Showing 123001 words to 126000 words out of 227321 words

Chapter 42 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1566

yafe ta, zunubi ne mai girma, amman malamai sun ce Allah yana yafewa idan an tuba da gaske

 Na tuba da gaskiya, amman ina jin kamar akwai wani illa da na yi ma kaina akanta

 Illar me?

Yayi shiru tare da sauke kansa kasa.

 We shouldn't talk about this...

 Safeena ce matar?

Ya kalleni da sauri.

 Me yasa ita ta zo miki a rai?

 Saboda na lura da tana kishina lokacin da take zaton ko akwai soyayyar a tsakaninmu, kuma ta zo gurinka ka tuna? Amman tana da aure ko?

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya daga min kai.

 Tana da aure kake tare da ita?

 A da ba, amman yanzu na riga na daina, macen da mahaifiyata bata so, kuma abokina ya tsana yake ta kokarin ganin na guje mata amman hakan be samu ba sai bayan rayuwarsu it pain me, and tana da iyali ina da iyali be kamata muna haka ba, abaya duk ban gane haka ba sai bayan na rasa mutane masu muhimmanci

 Da gaske ka daina?

 Na daina saboda ba abu ne mai kyau ba, Na rantse da qur'ane da wanda ya aiko da shi da gaskiya na daina kuma ba zan sake ba, daman tun farko bana so kawai dai na biye sherin zuciya ne kuma bana son ta ga kamar da gaske na yaudareta ne na ki aurenta shiyasa na biye mata, amman yanzu Wallahi bata burge ni gaba daya

 Indai da gaske ka yi nadama, Allah mai yafiya ne zai yafe maka, kuma ni ma zan yi ta rokon Allah ya yafe maka

 Na gode

Ya fada da murmushi a fuskarsa irin na wanda ke kokarin kore damuwa.

 Sai kuma nadamar me kake yi?

 Na rashin amincewa da kudurin abokina kuma abun da zuciyata take ta muradi a yanzu

 Akwai abun da Hafiz ya bukata baka masa ba?

 Yeah, and yanzu ina bakincikin haka

 Minene?

 Ba zan iya fada miki ba

Ya amsa min da sauri.

 Amman I'm your best friend

 Na sani, amman ba zan iya maganar nan da ke ba

 To fada min muradin zuciyarka

Yayi murmushi ya mike tsaye.

 Noor kina ta min tambaya kamar wani karamin yaro

Ya kalleni da sani irin duba, yayinda yake tsaye ni kuma nake zaune a gurin.

 Kin samu kaina sosai

 Zauna Kareem

Na bukata sai ya duba agogon hannunsa.

 Akwai inda ya kamata na tafi

 Gurin budurwarka? Ita ce muradin zuciyar?

Ya dawo ya zauna with shock.

 Ganinki ake kamar baki da wayo, amman kina da shi Noor yanzu na gani

Na yi murmushi ina boye fuskata, shi ma murmushin yayi yana kallona.

 Ni dai fada min toh wata kake so?

 Me yasa kike son ki sani?

Na bude idon kuma na yi shiru.

 Akwai, akwai wacce nake jin tsananin sonta a yanzu, amman ina ajin kamar ita din mai tsabta ce ni kazami ne, saboda na aikata sabo a baya, da ban dauka ina sonta ba sai yanxu na san ina sonta, ina jin farinciki da farincikinta, ina damuwa da damuwarta, ina son kusanci da ita, amman ina tsoron yadda za'a kalli lamarin, domin na yi ma kaina illa tun farko na gujewa shawarar makusanci na, but i feel guilty, I'm hopeless

 Kana sonta sosai?

Ya rutse idonsa da wani farin ruwa ya fara taruwa a ciki.

 Kamar yadda kake son Safeena?

 Fiye, kaunarta rayuwata ce, ina sonta irin son da nake jin ita kadai ce bukatar da ta rage min a duniya yanzu, ina sonta irin son da nake jin da za'a raba ni da komai a yanzu a bar ni da ita ba zan ji komai ba, she's my last hope ina jin kamar aurenta ne zai yaye min damuwata kuma zai saka na fahimci waye ni

Tausayinsa ya kama ni, as well as nake jin wani abu marar dadi yana zagaye kirjina.

 Kareem

Na kai hannu na gafen fuskarsa zan yi masa magana irin wadda ban taba zama da wani na bashi irinta ba.

 Lokacin da nake tafiya makaranta, Malamin ya taba fada mana cewa Allah yafe yafe ko wane laifi amman ban da shirka, kai kuma ba shirka ka aikata ba, Allah zai yafe maka, kai mutumen kirki ne mai taimako mai juriya, saboda Yusura bata son ka kar ya karya maka guiwa ka ji cewar kamar wata ba zata so ka ba, kana da kyau kana da kudi kana da hankali, kuma dan ka aikata sabo kar ya hana ka ganin kamar ba zaka dace da rahamar Allah ba, ance babu mai yanke kauna daga rahamar Allah sai batattu, Kareem indai ka tuba da gaske zaka dace there's no?need?to?feel?guilty?about?it, kawai ka aureta

Ina masa maganar yana juya fuskarsa a hankali a tafin hannuna da yake kuncinsa na dama, sai da ya shinshina hannuna sannan ya bude idonsa ya mike tsaye.

 Kin karfafa min guiwa, thank you

 Yanzu ka yi min alkawari ba zaka bari yarinya ka guje maka ba? Zaka aureta?

Ya tsaya kallona har na mike tsaye na sake fada.

 Ka yi min alkawarin Kareem, ina sonka da farinciki, bana son na ji kana damuwa kuma indai har ka samu wanda kake so a yanzu be kamata ka bari ta maka nisa ba ko be kamata ka yi ta zama a haka da bakinciki ba, ina son ka yi aure ko dan matarka muguwa, kuma zaka samu farinciki idan ka auri wanda kake so

Ya miko min karamin yatsansa yana kallon kwayar idona.

 I pinky promise you zan aureta

Na ji dadi domin har ga Allah ina son Kareem da farinciki. Ina jin damuwa da matsalar ko da kuwa be fada min ba. Na lakam yatsan ina dariya sannan na yi gaba ina tsalle da dariya har da daga hannuna sama ina jin wani irin farinciki.
Kallona kawai yake yana murmushi har muka fito daga gurin.

 Noor ga wannan ki hau Napep, I'm sorry ba zan iya kai ki gida ba yanzu, dole sai kin yi taka tsantsan da rayuwa, saboda mutane za su saka miki ido kuma kin san waye mahaifinki

Ya miko min 5k. Na karba na cire 1k na mayar masa da sauran.

 Yayi yawa wannan ya isa

Ya karba ya rike yana kallona. Har na fara tafiya sai kuma na juyo ina murmushi jindadi da farinciki a fuska fal.

 Thank you so much Kareem you make me feel so special, wani be taba zama da ni ya fada min damuwarsa ba, ban taba bawa wani shawara ya dauka ba, ba a taba tsayawa an saurare ni kamar yadda kaka yi ba, ba a taba daukar kalamaina da muhimmanci ba sai kai, ban taba bawa wani shawara ya yarda ya dauka ba sai kai, ka saka na ji kaina a dabam, am felling so proud so good so happy

Ina maganar ina shisshekar farinciki. Murmushi yayi min yana yawo da idonsaa fuskarsa.

 Your Welcome, My Best sweet friend, daman you're special mutane ne ba su gane ba

Na yi dariya mai sauti ina tafiya baya baya kamar ba ni ba, gaba daya na manta da wata damuwar da bakinciki a lokacin har sai da na isa unguwarmu, sannan komai ya dawo min. Na yi mamakin ganin Abdull zaune a kofar gidanmu, ganina ya saka shi mikewa tsaye yana kallona har na karasa. Hade rai na yi na bata fuska sosai domin ban jidadin abun da yayi min a dazun ba.
Ina kokarin wuce na shiga gida ya sha gabana.

 Haba kyakkyawa wannan fushin na minene? Tun da na sauke ki a can na zo nan gidanku jiranki aka ce baki dawo ba

 Me zan maka?

Na tambaya fuska babu annuri.

 Hakuri zan baki na abun da nake miki, kuma na fada miki gaskiyar abun da yake raina

Na gyara tsayuwata.

 Uhmm

 Zaki taimaka mu tafi gurin motata mu tsaya? Please

Na kalli gurin da ya faka motar nesa da gidanmu. Na fara tafiya sai ya jera da ni yana tafiya har muka isa gurin motar ya fi ni tsaye sosai domin ya dara Kareem tsayi.

 Da farko dai zan fara da baki hakurin abub da ya faru, ba wai na yi da wata manufa ba, kawai gwadaki zan yi

 Miye hujjarka na gwada ni toh?

Ya sauke ajiyar zuciya ya cire facing cap din dake kansa.

 Noor gaskiya tun a lokacin da na fara ganinki a shopping mall, kin burge ni, natsuwarki kyaunki, farinki da kuma yadda kike da rashin jiki komai na ki yayi min, sai dai an samu akasi a lokacin kina tare da mijinki, sai dai damuwar da na sake yi dake bayan mutuwar mijinki a gidanmu, ya sake motso min da burina akanki, kin ga sanadi sai Allah yasa Alhaji ya auro mahaifiyarku gashi yanzu har ina magana dake, wata kila da ba zan ma san mijinki ya mutu ba

Na kalleshi kawai domin ban gama fahimtarsa ba.

 Noor ba zan boye miki ba, ina son k????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
i kuma ina son na aureki idan har Allah ya kaddara, kuma ni ba da wasa na zo ba, bana ma son a bata lokaci, har ga Allah ni dai kin yi min, ina son mace irinki kuma daman ina da burin kara aure saboda inda nake aiki ni kadai nake zaune a can matata kuma tana nan tare da yara, na kan dauki wata hudu uku ban zo ba, mahaifiyata ma tana son na kara aure amman dai ban ga wanda ta yi Sai a yanzu da na hadu da ke, babu wanda ta sace min zuciya ba sai ke

Na nuna kaina.

 So na?

 Eh, kuma idan kika bani dama zan tabbatar miki da gaske nake iyaye za su shiga maganar da yardar Allah, already ma na yi maganar ki da Mama, amman dai ban fada mata kudirina akanki ba tukuna

 Ni ba aure zan yi ba yanxu, yaushe ma mijina ya rasu da zan sake yin aure?

 Ke yarinya ce, karki cutar da kanki kuma ki cutar da masu kaunarki ki ce ba zaki yi aure ba sai nan gaba, wata kila nan gaba babu wanda zai kalle ki ya yi sha'awar aurenki komai yana da limit Noor, zai fi kyau dai ki yi shawara

 Toh zan yi shawara

Ita ce kawai amsar da na bashi na juyo ina tafiya, har na shiga gida ban juya na kalli inda yake ba. Ina shiga gidan na samu Baba a gida sai ya rufe ni da fadan batar da bokitan da na yi, Allah ya shiga lamarin dai be doke ni ba.

 Kuma gidan uban waye kika fito yanzu?

 Gurin neman kayan na fito, kuma ban gansu ba

Na fake da hakan domin ba ni da wata hanyar wanke kaina.

 To su kuma kudin da kika bata a ina kika samu?

 Alhaji ne ya ba ni ranar da muka je gidan ni da Yaya gurin bankwana

 Wane Alhaji

 Mijin Mama

Baba ya bude baki

 Har dubu goma?

 Eh yace na hau Napep

 Yanka kai yake ne ko kuma minene? Allah yasa ba jininki zai sha ba, dubu goma a take?

 Mai kudi ne sosai Baba, gidan ma kowa da bangarensa

Mtscheeeeeeee yaja dogon tsaki ya nufi gurin da buta take ya dauka ya shiga bandaki. Ni kuma na nufi dakinmu na shiga na zauna, ina tunawa da Mama ba san zaman gidan Baba be da dadi a gareta da mu, amman duk da haka ina jin kewarta kuma ina jin babu dadi idan na tuna a gidan wani take rayuwa a yanzu ba gidan mahaifinmu ba.

Kamar an kare ni haka hankali ya tattara ya koma gurin zancen da na ji na auren da Zafeer zai yi, ko yana sonta kamar ni ko kuma dai shi ma zai aureta ne kamar yadda na auri Hafiz ba dan ina son shi ba. Ya yake a yanzu? Ya sauya rayuwa ya cireni a zuciyarsa ko kuma ina ciki? Tunaninsa ne ya karkato da ni na tuna da wunin yau dan karamin lokacin da Kareem ya ba ni kuma ya saurare ni ya yarda da zance.

 Allah ka yafe masa ka yaye masa damuwarsa kuma ka bashi abun da yake nema, macen da yake so Allah kasa ta so shi, yana da kirki sosai

Har cikin zuciyata nake da masa addu'ar da kuma fatan dacewa da rayuwar da yake ta mafarki. Tun daga lokacin ban sake saka Kareem idona ba, shi ma be sake ganina ba, daman baya zuwa nemana sai da dalili yanzu kuma babu wannan dalilin, amman addu'ata tana tare da shi a kullum. Zuciyata kuma ta ki bari na huta da tunanin Zafeer da rayuwarsa, sai na yi ta hasashen irin zaman auren da zai yi da Amaryarsa she turn to be my enemy a yanzu.

Duk bayan kwana daya biyu sai Abdull ya zo gidanmu ya saka sallamo ni, a duk lokacin da yayi min sallama sai na fito mu gaisa ya ba ni tsaba ya tafi, tun ina kin karba har na saba idan ya ba ni dole na karba na shiga da shi gida. Kuma sai na lura Umma har farinciki take da zuwansa saboda baya zuwa hannu sake, yana yawan fada min labari akan rayuwarsa tsarinsa irin zamantakewar da yake da iyalinsa da kuma wanda zai yi idan ya aure.

Ni dai saurarensa kawai nake idan ya tambaye ni sai na ce masa har yanzu ina tunani ne ban gama yanke shawara ba. Ni da shi kuma muka taki sa'a duk zuwan da yake ba taba haduwa da Baba ba, ni kuma be taba zuwa ko aikowa kirana na Baba yana nan ballle ya tambaye ni alakata da shi.

It's Friday again ina zaune ina wanke wanke Baba ya fito da shirin na masallaci, farar shadda ce jikinsa da babbar riga sai hula da yake gyara tsayuwarta a kansa, kusa da ni ya karaso ya tsaya ina ganin haka na san akwai abun da zai fada, ko dai na yi wani abun ba daidai ba ya rufe da fada da zagi ko kuma umarni ne ga yin wani abun ko hani.

 Nooriya

 Na'am Baba

Na amsa ina jefa kwano a ruwan kumfa, sannan na juyo na kalleshi.

 Ko kina da wanda kike so?

Na yi shiru na sauke kai kasa ina jin abun wani kala, domin be taba min irin wannan tambayar ba.

Na dauki lokaci a haka ina ta sake saken me zan fada, na yi karya na amsa ina da shi alhalin babu shi a yanzu? Ko kuma na fadi gaskiya na ce babu din?

 Toh na dai baki lokaci ki yi shawara nan da kwana biyu, idan akwai wanda kike so, to sai ki gabatar kar na gabatar miki ace na sake yin karan tsaye, idan kuma babu to ina son na hadaki da an yar'uwata Ridwan mahaifiyarsa ta yi min magana, kuma shi ma yayi min magana da kansa, amman Anty Larai tace sai idan babu kowa, zan tafi masallaci sai na dawo

Na hade yawu da karfi na daga kai ina kallonsa har ya fice na kasa ce masa Allah ya tsare ko a dawo lafiya, Ridwan kuma? Wane irin Ridwan mutum mai mata biyu da yara tara ga kuma suruka duk a gida daya, gidan da ba wadatacce ba? A ciki zai aje ni ko kuma dabam? Ina ma zan iya zama da Ridwan. Gaba daya sai kasala ta kama ni tunanin ma na rasa wane zan yi.

Haka dai na yi aikin na gama, ina ta tunanin mafita, ba ni da wani da zuciyata take so a yanzu duk wanda zan tsayar sai dai na tsayar kawai amman ba dan ina kaunarsa ba. Ban yi shawara da kowa ba, ban nemi jin bakin wani ba na yanke shawarar da ban sani ba, ashe na yi ma kaina da yar'uwata babbar illa ne. A daren ranar da Abdull ya zo yayi min hira sosai, yawancin zuwan da yake shi yake min hira ina saurarensa gurin dariya na yi ko murmushi.

Daf zai tafi ya kalle ni ya ce.

 Har yanzu dai hakona be cin na ruwa ba? Har yanzu sarauniyar bata samu amsa bukatata ba? Gashi ina ta shirye shiryen komawa dan hutun da suke ba ni na wata biyu ya kare, gashi babu waya a hannu kuma ina tsoron siya miki ki ce ba zaki karba ba

Na dube shi cikin duba na rashin aminta da abun da baki yake furtawa a gareshi.

 Hakanka ya cin ma ruwa Abdull ka yi yaki kuma ka yi nasara, zan sanar da mahaifina sai ka gana da shi idan ka shirya

 Yes Yes yes...

Ya fada yana daga hannunsa sama cikin farinciki da murna, wanda ya saka samu ni, na sani ni kam dai na rasa so tun a lokacin da na rasa Zafeer, bana jin kaunar kowa ko sha'awar zama da kowa a yanzu. Shi ma dai saboda ba ni da wata mafitar ne da ba zan aminta da bukatarsa, kamar zai dauke ni ya goya a baya haka ya rika murna yana farinciki da jindadi.

Washe garin ranar na sanar da mahaifina cewar akwai wanda nake kauna kuma nake da burin aure, sai kuma na samu nasara Umma ta saka min baki tana taya ni siyasar gurin Baba ta yardar yaba Abdull duk da kasancewar bata wani san shi ba, ita dai ta dogara ga alheri da yake min ne kawai. Na lura da wani abu sabo a gurin Baba da ban saba gani ba, gabatar masa da Abdull be masa dadi ba. Wata kila saboda be san mahaifin Abdull mai kudi ne ba kuma shi ma kansa mai rufin asibiti ne, sai ya nuna min ya fi kaunar an yar'uwarsa wacce take Gwaggo a gurina wato Ridwan.

 Shikenan tun da kin nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login