Showing 126001 words to 129000 words out of 227321 words

Chapter 43 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1551

kin fi son bari da dan'uwanki, duk abun da zai faru babu ruwana, ba zan miki dole ba amman ni dai ba zan so bare sama da jinina ba, ki fada masa ya same ni mu kare magana idan da gaske yake, sai mu gani kuma ni ba dade nake son ayi ba, sannan kuma ki sani ni ba ni da wasu kudin yi miki hidima shi ma margayi saboda ya dauke komai ne ya saukaka min, wannan kuma ba mu san ya yake ba

Yana gama fadar hakan ya mike tsaye ya fice daga dakin fuska a daure. A takaice dai jari mahaifina yake son yi da ni, in ba haka ba ta ina za ace ko da yaushe mijin da zai aureka ne zai maka kayan daki?

 Umma dan Allah ki fada masa, ina son na tafi na duba Mama yau, na dade ban je ba

 Toh bari na fada masa

Ta amsa da far'a ta fice daga dakin, wata kila tana murna zan yi aure na bar mata gidan ko kuma dai da gaske farinciki take zan yi aure! A waje ta sami Baba dake ta fada masa bukata ta sai yace

 Allah ya kiyaye

Ina jin haka na tashu daga dakin na fito waje na shiga dakinmu sai na samu Hana tana hawaye.

 Idan kika yi aure kika tafi kika bar ni, ni za su kashe da aiki a gidan nan, na gaji Wallahi

 Baba ya shirya aurar da ni, idan har ban fitar da wani ba, zai aura min Ridwan ne ni kuma ina ganin kamar zaman gidansa ba zai min dadi ba

 Allah yasa alheri ya sa gurin zamanki ne, kin huta Wallahi

Na amsa da Ameen, na fita na yi wanka na shirya na dauki ragowar canjin da Kareem ya ba ni na hau Napep da su na tafi gidan Mama. Na wuni a can na fada mata kudurin da na yake sai ta nuna min farincikinta fiye da yadda na zata, hakan kuma ya karfafa min guiwa na ji cewar kamar amincewa da Abdull a matsayin miji da na yi, na yi abu mai kyau, a gidan na wuni sai dare na dawo gidan mahaifina tare da yi ma Hana albishirin Mama ta ce da zarar na yi aure zata dauke ta daga gidan ta maida ita gidanta ta saka ta makaranta a can.

A daren da na dawo a daren Abdull ya gana da Baba ya gabatar masa da kansa Baba yayi masa tambayoyi ya amsa gamsasshen amsoshim da yake so, sai kuma ba lura yayi na'am da shi saboda ya fahimci mai rufin asiri ne irin yadda yake so. Na je masa rakiya ne nake bayyana masa mamaki ne zuwa da wuri gurin baba.

 Ai ba a bori da sanyi jiki, kuma ance a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, zumudi ba zai bar ni na dade ban zo gurin mahaifinki ba, turawa sun ce dama tana zuwa sau daya a rayuwa

Na dan yi murmushi.

 Yanzu ina son iyaye su shiga maganar ne, idan komai ya kam na tabbatar da an ba ni ke sannan na sanar da matarta cewar zan kara aure, gashi na yi sa'a ta sauka yanzu ta haihu balle ace zan kunsa mata bakinciki

 Wacece matarka?

Na tambaya da mamaki a fuskata, sai ya ciro wayarsa ya kamo hotonta ya nuna min.

 Safeena, kin ganta, ita ma kyakkyawa ce kamar ke, amman ita tana da dan jiki kadan ba kamar ke ba

Na kalli hoton na sake duba na sake kallo...




KAREEM POV.

It's a faithful Monday for him today. Tun daga wacan ranar da ya zauna da Noor ya barke mata cikinsa ta ba shi shawara kuma ta karfafa masa guiwa sai ya ji damuwarsa ta yi kasa. And when ever ya tuna da yadda take dariya ta ba shi shawara sai ya samu kansa da murmushi. A zatonsa idan ya fada mata laifin da ya aikata da Safeena zata tsorata kuma ta guje masa a take ko ma nuna masa bacin ranta.

But ta masa abun da matarsa bata yi masa ba, wata kila saboda ita din bata sa munin abun ba ne, wata kila kuma saboda tana da sauran kurciya ne har lokacin bata gama fahimtar duniya ba, amman ko ma dai yaya ne, ta fada masa kalamai masu dadi da kwantar da hankali, hakan kuma ya rura wutar alakar zuciyarsa da ganinta. Amman haka yake daurewa zuciyarsa gudun abun da mutane za su fada ko kuma ita kanta kallon da zata masa idan ya matsa da zuwa gurinta.

To me zai rika a matsayin Hujjar tafiya a gurinta, babu dan haka ya shafawa kansa lafiya. After ya gama saka key din a mota ya bude ya shiga yayi warming dinta sannan ya fara tukawa, as usual every Monday yanzu yana fara zuwa family house dinsu ne gaishe da iyayensa sannan ya wuce aiki. A harabar gidan ya faka Aaryam dake tsaye jikin tasa motar ya dago yana gaishe shi.

 Ranka ya dade

 Aaryam ya kake?

 Lafiya kalau, ya aiki

 Gashi mun yi shirin tafiya

 Daddy ya fita da safen nan kuwa

 Lafiya?

 Lafiya kalau, wai akwai abun da za su yi

 Okay

Ya amsa sannan ya shiga ciki ya gaisa da Hajiya Hassana da kanensa ya fito, har ya bude motarsa zai shiga sai kuma ya rufe ya nufi inda kanensa yake zaune a balcony ya zauna. Aaryam ya kalleshi cike da damuwa irin na dan'uwa mai damuwa da dan'uwansa ya ce.

 Lafiya big Bro?

Kareem ya sauke ajiyar zuciya.

 Lafiya, i just need some advice

Aaryam ya aje wayarsa a gefe ya fuskanci jininsa.

 Ina jinka

Kareem ya kasa cewa komai, har Aaryam ya fara guessing.

 Ko matsala kuka samu da Yusura again?

 No ba ma fada juna ai, it's just that dai ba ma zama kamar sauran ma'aurata, saboda tana jin na takura mata, ni ma haka

 Kamar ya?

 Aaryam ba zaka fahimta ba ko na fada maka

 Ban kai na fahimta ba ne?

 Ka kai amman ba zaka kalli abu ta sigar da nake kallonsa ba

 Fada min dai minene?

 Ni da Yusura ba mu taba son juna ba fa...

 Na san wannan abaya, duk wanda ya tashi gidan nan ya san kai da ita abokan gaba ne, amman bayan aure kake nufi ko kamin aure

 Har yanzu, har gobe har jini and abun yana damuna sosai

 Subhanallahi, taya kake iya zama da ita kuma baka sonta? Indai har da gaske ne to tsanarku mai girma ce

Kareem ya dan daga girarsa ya rage idonsa yana kallon harabar gidan.

 Idan baka son mutum baka son shi ne Aaryam, haka dai nake ta zama saboda kaddararmu ce a haka

Cike da tausayi Aaryam yake kallon yayan nasa ya ce.

 Ita ma har yanzu bata sonka?

 Da zaka mata albishir da na mutu yanzu, zata baka goro

 Innalillahi,,, to miyasa za ku cigaba da zama?

Kareem ya kalleshi.

 Shiyasa muka rabu, amman Daddy ya kasa fahimta ya cilasta mana sake zama, kuma halayen da take min a yanzu sun fi muni fiye da na baya

 Ku sauwakewa junanku kawai zai fi, zan yi magana da Daddy zan fahimtar da shi...

 A yanzu ba rabuwar ce damuwata ba, Aaryam aure nake son na kara, maybe haka zai saukaka min wasu abubuwa kamar yadda Hafiz yake ta hararo min

 Kana da wanda kake so ne?

 Eh akwai ta, amman ban san ya ku da sauran mutane za su kalli abun ba, gashi abokin shawata ya tafi ya bar ni, shiyasa nake neman shawararka

Slowly Aaryam ya kalleshi.

 Hope dai ba Safeena ba

 Har bada, ba zan taba auren Safeena ba ko da mata sun kare a duniya, wata yarinya ce mai tsananin bukata ta, ina jin kamar zan iya zama da ita zan iya kyautata mata, zan maye mata gurbin abubuwa da yawa da ta rasa, ko zata rasa a nan gaba

 Indai yarinyar kirki ce, babu wata matsala ka yi aurenka Bro, ka yi kokarin ni ba zan iya irin jihadinka ba, ba zan iya auren macen da bana so ba, ka kyauta ka saka Momy farinciki kai ma naka farinciki yana tafe, sannan ina mai baka shawara karka bari wannan yarinyar ta suBuce maka, Daddy ba zai hana ka kara aure ba, mu kuma kanenka ne ba mu zamu zauna da ita ba

Kareem ya aje numfashi ya shafa kansa sannan ya fadawa Aaeyam yarinyar da yake so, da kuma alakarsa da ita da kuma mijin da ta aura.

 Ba haramun ba ne, kuma ba abu ne sabo ba, indai kana sonta tana sonka ba wani abun tsoro a ciki, karka duba abun da mutane za su fada zaka saka kanka ne a damuwa kawai, kuma gashi Hafiz din ya fada maka kamin ya bar zuciya, ka amsa masa kawai kuma ka yi addu'a, kuma karka manta tun farko kai aka tashi aurawa ita Allah be yi ba har haka ta faru, dan Allah ka aureta, idan ka aureta ka samu abun da kake so kuma ka cika burin abokinka, ita ma kuma ka taimaka mata, wata kila ma hakan ya zama silar rabuwarku da Yusura cikin sauki, ita ma ta samu wanda take so ta aura shikenan

Shirruuuu Kareem yayi yana ta saurare ni dan'uwansa.

 Duniyar nan bata da tsawo ga wasu, kara ka bawa kanka abun da kake so karka yi sanya, ka same ta kawai ku tattauna idan kun kai karshe sai ka fadawa Daddy, wata kila ma a hade tare da nawa auren

Kallonsa Kareem yayi yana murmushi.

 Shikenan sai ka taya ni da addu'a, thank you

 Allah ya bada sa'a

 Ameen

Ya mike tsaye ya nufi motarsa Aaryam ya bishi da kallo yana mai tausaya masa da mamakin karfin hali da kuma tsananin biyayya irin ta dan'uwansa wadda yake jin shi kam ba zai iya yi ba. Ya wuni a office da nazarin kalaman Aaryam yana amsawa zuciyarsa muradinta, a yanzu ma kanansa ya kafafa masa guiwa abu daya ya rage masa ya gabatar ma da Noor bukatarsa ya ji ya zata karbi abun.

After work ya koma gida ya shirya cikin kananan kaya ya sake fita zuwa gurin da yake zama a yanzu, ya saka an yi masa gurin zama na kujerar sumitin a gurin amman ranar be yi sha'awar zama a can ba, sai ya zauna daidai gurin da yayi wacan zaman a wacan ranar da suka yi hira da Noor ta fada masa damuwarta ya fada mata ta shi. Sai da yamma ta fara yi sannan ya nufo motarsa yana shan ruwan gora ya bude motar ya shiga ya sake kama hanyar gida. A hanya yayi sallah Magariba sannan ya karasa gidan ya sake sabon wanka ya saka sabuwar shadda sai kamshi take tun kamin ya saka mata turaren.

Ya hada kamshi kusan kala biyar sannan ya fito fuskarsa da haiba, feeling some how for the second time zai sake fita neman aure, so yake ya kwankwasa ya ji idan Noor zata iya daukuwa. Har ya sauko be kalli gefen da Yusura take zaune ba, ita bata yarda ta kalleshi ba sa ta gafen ido. Yanayin yadda yayi dress din da kamshi dake take masa bayan, zuciyarta ta raya mata neman aure zai je. Mikewa ta yi tsaye ta isa gurin window ta daga curtain din tana kallon motarsa har ya bar gidan mai tsananin haske kamar ba dare ba.


Ya isa kofar gidan su Noor a lokacin da ake ta kiran sallah Isha'i, a kokarinsa na samu Jam'in sallah ya rufe Motar ya nufi masallacin dake kusa yayi alwala a gurin ya shiga aka sauke farali tare da shi, sannan ya fito ya dawo gurin motarsa. Yayi knocking kofar gidan saboda babu yaron da zai aika a lokacin, babu bata lokaci Hana ta leko suka gaisa.

 Noor na ciki?

 Eh tana ciki, bari na kira ta

Ta juya ta koma cikin gidan, babu jimawa Noor ta fito sanye da atamfa da karamin mayafi a kanta zuwa kafadarta. Suna hada ido ta sakar masa murmushi shi ma ya mayar mata.

 Ka yi kyau, kana ta kamshi kamar ango

Farinciki furucinta ya saka jin kamar an yaye masa rabin damuwarta, when last yayi kwalliya ace masa yayi kyau, yana kamshi ya manta. Lumshe ido yayi ya tsotsa bakinsa ya bude.

 Besty ta yaba kwaliyata hakan ma yayi

Ta yi murmushi kamar ba ita ba.

 Mun kwana biyu ba mu ga juna ba, i miss this face so much, tare da murmushin nan mai tsada

She then looks at him jin wani sabon salon furuci wai murmushi mai tsada.

 Shiyasa ka zo ko wani abun ne ya ta so

 Eh to wani abun ne ya taso, da ina jin tsoro ina sanya yanzu kuma na shirya fuskanta ko miye ma a wuce gurin

 You want us to talk about something?

 Yeah Besty

 Kamar ka san ina nemanka, ni ma akwai abun da nake son fada maka

Ya jingina da motarsa.

 To bari na fara jin na ki, ladies first fara fada min na ki

Shiru ta yi na dan lokaci sannan ya dago ta kalleshi.

 Kareem idan...

Ya dakatar da ita.

 Besty, I'm your bestfriend remember?

He said try to correct her, sai ta yi murmushi ta daga mishi kai.

 Yeah

 Okay carry on

Yayi mata alama da hannu. Rumgume hannayenta ta yi.

 Besty idan mutum ya taba son wani, yana jin zuciyarsa ta rufe kamar ba zai sake son wani ba again?

Kallonta yake kamar his life depends on her.

 Haka kike ji?

 Eh shiyasa nake son na tambaye ka, ai kai ka taba son wata baka samu ba how do you feeling tun da gashi har kace ka samu wata dabam da kake so?

Ya daga kansa sama.

 Wow... Abun is not easy, amman Hafiz yana yawan fadar wani abu cewar wani lokacin mutum be san abun da yake so ba, ko ya dace da shi sai a gaba. Noor lokuta da yawa mu kan kasance da wani abu ko kuma ma mu so kasancewa da shi alhalin ba son shi muke ba, shakuwa ce kawai da shalholiyar zuciya, daga baya zaka fahimci abun da kake so kuma ya dace da kai. Wani sa'ilin idan Allah ya hana ka abu shi ne mafi alheri a gareka, na fahimci hakan ta dalilin rashin auren Safeena da ban yi ba a yanzu

 Amman ya aka yi ka fara jin kana son wata a yanzu?

Ya maida idonsa akanta

 Wallahi ban sani ba, mun hadu a kan kuskure i think i like so many things about her and her life, i like her laugh, her smile, her jokes, her sincerely, most of all i love her heart and her happiness... Shi ne kawai abun da zan iya fada amman ban san ya aka yi na fara sonta ba, kuma ban fahimci ina sonta ba sai yanzu

 Wata kila saboda kai din na dabam ne, amman ni har yanzu ban ji ina kaunar kowa ba

Tana maganar kamar da shagwaba, furucinta kuma ya dan tsare masa guiwa.

 Zaki ji nan gaba, babu abun da yake zuwa da sauki Besty

 Me kake son mu tattauna?

 Ina son mu tattauna ne akanki da kuma kaina, yarinyar dana fada miki ina kauna akanta nake son mu tattauna

Ta yi murmushi na taya shi farincikin yarinyar da yake so.

 What a lucky girl, but ni ma ina son na fada maka wani abu

Na maida hankalinsa gurinta sosai.

 Fada min, komai na ki ne first na wa zai zo daga baya

Ta taka ta isa gurin motarsa ta jingina damuwa ta bayyana a fuskarta.

 Kareem daman ina son na fada maka na tsayar da wanda nake son na aura...

Sai kuma ta dube shi kamar yadda yake kallonta with heartbreak.

 Amman dai har yanzu ban ji wani abu akansa ba, kawai na amince ne saboda bana son Baba ya sake yi min auren dole...

As how? Is she for real? Ya tambayi kansa feeling so downfall, fell?in the?hot fire and?drowned...




NOOR POV.

ya dauke idonsa daga kallona ya juya ya jingina da motarsa ya kifa kai, sai kuma ya dago ya bude motar ya shiga ba tare da yace min komai ba yayi motarsa key ganin hakan na saka na dago daga jinginawar da na yi jikin motar ina mamakin me na fada ba daidai ba. Da reverse yaja motar har yayi nisa ina kallonsa, sai kuma na ga ya tuko ya sake zuwa inda nake tsaye ya faka, ina hango yadda ya kifa kansa jikin sitiyarin motar kamin ya dago ya kalleni.
Karasa na yi na bude murfin motar ina kallonsa.

 I'm sorry

Ya juyo ya kalleni.

 Sorry for what?

 Ban sani ba ko na fadi wani abun ba daidai ba ko be maka dadi ba, bana son ka ji haushina

Na fada a shagwabe ina jin kamar na fasa masa kuka. Yayi min murmushi yana kiran sunana.

 Noor...

Na matsa baya ganin yana kokarin fitowa, sake rufe motar yayi ya jingina jikin motar ya sauke ajiyar zuciya yana kallon kofar gidanmu.

 Waye wannan mutumen?

 Wane ne, sunanki Abdull a Lagos yake aiki, yana da mata da yara

 Ina kika hadu da shi?

 Mun taba haduwa tun Hafiz yana raye a Mall yayi min magana be san ina da aure ba, sai na fada masa ina da aure, sai kuma na sake haduwa da shi a gidan da Mama take aure a yanzu, kuma Mama ta yaba da halinsa

Ya dan bata fuska kadan wata kila ya tuna da abokinsa ne, ko kuma taya shi kishi yake.

 Amman an yi bincike ba shi da wata matsala?



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login