Showing 135001 words to 138000 words out of 227321 words

Chapter 46 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1536

ya ba mu zama lafiya

 Ameen

Ya amsa sannan ya kashe wayar, shi ne mutum na farko da ya fara min albishir, kamin gidan mu ya dauki guda har Hana ta shigo dakin tana rangwada guda tana farinciki, sabanin wacan auren na farko da bata yi farinciki ba. Madadin na yi murna sai na fashe da kuka na zube a gurin an rufe idona ina ta rutsar kuka kamar wanda aka sake yi ma auren dole.

Haka na wuni ban iya cin komai ba, sai da Anty Larai ta siyo fura ta dama min ta saka kankara sannan na iya sha shi ma ba da yawa ba, yan'uwan Abdull sun leko mana wuni, daga bangaren mahaifiyarsa da kuma na mahaifina. Angon kuma be duro gidan ba sai isalin karfe takwas na dare. A lokacin da na kira a waya ya sanar min yana waje, sai na jin kunyar fita a dole na yi masa karyar Gwaggonta tace ba zan fito ba.

Ban san da wa yayi magana ba, sai ga Baba ya shigo yana fadin na tashi na leka waje mijina ya zo tare da abokinsa yana son magana da ni. Jin cewar yana tare da wani ya karfafa min guiwa kuma ya rage min kunyar da nake ji ta mutane. Hana ta dauko turare ta kara fesa min, Anty Larai kuma ta saka na cire lace din dake jikina na saka farar lafaya sannan na fita gashin kaina na yawo domin ban saka ribbon ba.

Nesa da gidanmu ya faka ta inda mutane ba za su ganshi ba, ni ma ba dan na kira shi a waya ba ba zan iya gane shi ba. Kamar ana daure min kafafuwa haka na karasa gurin motar sai ya sauke gilashin ya kunna hasken wayarsa ya haska fuskata.

 Amarya ba kya laifi, kyakkyawar amarya mai tsaye siririya duk ni kadai

Kunya ta saka ni sauke kai kasa ina murmushi.

 Shigo motar mana, kar na gajiyar da matata

 zan iya tsayuwa a nan

Bude motar yayi ya fito ina kallonsa ya kama hannuna ya zagaya da ni ta baya ya saka ni a back seat sannan shi ma ya shiga. Rabon nake ko zan ga abokinsa amman ban ga kowa ba.

 Ka ce kana tare da abokinka...

 Na fadi haka ne saboda na rage miki kunyar dake kanki

Ya yana maganar kallon bakina zuwa kirjina.

 Ko ban kyauta ba?

Kamin na amsa na ji na kara matsowa kusa da ni sosai har ina jin numfashinsa, ta dama da ni ya lakamo hannunsa yana lasa cikina a hankali.

 Ya gajiyar biki?

 Alhamdullahi

Ina kokarin cire hannunsa sai ya juyo da fuskata zai sumbance ni, na dauke kai na dauke numfashi ina jin wani iri. Murmushi yayi ya saka dayan hannunsa ya juyo da kaina.

 Da alama dai kunyar nan zata cutar da ni

Ya sumbanci goshina ya shinshina hancina kamar mai kokarin tantance wani abu. Rufe ido na yi jikina ya hau bari ina jin wani bakon al'amari. Hakan kuma be hana shi kai bakinsa cikin nawa, sai da na ji yana kokarin wuce gona da iri tukuna an matsa baya na rike hannunsa.

 Abdull za a iya ganinmu fa

 Babu wanda zai gani bakin gilashi ne

Ya sake kai hannunsa a jikina sai na tare.

 Baba zai ga na dade

 Me yasa kike ta guje min ne Noor? Kin san how long nake ta jiran wannan ranar? Ni fa yanxu halalinki ne

 Na sani amman ban tare ba, kuma na fito gida ne da sunan zaka yi magana da ni

 An riga an daura ko da sadakin da na biya kin zama mallakina balle kuma an daura, sadaki shi ne aure ai wasu da zarar an biya sadaki ma suke sakewa juna balle mu da har an daura mana aure

 Auren dai shi ne gaskiya, amman biyan sadaki ba aure ba ne, tun da har ana daura mana ai ya kamata mu yi hakuri har zuwa lokacin da za mu tare babu dadewa

 Allah yasa zan iya jira, sai monday zamu bar garin nan Noor, kuma ba wani abu zan aikata da ke ba a yanzu, it's just a kiss, ina kokarin wayar da ke kamin mu tare domin na lura kamar baki gama fahimtar rayuwa ba

Na yi murmushi karfin ina mamakin yadda yake da rawar jiki haka, kuma ina yaba kokarin Hafiz na jurewa da yayi ashe shi din jarumi ne sosai. Na matsa ta gefen da kofar take na bude na fita.

 Sai da safe

 Sai da safe my shy Bride, an hana ni kiss ko? Zan rama

Murmushi na kawai abun da na yi na fara takawa ina tafiya har na isa cikin gidanmu. A dare wata kanwar Mama ta cika min ciki da wasu kayan mata har sai da kaina ya fara ciwo. Haka na kwashe kwana biyu ana ba ni abubuwan nan da bana bukata, ban kuma isa na ce aa sai a rufe ni fada.

A cikin kwanakin da na yi a gida bayan daura auren, babu ranar da Abdull baya zuwa da dare a kowa dare kuma sai yayi kokarin taba ni har ya wuce gona da iri. Baba yayi min nasiha da kuma jan kunne, ranar Lahadi Mama ta aiko da mota aka dauki zuwa gidanta ta yi nata nasihar, acan na kwana sai washe gari na dawo. Na dawo gidan na tarar Hana ta gyara min kayana ta kintsa komai, a take na fara jin kewar gidanmu duk kuwa da kasancewar ba wani dadin zaman gidan nake ji na.

Ranar Monday da misalin karfe 2pm Abdull ya iso gidanmu tare da wani abokinsa da kanensa mata biyu da sunan za su dauke ni. Sai Baba ya tsayar da shi jege suka tattauna, ban san me suka tattauna a kai ba, bayan sun gama na fito ina sanye da green abaya da mayafinta sai mask da na saka na rufe fuskata. Handbag dina tana hannuna tare da wayata da karamin akwaitin da yace da shi kadai zamu tafi a yanzu saboda jirgi zamu shiga.

Yace daga baya zai aiko da mota a dauki saura kayan nawa da kuma yan'uwana domin su ga gurin da muke rayuwa. Da ace ina da iko da tun a yanzu zan tafi da Hana domin ta rage min kewar gida da kuma bakuntar gurin da ban sani ba. Na yi kuka sosai ina jin kamar wata kasar zan tafi ba iya Lagos ba. Har gurin mota Baba ya rako mu tare da Hana da Umma, na shiga gidan baya tare da kanensa shi kuma yayi ma Baba sallama ya shiga front seat kanensa kuma yaja motar sai airport....


Ban taba ganin airport a fili ba sai a ranar da muka isa gurin, ashe babban guri ne mai hada hadar jama'a mun zauna a wani guri jiran jirgin bayan an gama yi mana check-in. Id card din dake hannuna nake ta kallo, sai dai zuciyar da tunanin yana can wani guri. Hannun Abdull na ji cikin nawa yana kokarin saka yatsunsa cikin nawa.

 Amarya are you Okay

Na kalleshi sai na ji hannunsa a fuskata yana share min hawayen da ban san taya suka zubo ba.

 Har kin fara missing din gida ne?

Ban yi magana ba na kalli kanensa dake can gefe zaune suna ta hirarsu, jira suke har sai jirginmu ya tashi sannan su koma gida.

 Ka yi min wani alkawari

 Cewar ba zaka taba cutar da ni ba

 Me yasa kika fadi haka Noor

 Ba komai ni dai ka yi min alkwarin rike ni amana, ina fatan wannan auren da muka yi mutuwa ce kadai zata raba

 In Shaa Allahu, na miki alkawari ba zan taba cutar da ke ba Noor

Ya ba ni tabbacin da nake bukata sannan ya amsa kiran dake shigowa wayarsa ban san da wa yake magana amman na ji yana fada masa lokacin da zamu sauka. Ni kuma na juyar da kaina ina kallon wani gafen.
Kalamansa sun saka na ji hankalina ya kwanta, na samu natsuwar da na rasa.

Na sani mutum ba zai taba samun abun da yake so dari kan dari ba, shiyasa na yarda da wannan kaddarar kuma na shiryawa wannan zaman aure da dadi babu dadi zan zauna, ko da Abdul zai rika yanka naman jikina ya siyarwa ne. Zan jure ko wace kalar azaba da ukuba ko da kuwa ita ce zata yi silar ajalina...

An samu delaying gurin tashin jirgin, karfe biyu da mintuna goma sha biyar ya kamata mu tashi amman ba mu tashi ba sai misalin Karfe uku daidai muka tashi daga filin jirkin saman Aminu Kano, bayan mun yi bankwana da yan'uwan Abdull, har na ji ina ma ace ni ma nawa yan'uwan sun rakoni kamar yadda na shi suka yi. Abdull ne ya saka min belt ya sakawa kasa ya rike hannuna ganin yadda nake jin tsoro sosai lokacin da na yi arba da jirgin for the first time.

Sai da muka yi nisa da kasa sosai jirgin ya fara tafiya sannan ya cire min belt din shi ma y







https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0



Can cikin bachi na ji ya taba an taba ni, hakan ya saka ni bude ido sai na ga wutar dakin a kunne.

 Taso mu yi magana

Ya riko ni na tashi zaune ina sanye da kayan bachi wando ne da ya tsaya oya cinyata dai karamar riga marar hannu. Shi kuma yana sanye da pajamas dark green.

 Me ya faru?

Na murza ido. Ajiyar zuciya ya sauke ya kama hannuna ya rike.

 Noor ina son ki fahimce ni please, ba wai bana son haihuwa ba ne kawa...

 Indai maganar zubar da ciki ne, zai fi maka kyau ka tafi ka kwanta, ba zan zubar ba Abdull

Ya kara sassauta muryarsa alamar rarrashi.

 Baki gane ba, ni gani nake ma kamar ba zaki iya haihuwa ba, kalli kunkurunki ma fa, karami ne sosai kuma be kamata ki fara haihuwa da kurciyarki kamar haka ba, Safeena ma sai da muka yi shekara biyu tukuna ta fara haihuwa...

 Babu wasu kalamai da zaka iya daure ni da su Abdull, ni dai kawai abun da zan roke ka ka aje sirrin nan a tsakaninmu, bana son yar'uwata ta san mijina ya juya min baya, kuma bana son ta san baka son abun da zan haifa, mu kwana lafiya

Na juya na kwanta na ja bargo na lulluba har kaina. Kwafa na ji yayi ya tashi ya fice ba tare da ya kashe min wutar dakin da ya tarar a kashe ba. Tashi na yi zaune na ina hawaye. Daren be mini dadi ba saboda haka ban runsa ba. Sai bayan na gama sallah na kishingida jikin gadon dake dakin sannan bachi ya dauke ni kadan, domin ban dade ba na farka saboda kiran da yake ta kwala min kamar zai tashi gidan.
Na zabura na fito falon ina kallonsa.

 Karfe Nawa ace baki hada abun karyawa ba? Ko salon na yi magana ki ce layi kike ke ga mai ciki

 Zan shiga na hada yanzu

Ita ce amsar da na bashi sannan na cire hijabina na aje akan kujera na shiga kitchen na fara dora ruwan zafi, ina tsaka da soya kwai amai ya taso min domin bana son karnin kwai a yanzu. Da gudu na fito na shiga bandaki na yi amai na wanke bakina da hannuna da fuska sannan na fito na shiga ba da aikina. Sai da na gama hada masa komai na kawo a dinning na aje sannan na koma kitchen din na gyara shi.

Na fito cike da gajiya sai na ganshi da shirinsa na fita. Kallon mamaki na yi masa kamin na yi magana ya ce.

 Ba zan iya cin wannan breakfast din na kazanta ba, sai ki zauna ki ci

Wani bakincikin ne na ji ya ratsani, yanzu ya san ba zai ci ba kuma ya saka na girka? Ai ya sani dole zan yi amai me yasa be girka da kansa ba? Da kallo na bishi har sai da ya kai kofa sannan ya juyo ya kalleni ya ga har lokacin kallonsa nake na ma kasa motsawa daga inda nake tsaye.

 Barakallah Maa Shaa Allah, babu abun da zaki iya yi da ni, idonki ko mugun nufinki a zuciya ba zai min komai ba, na sha tabara na sha yasin nan gani nan bari Abdullahi kam, duk wani nufin da kike da shi akaina sai dai ya koma kanki lafiya zan tafi lafiya zan dawo kuma lafiya zan cigaba da rayuwata

Ban san lokacin da hawaye ya zubo daga idona ba. Shi kuma ya bude kofar ya fita ya bar ni rumgume da bakinciki. A gurin na zauna ina tambayar rayuwa me yasa take min haka? Ina tunanin kamar na dace sai kuma wannan ya bullo min? Kamar an karfafa min guiwa haka na ji sai na mike ina fadawa kaina cewar zan iya jure wannan ma kara bakincikin gidan miji da wanda zan fuskanta a gidanmu ko unguwarmu.
Dakina na shiga ina gyarawa ina mamakin wai haka Safeena take rayuwa da shi idan yana kusa da ita ko kuma dai ni yake yi ma haka saboda baya son haihuwa? Wata kila shiyasa take son Kareem sosai take ta rufe ido tana aikata abun da zuciyarta take so. Waya sani ko ita ma bata jindadin zama da shi.

Na yi zaton shi zai aika mata da kudin mota ko ya siya mata ticket din jirgi ta zo ta jirgi amman be yi ko daya ba. Dan kudin da nake samun gunsa ne lokacin da yake so na na hada na bawa Mai gadi ya saka mata a pos ta account din mai pos din unguwarmu. Sannan na fada mata ta rubuta number wayata a takardar saboda idan ta iso ta ari wayar wani ta kira sai a na fada mata inda za a kawo ta.

Sanin dakuna biyu ne a gidan ya saka na kwshe kayan Abdull da suke dayan dakin na dawo da su dakina kamar yadda suke a da, domin ba zan kwana da ita a dakina ba shi kuma ya kwana a daki daya dabam, hakan ma be dace ba, kuma zata iya fahimtar kamar ba ma zaman lafiya tsakaninmu.

Ana gobe zata taso sai gashi ta kira ni da bakuwar number ta fada min karamar waya ce Mama ta bata tare da layi a ciki, kuma ta kara mata wani kudin da zata rike saboda expensive na hanya. Na jidadi sosai hakan zai taimaka mu rika communication kamin ta iso. Washe gari misalin 6am na kirata domin ta fada min tun asuba zata tafi ta sha. Duk bayan awa daya sai na kira ta fada min yanzu suna guri kaza da haka dai har suka sauka Lagos.

Na fada mata sunan unguwarmu ta tari okada ta hau, a nan sai da aka kara bata lokaci saboda yamma ta yi, akwai cinkoson mutane sosai. Ina jin an taba gate na fito daga falon da sauri na, a lokacin da muka hango juna ni da ita sai murna ta bare na je gurinta a guje ita ma ta yo kaina a guje ta bar jakar kayanta a gurin tana murna. Tsalle nake ina direwa tsabar murna da jindadi na ga yar'uwata, domin na san abubuwa za su zo min da sauki.

Mai gadinmu ne ya riko jakarta ya shigo da ita cikin falo, sannan mu ma muka shiga ina tambayarta ina Mama ina Baba. Sai da ta huta na kawo mata indomie da na dafa ta ci sannan take ba ni labarin yadda aka yi ta rigima kamin Umma ta amince mata ta zo saboda ganin take idan Hana ta zo sana'ar da take zata gurgunta babu mai fitar mata da awara.

Abdull be dawo gidan ba sai misalin 10 na dare, ina zaune falo ina kallo ya shigo fuska babu annuri, a lokacin Hana ta yi bachi a dakin da na nuna mata zata rika kwana.

 Sannu da zuwa

Yayi kamar be ji ba ya nufi dakin.

 Hana tana ciki na maida kayanka a dakina tare zamu rika kwana har sai ta tafi

Ya juyo ya kalleni.

 Saboda kin raina ni ko saboda me? Vabu sanarwa babu ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 komai zaki kwashe kayana ki kai can, kuma ki aje ta nan?

 Amman dai ai ba falo zata kwana ba? Kuma zai yiyu na kwana da ita daki daya ba alhalin kana mijina, na fada maka bana son kowa ya san zaman da muke yi, amman idan haka ya bata maka rai ka yi hakuri

Guntun tsaki yaja ya wuce dakina ba dan ransa ya so ba.

 Allah ka ga halin da nake ciki, Allah ka shirya min mijina ka karkato da shi ya fuskance ni

Na yi addu'a na shafa sannan na mike tsaye na bi bayansa. Washe gari ma be ci abun da na girka na breakfast ba saboda ni na girka, Hana tana daki tana ta bachin gajiya bata farka ba sai 11am a lokacin Abdull ya dade da barin gidan. Tsintsiyar dake hannuna ta karba.

 Kawo na share miki ba dan halinki ba

Na kai mata dudu a baya daman ta fini naman jiki, ni babu komai a jikina sai kashi ba kamar ita ba da take da cikar gaba da jiki, wasu har cewa suke ma ni ce kanwa ita ce Yaya. Ta share gidan tass ta gyara ko'ina sannan ta dora mana girkin rana bayan ta gama cin nata breakfast din. A nan ma mun sha hira har Mama ta kira a waya muka gaisa, na kira Baba muka gaisa sannan ya fada min Hana ba zata dade a gidanmu ba, da zarar na fara jin sauki zata dawo, a haka din ma na yi masa godiya domin yayi kokari da ya barta ta zo ma.

A ranar ma Hana bata ga Abdull ba, washe gari ma ko da ta tashi ya tafi aiki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login