana ke kike rusa ta kuma ke kike ba su damar rusawa, ko a addinance ba ni da laifi tun da shi yace be shirya aurenta ba a yanzu, kuma wannan yaro da kike zargi Allah ya isansa domin har yau be fito yace min yana son Noor ba, dan haka ya barki da Allah da zargin lalata alaka da kika masa, kuma bari ki ji na fada miki idan yaron nan ya sake yin sallama kika bar Noor ta fita abakin aurenki....! Wato yan unguwa su yi da ni, na shigo cikin gida ki dora min tukunyar masifa, to ba zai yiyu ba, daman can Allah yayi ba matarsa ba ce

Ya saka talkaminsa ya dauki radio ya fice babu ko hula akansa. Mama ta dube ni ta kara min da wani bakincikin.

 Allah ya kara, duk abun da ya faru ke kika ja, shegen shishigin tsiya da iyayi da yawo da shashanci shi ya ja miki, kuma ni ba zan bari aurena ya mutu ba saboda ke, domin ba zan koma neman gurin zama ko rabawa ba kuma zan yarda rayuwar Hannatu da Nabil ta shiga wani hali ba saboda ke, kadan ma kika fara gani, hawayen da kika yi ta saka ni ina fada miki gaskiya kina bijirewa yau ga sakamakon kin fara gani, kuma wannan so min tabi ne baki san me zai biyo baya ba, sai ki zuba ruwa kasa ki sha...

Tana maganar tana nuna ni ta muryarta nake karantar kukanta domin nawa hawayen sun hana ni ganin fuskarta. A kananen shekaruna na fara dandana zafi da bakincikin rabuwa, Baba ya sauya tunanina ya rusa burukana, ya wargaza shirina, ya saka ni a wani gidan kurkuru da ban isa na fitar da kaina ba, ban san ma ya kofar fitar take ba....

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Talla=?G?=?G?=?G?*

https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA
*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARAS'DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORAL'*

*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI=ت?BA MUNA KAYABAL' HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*

*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER =؃?=؃?=؃?=؃?=؃?=?I? GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328

*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*

*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*

AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAY??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????A SAKA KIBA=؃?=؃?=؃?

GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA=?F?=?F?=?F?




*Chapter - 13*

Babu kowa a tsakar gidan balle na ce wani ne ya rika ni ya isa da ni kofar dakinmu, haka kuma ba zan iya fadar cewar kafafuwana sun kawo ni ba, domin samun kaina na yi tsaye a tsakiyar dakinmu ina kallon hudun daren da ya cika daki. Can ka na ji an dafa ni muryar Hana ta fara isa kunnena.

 Da ni ce ke, zan auri mutumen nan ko dan na samu rabuwa da Baba lafiya, kuma zaki huta da duk wata masifa tashi da tashin hankali ko fada, idan kika yi aure zaki huta Noor

Na juyo na kalli ta saitin inda take tsaye. Amman na kasa ce mata komai sai hawaye ne suke min zuba, a rayuwa ban tana jin wani abu tashin hankali ba irin wadda na ji a yau din nan. Sai na ke jin kamar sanarwar mutuwa aka min cewar Zafeer ya mutu ya bar ni a raye.

 Noor ki yi addu'a kawai, kuma karki bari so ko shashancin da ake ganinki da shi ya zama silar lalacewarki saboda bakin da Baba yayi cewar be yafe ba idan kika kula Zafeer

Na sulale kasa a hankali na zauna a gurin, na rasa me zan yi ko na ce, kalamaina kamar sun kare, duk wani kuzari a yau ba ni da shi. Me yasa Baba zai min haka? Anya ya san yadda nake son Zafeer kuwa ko kuma yadda shi Zafeer din yake so na? Mama ta yi gaskiya tace ni ce na janyowa kaina kuma haka din ne, domin ni na yi silar zuwan Kareem da abokinsa a gidanmu gashi sun lalata baiko ba tare da na san waye mai so na a cikinsu ba, ba ma nuna suna so na ba, kuma ba su furta ba ban taba ganin wata alama dake nuna soyayyata a garesu ba.? Gaba daya sai na ji kamar mafarki nake wunin ranar sai ya zame min kamar ba gaske ba, ni dai na san ina matukar kaunar Zafeer irin kaunar da nake jin idan ba shi ba ba zan iya zaman aure ba. A inda na zauna ban tashi ba har garin Allah ya waye kuma bachi be kusanci idona ba, haka kuma ban bude baki na ce da kowa komai ba ban kuma ihu ko kururuwa ba, saboda ina jina a wani yanayi na dabam da ban saba jina ba.

Bayan na yi sallah asuba na nemi gurin kwanciyata na kwanta sai idona suka ce firr ba dai bachi ba Nooriyya, karyarki ba a wannan wunin ba, haka na tashi zaune na kurawa kofar wajen ido, na dade a zaune kamin na iya bude baki na fara ambaton Allah, Ban yi wani kwakwaran motsi ba har Hana ta gama shirinta na makaranta ta fita ta zuba kunu sannan ta kawo min nawa har inda nake kallo daya ta yi min ta fahimci a tsorace nake ga idona yayi wani Ja kamar wadda ta shekara bata yi bachi ba.

 Ga kununki in ji Mama...

Na kalli kunun na dauke kai ina jin ba zan iya kai komai a cikina ba yanzu. Ni dai ba wani sanin damuwa na yi ba amman ina jin dakinta na daf da ni domin kokarin rabani da Zafeer da Baba yake ko ma yayi wani abu da ban taba mafarkin faruwarsa ba.

 Wa'alaikusalam

Muka ji Mama ta amsa sallamar Zainab dake sanye da uniform din makaranta, Hana ta jiya ta fice daga dakin kamar dai babu wadda ya damu da halin da nake ciki, wata kila ba su yi zaton soyayya ta ta kai haka ba, ko kuma ganin suke wani abu ne da zan iya mantawa a take. Ko kuma dai saboda ni na janyowa kaina ne shiyasa lamarin ya zo min ta haka.

 Noor... Lafiya kike kuwa?

Kamar an bude min kofar sassauci tana tambayar haka sai na fashe da kuka na kwanta jikinta amman na kasa fada mata damuwata har ta gaji da tambayata ta koma rarrashina.

 Allah dai yasa lafiya, Zafeer ya je gidanmu shi ma cikin damuwa yace na fada miki ya zo jiya amman be samu ganinki wai yana son ku hadu a gurin aikinsa ko kuma kwanar dan musa mai itace anjima da karfe goma

A sirrance take fada min sakon na Zafeer, abun da hausawa ke cewa ga bikin zuwa babu zanen daurawa, domin ban isa na tsallake umarni da furucin mahaifina na je na ganshi ba, kuma a yau bana jin zan iya budewa kawata cikina balle na fada mata damuwata da babu mai min maganinta sai Allah.

 Noor akwai wata matsala ne? Fada min ko minene dan Allah

Na girgiza mata kai na matsa baya na kwanta ina maida numfashi daker.

 Wai fada kuka yi da shi ne ko kuma me?

Nan ma dai ban ce mata komai ba. Har ta gaji ta tashi ta fita ta barni rumgume da bakincikina. Ban iya fitowa na yi komai ba har Mama ta gama aikinta na gida, Yaya ya dauko ruwa sannan yayi wanka ya fita, a nan na samu mikewa tsaye ina jin kaina na masifar ciwo ga wani jiri jiri da nake ji yana dibata yana yawo da ni. Ruwa na zuba na shiga bandaki wai saboda na samu na yi wanka amman sai na saka yin wanka na zauna a bandakin ina ta kuka. Hankali be kara tashi ba sai da wani almajiri ya shigo ya ce Zafeer na sallama da Noor Mama tace masa yaje yace bana gidan. Rumgume kaina na yi ina ta kukana babu mai rarrashina har sai da na gaji na tashi na daura zanena na fito ba tare da na yi wanka ba na aje ruwan a waje sannan na nufi dakin Mama na zauna daga bakin kofar dakin ina kuka na ce.

 Mama Wallahi duk na daina abun da nake, ba zan sake kin jin maganar kowa ba, Mama ki yafe min kuskurena, kuma dan Allah ki roka min Baba yace ya yafe min yayi hakuri ya bar ni na auri Zafeer dan Allah Mama

Kaya take ninka amman haka be hana ta kalleni ba ta ce.

 Kin fi kowa sanin halin Babanki ai, yanzu ya ga mai kudi ba zai yarda da soyayyarki da yaron nan ba, kuma ni ban ga laifin ubanki ba, daman tsuntsu da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka, tun abun nan be yi nisa ba ya kamata ki gane gadar zare kike yi ma kanki amman ina, hankali yayi yamma ke kin yi gabas, idan kika ga Babanki be hada aurenki da wannan mutumen ba to sai idan shi din ne yace baya sonki ko kuma wani ya gani wadda ya fishi

 Ba so na yake ba Mama Wallahi wata kalmar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi ba

Na fada da muryar kuka wani kukan na cin karfina.

 Wannan kuma ke kika jiyo, ga dubu biyu nan tashi ki kai gidan mai adashe, bashin da kika ci ne ban gama biya ba

Ta jego min kudin ni kuma sai na kai hannu na dauka, na kalleta sannan na tashi na fice daga dakin ina hawaye. Dakinmu na koma na zauna gaba daya sai na rasa abun da ke mini dadi. Na kusan minti talatin a dakin ina kuka har sai da Mama ta yi magana sannan na yunkura na tashi idona a kumbure na saka rigata da hijab na riko kudin na fito na saka talkamina na fice daga gidan. Kamar wata marar lafiya haka nake tafiya har na isa gidan mai adashen na bata kudin na juyo na fito ta babu wani kuzari a tare da ni. Daf da zan isa gida na ji muryar Zafeer yana kiran sunana amman na kasa waigawa saboda bana son na yi arba da fuskarsa kar rauni ya saka ni karya doka da mahaifina ya saka min, amman hakan be hana shi shan gabana ba.

 Noor magana fa nake miki kina tafiya kamar baki gan ni ba, me ke faruwa ne?

Na dauke kai na kauce daga gabansa na cigaba da tafiyata.

 Noor... Noor.. Ni ne fa, Noor

Na kasa juyawa kuma na kasa amsa masa sai hawaye suka zubo min. Ya sake shan gabana.

 Jiya na tafi gidanku ban samu ganinki ba, idan har Baba zai juya min baya ya ki sauraren uzurina ban yi zaton haka daga gareki ba Noor, kin san ina sonki sosai zan iya jure komai ban da rashinki Noor, na roki Baba jiya na ce ya yi hakuri ya ba ni wata biyu zuwa uku zan yi na yi duk yadda zan iya, zan aureki Noor ko haya ce zan kama mu zauna kamin na samu aiki, amman me yasa kike kokarin canja min? Ko wani abu aka ce na miki? Ko kuma an fada miki wani aibuna ne...?

 Babu wani aibunka da za a fada min da zai saka na tsane ka Zafeer, babu wadda zai iya shiga tsakanina da kai, babu wani laifi da zaka aikata a duniyar da zai saka na juya maka baya

Magana nake masa a zuciyata amman a zahiri na kasa furta komai sai kallonsa nake.

 Noor...

Ya sake kiran sunana muryarsa a sanyaye, nan din ma ban amsa ba sai ma kauce da nake kokarin yi daga gabansa na cigaba da tafiyata.

 Baby Noor Noor yau ni nake miki magana kina tafiya? Ina kiranki kin ki amsa min? Me yake faruwa? Fushi kika yi? Saboda na ce ba ni halin aurenki a yanzu? Zan aureki Noor ko ta halin Yaya na miki alkawari hakan yayi miki?

Nan ma ban juyo ba shi kuma be fasa bin bayana yana bayyana min kalaman da suke kara tsuma zuciyata ba.

 Noor please, ina binki a baya kina tafiya kamar wani bakonki miye haka?.... Nooorr!

Daga karshe ya kira sunana a tsawace har sai da na tsaya cak daga tafiyar da nake.

 Ko dai mutumen nan ne ya fada miki wani abu a kaina? Ko kuma Baba ya fada miki wani abun ne dabam da ba shi na fada ba, me yasa kike min haka? Why?

Na hade yawu na cigaba da tafiya da sauri na barshi a gurin tsaye, ina shiga gidan na samu Mama sanye da hijab ta nufo kofar fita.

 Alhamdullahi, daman bayanki zan bi saboda na san halinki zaki iya satar kafa ki tafi gurin Zafeer din nan

Ni dai ban ce komai na nufi dakinmu na kwanta ina ta gurzar kuka kamar babu gobe. A haka Hana ta dawo daga makaranta ta same ni har na yi rama tsabar kuka da tashin hankalin da na samu kaina a ciki.

 Noor dan Allah ki ba kanki lafiya, ki yi ta addu'a idan Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isa ya hana

A nan na samu damar amsa mata da toh sannan na tashi zaune ina kallon kunun da ya aje min tun safe.

 Baki sha kunun ba?

 Ba zan iya cin komai ba, Hana

Na kira sunanta sai ta amsa min ta duko.

 Dan Allah ki roka min Baba yayi hakuri Zafeer yace zai nemo kudi nan da wata uku zai aureni, ki ce yayi hakuri ya bar ni na yi magana da shi, hukuncin yayi min tsauri...

 A ina kika ga Zafeer din?

 Dazun da Mama tace na kai kudin adashe...

 Amman dai ke kam Noor baki jin magan yanzu duk bayan gargadin da Baba yayi miki yace miki be yafe ba idan kika sake magana da Zafeer sai da kika yi? Kin san abun da tsinuwar iyaye take nufi kuwa...

Na girgiza mata kai da sauri.

 Ban yi magana da shi ba, shi ne yake bibiyata yana fada min haka, ransa ya bace da ban yi magana da shi ba, ni ma na ji kamar na mutu saboda yayi min magana ban amsa masa ba, Hana babu dadi dan Allah ku yi magana da Baba ko zai ji, ni na san haushina yake ji amman ke zai iya saurarenki saboda ya san kina da hankali

 Aa Mama ma bana jin zata iya tunkararsa da wannan maganar balle kuma ni, indai ba son kike ya tsine min albarka ba ni ma, ki dai ta addu'a ni ma zan taya ki

 Na gode

Na fada mata sannan na tashi kamar yakusasshen lawashi na fita daga dakin, alwala na yi na dawo dakin na yi sallah azahar na yi ta addu'a. Misalin karfe hudu na yamma Yaya Nabil ya shigo gidan da ledarsa kamar yadda ya saba, ko da an yi girki balle yau da ba a girka komai a gidan ba. Awaje ya zauna gurin da Mama take zaune domin kusa da kofar dakinmu ne, ina jinsa yana ta fada da alama ransa a bace yake ban fuskanci me yake magana akai ba, amman na ji sunan Zafeer da Oga Kareem kuma na ji zancen yan sanda. Hakan ya saka na mike tsaye ina jin jiri na taka na isa kofar na rike kofar na tsaya ina kallonsa.

 Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un abu be yi dadi ba, yaushe wai?

Na ji mama ta fada sai Yaya yace.

 Yanzu nan ba a dade ba Wallahi, kuma duk Baba ne sila, shi ai yana da gaskiya ko nine zan aikata fiye da haka, me yasa Baba zai yi halin karanta miye amfanin haka? Fisabillilahi haka ake yi, ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login