Showing 27001 words to 30000 words out of 227321 words

Chapter 10 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1504

Mama tace zata yanka ni? Ashe uwa zata iya kashe yarta? Na mike tsaye ina jin kamar wata murya na fada min na juya na fice daga gidan, sai dai idan na fita ina zan je? Wa zan je na roka ya bawa Mama hakuri? Yau ta yi fushin da bata taba yi ba, yau ta furta min kalmar gajiya, ta furta sao ta yanka ni, na tabbatar babu wadda zai ceto ni a yau na kwana da rai.

Na fito na tsaya daga bakin kofar gidan na raba jikin ginin na rumgume hannuna ina tunanin inda zan je. Kamar ance dago kai ina dagowa na yi arba da Hana tana kuka ashe tana cikin gidan amman ban ganta ba duk abun nan da ake.

 Ki tafi gidansu Maman Zainab ki kwana, dan Allah karki gudu ki karawa kanki laifi, Baba yayi min duka saboda na ki fadar inda kika je lokacin da na dawo daga makaranta har sai da na fada sannan ya kyale ni, Noor miye amfanin abun da kike yi? Dubi yadda kika sakawa kowa bakinciki yau

Ita ma dai bani da amsar da zan bata dan haka na duka na duka a gurin ina jin halshena yana zogi saboda marin da Yaya Nabil yayi min.

 Hannatu...

Mama ta kira da karfi, sai ta juya da sauri ta koma cikin gidan ta bar ni a gurin duke ina tunanin makoma. Can kuma na mike tsaye na nufi gidansu Zafeer domin ban san wani abun da zan yi ba, sai dai tunawa da ba lallai ne Mama ta hakura ba ko da ya mata magana ya katse hanzarina, a madadin shiga cikin gidan sai na mike na kama hanyar gidansu Kareem. Tafiyar da zan biya 200 a kai ni gidan ita nake yi a kafa ba tare da gajiya ko kasawa ba. Zan iya shaidar kaina ina ba basira da gane abu ko da kuwa sau daya na gani, hakan ya saka na yi saurin gane gidan sai dai na shiga unguwar a lokacin da sawu ya fara daukewa ne, bana da agogo balle na iya fadar karfe nawa, amman tabbas dare yayi domin mai gadin gidan ma hanani shiga yayi bayan na kwankwasa.

 Toh dan Allah ka fada masa Noor ce tana waje

Na bashi sako sannan na ja na tsaya ina jin tsoron wajen saboda babu kowa.

 Ki jira a nan ina zuwa

Ya rufe gate din ya bar ni a gurin tsaye, bayan dan lokaci na sake jin an bude kofar.

 Shigo

Na shiga cikin gidan, na doshi main door kamin na karasa Kareem ya fito sanye da pajamas ya nufo inda nake sai muka ci karo a tsakiyar gida.

 Noor lafiya?

 Mama tace sai ya yanka ni, tace yau ba zan kwana da rai ba, ta nuna min wuka kashe ni zata yi, Yaya yayi fada da Baba har ya koreshi saboda ni, kanwata ma an mata duka saboda ni

Ina maganar hawaye suna fadar yau ce ranar mu, jikina na karkarwa kamar mai jin sanyi. Shiru yayi yana kallona kamar mai tunani me zai fada ko ya aiwatar.

 Babana yana jin maganarka, Mama kuma tana jin maganar Baba, so nake ka tafi ka bawa Baba hakuri shi kuma ya bawa Mama hakuri ta yafe min, ka fada ma Baba ya fada mata daga yau ba zan sake ba, ka ce ina rokonta ta yafe min

Na fada masa bukatata.

 Waya kawo ki nan?

 A kafa na zo, ka yi hakuri ba zan sake takura maka ba daga yau ba zan sake batawa kowa rai ba

Ni dai ban san ya aka yi ba na jini na jikinsa ya rumgume yana rarrashina.

 Ya isa haka Noor I'm sorry

Ji na yi kamar na samu wata mafaka sai na fashe da kuka mai mugun karfi.

 Ya isa ya isa haka kar yarana su ji

Ya sake ni da sauri.

 Shigo ciki na canja kaya sai mu tafi gurin mahaifin naki

Na bi bayansa muka shiga cikin falon sai na tsaya daga bakin kofa ina kallon matarsa dake zaune tana cin abinci. Sama ya nufa be jima ba ya sauko sanye da jallabiya da hula hannunsa rike da keys.

 Wani taimako take son na yi mata, zan je na dawo yanzu

Ya fadawa matarsa, sai ta dubeshi ta dauke kai.

 Kai ka ta shafa, idan ka aikata abun kunya yayanka ne a kunya ba ni ba, ni matsalarka bata gabana

Amsar ta bata ba ni mamaki ba kamar yadda shi din ya ba ni mamaki ta hanyar dauke kai ba tare da ya ce mata komai ba ya kalleni ya ce

 Mu tafi

Na juya na fara fita sannan ya fito, sai da ya janyo mota sannan na bude da hannun hagu na shiga domin na dama a daure yake. Tun da muka shiga motar be ce min komai ba, ni ma ban ce masa ba muka isa unguwar yanayin yadda na ga mutane sun rage ya tabbatar da dare yayi sosai.

 Ina zamu samu ganin Babanki a yanzu?

 Yana zama a majalisa kamin ya shiga gida

 Ina majalisar take?

Na fada masa sai ya bude motar ya fita yana kara tambayar kwatancen domin be san kan unguwar ba.

 To jira ni a nan

Na daga masa kai na bishi da kallo har na daina hangoshi. A kiyasina za'ayi minti talatin da fitarsa sannan na hango bullowarsa tare da Baba dake rike da fitila duk da kasancewar akwai wutar nepa. Na bude motar na fito ina kallon Baba.

 Ah ah Noor to ai da sauki ma tun da gurinka ta tafi, da ta fi duniya ai shikenan to zo mu tafi gida

Na nufeshi ina jin tsoro, Kareem kuma ya koma cikin motar ya zauna har sai da muka yi nisa sannan ya biyo bayanmu. Baba ne ya fara sallama ya shiga cikin gidan sannan na bi bayansa.

 Ke Hajara fito ga Noor din gata nan ki yanka ta

Da gudu na ga Mama ta fito har sai da na tsorata naja baya.

 Noor ina kika je?

Ta tambaye ni tana kuka

 Ina kika tafi na aika nemanki ko'ina baki nan

Ban samu amsa mata ba Kareem yayi sallama ya shigo sai Baba ya amsa masa sallamar. Kareem ya kalli Mama ya gaisheta

 Dan Allah ayi hakuri, abun da kika furta kin tsoratata ma bar gida ta tafi a kafa ta same ni har gida tace na zo na baki bakuri tare da Babanta, kuma tace na fada miki ba zata sake ba, dan Allah ki yi hakuri

 Babu komai na yafe mata, ni ma na gane kuskuren fadar hakan da na yi bayan ta bar gidan, domin bayan gidan nan bata da wani masauki, kuma mace ce hankalin ya tashi sosai a lokacin da aka duba ko'ina ba ganta ba, wani lokacin rai ne yake baci ka aikata abun cikin bacin rai, Zafeer ma be dade da aikowa kiranta ba nace a fada masa bachi take, na mata haka ne saboda ta tsorata ta daina abun da take, ba dan ina da niyar aikatawa ba

 Alhamdullahi, daman na san uwa dole zata nemi yarta duk runtsi, addu'a ya kamata ana yi ba sai tsoratarwa ba

Kareem ya fada sai Mama ta mika hannu ta janyo ni ta rike.

 Ai Alhaji Noor din ce sai hamdala, ni ina ganin aurar da ita kawai zan yi na huta, shi yaron nan idan ya shirya ya fito idan kuma be shirya ba ko a Masallaci ne zan yi cigiya na bada ita sadaka, ita ta huta mu ma mu huta

Baba ya fada, sai Kareem ya kalleshi ya ce.

 Noor din nawa take da za'ayi mata haka? A dai yi hakuri, ni zan koma ga dubu ashirin a siya wani abu

Baba ya saki fitar hannunsa ya mika hannu ya karba.

 Ahhh Allah da iko yake, kai yaron nan gajiya da kyauta, dazun ma fa sai da ka ba ni wasu kudin, Allah dai ya saka da alheri ya rabaka da iyayenka lafiya Allah ya kara budi

 Ameen Ameen

Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalli Baba dake kokarin yi masa rakiya.

 Am Baba dan Allah ina son na bada hakuri akan Nabil ka yafe masa shi ma dai ya dawo gida ya zauna, ku daina daukar zafi akan yaranku ayi hakuri dan Allah

Baba ya amsa da sauri.

 In Shaa Allah, babu komai na yafe masa ya ci albakarcin ka ba komai

 To na gode

Ya juya ya fice Baba ya bishi yana addu'a, ni kuma na kalli Mama.

 Mama ki yo hakuri daga yau ba zan sake ba

Sai ta kwantar da ni jikinta tana kuka.

 Na yafe miki Noor, bakincikin ne yana min yawa, amman dai idan bana duniya babu wadda zai fada miki gaskiya, Allah ya sauya miki rayuwa ya canja wannan hali na ki

Ta nufi dakinta da ni tana rumgume da ni, wani dadi da natsuwa na ji marar misaltuwa saboda yafe min da Mama ta yi har ta rumgume ni.






KAREEM POV.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya faka motarsa a harabar gidan, sannan ya ciro wayarsa ya shiga WhatsApp dinsa da datarsa take always on ya shiga chatting dinsa da Safeena ya rubuta mata sako.

 Safeena wannan ya zama karo na karshe da zaki sake kai hannunki jikin yarinyar nan, babu wani abu tsakanina da ita, duk abun da ta fada ko Hafiz ya fada sun fada ne kawai saboda su fusata ki, ina sonki kin sani, kuma na san kina so na, amman hakan ba zai baki damar ki aikata sakarci a gaban kowa ba, ko kuma ki yi yunkurin cutar da wani ba zan lamunce miki wannan ba, kuma babu ruwanki da yarinyar nan daga yau

Yana aje mata sakon ya bude motarsa ya fita ya rufe sannan ya kama hanyar falon gidan. Shiga falon ke da wuya sakonta ya shigo wayarsa sai ya bude arba yayi da hoton bari da kuma rubutun sakon dake bin bayan hoton.

 I lost my baby today saboda bakincikin jin cewar kana son wata Kareem, mijina ya kasa gane kaina yau saboda kai, na fitunu da kaunarka da Kareem, amman kokarin cire ni kake a rayuwarka bayan duk budulcin da ka yi min na kin aurena

Ya karanta sakon kusan sau uku sannan ya sake duba hoton barin da ta turo masa, a madadin ya ji dadi abun da yake nema ya samu wato cikin ya zube, sai abun ya tsorata shi, har ya fadi zaune a kujera yana mamakin kansa.

 Ta ya yayi zurfi a zuciyar matar wani haka? Har bakincikin jin cewar yana son wata zai saka cikinta ya zube, me yake aikatawa haka? Wane irin mutum ya zama? Wane kalar uba ya zama? Wane kalar miji? Wane kalar a? Ashe tasirin sabon da zuciya take kwadaituwa da aikawa ya kai haka?

Ya mike tsaye zuciyarsa na bugawa da karfi, idan ya mutu a cikin daren nan yana da wata hujja da zai fada ya fanshi kansa a gurin Allah? Me ya aikata haka? Zina ba halinsa ba ne me yasa zuciya ta kai shi? Ta ya yake kokarin lalata rayuwarsa? Su ne tambayoyin da suke masa yawo a kai idonsa suka cika da hawaye. Ya nufi sama da sauri ya tura kofar dakin yaransa ya tsaya daga bakin kofar yana kallon Tine dake bachi ya karasa ya zauna kusa da ita ya kai hannu ya shafa kanta yana tuna maganar matarsa.

 Kai ka ta shafa, idan ka aikata abun kunya yayanka ne a kunya ba ni ba, ni matsalarka bata gabana

Ya hade yawu ya mike tsaye ya gyara mata bargonta sannan ya fice dakin a hankali ya ja kofar. Dakin matarsa ya nufa nan ma a hankali ya tura kofar ya shiga sai same ta kwance tana bachi Areef na gafenta shi ma yana bachi. Karasa yayi ya kalli dansa ya kalleta ya mika hannu ya shafa dansa sannan ya juya ya fice.
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Talla=?G?=?G?=?G?*

KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN S'=?G?=?G?=?G?
To kiyi saving numba ta ki danna wannan link=?G? https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI=?
?ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI=?G?=?G?
1.INFECTION CIWON SANYI =?I?LALACEWAR BREAST=?I?RASHIN HIPS & BUTT=?I?KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING=?I?TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?=?I? AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only =?L?

KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA =?I? KIYI SAVING NUMBER TA DM ME https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1


Chapter - 9


KAREEM POV.

8:19am ya nade sallayar da yayi sallah ya aje, sannan ya dauki wayarsa dake ringing ya duba. Ganin number mahaifiyarsa ya saka shi farinciki.

 Hello Momy

 Ashe zaka dauka, ai na dauka idan an kira ka ma ba zaka dauka ba

 Haba Hajiya me ya kawo wannan maganar kuma?

 Yaushe rabon da ka kira ni?

Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna gefen gadonsa.

 Na kira sai Baba Karami ya dauka ya ce min kina bachi kuma likitocin sun ce a barki ki huta na kwana biyu kar a takura miki, ana son ki samu bachi

 Wannan ba hujja bace, hakan ai be hana matarka kirana safe da rana da dare ba, kullum sai ta kira ni sau uku ko da ban amsa wayar ba zata ce idan na farka a sanar min ta kira waya, haka ma mahaifinku kullum sai ya kira ta gaishe shi

Yayi shiru for few seconds sannan ya ce.

 Yi hakuri Momy, Wallahi saboda likita yace a barki ki huta ne yasa ban takura da kira ba, Daddy kuma ina son na shiga this Saturday na gaishe shi

 To ya dai kamata dai, ina yaran?

 Suna lafiya Momy, ya karfin jiki

 Alhamdullahi ina samun sauki, yanzu dai suna gasa min kafafuwan ne, sun ce jinin ya sauka

 Maa Shaa Allah haka nake son ji, Allah kara sauki ya dawo mana dake lafiya

 Ameen, Allah ya muku albarka kai da yaranka, Yusura ma Allah ya mata albarka mace ce mai mutumci samun mace irinta akwai wahala yanzu, yarinya ce mai kirki da biyayya duk da kasancewar ta yar'uwa ta kara karfafa zumuncin, bata taba nuna min cewar ba ni na haifeta ba, shiyasa ko da yaushe nake jan kunnenka akan riketa amana, duk da na san kai ma yaro ne mai biyayya da kulawa, Allah dai ya muku albarka

Sai da Kareem ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya sannan ya amsa da Ameen yayi mata sallama ya sauke wayar. Sannan ya mike tsaye ya aje wayar ya nufi kofar dakin ya bude ya fita, sai da ya fara leka dakin Tine ya duba bata cikin sannan ya rufe kofar ya sauko kasa.

 Ina kwana?q

Ya gaishe da Yusura dake jera kuloli a dinning. A madadin ta amsa sai ta tambaye shi domin shi da ita ba al'adarsu ba ce gaisawa da juna da safe, kara ma shi ya kan fada mata wani sa'in idan zai fita, ko kuma gaisheta musamman idan yaransa suna nan.

 Wani abu kake bukata ne

Ya kalli tv domin shi ma ba son kallonta yake ba, yana daga cikin dalilin da ya saka duk yadda yake son tsara gidansa ko tsara zama fa matarsa wannan rashin son, da kuma rashin ba shi hadin kai sai ya wargaza tsarinsa. Ya dauke ba tare da ya kalleta ba ya ce.

 Momy ta fada min kina kiranta kullum ki ji ya jikinta

 Ba saboda kai nake yi ba, bana bukatar godiyarka, ina yi ne saboda kulawa da ita da girmamata wani abu ne da na saba da shi tun kamin na aureta, aurenka ba shi da tasiri a gurina baka da kimar da zan maka alfarma

Ya zuba hannayensa a jallabiyarsa ya daga kai ya kalli yadda Allah ya wadata da mazaunai da shape kamar wadda ta yi surgery.

 Me yasa tun farko baki fada mata baki son danta ba, wannan soyayyar karya kike nuna mata

Ya juyo ta kalleshi.

 Danta ya kasa fuskarta ya fada mata be son matar da ta zaba masa sai ni? Dukan abun da na ke yi ma Momy ina yi saboda Allah kuma saboda ita din uwace a gareni, ta rike ni a lokacin da uwata ta tafi ta bar ni, ta rike ni a lokacin da yan'uwan mahaifina suna wofintar da ni, ta rike ni a lokacin da ban san komai ba, tun bana iya cin komai sai madara har na mallaki hankalin kaina, a hannunta na yi ilmi a hannunta na girma ita nake kallo a matsayin uwa, da Momy zata ce Yusura dauki wuka ki dabawa kanki Wallahi zan daba. Na fada maka duk wannan ne saboda ka san ba saboda kai nake yi ba

 Ni ma bana fatan shiga alfarma, bana fatan kasancewa a karkashin inuwar alfarmarki, ina jin fiye da abun da kike ji game da auren nan

Ta tintsire da dariya.

 Na nawa kuma? Ai na gama yi maka alfarma Kareem tun da har ka kasa rike kanka ka keta rigar mutuncina, kuma ka yi nasara har na haifa maka yaya biyu, ka gama cin alfarmata, sai kuma me?

Ta daga masa gira tana jiran amsarsa. Baya jin zai biye mata su fara abun da suka dauki lokaci ba su yi ba, ta saba fada masa magana marar dadi amman a haka yake hadewa ya danne saboda yana jin shi namiji ne ya fita hankali da tunani, and wani lokacin yana jin kamar ta ci albarka cin yaransa. Yayi murmushi ya sake kallonta ya dauke kai ya juya ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login