Showing 69001 words to 72000 words out of 227321 words

Chapter 24 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1531

Mamaki ya kara kama shi har zai yi rejecting sai kuma ya amsa da zimmar yi mata fada.

 Noor What?

 Noor....

Safeena ta furta sunan daga dayan bangaren sannan ta cigaba da magana da murya mai ban tausayi da lafazi mai karya zuciya.

 Yarinyar nan ta yi nasarar shiga tsakanina da kai Kareem, ina ji ina gani ka juya min baya hankalinka ya koma gurin wata karamar yarinya, ka mata soyayya da ke tsakaninmu, fada min ba zaka cutar da ni ba ashe karya ne? Cewa auren dole aka maka ma karya ne, domin gashi yanzu zuciyarka ta bude har ka fara son ta, ni kuma ka raya ni da soyayyarka irin rayuwar da yau zan iya aikata komai saboda kai, ka saba min da rabar jikinka, na saba da mu'amala da kai ina gamsuwa fiye da mijina, rashinka ya saka na auri Abdull amman son ka be bar ni na ga laifinka ba, kaunarka bata bari na samu salama ba har sai da na rabeka, yanzu kuma ka juya min baya a karo na biyu, tsawon wata bakwai ban samu kebancewa da kai ba Kareem gaba daya ka sauya min, baka daga kirana baka maida amsar sakona, idan ina son ganinka sai dai na kama hotonka ko kuma na shigo motata na zo na faka a restaurant dinka ina shiga ko fitarka, shin baka tunanin ka azabtar da Ni? Kana ganin hakkina ba zai bibiye ka ba? You don't care how bad it hurts, kanka kawai ka sani Kareem? Ka yi hakuri mana son ka ba zai bari na yi rayuwa mai tsawo a duniya ba zan tafi sai ka so wata sai ka auri wata amman ina raye? Abdull gangar jikina kawai yake aure amman ruhina yana tare da kai.. Kareem ina zaka kai hakkina? You broke me first...


Gaba daya sai jikinsa ya mutu iska ya busar daga bakinsa zuwa sarari.

 Noor... Sorry Safeena abun ne yayi yawa, kina da yaya ni ma ina da su, kina da miji amman mun biyewa shedan muna jefa kanmu a halaka, tun da Momy ta kawo ni a duniya ban tana aikata zina ba, kawai na biye miki ne saboda na faranta miki rai, na san na cutar da ke da farko amman ba kudirina kenan ba, kaddara ce ta zo mana a haka kuma ba zan iya cewa Momy aa ba, kuma da ace na san tun farko Momy ba zata yarda na aure ki ba ba zan zurfafa a soyayyarki ba, balle har mu wahala da yanzu ba mu kawo a wannan matsayin ba, da za ki fara tunanin haihuwa da ni alhalin kina da aure...

 Shi ne kawai matsalar? Ba zan sake yi ba, i need to see you now i miss you so much, zan zo gidanka yanzu

Yayi saurin tariyar numfashinta.

 No karki fara ba mu taba haka dake ba, and ba mu gida ina gurin Momy

 Zan zo gurin Momy din ko kuma ka zo k same ni a inda muka saba haduwa, ba zan iya bachi ba a yau sai na ganka Kareem...

 Zan yi tunanin

 Zan zo yanzu Wallahi ba zan bari wata macen ta karbe min kai ba...

Ta yanke kiran, ya duba wayar ya sake kiran layi bata daga ba ya sake kira bata daga ba. Juyawa yayi ya koma cikin falon, be kalli kowa ya wuce kitchen ya wanke hannunsa ya zari tissue ya goge wayarsa ya goge hannunsa sannan ya fito, ba tare da ya zauna ba ya kalli Yusura ya ce.

 Tashi mu tafi gida

 Lafiya?

Ta bukaci sani. Ya daga mata kafadunsa.

 Lafiya mana, by this time muke tafiya gida i think?

 Noor din ce ta kira?

Momy ta tambaya, sai ya kalleta.

 Eh tsabani suka samu da Hafiz, ina son na sauke Yusura gida sai na je na yi magana da shi

 Ya kamata kam, ana shirin daura aure gobe ne ko jibi kuma ace an fara samun tsabani, ai ba dadi

 Allah ya kara sauki Momy sai na shigo gobe da safe

Yana fada yana aikawa Safeena sakon cewar zai zo ya same ta a inda suka saba haduwa. Shi ya fara fitowa ya shiga motarsa yayi mata key sannan Yusura ta karaso yaranta na yi mata sai da safe ya shiga motar yaja yana daga musu hannu. Tun da suka shiga motar bata ce masa uffan ba shi ma kuma be kalli gafen da take zaune ba har suka isa gidan. A haraba ya faka ta bude ta fita yayi reverse ya sake ficewa daga gidan.
Ya hau titi da zai kai shi guest house dinsa bangaren da ya fi kyau na zuciyarsa na nuna masa illar hakan yana sanyaya masa jiki. Sashen da ya fi muni na nuna masa halin da Safeena zata shiga idan be tafi ba, domin ta siye kwarin guiwarsa da kalamanta na dazun. Ya kasa zaba tsakanin daidai ta akasin haka shedan ya shiga ciki har dayan bangaren ya rinjaye dan'uwa ya faka a harabar gidan bayan mai gadi ya bude masa gate. Motarta ya fara kallo ya sauke ajiyar zuciya kana ya bude tasa motar ya fito ya rufe cikin rashin kuzari ya doshi kofar. Kamar an masa dole haka ya kai hannu ya murda kofar ya bude ya shiga, da wani irin fitinannen kamshi ta tarbe shi wani kalar sexy perfume ne mai daga hankalin namijin da ya amsa sunan Namiji. Kofin ruwan dake hannunta ta aje ta mike tsaye ta nufo inda yake cike da zumudi jikinta har rawa yake idanuwanta suna auna marmarin Kareem da ta yi. Kamin ta karasa ya zuba hannanyensa duka biyu aljihu a kokarinsa na hana kansa taba abun da ba halalinsa ba. Bata tsaya komai ba ta rumgume shi, daman ya san ba zai iya hana ta aikata hakan ba amman zai iya hana kansa taba jikin matar da ba tasa ba.

 Na yi marmarinka...

Ta sumbance bayan ta dago daga jikinsa sannan ya sake rumgume shi wuyanta a kafarsa, har sai da ya runtse ido saboda fitinar da turarenta yake kaiwa hancinsa, ta san weakness dinsa turare da Physical touch, hakan ya saka ta sumbantar wuyansa har sai da tsigar jikinsa ta tashi. A karo na biyu da ta dago daga jikinsa sai ta zuba masa ido har sai da ya bude nasa idon ya kalleta. Sai ta cire dankwalin dake kanta kananan kitson dake kanta suka bayyana, numfashi ya sauke a hankali ya hade yawu slowly, yana marmarin abun da ya kwashe wata 8 be hada numfashi da Yusura da nufin shi ba. Bakinta ta kai saitin sansa ta san ba zai hana ta ba kuma ba zai iya gujewa haka ba, in less than second he lost control again. Hannayensa ya cire daga aljihun ya rumgumeta ya fara mayar mata da martani tun suna tsaye har tsayin ya gagara suka zauna daga bisani suka canja musalli daga Sitting room to Bedroom...



NOOR POV.

Ban kwanta da nufin farkawa ba, fata na yi idan na kwanta kamin safiya Allah ya karbi rayuwa. Sanin yau ce ranar daurin aurena sai nake ji kamar ranar mutuwa zata fi min farinciki fiye da wannan ranar da za'a daure da igiyyoyin aure. Misalin karfe bakwai na safe Anty Larai ta kawo min wani kaza mai tsananin daci wai na cinye ni kadai kuma kar na rage ko kadan. Tana fita na na saka yara suka debo min ruwa a bota na na nade kazar a dankwali na shiga bandaki na jefa a shadda sannan na dawo dakin na zauna kamar na ci. Ba a jima ba aka sake zuwa da mota aka dauke ni zuwa gidan wata mai lallen. Ban dawo ba sai Azahar bata min da yawa ba amman yayi matukar kyau domin kwarariya ce mai yi ma mare kunshi.
A lokacin da na dawo gidan na tarar da yan'uwan mahaifiyata suka fara shigowa sai kewarta ta kama ni, na ji ina ma ace tana kusa da ni wata kila zan ji sanyi fiye da kuncin da nake ji a yanzu, a jikin Mama Shafa na kwanta kaina na ciwo sosai kamar zai rabe gida biyu, hakan kuma ba zai rasa nabasa da rashin samun bachi da kuma tunanin da ke kokarin fi karfin kwakwalwata. Ban damu da sanin yaushe daurin auren ba abun da kawai na sani shi ne yau za a daura auren ko ma aka daura. Domin ban dade da shigowa ba ina daga kwancen a cinyar Mama Shafa na hango shigowar Yaya da Baba da kuma wasu daga cikin iyayena maza cikin shiga ta manya kaya sai gabana ya fadi, kuka ya rufe ni na kasa rike kaina ina ta kuka sosai jikina ya fara rawa numfashi yana fita da karfi. Wai yau da wani aka daura aurena ba da Zafeer ba Wallahi ban taba tsammanin haka ba. Yan'uwan Mama suka yi ta rarrashina suna kwantar min da hankali har suka samu na yi shiru sai dai na ci kuka kuma kuka ya ci ni har idanuwa sun sauya kala.

Har aka ci aka cinye ni dai bana wani kwarran motsi kuma bana da walwala balle sakewa ga wani irin tsoro da fargaba da ya rufe ni. Ba yi wani wuni da na ga saurin karewarta irin ranar yau Assabar, kan kace kwabo har hudu ya fara shigowa ana maganar a tafi da ni na yi wanka na shirya kamin masu daukar amarya su ta iso. Wani gidan na makota aka tafi da ni, amman na kasa wanka haka na zauna a bandakin ina ta rusar kuka har aka gaji da jira aka shigo aka fita da ni. Haka na sake saka wasu tufafin ba tare da na yi wanka ba domin bana iya komai babu kuzari a tare ba. Na samu kaina cikin wani irin rashin hankali da bakinciki na rabuwa da wanda nake so da kuma auren wanda bana so! Ashe haka abun yake ashe haka ake ji, wata sabuwar rayuwa zan shiga wani matsayi zan taka amman ba da wanda nake mafarki ba.
Wani ya zo ya mana shigar rago ya shafe tarihin da muka so kafawa, ya rusa gina da muka fara, ya dauki ajiyar da ba ta shi ba.

Bakinciki be kara rufe ni ba, sai da Baba ya tsaya kai da fata akan cewar ba za tafi dani gurin Mama da sunan ta yi min huduwar aure ba, idan ba zata tako ta zo ba to be yarda akai ni, duk yadda dangin mahaifiyata da wasu daga danginsa suka so ya bari na tafi hakan ya ci tura, domin Baba murdadden mutum ne idan y tsaya kan abu baya sauya. Ina ji ina gani aka hana ni ganin uwata har yan'uwan Mama suka fusata suka yi fada da Baba kacha kacha babu dadi. Bayan sun tafi na koma jikin Hana ta rumgume ni ita kuka ni kuka. Yaya ya shigo dakin ya mika min wayar

 Ga Mama zata yi magana da ke

Na karbi wayar na kara a kunne na saka hannu biyu na dafeta a kunnena na kwanta a kasa ina jin kamar ina kwance a jikinta ne...

 Mama... Mamma... Mma... Mmama... Ma

Na fada cikin wani irin kuka mai sarke numfashi.

 Noor ki yi hakuri haka Allah ya kaddara, kuma ki yi biyayya ga mijinki ni na yafe miki duk abun da kika min, Allah ya miki albarka... Ki roki kowa yafiya haka ake idan za'ayi aure

Daga karshe sai ta fashe da kuka ni ma na fashe da kuka ina kiran sunanta. Bayan ta kashe ya dago na mikawa Yaya wayarsa.

 Yaya dan Allah kai ma ka yafe min

Ya rage tsawonsa ya rumgume ni.

 Na yafe miki Noor, na fi kowa son farincikinki, Allah ya auren wannan shi ne mafi alheri fiye da Zafeer shi kuma ya ba shi wata wadda ta fiki zama alheri a gareshi, ki yi hakuri Noor kin ji ki yi hakuri

Na sha kuka a jikinsa sosai sannan ya sake ni ya fita, Hana kam kasa ce mata komai na yi ni da ita muka rika kuka kamar an mana mutuwa muna rumgume da juna. Har sai da Baba ya shigo ya fara min huduba tare da yan'uwansa shi ma na roke shi yafiya ya yafe ya saka min albarka da addu'ar Allah yasa gurin zamana ne. Manya motoci na alfarma aka jera daga kofar gidanmu zuwa gidansu Zainab, gurin fitowa da ni ne ya zama aiki na kama Hana na rike gam ita ma ta rike ni daker aka banbare ni a jikinta aka saka ni motar, kuka be barta ta bi ni ba sai Gwaggwani da suka shiga motar tare da ni suna min fada wai sai kace kaina farau aure ina wannan kukan na tashin hankali.
Daga gidanmu aka dauke ni zuwa gidan da za a rusa farincikin.


I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne. If you want to subscribe Pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

Or

6484787074
Khadeeja Candy
Moneypoint

And send the evidence of payment to 08036126660

See you>?p? ' #KhadeejaCandy
PAID PAGE 4??


?KhadeejaCandy
??Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______" " " _______


Zaunawa yayi bakin gadon yana kallona.

 Noor dan Allah ki kwantar da hankalinki, abun nan be kai yadda kike tunani ba, kuma ke ba fa jaririya ba ce da za ace idan zan matsa kusa da ki ri rika ihu kina daga hankalinki kamar yar shekara shida, haba Noor tun yaushe muke abu daya gashi har yau nake shirin barin dakinki? Hmmm i promise you i won't hurt you

Ya miko hannunsa gaba daya sai na ji hankalina ya kara tashi, ko da ace ina son shi yadda Aisha ta fada min halinshi yake da yadda zafin abun yake dole na tsorata balle kuma bana son shi.

 Zo mana Noor...

Na matsa can nesa ganin ya mike tsaye, ina ganin ya doso inda nake ya rikona na fara masa ihu iyakar karfina irin da na tsira yi masa a duk lokacin da ya nuna zai yi forcing kansa a gareni, sai dai a duk lokacin da na fara ihun yana saurin saki na ya kyale ni ba kamar wannan karon ba, da ya rike sai ya rikide min kamar ba shi ba ya sakar min karfinsa na kasa motsa hannuna ma ihun kawai nake iya yi, kamin mu ji ana dukan kofa da karfi kamar za a ballata, can kuma aka dawo gurin windows din ana bugawa da karfi. Sakina yayi dan dole ba dan ya samu abun da yake so ba, ya sauka daga kan gadon ya dauki rigarsa ya saka ya bude kofar dakin ya fita, ni kuma na tashi zaune na gyara rigata na ina jan numfashi da karfi. Aisha ce ta shigo dakin da gudunta

 Noor Lafiya?

Na rumgume jikina ina hawaye sai ta juya ta kalleshi.

 Barristers miye haka? Da yamma haka? Wane irin rashin hakuri ne? Sati daya da aka yi a bangarenta be wadatar da kai ba sai ka nuna mata fin karfi da ido na ganin ido? Kowa ya san halin da kuke ciki? Mai gadi ne fa ya fada min ihun da yake ji a nan yayi yawa naje na duba? Yanzu wannan ba abun kunya ba ne? Kuma duk zaman da ka yi be wadatar ba sai ka shiga hakkina? Yau fa zaka bar nan, daga yin auren kuma sai ka fara abu kamar karamin yaro ko wanda ya fita hayyacinsa? Me kake haka Barristers kanka farau auren budurwa?

Ta fashe da kuka ta fice daga dakin, sai ya juyo ya watso min wani mugun kallo.

 Kin ga abun da kika ja ko?

Na sauke kaina kasa.

 Ke wai wace irin yarinya ce? Wawuya kawai sakarya, marar hankali marar tarbiya

Uffan ban ce masa ba, ba dan kuma bana jin zafin kalaman nasa ba, sai dan na san nice marar gaskiya a nan, be kamata na yi ihu ba amman kuma kiyayyarsa da tsoron da matarsa ta ba ni ba zai bari na zame masa yadda yake so ba. A fusace ya fice daga dakin, ni kuma na kwanta a gurin ban tashi ba sai da aka yi kiran sallah Magariba bayan na yi sallah na fito daga dakin na sai na samu plate din abincin da ya zuba a dazun aje a gurin, kadan na ci na ji gishiri kamar zai yanka halshena da sauri na zubar kasa na kasa hadewa na nufi kitchen da sauri ina taba kofar na ji ta a rufe da makulli a dole na dawo dakina na shiga bandaki na wanke bakina ina mamakin yadda gishiri yayi yawa haka domin na dandana abinci a lokacin da na gama girkin ban ji gishiri haka ba. Dawowa na yi na zauna a dakina domin zuciyata bata raya min cewar Aisha zata iya kara min gishiri a abinci ba balle na zarge ta, da ma dai ace bama zaman lafiya ne, wata kila kuma jika yayi a yanzu shiyasa yayi yawa.

Bayan sallah Isha'i na sake fita na taba kofar kitchen din sai na same ta a rufe da alama da Hafiz ya rufe kitchen yayi tafiyarsa ya bar ni da yunwar cikina. Ni nake kamar zan iya jurewa na dan lokaci ne zai hakura ya dawo min da keys din ko kuma ya shigo ya bude min idan ya gaji. Saboda haka na shiga dakina na kwanta cikin tsoro domin wannan ne karo na biyu da na kwanta ni kadai a bangaren bayan kwanan da na yi na daren farko a?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? gidan. Washe Gari na farka da tunanin yadda za'ayi ni ma kanwata Hana ta zo ta rika taya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login