Showing 21001 words to 24000 words out of 227321 words

Chapter 8 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1506

maida abun na dariya ta saki fuska ta sauko wata ta fahimci ni ma muna da matsayi, ba dan ma muna cikin yan makarantar mu kuma kowa ya san Zafeer zan aura da sai na yi mata karya na ce saurayina ne. Sai dai wani abun da ban gane kansa ba shi ne kallona take har ta gama gaisawa da Malam Sule ta mike tsaye idonta a kaina yake. Gabatar da ita da Malam Sule yayi a gurin Malam Babba ne muka ji cewar ita ce silar ciwonsa saboda kade shi da ta yi da mota.

 Malam dan Allah ba ni aron dalibar ka zan yi magana da ita

Ta nuna ni, ni kam abun nema ya samu daman so nake na nuna mata karyar arziki take da kurin banza na ga mai arzikin da be dauki kansa wata tsiya ba, ba kamar ita ba daga magana ta fara ruwan masifa. Malam ya juyo ya kalleni.

 Allah yasa dai ba wata matsala ba ce?

 Babu wata matsala Wallahi tambayarta kawai zan yi

Ta amsa fuska a sake. Malam yayi min izini da na tafi sai na mike tsaye na isa gurinta, sai ji na yi ta dafa kafadata muka fita tare bata min magana ba sai da muka isa waje, gaban motar da nake kyautata zaton ta, ta ce muka tsaya tana murmushi ta ce

 Ya sunanki?

 Noor

Na amsa a takaice.

 Shi Kareem din mai Kareem Restaurant Saurayinki ne? Ko dan'uwanki

Jimmmm na dan yi ina tunanin na zaba sakanin saurayi da dan'uwa, idan na ce mata dan'uwa zata san ina da muhimmanci amman Saurayi zai fi karamin kwarjini a idonta dan haka na amsa da.

 Saurayina ne, me yasa kika tambaya?

Ya sauke ajiyar zuciya da alama jin haka be mata dadi ba.

 Kawai na tambaya ne, saboda ina yawam siyen abinci a restaurant din, kuma a yadda na ji shi Kareem din kwararen likita ne mai duba mutane, na so na samu maganinshi tun da dadewa amman ban samu haka ba, saboda masu aikinsa basa bari na ganshi kuma asibitin idan naje bana samun na duba ni, shiyasa yanzu da na ji kin ce kin san shi na ji dadi kuma har na nemi magana dake private

 To me zan yi miki?

Gabana ya fara faduwa karta roki na yi mata alfarmar da ba ni da halin yinta.

 So nake ki hada ni da shi dan Allah

 Aa gaskiya shi baya son haka

 Taimaka min zaki yi ina cikin matsala ne, ina fama da wani ciwo ne na kansa a ciki, kuma ance idan har na samu ganinsa ya rubuta min magani zan samu lafiya, dan Allah ki taimaka min kinji kanwata, ni zan ma iya biyanki

 Aa gaskiya, ni yanzu ganin Malaminmu muka zo, gidanmu idan aka ji za'ayi min fada

 To karya kike yi ba saurayinki ba ne kenan?

Na fara saurin kare kaina.

 Aa da gaske ne mana

 To ki nuna min, indai har da gaske ne, ki kai ni gurinsa

 Toh ai yanzu baya gida

 Eh yana restaurant dinsa, daman ance idan Yamma ta yi restaurant dinsa yake zama, idan kin yarda ga mota nan mu tafi yanzu, ga mota nan sai mu shiga, ni zan ma biyaki zan baki ko nawa kike so, ni dai ke hada ni da shi kawai na yi magana ne burina

Na yi shiru ina nazari na bita ko kuma dai na ki tafiyar, idan kuma na ki tafiyar zata karyata ni, idan kuma na tafi ba lallai ne nima su bar ni na ganshi ba.

 Mu tafi? Dan Allah ki taimaka min, sai magiya nake miki kamar ba musulma ba? Ke baki da tausayi ne a zuciyarki?

Na kalleta, bata yi kama da mayaudara ba balle na ce karya take, kuma yadda ta marairaice murya nan sai na dan ji tausayinta.

 Ba zamu dade ba?

 Ba zamu dade ba, kina hada mu zan baki kudin Napep ki dawo sai ki bar mu a can

 Toh

Ta bude min mota na shiga sannan ta shiga, ni dai zan taimaka mata ne saboda ta nuna tana cikin damuwa, ba wai dan kar na karyata kaina kawai ba. Har muka isa Restaurant din wata kalma bata shiga tsakanina da ita ba. Na bude motar na fita ita ma ta fito bayan ta saka mask kuma ta maida mayafin dake wuyanta zuwa saman kanta. Gabana na faduwa muka doshi reception din ina ta sake saken kar na ga Yaya duk da na san by this time ya wuce gida domin karfe shida ta yi. Me zan fadawa ma'aikatan su bar ni na shiga ciki shi ne abun da ya tsaya min a rai, idan ma sun bar ni ban san a ina Office dinsa yake ba.

Ta inda na yi sa'a na samu abokin Yaya da duty a gurin kuma ya san ni farin sani, hakan ya taimaka min gurin fada masa ya shiga ciki ya fadawa Dr Kareem Noor ce take son magana da shi.. Babu jimawa ya dawo sai ya ce Dr Kareem din ya ce a shigo da ni ciki, dadin dake cikin raina baya misaltuwa haka na wuce gaba matar da ban san sunanta ba tana bayana abokin Yaya kuma yana gaba har muka isa office din sannan ya nuna min kofar ya juya ya koma. Na juyo na kalli matar dake jan numfashi da karfi tana fitarta wata kila saboda ciwo ne oho dai, na yi murmushi na juya na kai hannu na murda kofar na bude na shiga ciki.

 Noor... Lafi...

Be karasa ba yayi shiru yana kallon gefena, matar dake bayana tana shigowa wani mutum dake zaune tare da Kareem din da ban san waye ba ya kalleni yana murmushi ya ce.

 Noor Amaryarmu!!!

Na kalleshi da sauri ina mamakin jin furucinsa kamar wadda ya san karyar da na shiryo. Kareem din ma kallonsa yayi tare dake bayana kuma na ji ta sauke numfashi da karfi ta juya. Ni kuwa na kai hannu na taba ta wai na fada mata ga Dr Kareem din nan, sai jin na yi ta kama hannun ta murde tana kokarin karyawa.

 Safeena...

Na ji Dr Kareem ya kira sunan da karfi sannan ya nufo inda muke yana kokarin kwace ni a hannunta...







__________________________

Domin samun littafaina akan kari, ku yi following din Channel dina mai suna KHADEEJA CANDY za su samu TA KI ZAMAN AURE daga farko har zuwa inda ake, kuma a can zan rika posting duka littafaina In Sha Allah.


Amman kamin nan ku fada min wane Team kuke.

Team Kareem
Ko
Team Zafeer

Anya kuna ganin Kareem yayi ma kansa adalci kuwa? Mu'alama da matar aure mai yaya har uku?
Shin kuna ganin akwai Uba irin Baba kuwa? Babu dadi gurin matar gidan haka kuma babu gurin yayan gida?
Anya abun da Mama take yi ma Noor tana kyautawa kuwa?


Ku aje min ra'ayinku ni kuma na aje muku dogon shafi gobe idan Allah ya amince.



#KhadeejaCandy

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -7


KAREEM POV.


Kareem yayi kanta da sauri ya rike Safeena yana kokarin kwatar hannun Noor da ihunta ya cika dakinta tana fadin hannunta.

 Safeena karki karya mata hannu

Daker ya kwaci hannun Noor a hannunta ta murgude hannun har yayi yaushi, gaba daya Noor ta rude kamar wadda ta fita hayyacinta ta fadi kasa ido a zare tana haki.

 Kin fita daga hayyacinki ne? Me ke damunki?

Kareem ya tambaya cikin tsawa kamin ya juya ya rika ya kai hannu zai taba hannun Noor sai ta juyar da shi dayan gefe.

 Ya karye Azzaluma yar masan wuta ta karyashi

Noor ta fada cikin kuka. Kareem ya shiga mata magana a hankali cikin rarrashi yana kokarin rika hannun ya duba.

 Be karye ba, kawo na gani

Wani hawaye mai zafi ya saukowa Safeena, zafin da take ji a zuciyarta ya fi wadda Noor take ji a hannunta. Duk abun da ake Hafiz na zaune yana kallo be ce kuma be yi yunkurin yin wani abu ba, sai a lokacin da ya ga hawaye ya sauko a idon Safeena.

 Tirr da ke, tirr da uwa irinki... Tir da mata irinki... Tir da haihuwar ya irinki, tir da auren mace irinki, indai har sabon Allah ya kai ya rufe miki ido ki kama hannun wata ki murde saboda kishi, A gaban idona to kin yi hasara kuma kin cika tantiriyar yar iska, kuma haka da kika yi ba zai hana Kareem auren yarinyar nan, albashi sai ki hade zuciya ki mutu

Ta dauke idonta daga barin kallon Noor ta kalli Hafiz, kamin ta kai hannu ta taba hawayen da bata san da saukarsu ba sai a lokacin, ta yi murmushi ta dubi Kareem dake fadin.

 Babu komai tsakanina da Noor, wace magana kake haka? And ka cire bakinka daga magana da ita, babu ruwanka idan zaka yi magana ka yi da ni ba da ita ba, ba ka da wannan hurumin

Dauke kai Safeena ta yi ta juya ta fice daga office din. Kareem ya kalleshi cikin damuwa ya ce.

 Akan me zaka fadi wannan maganar? Zata dauka da gaske ne, Safeena tana da mugu mugun kishi, baka san abun da zai je ya dawo ba

Hafiz ya wulga masa wani wulakantaccen kallo. Har zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Noor da ta cire hijabi saboda wani azabar zafi da take jin ya game jikinta gaba daya sai kuka, Kareem ya ci albakarcin Noor tana gurin ba dan haka ba, Hafiz zai fada masa magana ne marar dadi, sai dai baya son Noor ta san komai dan haka yayi shiru. Kareem ya juya ya kalli Noor sannan ya nufi gurin da keys dinsa suke ya dauka, ya nufi inda take.

 Taso mu tafi asibiti zan duba miki a can

Noor ta girgiza kai tana jin wani irin azaba a hannu.

 Aa a barshi haka, gyaran akwai zafi ni taimakonta kawai na yi, me yasa zata min haka? Miye laifina ni?

Kareem din take tambaya tana kuka sai gumi take. Kareem yayi shiru yana kallonta cike da tausayawa ya rasa me zai ce.

 Mamana bata san na zo nan ba, jiya sai da ta yi min duka sai da kaina ya fashe saboda kai, bata bar ni na ci komai da na tafi da shi ba, yau kuma wata ta karya min hannu saboda kai, kuma na san Mama sai ta min duka ko Baba, na san haka zata min ba zan biyota na zo ba

Tausayinta ya kama shi. Ya sake mika hannu ya rika hannun ta kauce tana kokarin mikewa tsaye.

 Be karye ba Noor, duba kawai zan yi sai na baki magani, idan akwai zafi ba zan taba ba na miki alkwari

Ta kalleshi.

 Rantse

Ya daga hannunsa.

 Na rantse

 Ce ka rantse ba zaka taba min ba idan akwai zafi

 Na rantse ba zan taba miki ba idan akwai zafi

 Ce Wallahi Wallahi ba zaka taba ba idan akwai zafi

 Wallahi Wallahi ba zan taba ba idan akwai zafi

Ya rantse kamar yadda ta bukata sannan ta yarda, ya dauki Hijabinta zai saka, sannan ya nufi kofa ya bude mata, ta fita tana kuka, a yar fahimtar da yayi mata daga jiya zuwa yau ya san ba lallai ne yace ta yi shiru ta yarda ta yi shirun ba, balle yace ta hakura da kuka saboda hankalin mutane dake karkatowa izuwa garesu a duk inda suka wuce. Ya riga isa gurin motar ya bude motar ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga bangarensa ya tashi motar.
Har suka isa asibitin kuka Noor take domin a tunaninta hannunta ya samu kariya ne. Wannan karon be shiga da ita office dinsa ba ya tsaya da ita a gurin da ake duba marasa lafiya kamar kowa. Ya nade hijabin ya kalli hannu yana son ya taba yana tsoron tsare da ido da ta yi.

 Har yanzu akwai zafi?

 Eh mana, kana ganin hannun ya karkace ba

 Kashin ne ya bar gurinsa, amman ba kariya ba ce

 Wallahi Wallahi da ace ni mai gata ce sai na yi shari'a da matar nan, amman na barta da Allah Allah ya isar min, Allah yasa ciwon jikinta kar ya warke har abada

Kareem dai be ce mata komai ba sai kallonta yake kamin ya mike tsaye ya bar gurin. Be yi minti goma da tafi ba wata likitar ta zo ta duka tana duba hannun Noor.

 Ta so muje

Noor ta mike tsaye ta bi bayanta suka shiga bani dakin jinya, a nan suka samu Dr Kareem ya sanya safar hannu yana aje wasu kwalabe a saman karamin teburi. Da kai Dr Kareem yayi ma likitar da ta shigo da ita magana da ma wadda ta shigo bayanta. Sai da ta bari Noor ta zauna sannan dayar ta kama hannun ta rike gam, Noor ta kalli Kareem da sauri.

 Kace ba zaka taba ba

Ya daga hannunsa sama ya cire safar ya juya yayi ficewarsa daga dakin. Be dawo ba sai da aka gama komai, Noor ta yi kuka har ta galabaita.

 Sannu...

Ta kalleshi kurun tana hawaye, shi kuma ya kalli bandajen dake kanta sai a lokacin ya lura da ba wadda ya saka mata ba ne a jiya.

 Waya canja miki wannan?

Ta yi shiru tana haye yawu kamin ta fara kokarin sauka kam gadon.

 Ina saki je?

 Gida

Ta amsa tare da fara takawa tana rike da hannun da aka daure mata.

 Okay zan kaiki gida, amman me zamu je ce? Ko dai mu kira Yayanki ya zo asibitin nan?

Ta girgiza kai da sauri.

 To me zan fadawa Iyayenki?

Ta girgiza kai.

 Kira min Zafeer

 Waye Zafeer?

 Shi ne wadda zan aura

 To zo ki zauna

 Bana son asibitin nan bana sonta

Ta fashe da kuka.

 Shi kenan, muje na kira shi a mota sai ya same mu a restaurant haka ya miki?

Ta daga kai, sai ya nufi kofar ya bude mata ta fita sannan ya fita. Har suka isa gurin motar tana rike da hannunta kamar wadda ke dauke da jariri. Sai da ya fara tukin sannan ya kalleta a hankali cike da tausayawa ya ce.

 Noor ina kika hadu da wannan matar?

Ta bashi labari cikin kuka. Sai yayi mata wata tambaya da ya saka ta watsa masa harara.

 So na kike yi?

Ta hada masa da kwafa.

 Toh why do you lie me yasa kika mata karya?

 Kaddara da rabon sha wahala, ashe ma ta sanka ita din budurwar ka ce?

Yayi shiru be amsa mata ba ya dauke kai ya cigaba da tukinsa.

 Ina ta sanka?

 Ba kin ba ni shawara kara aure ba?

Ya fada yana kokarin kawar da maganarta.

 Wallahi karka aureta, zata hadu da wacan matar ta ka su yi ta maka hauka

Yayi murmushi sannan ya dauki wayarsa ya mika mata.

 Saka number saurayin
Ta karba tana kallon yadda wayar ta cika mata ido.

 Me yasa Mama ta dake ki? Gaskiya kika fada mata?

 Aa bata fada min laifina ba, wata kila ta dauka ko na roke ka ne

Ya kalleta.

 Duk abun da kika zaba jiya baki ci komai ba?

Ta daga masa kai tana kokarin kai wayar a kunnenta.

 Ni zan yi magana da shi

Ya karba ya kara wayar a kunnesa.

 Wa'alaikusalam ina magana da Zafeer ne

 Eh wake magana?

 Sunana Kareem, kuma ina tare da Noor yanzu haka, sai dai ba wata matsala ba ce ta ji ciwo ne a hannu shi ma ba sosai ba, tace a kiraka ka zo ka tafi da ita gida

A take hankalin Zafeer ya tashi.

 Subhanallahi garin yaya? Ina take tana lafita me ya same ta?

 Ka kwantar da hankalinka da sauki ba sosai ba ne, gata ka yi magana da ita

Ya mika mata wayar sai ta karba ta fara zuba masa shagwaba.

 Wata ce fa daga na taimake ta sai ya rike min hannu ta murde, sai da aka daure min aka gyara

 Kina ina?

 Ina cikin motar Kareem din, shi ne wadda ya kade ni jiya, gamu mun iso Restaurant dinsa ka zo ka tafi da ni gida, bana son ya kai ni kar Mama ta sake yin fada

 Noor me ya kai ki gurinsa? Me yasa baki jin magana ke? Taya ma kika tafi gurin? Why Noor why?

Ta yi shiru bata ce masa komai ba. Kareem na ganin yanayin fuskarta ya sauya ya mika hannu ya karbi wayar ba dan ya san me Zafeer din ya tambaye ta ba.

 Ka zo Kareem Restaurant ka dauke ta, idan ka zo kace a kawo ka office dina kai tsaye

Ya kashe wayar.

 Jiya na so na kira Yayanki na ce ya jikinki, amman wata damuwa ta saka ni a gaba, na manta da komai

Bayan ya karbe wayar yake fadar haka a daidai lokacin da ya faka a harabar.

 Kasan wannan matar ko?

Ta aiko masa da tambayar da be san yadda zai sarrafa halshe ya amsa mata ita ba.

 Na ji ka fadi sunanta, ni ban ma san sunanta ba, budurwarka ce?

Yayi shiru na tsawon lokaci yana kallon waje ta cikin gilashin motar.

 Aa

 Tace min tana son ta ganka, mesa ta yi karya?

 Ke me yasa kika yi karya? Already kina da wadda zaki aura akan wace hujja zaki yi karya?

Ta yi shiru, sai ya bude motar ya fita ya rufe ya bar Noor a ciki, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login