Showing 51001 words to 54000 words out of 227321 words

Chapter 18 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1553



Baba ya nufi i da fitilarsa take ya duka ya dauka ya haska fuskar Mama da kyau.

 Hajara yau ni kike fadawa haka? Idan kika sake fadar wata kalamar a gareni marar dadi to a bakin aurenki...

Wani irin karfi da kuzari da ban san Mama da shi ba, ta yi sufa ta isa gurin da Baba yake tsaye ta saka hannayenta biyu ta tureshi da karfi sai da ya fadi kasa.

 Na aikata wanda ya fi wannan ka kashe ni yau karka bar ni na kwana da rai... Tun da na aureka ban huta, yara har sun girma su ba su huta ba ni ban huta ba, cin mutunci babu kalar wadda baka min ba, to na gaji aure kuma na hakura da shi na fi sha'awar na mutu a haka

Ni da Hana muka nufi Mama muka rike ta da karfi muka kuka domin ba halinta ba ne, macen dake tsoron daga kai ma ta kalli Baba yau ita ce ta saka hannu ta ture shi a kasa.

 Kalu Innalillahi.... Wa'Inna..... Ilaihirraji'un.... Hajara... Ba ke bace, Wallahi ba ke bace..

Yana fada yana girgiza kai, sai kuma aka yi sa'a nepa ta dawo a lokacin, daga ni har Hana muna kallon yadda yake yunkurin tashi ya kasa domin ba karamar faduwa yayi ba. Na saki Mama na nufi inda Baba yake na rika shi ya mike tsaye sai dai be tsaya daidai ba hannunsa daya yana rike da kunkurunsa, na nufi inda fitilarsa take na dauko na kawo masa sai ya karba ya nufi kofar gidan ya fIce ba tare da ya sake cewa komai ba. Ni kuma na gurin ina jin kamar an dora wano nauyi a kai saboda na zama silar fadan iyayena a yau ma, gashi an doki Mama kuma Baba yayi rauni. Na dade a haka ina hawaye sannan na nufi kofar dakin Mama na zauna na fara rusa kuka kamar ba ni ba, Mama da kanwata Hana kuma suna cikin daki suna na su. Shigowar Baba ne ya saka na tashi tsaye da sauri kuma na yi hanzarin yanke kukan da nake ina kallonsa tare da wasu abokansa biyu.

 Ina take?

Suka tambaya bayan sun yi sallamar da ban samu amsa musu ba saboda kuka da nake ta kokarin ganin na ci karfinsa.

 Tana can ciki ko ta fita Noor?

Baba ya fada yana tsaya daga can baya su kuma suka shigo cikin gidan suka isa gurin kofar Musamman ma Malam Isuhu da ya kasance Malamin Addini.

 To wai magana suka yi ne ko me? Ke Noor Mamanku tana ina ne?

Na nuna masa kofar daki. Baba kuma ya ce.

 Ai na san ba ita bace yadda ta tureni din nan ba karfinta ba ne, kuma duk zamana da ita bata taba nuna min yatsa ba, amman yau tureni ta yi a gaban yara, yanzu haka bana iya tsayawa daidai, ai ba ita ba ce shiyasa ban sake ce mata komai ba, na fita na kira ku ayi abun da ya dace idan karatu za a mata ko addu'a sai ayi

Baba na rufe baki Mama ta taso ta fito daga dakin a fusace.

 Babu wasu aljannu Malam Isuhu kar ya wahalar da ku, azaba ce da zaman auren na ukuba na ganshi a gidan har na gaji, yace idan na sake yi masa masifa a bakin aurena to na yi aure ya kare, ka aurawa Noor wadda duk ranka yake so amma zamana a gidanka ya kare, yara ba kanana ba ne da wayonsu ranar da duk suka so ganina sai su tararda ni inda nake

Malam Umar da Malam Isuhu suka juya suna kallon Baba cike da takaici da mamaki.

 To wai miye silar wannan abun ne?

Baba ya nuno ni da fitila ya karaso cikin gidan yana kashe min ido.

 Ka ga yar iskar yarinyar da ta assasa komai nan, ita ce silar komai ita ta lalata lamarin nan

Mama ta shiga tsakani ta tare ni.

 Babu ruwan Noor a ciki, ni ka saba yi da ni ka yi da ni, yarinyar da abinci ma ya gagareta ci saboda mugun bakin halinka ita kake dorawa laifi, daman kullum cewa kake saboda na haifo maka ita rayuwarka take cikin matsala, saboda baka yarda da kaddara ba

A take masifar ta koma gurin Mama ya koma yana haskata da fitila yana tafiya a karkace ka ganinsa ka san kunkurunsa ya bugu.

 Toh... Wai da kike wannan hakilon kina hauka kin isa ki hana ni aikata abun da na yi niya ne? Ai daman na fada miki idan kika sake magana a bakin aurenki to ki je na sake ki saki uku Hajara na gaji da ke na gaji da halinki, kije kya gani Noor kuma sai na aura mata yaron nan mai mutunci mai karamci sai dai ki hadi zuciya ki mutu, ita kuma idan ta haihu ta bijire min na gani...

Ban san lokacin da na dora hannu a kai na kwala ihu ba, domin na san miye saki na kuma san abun da saki uku yake nufi babu sauran zama a tsakanin iyayena kenan. Kuma duk ni ce sila. Malam isuhu ya rufe Baba da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Malam Umar ma fadan yake yana Allah wadai da abun da Baba ya aikata a gabansu. Hana kuma ta shiga zubewa kasa tana tashi tana ihu.

 Mun shiga uku mun lalace, Mama idan kika tafi mun shiga uku Innalillahi...

Na yi zaton Mama zata tausaya mana ko ta tausaya ma kanta amman ban ga alamar hakan a tare da ita ba, domin babu hawaye ko daya a idonta. Sai ma juyawa da ta yi ta shiga dakin ta fara hada kayanta. Malam Umar yana bata hakuri sai abokinsa da suka zo tare wato Malam Isuhu ya ce.

 Hakuri me zata yi lamari ya lalace ya sake ta har saki uku? ABu dai kamar wadda aka jefa, baka dubi yaranka ba baka kalli kai kanka ba ka saki mace da girma ya fara kama ku a tare, har ina aka taba haka?

Baba ya fara kokarin kare kansa.

 Baka san halin matar nan ba, Wallahi hakuri kawai nake da ita, yanzu ai sai ta koma can ta zauna cikin dangi ta ji idan akwai mai iya daukar abun da nake dauka, wulakanci take min kala kala duk ita ce silar lalacewar yarinyar nan Noor, ga bakinciki kamar ba mijinta ba, bata kaunar wani abun farinciki ya same ni, na gaji....

Takaici ya saka Malam Isuhu ficewa daga gidan, Mal Umar ne kadai ya tsaya ya fitar da Baba yana masa fada abun da yake be kamata ba. Na taka na isa cikin dakin na tsaya ina kallonta.

 Mama tafiya zaki yi?

 To zama zan yi? Auren ubanku har aure ne? Ku dai da yake ubanku dole ku yi hakuri ku zauna a haka amman ni yanzu kam Allah ya sama min yanci, kuma kin fi kowa zama sakarya wawuya a gidan nan, idan zaki canja hali ki canja idan kuma ba zaki canja ba, to zaki sha wahala rayuwa ba yanzu ba har nan gaba

Na matsa baya na jingina jikin kofa ina kallon Mama har ta gama hada kayanta.

 Kar wadda ya bini yana min ihu kuma kar wadda ya sake min kuka, kukan be hana ni tafiya, kuma ni da mahaifinku zama ya kare har a bada....!

Haka ta saka kai ta fice a fusace ko kadan kuka be ziyarci idon Mama ba, ni yau sai ta canja min ma kamar ba ita ba. A dakin muka zauna na tsawon lokaci muna kuka ni da Hana dake ta dora min laifi.

 Sai da na ce kar ki fita amman baki ji ba, gashi nan kin yi sanadin da Mama ta tafi, jindadi da sanyi da muke ji ta bangarenta kin yi sanadin da muka rasa shi, kuma duk saboda Zafeer din nan ne, kamar kanki farau soyayya, yanzu kuma sauran ki yi sanadin da Baba zai tsine miki sai kiji sanyi, kullum ke kike janyo mana matsala a gidan nan kullum da ke ake kuka...

 Babu wadda zai sake kuka da ni Hana ba zan sake aikata abun da wani zai yi kuka da ni ba

Na tashi ina jin jikin babu karfi, gurin da Yaya yayi min wacan dukan yana taso min da ciwo. Na koma dakinmu na kwanta hankali be kara tashi ba sai da na ji shigowar Yaya Nabil domin na san ba z???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai min da sauki ba, a take na tashi zaune na zubawa kofar dakin ido ina jiran shigowarsa. Shiru shiru ban ji ya shigo ba, hakan ya saka na tashi tsaye na isa gurin kofar sai na hango shi zaune bakin kofar Mama rike da yar leda ya kifa kai da guiwa a kasa...




*** **** ***

GAM..... ya rufe motar ya saka key din a aljihunsa sannan ya fara waigewaige inda zai samu yaron da zai aika. Daga karshe sai ya nufi kofar gidan ya kwankwasa yaja baya ya tsaya yana kallon agogon hannunsa da ya nuna karfe goma sha daya da rabi. Nabil ya fito yana murza ido da alama a lokacin ne ya farka daga bachi.

 Nabil kana ciki...

Sanin cewar abokin ogansa ya saka Nabil ya mika masa hannu da sauri suka gaisa.

 Ina Baba fa yana ciki?

 Aa magana zaka yi da shi? Allah yasa ba wata matsalar bace?

 Aa babu wata matsala na zo ne kawai na yi magana da mahaifinka?

 A game da ni ne? Ko oga ya kore ni ne? Saboda Noor ta ari wayata ta yi masa maganganu marasa dadi

Hafiz ya girgiza kai.

 Aa ba haka ba ne, wannan abun ai be kai a koreka ba, ni kaina na san halin Noor a yanzu balle kuma shi Kareem da ya fi kowa fahimtar ta, ba mamaki ace baka sani ba ta ari wayarka ta kira ko?

Ya daga kansa da sauri.

 Eh ba da sanina ba ne

 Ba matsalar ce ta kawo ni ba, wata maganar ce dai mai muhimmanci, kuma bana tunanin Kareem zai koreka gaskiya saboda ya san hanyar cin abinci ka a nan take, Kareem yana da kirki sosai fiye da yadda kake tunani, kuma yana da saukin kai amman be san ma na zo nan ba 

Nabil ya ji hankalinsa ya dan kwanta kadan, sai dai tashin hankali rashin mahaifiyarsu yana nan a cikin ransa. Ya juya zai koma cikin gidan.

 Bari na sallamo maka shi

Hafiz yaja ya matsa baya ya jingina da motarsa yana kallon yanayin unguwar, ta dayan bangaren kuma yana jin bakinciki yadda Kareem ya watsa masa kasa a ido. Babu bata lokaci Baba ya fito yana gyara hula, ganin Hafiz ya saka shi murmushi ya karasa da kansa ya mikawa Hafiz hannu suka gaisa cikin girmamawa.

 Yanzu ake tafe?

 Eh Wallahi wani abun ne ya kawo ni, na yi tunanin za a fi samunka da safe ne shiyasa na zo kamar yanzu...

 Maa Shaa Allah aiko na jidadin zuwanka, daman ina nemamka har ina shirin fadawa Nabil ya kira min kai

Hafiz yayi fuskar mamaki tare da murmushi a fuskarsa.

 Ikon Allah toh Allah yasa lafiya dai?

Baba yayi dariya.

 Lafiya kalau, sai alheri a game da Noor ne amman dai bari na fara jin abun da ke tafe da kai tukuna

 Aa Baba a sawun giwa ya take na rakumi, fada min na ji dalilin neman tukuna

Baba ya gyara tsayuwarsa ya jingina da motar Hafiz tare da sauke ajiyar zuciya.

 Watooo ka san lamarin mace, ko da babba ce balle karama kamar Nooriyya, ni abun ma sai yayi min wani iri Wallahi, ina ce yaron nan yaje yayi muku tashin hankali jiya?

Hafiz ya daga kai sama.

 Eh haka ne, shi ne ma dalilin zuwa na bada hakuri kuma na bada shawara....

 Toh ai saboda kai ne yaje yayi wannan tashin hankalin

 Saboda ni kuma Baba?

 Kwarai kuwa, ai yarinya buga kafa ta yi a kasa tace kai take so, saboda na yi masa maganar idan be shirya ba to fa ya kauce saboda ina son na aurar da ita, shi ne ya zo yana rokonta yana rokona sai na sake zaunar da su na fada musu dalilina na son aurar da ita, sai ya tashi yana zage zage kasan abun ka da marar tarbiya, ita kuma ta fusata tace ba zata ma sake kula shi ba, to in takaice maka da magana uwar ta saka ta a gaba da masifa tace to idan ta juya masa baya sai ta fitar da wadda take so, ita kuma tace kai take so...!

Da mugun mamaki Hafiz ya nuna kansa.

 Ni kuma Baba? Ni ko dai abokina Kareem?

Baba yayi dariya kamar gaske.

 Kai din dai, sanadin haka uwarta ta yi fushi yanzu haka bata cikin gidan ma, amman waka a bakin mai ita tafi dadi bari na kira maka ita Nooriya sai ka yi magana da ita ka ji

Kamin Hafiz yayi wani yunkuri Baba ya nufi cikin gidan ya shiga. Hafiz ya nuna kansa har lokacin mamaki yake.

 Ni...? Baba dai ba fahimta da kyau ba

Ya furta yana kallon kofar gidan zuciyarsa na bugawa da karfi...





____________

Toh fa ana zaton wuta a makera....

Anya ana samun uba irin Baba Naziru kuwa?

Auren Mama dai ya kare amman an bar baya da kura.

Nikam na tambaye ku mana, Zafeer be baku tausayi ba?

Hafiz na kokarin kulla alheri reshe na shirin juyewa da mujiya yaya kenan?


Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


TALLA =?G?=?G?=?G?


https://chat.whatsapp.com/DUwtFhhxfsS4zLHhxb28Wo

About us
*Legit contacts
*Verified address including shop address and social media handles
*Wholesale price
*Group support
*Group buying if you can't afford moq
*Connect with supplies from Yaba, trade fair, Lagos island, balugon, e t c just for 2k=?L?


*Chapter 15*


Ni da Hana kuka muka sha har muka gode Allah, ni dai sai tunanin ya zame min biyu tafiyar Mama da kuma Zafeer, tsammanin da nake Yaya Nabil yayi min fada ko duka ko ya min wata maganar babu ko daya, haka muka kwana cikin bakinciki da kuka. Baba be shigo ba sai da safe, a lokacin ragowar karfin jikin ma ya tafi ya bar ni, zazzabi kuma ya rufe ni har bana iya daga ido da kyau, ina jin lokacin da Baba ya shigo ya bawa Hana kudi wai ta siyo kunu, ta tashi ya fita bata jima ba ta dawo da kofin kokon ta aje a nan dakin ta nemi guri ta zauna ta yi tagumi, duk irin yadda take kaunar makaranta da rashin son wasa da karatun da take a yau ban ga tana shirin tafiya makarantar ba. Ina jin motsin fitowar Ya Nabil amman be cewa Baba uffan ba ya koma ciki, ba kamar yadda yake gaishe shi da safe idan ya ganshi ba, ni ma da na saba lekawa na gaishe shi a yau sai na ji bana bukatar ganin fuskarsa ko yi masa magana. Muna zaune dakin kamar wadanda aka yi ma mutuwa har wajen karfe goma sha daya, sannan Yaya ya sake fitowa yana wanke baki wato brush muka ji an buga kofar gidan, gabana ya fadi wata zuciyar na raya min cewar Zafeer ne ko wasani nasa. Sai da Yaya ya gama wanke bakin sannan leka waje, ya dan dauki lokaci sai dai ba sosai ba ya dawo cikin gidan ina hange lokacin da ya shiga dakin da Baba yake wato dakin Mama, sai na ga hango Baba ya fito da sauri ya fita. Wata zuciyar sai ta raya min cewar wani ne daga familyn Mama wata kila ya biyo sawu ya ji abun da ya faru. Sai dai yadda Baba ya dawo ya shigo dakinmu da kuzarinsa ya katse hanzarina.

 Ina... Nooriyya...

Na tashi zaune jiki babu karfi.

 Taso ga Alhaji nan ya zo

Na tashi tsaye ina jin kamar ba zan iya tsayi ba, ba kuma dan na san wane alhajin yake magana a kai ba.

 Saka Hijabinki mana

Na juya na dauko hijabin na saka na bi bayansa, sai da muka fita waje sannan Baba ya tsayar da ni ya ce.

 Ke saurara kar kije ki yi hauka, kin ga dai mutumen nan mai mutumci ne, kuma yayi mana karamci yadda ya dace, zuwan da yayi yanzu yace min ya zo da magana ne, kuma na fahimci maganarsa ta neman aurenki ne, ban riga na bashi ba, amman dai na fada masa ke ma kina maraba da hakan, karki kunyata ni Noor, Allah ya ba mu wannan damar ya ba mu wannan ikon na zabawa yarinyar mijin da zai dace da ita, kuma ni ubanki ne ba zan zaba miki abin da zai cutar da ke ba, dan haka nake son na baki umarni ba shawara ba, duk abun da ya tambaye ki ki amsa da eh karki karyata mahaifinki karki saka kimata ta zube a idonsa, ki tafi a natse ku yi magana ta hankali idan kika dawo zamu yi magana ta fahimtar juna kin ji ko?

Na daga masa kai ba dan na fahimci duka yaren da yake karanta min ba, ina mamakin yadda ya kwantar da murya yana min magana kamar ba shi ba, abun da tun da na zo duniya be taba min ba, na bude ido ne da tsawarsa da duka ta tsana da fargabar fadan yau dabam gobe dabam. Na fara takawa ina ganin hanyar tana rabe min na isa gurin kofar na fita daga kan da zan yi na kalli dama da ni sai na hango Zafeer a tsaye nesa da kofar gidanmu ya rumgume hannayensa yana kallona. Na dauke kaina na nufi gurin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login