Showing 219001 words to 222000 words out of 227321 words

Chapter 74 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1561

kuma ya ji babu wanda yake bukatar gani ko ji sai Noor dinsa. A take ya aika mata kira tana picking ya ce.

 Hey Beautiful

 Hey handsome

Ta amsa mishi with awesomeness, ya kwanta jikin kujerar yana shafa kansa da murmushi a fuskarsa feeling so heart warming.

 I miss your hairy chest, i need cuddle

Ta fada a shagwabe. Gaba daya sai ya ji ya rikice.

 I will be there right away my beautiful

Ya sauke wayar ya dauki abubuwan bukatarsa daman lokacin tashinsa yayi sai ya fice daga Asibitin da sauri. Tun kamin ya fara harabar gidan ta fito sanye da hijab yana ganin haka ya san kananan kaya ne a jikinta domin ya fada mata idan zata fito harabar gidan ta rika rufe jikinta saboda mai gadi.

Waving dinsa ta rika yi daga bakin kofar falon da take tsaye har ta karaso ya sauke gilashin motarta.

 Hey Beautiful

 Hey Handsome

A kokarinsu na rigen rigen futarwa juna suka fada a tare, sai duk suka saka dariya. Yana fitowa motar sai ta zo a guje ta daka tsalle ta fada jikinsa ya cafketa ya daga sama ta lake kafafuwanta a kunkurunsa.

 I miss this face, i miss this girl

Ya fada yana jan kumatunta, ita ma sai ta ja nashi tana fadin.

 I miss this hug, i miss this guy

Yayi dariya ya nufi entrance din da ita. Suna shiga falon ya fara kissing dinta, sannan ya sauke ta kasa.

 What's up Beauty

Ta yi dage ta lakaci hancinsa.

 I cook something delicious...

 Let me smell it then

Ya fara kokarin cireta mata hijab yana shinshinar kamshin dake tashi a jikinta.

 I said i cooked not in my body

 Ouoooo, my bad, i have dirty mind

Ya daga ta yana dariya...
Bayan Shakara Daya...


NOOR POV.

Na bullo da kaina gurin wuyan rigarsa na tura hannuna da gun da hannunsa yake, sai ya zama na ni ma na shiga cikin T-shirt din dake jikinsa, shi yana daga kwance rairai ni kuma ina samansa na lafe a jikinsa skin dina yana taba nashi.

 Baki karasa min ba, sai aka yi yaya?

Na dan yi shiru ina tunanin a ina na tsaya da labarin da nake ba shi na sabon littafin Khadeeja Candy mai suna ABOKIN RAYUWA.

 Yauwa sai be aureta ba, ita fa yarinyar christen ce, bayan ya musuluntar da ita sai kuma yan'uwan shi suka rika cewa ba bahaushiya bace saboda ita din igbo ce amman tana da kyau, sunanta Emily

 Ta yi kyaunki?

Na daga na kai masa cizo a gemu har sai da yayi kara.

 Ita fa kyakkyawa aka ce

 To ni yanzu akwai mace mai kyau da ke burge ni irinki, kin mamaye zuciyar kin hana ni ganin kyaun kowa ai, da zarar na motsa nan sai na ji ana Noor idan na juya can na ji ana Noor, to ya zan yi? Kin saka kwado kin kulle idon da zuciyar gam

Na yi dariya mai sauti.

 Kuma na jefar da makullin ya bata

 What ever ni dai abun da nake so na samu, Noor kin cika rigima na fada miki ki daina shigowa rigata ta front ki rika juyawa so that idan ina son na yi hugging dinki sai na yi, yanzu ya zan yi hugging dinki a haka?

Na turo masa baki a shagwabe na ce.

 To ni haka nake so

Yayi kasa da kansa ya goge min hancinsa.

 Rigimammiya duk kin bare min riguna

 Skin to skin, ruhi to ruhi, love to love

Na daga mishi gira na kashe mishi ido irin yadda yake min. Sai ya saka dariya sosai yana girgiza kai.

 Funny girl, Allah ya shirya min ke

Na kwantar da kaina a kirjinsa.

 Ameen

Na yi lamo ina jin bugun zuciyarsa.

 My king

 Yes my Queen

 Satin nan ya Nabill zai tafi kauye gurin yan'uwan Babanmu da suke can, zaka bar ni na je

 No...

Ya amsa min kai tsaye, fita na yi a rigarsa na matsa gefe na rufe jikina da blanket na hade rai na ci magani. Sai ya sauka daga kan gado ya shiga yayi wanka ya fito na dauke fuska na juya dayan gefen, sai ya zo ya kama fuskata.

 Hey Angry Girl bring back my Beautiful Girl

Na kara hade rai, sai yayi dariya ya sake ni ya shirya kansa. Sannan ya dawo inda nake ya rika fuskata ya goge min hancin.

 Hey Beautiful saki fuskarki mana, za ki tafi amman ba yanzu ba, sai kin haihuwa

 To ai yanzu babu cikin ka bari idan....

Be bari na karasa ba ya rada min.

 We ganna make one tonight

Yayi kissing front head dina ya nufi kofa.

 Off to work, i love you

Na nade hannayena na turo baki na ki nace masa i love you too kamar yadda muka saba, sai ya juyo yana rike da kofar dakin.

 Can i hear i love you back

 No

 Come on Beauty

Ya dawo ya fara min cakulkuli har sai da na fada.

 I love you back

 Nope ina son na ji i love you too

 I love you too

 Good girl

Ya sake ni sannan ya fice. Hausawa suka ce fadi gareka cikawa ga Allah it take us another year kamin na samu ciki, ba dan kuma ina da matsalar komai ba sai dan lokacin hakan ne be yi ba.

Na fara ne da rashin lafiya, sai kuma na fara jin sauki but jiki ya zama so weak, sai dai gane cewar ciki ba ne till one day na dauki wani karfe da Kareem yake workout da shi sai yayi saurin hanawa ya rike ni.

 Mace mai karamin ciki bata daukar abu mai nauyi careful don't hurt yourself

 Ai ba ni da ciki

 Says who?

 Says me

 Are you a doctor?

 Amman ai ni matar likita ce?

Yayi murmushi ta lankamo wuyana.

 Kina matar likita baki san kina da ciki ba?

Na yi shiru ina nazari, sai ya dauke ni ya bude kofar baya ta falon ya shigo da ni falo ya aje kan kujera ya zauna kusa da ni.

 Ina mutuwar Sonki Noor balle kuma abun da zaki haifa, dole sai kin yi taka tsantsa kar wani abu ya samu cikin nan dan Allah, kwanta ki huta zan motsa jini waje

Ya mike tsaye sai kuma ya dawo ya rumgume ni ya sumbance ni.

 Thank you, my happiness, my love

Na yi murmushi na lafe a jikinsa.

 Baby be son ka yi workout he need a cuddle

Ya daga kafafuwana ya matsar da ni jikin kujerar sannan ya kwanta a gurin ya rungume ni.

 I will do what ever pleased you and my baby

Na saka hannuna ina jan gashin dake kirjinshi kamshin turarensa na kwantar min da hankali.

 Da gaske ina da ciki?

 Uhmm. Why would i lie?

Na jidadi ya rufe ni.

 Kuma kana son Babyn?

Ya saka hannunsa ya dago kai.

 Har tufafinki ina so balle babyn da zaki haifa, ba ki san irin dadin da na ji ba lokacin da na gane kina da cikin nan

Na saka hannu biyu ina jan gashin chest dinsa.

 Shiyasa ka ce na daina zuwa da gudu ina rumgume ka idan ka dawo?

 Yap

 Me yasa baka fada min ina da ciki ba?

 Saboda fitina ta zaki yi, yanzu da kin tashi fita ki ce Baby yana son yawo, and kin san yadda nake kishinki bana son kina fita ko kadan

Na yi dariya, domin ya canka a daidai yadda yayi zato haka nake aiwatarwa, a duk lokacin da aljannun yawon suka motsa kuka kawai nake kasa masa na ce baby yana son yawo, idan har yana kaunar zaman lafiya a ranar dole ya kai ni yawo ko kuma ya bar ni na tafi gidanmu. Haka muka yi ta fama abinci ma sai an jera min shida bakwai sannan na samu wanda zuciyata take so, abu kadan ya bata min rai, ni kaina taka tsantsan nake da kaina balle kuma Kareem da har tsoron kallona yake domin zan iya cewa kallon be yi min ba haka dai har na shiga wata na takwas.




KAREEM POV.

Sautin kukanta ne ya tashe shi daga bachin da yake, ya mika hannu ya kunna bedside lamp sai ya ganta zaune tana kuka. Ya tashi zaune da sauri ya rikota.

 Hey Beautiful me ya faru?

Ta ki ta yi magana sai kuka take, sauka yayi daga kan gadon ya dauki jallabiyarsa ya saka ya fita dakin be dade ba ya dawo dauke da ruwa ya rika kanta ya kai mata ruwan a baki ta sha, har tana sauke ajiyar zuciya sannan ya aje kofin ya zauna gefen gadon ya bude kafafufuwanta yana matsawa.

 Me ya faru? Mafarki kika yi marar kyau?

 Aa

 Me kike yi ma kuka? Baki da lafiya

 Lafiyata kalau, na tuna da lokacin da ka zo gidanmu ka ce wai wata yarinya kake so, kuma tana sonka sunanta Hafsa, kuma ka san ni ce miyasa baka fada min gaskiya cewa ni ce wannan yarinyar ba sai da na ji babu dadi

Kallonta kawai yake ya rasa ma me zai furta mata.

 Yanzu wannan abun shekara biyu da wani abu ba ki tono shi ba sai yanzu? Kuma miye abun kuka a ciki ai ke ce yarinyar

 Miyasa baka fada ba tun farko? Ka yi breaking heart dina

 Okay I'm sorry ba zan sake ba, Allah ya baki hakuri, yar kyakkyawata

 Dauko min riga na saka

Ta fada a shagwabe kamar mai shirin fashewa da wani sabon kukan. Ya sauka ya nufi wardrobe dinta ya dauko mata rigar da gown irin ta masu ciki mai free size.

 Bana son rigata

 Tawa kike so?

Ta daga mishi kai, sai ya juya ya aje nata rigan ya bude side dinsa ta dauko mata T-shirt dinsa ya saka mata daman ko ba ciki tana saka kayansa balle kuma tun da cikin ya fara girma kayansa take sakawa.

 Da short

Ya bude wardrobe dinta ya dauko mata karamin short ya saka mata.

 Shikenan? Ko kina bukatar wani abu?

 Ni ka daina tambayata idan ina bukatar wani abu ba ina magana ba

 Allah ya baki hakuri, na daina

Ya kwantar da ita a hankali sannan ya kashe wutar ya kwanta bayanta ya rumgumeta. Washe gari ma haka ta tashi da rigima there is one food she hate the most tun da ta samu cikin nan bata son jollop rice, as early morning take fadawa Kareem wai su daina girka abinci a restaurant din

Yana tsaye gaban madubi ya juyo ya kalleta.

 Saboda me?

 Ba ke ake girkawa ba?

 To bana dai sonta

Da ya karanci matarsa rigima take ji sai ya amsa mata da

 Okay zan fada musu su daina girkawa, shi kadai ko da wani?

 Shi kadai, amman Hubby ina son idan ka dawo da dare mu tafi shopping na siya turare

Ya juya ya kalli mirror dake cike da turaruka kala kala.

 Okay za mu je In Shaa Allahu

Ya sumbanci bakinta ya sunbanci cikinta sannan ya sake kissing front head nata ya ja hancinta.

 Take care of yourself sai na dawo

Ya fice yana dariya shi kadai, domin be tana samun kansa a cikin wannan yanayin ba sai yanzu, yara biyu da suka haifa da Yusura bata taba masa haka ba. Sai gwanarsa Noor.

Yadda yayi mata alkawari haka ya aiwatar misalin tara na dare ya dauketa suka tafi shopping mall gurin siyen turaren da be san ya zata yi da shi ba. Sai da ya fara fita ya zagaya ya bude mata ta fito tana sanye da hijab har kasa.


NOOR POV.

Ina tura cikina muka shiga ciki turare biyu kwai kamshinsu yayi min dadi na zaba sai wasu shoes da abaya, idan na zaba shi nake bawa har na gama muka nufi gurin biyan kudi muna tafe muna hira. Gafen da nake tsaye Abdull yake tsaye amman ni ban kula ba domin hankalina yana gurin kayan wata mata da ake dubawa. Kareem ya bar gefensa ya dawo nawa gefen ya tsaya ya shiga tsakanina da Abdull.

Kamin ya aje kayan hannunsa a gurin ya riko hannuna, sai a lokacin na lura da Abdull din da shi ma jiran yake a duba nasa kayan ya biya kudi. Kallona yyai sai yai saurin dauke ido kamar wanda ya rikice ya bar gurin ta koma cikin mall din. Kareem be sake ni ba sai da muka iso gurin motarsa ya bude min na shiga.

 Abdull ne ko?

Kamar yana jira sai ya rufe ni da fada.

 Dole sai kin fadi sunansa? Kina da alaka da shi?

 Aa

 Na yi nufin na zo na saka ki a mota ki kira ne sai na gama biya mu tafi, amman yanzu na fasa ba za'a siye kayan ba

Ya rufe min gambun ya zagaya side dinsa ya shiga yayi ma motar key.

 To ni miye laifina dan kawai na ce Abdull ne

 Kara fada kike yi?

Na yi shiru kamar zan yi kuka.

 Ka san ai ba kaunarshi ne ke ba, domin ba zan taba manta abun da yayi min ba da Hana, rayuwarsa ba zata kare da kyau ba

 Kadan ya rage masa ai, ko a yanzu ya halaka tun da ya rasa aikinsa da yake ya koma karantarwa a secondary school, kuma ya kwashi ciwo

Na zaro ido.

 Da gaske? Taya ka sani?

 Wani likita naje gani asibitin da naje awo, na ganshi layin yan HIV ko dai ya kamu ko kuma yana tunanin ya kamu ne, in ba haka ba babu abun da zai saka shi tafiya awo

 Amman tabbas shi ne?

 Shi ne mana Beb saboda na tabbatar sai da na duba files din ma na ga sunansa, saboda ya saka mask da facing cap ya rufe fuskarsa

Na yamutsa fuska.

 Daman karshen alewa kasa, Allah ya kara masa ya isar mana, da ma ya rufawa kansa asiri ya maida maitarsa sun zauna, ko da yake ita ma ba zata yarda ba saboda yana da ciwo yanzu ko?

Be amsa ni ba ya faka gaban wani mai tsire.

 Zaki ci na siya?

 Eh

 Okay

Ya siya mana na 5k sannan yaja motar muka yi gaba.

 Ai Safeena ma bata garin nan ko Hubby?

 Tana nan

 Ba kace ta koma garinsu ba? Kuma kace ta yi hadari?

 Eh amman bayan ta koma gida daga asibiti, last year suka yi gobara a gidan iyayenta suka rasu ita kuma ta yi kuna a jiki, sai mahaifin Abdull ya daukota ya dawo da ita garin nan daman shi ya rika ta ko lokacin da iyayen suke da rai

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, bayan watan nin da ta yi asibiti kuma da ta koma gida sai iyayen suka rasu? Wayyo Allah bata da yan'uwa kuma?

 Tana da su mana, amman shi baban Abdull din yayan mahaifinta ne ya rigata shiyasa ya sake dawowa da ita yanzu

 Ta ba ni tausayi

Na fada har a raina domin rayuwarta abar tausayi ce a yanzu. Kareem ya kai hannu ya rika hannuna ya cigaba da tukin da hannu daya.

 Be kamata ma ki ji tausayinta ba, kin san wutar da ta tashi a gidanku? She's the reasons

Na rufe baki da hannu daya.

 Taya ka sani?

 Zuciyata ta raya min haka daman, kuma na karanci hakan cikin kalamanta lokacin da muka yi fada, ta aiko kawarta ta fada min kuma yana neman magana da ke

 So har yanzu....

Na tambaya cikin kuka, domin na tuna da mahaifina da yar'uwata.

 Nononononononononononono Wallahi tun da muka rabu ban sake sakata a idona ba, ban san labarinta sai da kawarta ta same ni a office, kuma kawarta nurse ce muna mutunci a tsakaninmu if not ba zan ma tsaya na saurareta ba

Ya faka motar ya fita ya zagayo ya bude min na fito, ya dauki tsiren ya riko hannuna muka shiga ciki ina kuka, kan tebur ya aje ledar ya zauna kusa da ni ya rungume ni.

 Idan ni na mata laifi me Baba da Hana suka mata?e yasa zata kashe min mahaifi da yar'uwa?

 Ke ta yi nufin kashewa sai kuma baki kwana a gidan ba, kukan ya isa haka Beb, i already told you no more tears

Ya rumgume ni tsantsam a kirjinsa yana shafa bayana alamar rarrashi...

Na dago daga jikinsa na kalleshi.

 Ina son na ganta

Ya kama fuskata da hannu biyu ya rike.

 Baki bukatar ganinta Love

 Ina son na ganta, ina son na yi magana da ita

Yatsunsa ya saka yana share min hawayen da saukowa.

 Saboda me amman?

 Ni dai kawai ina son na ganta

 Zan yi tunani akai, yanzu manta da ita bari na bude miki namanki ki ci huh

Ya sumbanci bakina.

 Ka dafa min indomie sai ka saka naman cikin ka saka kwai

 Okay

Ya sake ni ya mike tsaye sai na riga hijab dina sai ya rika min na cire na koma daga ni sai skirt da T-shirt dinsa dake jikina. Ya aje min hijab din da dayan bangaren sannan ya nufi kitchen ni kuma na mike kafa ina kallon tv amman hawaye nake kewar mahaifina da yar'uwata.

Tun da ya shiga kitchen din be fito ba sai da ya gama, a lokacin da ya hango hawaye a idona sai ya zo da sauri yana kallon fuskata.

 Na dade gurin dafawa ne?

Na girgiza kai alamar aa.

 Minene?

 I miss my Dad i miss my sister

 Wannan dalilin ne ya saka bana fada miki wani abu Beb, bana son hawayen nan na ki da tashin hankali

Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login