Showing 33001 words to 36000 words out of 227321 words

Chapter 12 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1556

nan? Kai kam uwar da ta haifo ka ta iya haihuwa, Allah mai iko na gode na gode Allah ya saka da alheri


Baba ya kai kasa yana masa godiya har da kuka, ni kam mamaki ya hana ni rufe bakin sai kallon ikon Allah nake. Muna hada ido da Kareem na sauke kai kasa na bata fuska, domin abun da Baba yayi be min dadi ba, ina jin yin haka ba daidai ba ne. Sai dai ba babu bakin yin magana baba ya dafa ni danya ya cinye. Kareem ya sauke hannunsa a hankali kasa yayi yana motsa agogonsa har sai da na dago na kalleshi sai ya daga min gira daya irin na wadda ke tambaya a boye. Ban ce komai ba daman ni me zance a gaban Baba ko ba a gabansa ba ne na riga na daina duk wani abu da be shafe ni ba.

 Baba anjima Nabill zai kawo Noor asibiti a sake daure hannu saboda ba son a kwance har sai ta ji sauki, kuma kar ayi wasa da maganin da na kawo

Na ji Kareem yana fada, sai na lake kafada daya bacin ran nawa ya kara bayyana na saka kuka a take.

 Aa Wallahi ni bana so, akwai zafi sosai

 Aa ba sake taba hannun za'ayi ba, daurewa kawai za'ayi

Ya amsa min hakan be canja kudurina ba na girgiza masa kai.

 Ni dai bana so a bar shi a haka

Baba ya juyo kaina kamar mai jirana.

 Aiko sai kin so, ka ga sakaryar yarinya ko? Haka ta da sakarci, ba da zafi ake cire zafi ba, shashashar yarinya kawai

Kareem ya kira sunan Baba a hankali sannan ya ce.

 Baba dan Allah ku daina kiranta da sunaye marasa kyau, kamar yanzu kace mata sakarya, su iyeye kamar wani bakin tabo ne a jikin farin tufafi duk yadda ya diga sai ya bayyana, shiyasa ake son a rika taka tsantsan da kalami, yara basa jin magana mun sani dukanmu muna da su, amman a haka muke kai zuciya nesa idan ba haka ba, sai mu yi barna kuma a karshe dai mu din ne za mu wahala, misali yanxu kana kiranta mahaukaciya to ba zata taba yin hankali ba, ko da kai mutanen unguwa ne suke mata wannan ikirarin balle mahaifi. Amman fa ka yi hakuri na shiga tsabgar da ba tawa ba

 Aa ai gaskiya ka fada, haka ne Wallahi ai bakin ne ya saba kuma ita wannan Noor din idan ka zauna da ita na wuni daya, In Shaa Allahu sai ka ji ta gundureka saboda bata jin magana sam, shiyasa ma nake so na aurar da ita na huta

Na kalli Kareem sai na rufe idona ina jin kunya ta rufe ni, ta dayan bangaren kuma ina jindadi, ni kaina ai na fi son ayi min auren ma na huta domin na san Zafeer ba zai min abun da ake min a gida ba, shi ba zai taba gajiya da ni ba.

 Baba yanzu, Noor tana da wadda zata aura kenan?

Abokinsa ya tambaya. Sai Baba ya ce.

 Shekara uku da yin baikonsu kuwa, amman har yanzu be shirya ba, ni ai idan be gama shiri a cikin lokacin nan ba to sai dai ya hakura da ita domin so nake na aurar da ita In Shaa Allah, Yaya yayyuna da suke kauye sa'aninta duk an musu aure

Na bude ido ina kallon abokin da ya kalleni yayi murmushi sannan ya juya yana fadin.

 Gaskiya kam idan ka aurar da ita hankalinka zai fi kwanciya, ita daman ya mace gidan aure aka santa

 Shiyasa ai nake son ayi komai na huta ta huta

Allah ya gani ni dai sai na ji na tsani abokin Kareem din nan ko ma dan'uwansa ne oho domin ya bawa Baba shawarar da ba zata taimaka wajen gyara soyayyata da Zafeer ba sai dai ma ta bata abun.

Suna daf da ficewa Kareem ya juyo ya dago min hannu kasa kasa. Ni dai kallonsa kawai na yi ban yi wani Yunkuri ba har ya fice. Fitar ke da wuya Mama ta fito daga dakinta da ta boya ta zauna a inda suka tashi tana fadin.

 Malam an samu hanyar kudi ina jin suna magana, baya ko tunanin gaskiya ta bayyana ya ji kunya

Hana ta fito daga dakinta ita ta zauna kusa da ni tana fadin.

 Mama ai kara da yayi haka wa zai bari wannan damar ta wuce shi haka

Mama ta tabe baki.

 Kudin me za su amfana mana Hannatu? Ai ba za su wuce ya bamu na cefane, sauran kuma idan be kara aure ba, su kare a gurin zaurawansa tun da Allah be raba shi da ganin mace ya ce yana so ba, ko ba shi ko sisi kuwa balle wata hanyar ta bude

 Shi ne kawai abun da yake bata min rai da Baba, wasu iyayen idan suka samu sai ka ga iyali sun wadata amman shi babu ruwansa da mu

Ni dai ban ce komai ba gudun kar na saka baki na fadi wata maganar ace na bata ran Mama ko Hana. Can na ji Mama ta ce.

 Ni ko wannan mutunen sai na ke jin kamar da biyu suke mana wannan dawaniyar

Na kalli Hana dake tambayar Mama

 Kamar Yaya Mama?

 Ta ya mutum zai shigo cikin gidanku haka nan kawai yace zai siye muku gida? Ko dai yana son ya bukaci auren Noor ne ko kuma wani abun dabam haka siddan kace zaka siyawa mutum gida daga zuwa? Kalli yadda yake kyautar kudi kamar tsintarsu yake

Na kalli Mama.

 Ya san ina da Miji na fada masa ina da Miji, kuma ya san Zafeer har ya kira min a waya lokacin da wannan abun ya faru

Mama ta bude baki ta sake magana sai ga Baba ya shigo baki har kunne.

 Kai kai kai Noor yau dai rashim jin maganar nan naki ya janyo mana alheri, gidan nan zai siya min, Allahu Akbar masu arziki na inda suke, ina ma ace ana ne wannan yaro

Mama ta ce

 Shi ma danka ba mu cire rai ba, wata rana inda rai da rabo zai maka komai Malam

 wannan Nabil din ko ya samu ai sai dai ya bawa uwarsa, ai baya kaunata sam bana saka rai ma

Ban yi furucin Baba ba, daman shi be yarda yayansa za su iya kawo masa abun arziki ba musamman ma ni.

 Yanzu Malam yarda ka yi ka karbi kudin gidan da yake naka? Wannan abun da ka yi zubar da girma ne be dace ba

 To... Wato na bari rabo na ya wuce ni kenan? Amman dai Hajara ba ki da hankali garabasa ce fa wannan sai kuma na bari ta wuce ni?

Mama ta sauke ajiyar zuciya.

 Indai domin Noor yake yi Noor tana da miji, ba za mu watsar da zancen shekara uku mu zama kananan mutane ba, be kamata ba Wallahi, yaron nan yana sonta kuma yana iya kokarinsa akanta

 Kokarin me yake da ita? Tun da nake da shi ya taba daukar dubu goma yace Baba gashi ka siya wani abu? Shi dai yana sonta kawai amman babu wani hidima da yake, kuma na zancen aurenta da yaron nan kika ji na yi ba har kike wannan maganar ke dai kam Hajara ba dan ina mijinki ba sai na ce hassada kike min, ke dai baki farinciki da samu na, ba ki son jin alherina, ina zaton ganin farinciki a fuskarka sai ki tare ni da wani zancen banza karuwa da zane! Ai da har ina cewa ko zane daya ne ya kawo ayi musu aure to yanzu na fasa yayi mata komai kamar yadda ake yi ma kowa, yau din nan zan kira shi na fada masa na shirya aurar da Noor, kudin gidan nan da za a bani ai sai na tsakuri wani abu a ciki na yi mata hidima sauran kuma na yi lalurar dake gabana, ba a bori da sanyin jiki kuma ice tum yana danye ake tankwara shi idan ya shirya ya fito kawai kamin kudin su kare

 Malam ina fada maka gaskiya ne kawai bana adawa da samunka, duk mace ta gari tana burin samun Mijinta musamman idam yana kyautatawa a gidansa

 To ni bana yi, Wallahi ba dan yau ina cikin alheri ba babu abun da zai yana na bata miki rai yanzu nan, shashashar mata kawai

Ya ciro wayarsa yana fadin

 Bari na kira dan iskan yaron nan ko yanzu sai da Alhaji yayi min maganarsa, kuma duk laifinki ne ke kike goyo masa bayan yi min rashin kunya

Ni dai ba zan iya cigaba da sauraren jin tsabani da sa'insa tsakanin uwa da uban da suka kawo ni duniya ba, dan haka na tashi na shige dakinmu na kwanta ina kallon ceiling, wata zuciyar na fada min idan ma taimako Kareem yake son yin to ba Baba ya dace yayi ma.




KAREEM POV.

Sai da suka shiga mota sannan Kareem ya kalli Hafiz ya ce

 Miye dalilinka na yin haka?

Hafiz ya kalleshi kamar be san abun da yayi ba.

 Me ba?

 Siya masa gida mana

 Oh taimako ne, after ma na siye zan gyara masa shi, ina da halin yin haka ya kamata na yi

 Me yasa baka yi ba tuntuni sai yanzu

 Saboda Noor ne

Hafiz ya kure tambayarsa dan haka yayi shiru ba dan ya gamsu ba.

 Wai ni kam ya aka yi kace a kawo maka Noor?

Hafiz ya tambaya yana taba agogonsa.

 Na ga alamar kamar tana son magana ne, kuma tana tsoro, and gaskiya ne ai dole za a sake daure gurin saboda kai ya ki warkewa

Hafiz yayi murmushi. Sai Kareem ya ce.

 Ba abun da kake tunani ba ne Hafiz, ba zan iya neman aure a cikin aure ba, Annabi ya hana, na san yadda ake ji idan ka rasa wadda kake so, ba zan yi kuskuren aikatawa wani ba, na auri wadda bana so ban ci da dadi ba, na bar wadda ke so na hakan ya jefa ni a matsala ba zan so hakan ya faru da kowa ba, indai saboda ni kake yi dan Allah ka daina Hafiz

Hafiz yayi kamar ba da shi Kareem yake magana ba ya kawar da kai dayan gefen yana jin haushin yadda abokinsa yake fadar Amnabi ya hana amman shi yake aikata abun da kisan kai da shirka sai yi da wani ne ya fi shi zubuni. A gida ya sauke Barrister sannan ya kama hanyar zuwa gurin aikinsa. Be fito asibitin ba sai karfe biyu, gidansa ya nufa kamar yadda ya saba yana shiga ya samu matarsa zaune a tsakiyar falon tare da yaransa, suna ganinsa suka taso da gudu suka tarbe shi dai ya daga su sama ya subance su sannan ya rika hannayensu.

 Baku tafi Islamiya ba?

 Yanzu za mu je, idan mun gama cin abinci direba zai kai mu

Tine ta fada tana tsalle ya fadada murmushinsa.

 Yayi kyau, Allah ya muku albarka ya tsareku ya shirya min ku

 Amin Daddy, anni Daddy

Tine ta amsa sannan Areef ma ya amsa, sai ya mike tsaye ya nufi inda suke cin abincin ya zaunar da su ba tare da ya kalli Yusura ba ya ce.

 Madam sannu da gida

Ta yi murmushin dole saboda yaranta suna kallonta amman amsa masa ne take jin be zama dole ba. Shi ma dai yana yi duk abun da yake ne saboda yaransa kuma saboda ya bata hakkinta. Sama ya nufa ya shiga dakinsa rigar jikinsa ya fara cirewa sannan ya nufi bandakin ya cire wandon yayi wanka ya fito ya sake shiryawa ya saka wasu tufafin sannan yayi sallah. Yana kokarin mikewa tsaye Noor ta fado masa a rai, sai yayi murmushi yana mamakin yadda bata yi surutu ba a yau, wata kila saboda tana tsoron Babanta ne ko kuma dai ta shiryu din ne kamar yadda ta yi ikirari, amman yadda ta natsu nan babu surutu sai ya ji duk ta ba shi tausayi kuma sai ya ga kamar ba ita ba. Kwantawa yayi saman gadonsa ya dan taba chat for like 30min yana ganin Safeena ta hau online sai yayi saurin kashe data ya sauka ba tare da ya bude sakonta ba, ba kuma dan be bukatar hakan ba, domin be saka nuna mata rashin kulawa ba, amman a yanzu yana kokarin ganin ya gujewa wasu abubuwan ne kamin ya san matakin da zai dauka a gaba, so yake ya saba mata da wasu hayyarsa da bata san da su ba, shakuwar dake tsakaninsu ta ragu.

Saukowa yayi ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin cikinsa na kukan yunwa, domin ya san ko yunwar zata kashe shi a gidan nan Yusura ba zata shigo dakinsa ta kawo masa abinci ba sai dai ta aje masa a dinning, shi tun da suka yi aure yau shekara bakwai be san wata rana da Yusura ta taba shigowa dakinsa yana ciki ba, ko gyara dakin da take takan gyara ne kawai idan baya ciki sai dai idan ya dawo ya tarar an share ko'ina an gyara. Sai dai shi yana leka nata dakin sau daya a wata idan zai sauke mata hakkinta, ya sauko downstairs da kuzarinsa ya nufi kofar fita falon.

 Ga abincinka a dinning

 Yarana sun ci ya wadatar, ni zan ci a waje

Ta tabe baki ta dauke kai ta cigaba da kallon da take daman yaran suna gama cin abinci suka wuce Islamiya. Cikin motarsa ya shiga ya zauna yayi shiruuuuuu yana nazarin rayuwa, kamin kira waya ya katse masa hanzari. Ganin number Nabil ya saka shi murmushi domin baya kiransa sai da wani babban dalili, a yanzu kuma ya san dalilin ba zai wuce Noor ba kawar nishadinsa.

 Hello

  Ranka ya dade barka da wuni

 Bakar Nabil ya kake?

 Lafiya Kalau ranka ya dade

 Ina fatar kun samu fahimtar juna tare da mahaifinka

 Komai ya wuce ina godiya Oga

 Toh Alhamdullahi ina Noor

 Eh daman saboda ita na kira, dubata da kace zaka yi nace kana asibitin yanzu mu tafi

 Ba sai kun je asibiti ba ka kawo ta, restaurant zan zo da abun daurin a nan idan na daure mata sai ku tafi

 Toh Oga

Ya kashe wayar sannan yayi ma motarsa key, Asibitin ya fara zuwa ya dauko abun bukata sannan ya nufi restaurant dinsa. A reception ya same Noor zaune a kujera zaune tana raba ido da alama shi take jiran bullowarsa. Suna hada ido ta sakar masa murmushi shi ma yayi mata murmushin yayi tsammanin zata taso ta tare shi ne ko kuma ta bi bayansa sai be ga ta yi ko daya ba sai binsa da ta yi da kallo har sai da ya kirata.

 Noor

 Na'am

Ta amsa sannan ta mike tsaye ana ta kallonta ta nufi inda yake tsaye yana jiransa har sai da ta iso sannan suka jera suna tafiya.

 Ya aka yi na ganki yau kamar ba ke ba?

Ta kalleshi murmushi har zuci.

 Ka karramani...

 Da na yi me?

Ya tambaya da kamar mamaki sai ya washe masa hakora.

 Ka ce Noor a gaban mutane, kai ne fa mai gurin nan kuma ka kira ni a gaban mutane kuma ka tsaya ka jira ni har sai da na zo, ba ka ga kowa kallona yake ba sun dauka ni ma wata ce

Ta yi tsalle kadan ta dire tana jindadin da ya haifarwa da Kareem jindadi.

 Oh just? Abu kadan ke faranta ranki baki da matsala yarinya i like your style


Ya fada sannan ya saka key ya bude office din ya bude mata ta fara shiga sannan shi ma ya shiga.


NOOR POV.

tsayawa na yi har sai da yayi min izinin zama sannan na zauna, ina kallon yadda kananan kayan jikinsa suka karbe shi yayi kyau da har na kasa boyewa sai da na fada.

 Ka yi kyau, kayan ya maka kyau

 Thank you

Ya fada yana murmushi tare da aje ledar dake hannunsa sannan ya janyo kujera ya zauna, a yadda na lura yanayinsa kamar ba a yadda ya saba ba, na lura akwai damuwa a tare da shi, sai dai ban ce komai ba domin damuwarsa ba tawa ba ce.

 Zaki ci wani abu a kawo miki? Yunwa nake ji zan ci abinci sai na daure miki hannu

Har zance aa sai kuma na tuna wannan abincin fa Free ne idan ma ban ci ba ni nayi ma kaina.

 Eh amman ba zan ci gabanka ba

Yayi murmushi.

 Me za'a kawo?

 Zan iya fada da kaina?

Ya daga min kai sai na ce.

 To ka kirata na fada mata da kaina ba zan iya fada maka ba, kuma idan ta shigo ka rufe kunnenka karka ji dan Allah

Cikin saukin kai yayi min yadda nake so ya kira matar a lokacin da ta zo sai yaja kujerarsa baya ya ce.

 Face her

Matar ta fuskance ni shi kuma ya saka yatsa ya rufe kunnensa. Dadin da na ji a lokacin da yayi abun da ya bukata ya fi dadin da na ji a lokacin da ya yi min tayin abincin. Sai da na gama fada mata sannan ya dauke hannunsa ya fada mata abun da zata kawo masa, bayan ta fice na kalleshi na ce.

 Ka ji me na fada mata?

 No kin ce ai kar na ji

 Ce Wallahi baka ji ba

 Wallahi ban ji ba, ai kin ce kar na ji i respect that

 Ya aka yi ka gane na gama fada to?

 Ina karanta bakinki ne

Na yi murmushi ina kallonsa.

 Kana da sauki babu ruwanka kamar ba kai ne mai gurin nan ba

 I wish people knew

Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login