Showing 36001 words to 39000 words out of 227321 words

Chapter 13 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1520

furta ya kalli agogonsa.

 Kareem daman ina son zuwa saboda ina son magana da kai, na jidadi da ka ce a kawo ni

 Daman na lura akwai magana a bakinki ai, fada min Minene?

Na dan yi shiru na sosai kaina da dayan hannuna ina dan jin nauyin maganar.

 Daman akan gidan da zaka siyama Baba ne...

Sai a lokacin ya dago ya dube ni.

 Uhmm hmmm

 Cewa na yi me zai hana kudin ka bawa Zafeer idan dai taimakon dan Allah ne zaka yi? Zai jidadi kuma zai siye gida, amman Baba shi yana da gurin zama ai

Murmushi yayi.

 Shi kuma Baban fa?

 Shi shi fa yana da gida, kuma idan ka ba shi kudin aure zai yi, amman Zafeer zai aure ni ne da kudin ya siye gida ko ya kama haya

 Sai a bar Babanki yayi ta haya kenan? Kuma fa ba ni ne zan siye gidan ba

 Ni dai daman ina son na fadi gaskiya ne, kuma ina son na roke ka dan Allah ka taimaka masa, Wallahi Babana ya boye muku ne amman gidansa ba haya yake ba, ban fada gabansa ba ne saboda kar ya yi fushi ya ce zai koreni ko ya dake ni

Dariya ya fara yi kadan kadan kamin ta fara yin yawa ni dai na san a cikin labarina babu abun dariya amman sai kyalkyalar dariya yake har sai da na dan ji tsoro.

 Sorry

Ya daga min hannu sai kuma ya sake tintsirewa da dariya ya mike tsaye ya nufi teburinsa sai da ya fara aje wayarsa dake hannunsa sannan ya dafa teburin yana girgiza kai.

 Wallahi ban taba haduwa da yarinya kamar ki ba, ke duk yadda nake misaltaki da ex dita kin fita, amman da babanki ya san kin zo nan kin fadi haka sai ya yanka ki ko Noor

Na yi dariya na sauke kai kasa kamar wata wadda ta yi abun arziki.

 Amman kar kace ka ji na fada kace mutanen unguwa ne suka fada, ko kace Malam Sani ne ya fada maka, abokin Baba ne na san Baba ba zai rasa fada masa ba

Ya sake yin dariya har da saka hannu ya tare kwalla da suka cika masa ido.

 Ya Allah Wallahi na dade ban yi dariya haka ba, ina cikin damuwa amman kin mantar da ni komai ina son mutane masu gaskiya sai na ji kin kara burge ni

Mamakin jin cewar yana da damuwa ya saka na manta da banbarar da na yi.

 Yanzu kai har kana da damuwa? Kana da kudi fa, kana da mata da yara kana da aiki kuma zaka shiga mota mai kyau ka saka tufafi mai kyau kuma ka shigo nan ka ci abincin da kake so a haka kuma kana da damuwa? Daman masu kudi suna da damuwa sukan? Ai damuwa sai talaka ko?

 Ke dai babu ruwanki, yadda rayuwa ta nuna miki haka kike tafi da ita i wish i was just like you

Ya fada har lokacin dariya yake. Matar da ta karbi order ta kwankwasa kofar office din yayi mata izinin shigowa sai ta shigo. Sai da ta fara aje min plate uku sannan ta aje manya ledado biyu a gabana.

 Gashi, zan dauko lemu yanzu

 No need akwai lemu a nan

Ya fada sai ta amsa masa da Okay Sir sannan ta fice daga office din.

 Karka ji babu dadi daman ina son na kai ma Zafeer ne, shi ma idan ya ci abu yana kawo min

Yayi murmushi kawai ya nufi kofar office din ya bude.

 Zan je na ci abinci ke ma ki ci na ki

Ya fice, aiko a nan na samu damar saka hannun hagu na sauka kasa na zauna na ci yadda raina yake so da hagu sai da na koshi sannan na nufi fridge na dauko kalar lemun da nake so na sha. Na dawo da ragowar zan zauna kenan wayarsa da ya fita ya bari ta yi ringing ban kula wayar ba, sai dai da alama mai kiram be san rashin samu ba, sai ya kara kira. Na nufi wayar na dauka babu suna babu number a jiki sai wasu dot dot dot da aka jera kusan guda hudu.
Na amsa wayar na kai kunnenta.

 Kareem

Na ji muryar ta fada.

 Baya kusa ya aje wayar ne ya fita

 Wacece ke?

Na yi shiru domin na ji mai tambayar ta tambaya ne da tsauri gashi kuma ni din ban san me zan ce ba.

 Ke ce yar iskar yarinyar nan ko? Wato ba zaki cire kanki a lamarin Kareem ba, karya miki hannu da na yi be zame miki darasi ba ko?

A take na gane ko wacece.

 Eh ni ce, kuma yanzu ma na zo ne ya daure min hannu bayan wadda yayi min, kuma ya kawo min abinci mai kyau na ci, kuma ina cikin office dinsa ni kadai saboda na isa, kuma hannu na ni be karye ba Wallahi arziki kika ce saboda Kareem ya fada min ke daman haka kike baki da hankali ba dan haka ba da dai Babana ya kulleki gidan yari, dan Babana ya fi ki bala'i, ke din banza Kareem dai ni zai aura na fada miki kuma ki cire da shi, ballagaza kawai mai karyar ciwo, ai ciwon zuciya sai ya kashe ki, azzalumar banza da wofi

Na yi hanzari sauke wayar na aje a inda na ganta ina jin tana magana amman ban saurara ba, ina ta kallo har sai da gaji da haushinta ta kashe wayar. Na koma na zauna na natsu sosai dan kar ya gane na yi wani abu, amman hakan be hana shi fahimtar na taba wayarsa ba, domin wayarsa ce farko abun da ya fara dauka a lokacin da ya dawo dakin.

 Ya aka yi wayata ta samu maiko?

 Fadowa ta yi na dauke maka

Ya kalleni kamar be yarda.

 Noor fada min gaskiya dai kirana aka yi kika daga kuma baki son na san kin daga haka ne?

Mamaki ya kama ni jin yadda yayi saurin gano gaskiyata.

 Halam kana da aljannu

Yayi murmushi kawai ya zari tissue ya goge wayar.

 Na manta da ita sai da na fita na tuna, kuma na yi tunanin kar na dawo na samu kina cin abinci ki ji babu dadi

 Na gama zaka daure min yanzu zan tafi

Ya saka wayar aljihunsa sannan ya janyo kujera ya zauna ya dauko ledar daya shigo da ita ya bude ya dauko abun daurewar ya daure min a hankali ba tare da ya matse na ji zafi sosai ba.

 Kareem me ye tsakaninka da matar da ta karye min hannu

Ya daga kai ya kalleni.

 Me ya kawo wannan maganar?

 Har yanzu ina mamaki me yasa ta yi min haka ne, amman dai ko miye na barta da Allah ba zata ga alheri ba

Be sake ce min komai ba har ya gama sannan ya kalli plate din da na ci tsutsusar nan da nake ta kwadayi.

 Ke kika ci? Daman zaki iya cin wannan?

 Tana da dadi, baka taba ci ba?

Ya girgiza kai.

 Bana cin sea food, bana cin English breakfast

 Ni kam na ci, akwai dadi ai

 Idan ba ki ci ba ai ba ke ba ce

Ya nuna ni yana murmushi.

 Wannan ce Noor din da na sani daman wacan da gani a gidanku shiru na san ba ke ba ce, this is the real you

 Na gode Kareem, dan Allah ka fadawa abokinka gaskiya idan yana son taimako to ya taimaki Zafeer

Ya amsa min da kai yana lumshe ido ya bude.

 Zan fada masa

Na mike tsaye na dauki ledodin da hannun hagu. Sai ya mike tsaye shi ma ya karbi ledodin ya aje ya matsa da ni kusa da teburinsa ya zari tissue ya goge min yatsuna dake da maikon naman da na ci, domin abinci dai da spoon na ci.

 Haka nan kake yi ma matar ka ko Kareem? Ni ma Zafeer zai iya min haka yana ririta ni kamar sarauniya

Yayi murmushi ya kalleni.

 Irinku haka ake tafiyar da ku sai a samu yadda ake so, ita mace awaza ce idan kace zaka lankwasa sai ta karye sai dai a lallaba, duk yadda mace yake ni ina iya zama da ita da zarar na karance ta, rayuwar duniya sauki ne da ita sai wadda ya so wahalar da kansa

Na mayar masa da murmushin sannan ya ce.

 Zauna bari na kira Nabil ya zo ya kai ki gida

 Bana son ya kai ni gida da kaina zan tafi

Na fada masa saboda na san fada Ya Nabil zai min akan ka karbi takeaway.

 Ai be san kin shigo nan ba, ya kamata ya sani

Ya dauki wayarsa ya taba sai na ga ya dago ya kalleni da fuskar mamaki amman be ce min komai ba ya maida idonsa kan wayar ya kira Yaya. Babu bata lokaci Yaya Nabil ya iso suka gaisa sannan ya fada masa ya kai ni gida.

 Toh ranka ya dade an gode Allah ya saka da alheri, ban ma san ka shigo ba sai da na neme ta aka ce kai ka kirata

Ya daga masa kai, ni kuma na mike tsaye

 Ko ka saka ta Napep tun da aiki kake

 Okay Oga

Ya amsa sannan ya daukar min ledodin ni dai ban yarda na kalleshi ba har na fice office din. Na yi zaton ko Yaya zai yi magana yace ka karbi takeaway amman be ce min komai ba har muka isa titi ya tari Napep ya saka ni ya fada masa inda zai kai ni. Mai napep yaja mota ina jindadin yadda be tsangwame ni ba, na kalli ledodin na yi murmushi daman leda daya ta Zafeer ce daya kuma ta Baba saboda plan din da nake da shi. A bakin hanya ya sauke ni, ban shiga gida ba sai da na fara biyawa gidan da Mama take zubin adashe na yi mata karya cewar Mama tace a bata dubu goma a ciki tana da wata lalura zata maido zuwa gobe, na yi sa'a Talatu ta ba ni dubu goma bayab ta gama karanta min na fadawa Mamarmu kar ya wuce gobe. Na karba na fito gidan na nufo gidanmu cikin natsuwa ni kaina na san na samu canjin rayuwa daga jiyan nan zuwa yau na natsu sosai.









____________________

Gashi nan na yi long page na biya bashin na jiya =??

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Talla=?G?=?G?=?G?*

https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA
*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARAS'DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORAL'*

*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI=ت?BA MUNA KAYABAL' HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*

*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER =؃?=؃?=؃?=؃?=؃?=?I? GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328

*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*

*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*

AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA=؃?=؃?=؃?

GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA=?F?=?F?=?F?




*Chapter - 11*


Ban bude ledar da na isa da ita gida ba, kudin ma sai na boye ban bari Mama ko Hana sun gani ba. Bayan na yi sallah La'asar Mama ta kira ni na fito ta ba ni danta malelen da aka girka, ko karba ban yi ba na ce na koshi daman wadda ya ci kayan dadi me zai yi da wani malele.

 Me kika ci?

 Na ci abinci a can

 Yanzu gaban maza kika zauna kika ci abinci saboda ki nuna ba ki da tarbiya? Kuma rokonsa kika yi? Ai na ga kin dawo da ledodi kin boye baki nunawa kowa ba. Yanzu duk abubuwan nan da suka faru kwana biyu ba su isa su zame miki darasi ba? Wai Noor idan baki yi hankali yanzu ba yaushe zaki yi hankali? Matukar baki canja rayuwa ba zaki sha wahala nan gaba, ki ce yayar Hannatu amman ke ce shashasha

Na sauke kaina kasa ina jin kalamin na Mama yana min yawo a zuciya ta bangaren rashin dadi.

 Ba a gaban maza na ci ba, ni kadai ce lokacin da na ci, ya bar ni a dakin ne sai da na koshi sannan ya dawo

Bata sake ce min komai ba, kuma daman bana wani abun fada dan haka na juya na koma dakin. Ban sake fitowa ba sai da aka yi sallah magariba ina gama sallah na kwanta ina jiran Yaya ya shigo na ari wayarsa na kira Zafeer domin na san Mama ba zata bar ni na fita na je gidansu Zainab na ari wayar Mamanta.
Bayan Sallah Isha'i Baba ya shigo gidan, ina jinsa na yi saurin dauko leda daya da na shigo da ita na dauko kudin da na boye na fito na tare shi.

 Baba sannu da zuwa

 Yauwa

Ya amsa min kamar yadda ya saba da daure fuska, na dan tsawon wuya na leka dakin Mama na ga bana hangota sannan na mika masa ledar hannuna.

 Gashi Zafeer yace a baka

Na hada masa da kudin da na karbo gurin adashen Mama. Baba ya karba yana dubawa.

 Me ye ne

 Ban sani ba ni ma cewa dai yayi a kawo maka

Ya bude abincin da ya fara expire saboda yana cikin leda kuma gashi na masa mugun boyo. Sannan ya kirga kudin na yi zaton dadi Baba zai ji saboda ya min gori jiya cewar Zafeer be taba ba shi ko dubu goma ba, a tunanina hakan da na yi zai haifar da faeinciki da jindadi a zuciyar Baba sai na yi arba da tsabanin haka.

 Fada masa kika yi? Ni fa bance ya kwashe kudin aikinsa ya kawo min ba, kar ya zo yana kuka da ni, kuma ban ce yayi sata ya ba ni ba, duk abun da zai biyo baya kar ya saka sunana a ciki

Na yi shiru na rasa me zan ce, ban san taya zan kare Zafeer ba, haka kuma ban zan iya fitowa na fadi gasjiyar cewar kudin adashen Mama ne ba, kamar yadda kalaman Baba basa min dadi a yanzu.

 Wai ance ana kiran in ji Zafeerrr

Almajirin da aka aiko ya fada bayan yayi sallama. Na kalli kofar Baba ma ya kalli kofar a daidai lokacin da Mama ta fito daga dakinta tana kallon ledar dake gaban Baba

 Je ka ce tana zuwa

Mama ta fada, sai Baba ya mike tsaye.

 Bari na fara magana da shi daman ina nemansa

Kan kace kwabo Baba ya mike tsaye ya fice daga gidan, ban ji komai a raina ba domin na san duk tsanani Zafeer ba zai tona min asiri ba ko da kuwa be san me na shirya ba ba zai taba fadar abun da zai haifar min da matsala ba. Bayan fitar Baba Mama ta dube ni ta ce.

 Fada masa kika yi Baban ki yace be bashi komai ba?

Na sauke kaina kasa kamar ba ni ba, cikin na tsananin ladabi da ban san ta ina yake fito min ba na ce.

 Aa Wallahi ban fada masa ba, kawai dai kila anyi dace da yayi niyar aikata hakan ne

 Amman wannan ledar tun dazun kika shigo da ita

 Eh shi ya bani, acan ya siya komai sai ya ba ni tare da kudin

 Allah yasa gaskiya kika fada, domin idan na gano rokon bawan Allah nan kika yi kudi saboda ki bawa Babanki sai na miki mugun duka a gidan nan

A take cikina yayi kuka ba irin kukan yunwa ko wahala ba, kukan tsoron shan duka da na san idan Mama ta gane a gurin adashenta na karbo kudin nan sai ta fi cin ubana ma fiye da roko

Ta dauke ledodin ta shige ciki ni kuma na juya na koma dakinmu ina ta tunanin matafitar da ban yi tunaninta ba tun farko. Bayan kamar minti talatin Baba ya dawo cikin gidan ya yana kwala min kira.

 Noor

 Na'am

Na amsa da sauri sannan na mike tsaye na fito.

 Tafi yana jiranki

Na juya na koma cikin gidan ina jin faduwar gaban da ban saba ji ba, kuma ban san na Miye ba. Hijab dina na dauko na saka zuciyata bata raya min ransa zai bace idan na ba shi abun da na zo masa da shi daga gurin Kareem ba, kwalkwalwa ta mantar da ni gargadi da yayi min har sai da na fita rike da leda na tsaya a gabansa ina kallon yadda yanayinsa ya canja ba kamar yadda na saba ganinsa ba.

 Zafeer

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalleni.

 Noor Baby Noor

Yanayin yadda ya kira ni ma muryarsa ta sauya, ina karantar damuwar dake tattare da shi tun kamin ya fada min.

 Baba ya maka wata magana marar dadi?

 Mai dadi ce amman dacin mai daci ne a gareni yanzu

 Me yace maka?

Ya kalleni.

 Baku yi magana da shi ba?

 Magana daya ce kawai? Ni dai ka fada min

Na masa magana a shagwabe kamar zan masa kuka.

 Baba ya min godiya, me kika bashi?

 Kyauta da kudi dubu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login