Showing 210001 words to 213000 words out of 227321 words

Chapter 71 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1503

baki.

 Kika bar shi a waje kika shigo Noor

 To ba Kareem ba ne wai yace na shiga gida da kai, kuma na shiga

 Ina kika ga Kareem din?

 Yana waje

 Oh Allah ya kyauta, amman haka au wulakanta mutum ne ba kyau, be kamata yayi haka

Na turo baki gaba, ina jin lokacin da aka sake aiko yaro kirana ban fita ba, sai bayan da yaron ya juya ya koma sannnan na tashi na bi bayansa na fita. Kareem kawai na samu tsaye a bakin kofar motarsa na nesa da gidan ta inda ya fakata.

 Ina wuni?

Be amsa min ba ha jefo min tambaya.

 Ba na ce ki kira ni ba?

 Mantawa na yi

 Amman shi wannan da ya sallamo miki ai baki manta ba ko?

 Ban san ko waye ba kawai dai ance ana min sallama da na fito kuma sai na ga shi ne

 Ke da kika ce ba zaki yi soyayya a yanzu ba, miye na kula shi? Ai da sai ki fada masa

 Ba mu gama gaisawa ba ka ce na wuce cikin gida kuma na tafi

Ya gyara rayuwarsa fuskarsa babu alamar wasa ya ce.

 Noor bana son ganinki da kowa, zuciyata kamar zata fashe take ina kishinki

 Kareem kana so na har yanzu?

Ya kalleni irin duban nan dake saukar da rashin natsuwa ga wanda ake yi ma shi har sai da sigar jikina ya tashi.

 To ai na ga kana da wadda zaka aura kuma kake so ka fada min you're my best friend kawai

 Kin san me yasa na zo nan?

Na girgiza kai.

 Saboda wata magana mai muhimmanci da Hajiya ta yi min a Jiya bayan na bar nan, kuma ganin wannan Ustazun da na yi ya karfafa guiwar abun da nake tafe da shi

Natsuwa na yi sosai ina kallon fuskarsa mai cike da kwarjini da haiba.

 Na ce ki kira a jiya me yasa baki kira ni?

Na yi shiru na maida kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna.

 Saboda baki bukata ne Noor? Kina jin kamar na takura miki ne?

Na girgiza kai da sauri.

 Aa

 To miyasa?

 Na ji haushi ka ce ka yi budurwa shi ne na yaga katin

Ido ya kura min yana kallona sai kuma yayi murmushi.

 Jiya bayan na bar nan, na tafi gida gurin Hajiya wadda i???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta ce uwa a agaremu yanzu, ta yi min maganar aure sai na fada mata akwai wanda nake so sai dai ina ganin kamar da dan sauran lokaci be kamata na kusanto da bukata ta aure a gareta yanzu, sai ta tambaye ni wadda nake so yarinya ce ko babba budurwa ce ko bazawara, na fada mata ko wacece ke, sai ta tunatar da ni abun da na manta, cewar aure na biyu zan yi na yi kokari na auri wadda nake so, kuma take fahimtata, kar na cilasta, and i have no time to wast, kuma tana da gaskiya be kamata na daukarwa zuciyyata abun da ba zata iya ba, ba zan miki karya ko na karya zuciyarko ba. Macen da kika ji ta kira ni jiya, kanwata ce na kira ta da Baby ne saboda na auna reaction dinki

 Kenan babu wata sabuwar budurwa da ka yi?

 Babu, ai na fada miki idan har ba zan sake miki ba, to wata ba zata same ni ba, i know baki gama hucewa daga tabon da Zafeer yayi miki a zuciya ba, but noor ina son ki sani ina kaunarki kuma ina rokon alfarma ki ba ni dama ta aurenki a yanzu idan zaki iya, Noor ba zan iya bari ki yi aiki ba ko da kin yi Karatu you need yo know this, Yusura ma ta yi karatu kamin na aureta amman bayan na aureta na hana ta aikin saboda bana ra'ayin haka

Yayi shiru na wani lokaci kamin ya cigaba.

 Bana son na karya zuciyarki da wani abun da za ki tararda ba hakan ba ne, burina na mantar da ke duk wani kunci na maida ke yar gata, amman hakan ba zai samu ba sai da amincewarki, Noor shiga karanta a yanzu zai janyo miki idon maza kala kala kuma ina da kishi, bana ra'ayin karatunki kawai na goya miki baya ne saboda abun da kike ra'ayi ne

Jiki ya fara sanyi kalamansa sun sanyaya min guiwa kuma sun saka ni tunani da jin wani iri.

 Noor I'm here to beg for your love, kin tambaye ni dazun, zan amsa miki yanzu ina sonki Noor irin da babu wanda ya taba miki irinsa a duniyar nan, idan aka cire iyayenki babu wanda ya kai ni sonki a duniyar nan

Na dan matsa baya idanuwa na cika da hawaye.

 Kareem ban shiryawa wannan ba, ni soyayya bata burge ni a yanzu, babu wasu kalamai da namiji zai fada ya siye zuciyata, ma dandana ba daya ba biyu ba na san yadda abun yake, ni bana sha'awar aure a yanzu

Ina maganar hawaye na sauko min.

 Yanzu ne lokacin da ya kamata ki yi sha'awar aure saboda ki dandani dadin dake cikinsa, shim ba kin taba fada min ba haka zaki yi ta yin aure har ki dace? Taya kika canja sha'awa? Idan kika ce ba zaki yi aure a yanzu ba, to baki yarda wannan jarabawa ba ce

Ya matsa kusa da ni calmly ya ce.

 Please stop crying bana son zubar hawaywnki, i can't force you idan baki
shirya ba, zan jira sai kin shirya kin natsu da hakan Noor

Na share hawayen kamar yadda ya bukata sai dai kuma tambayar da ta fito daga bakinsa ta saka wasu hawayen sauko min.

 Noor kina so na? Zaki iya aurena?

 Zuciyata babu komai a cikint yanzu sai tsoro da fargabar abun da zai faru da ni, na rufe babin aure ko soyayya Kareem, ina jin tsoro duniyar nan, da zaka hakura da ni da zan fi kwanciyar hankali

 Zan iya hakura da rayuwa Noor, na zabi mutuwa saboda na san idan na mutu zan manta da komai, amman ba zan iya hakura da ke ba son wani abu ne da ba zai taba mutuwa ba, na so ki Noor tun kamin na san ina sonki, na so ki bayan na san ina sonki, and now kaunarki kara tasiri take a zuciyata, i don't want to losing you

Kalamansa suna tsara zuciyata kalmar ina sonki a zahiri aikinta ya riga furucinta isowa a gareni, na sani Kareem yana so na, and na san a yanzu ya shirya aurena kamar yadda ya fada kuma ya kudurta kamin na bar shi ya auri Zafeer. Amman tsoro nake kar shi ma bayan auren wani abu ya faru, kar sai ya aure ni ya fada min ba dan Allah ya aure ni ba, kar sai ya aure ni wata fitinar ta taso.

 Tsoro kike ji?

Na daga kai har sau uku ina kuka sosai, ya daure ni da kalamai bana son na amsa da aa, sai dai kuma ina tsoron abun da zan je na tarar.

 Ki yarda da Allah, na baki dama ki bawa Allah zabin, ki kai kuka ga ubangiji ki roka ya zaba miki tsakanin aurena da fasawa, ni ma zan yi zan daga miki kafa na zuwan lokacin da zaki gamsu da zabin Allah, amman idan na dawo amsa daya nake son ji Eh ko Aa, abun da duk kika ji zuciyarki ta natsu da shi to shi ne abun da Allah ya zaba miki. Na barki lafiya

Ya bar ni tsaye a gurin ya nufi motarsa ba tare da ya juyo ya ba. A zauren gidan na tsuguna na rufe fuskata da tafin hannayena, irin zuwan da Kareem yayi shi duka mazajen nan suka yi, banbancinsa da sauran shi yace na bawa Allah zabi kuma zan yi hakan. Amman bayan shi babu wanda yake zuwa min da sunan yaudara ko cutarwa, nuna min suke su mutanen kirki ne, kuma zan samu rayuwa mai kyau idan an yi aure, idan kuma aka yi sai labarin ya canja abun da nake kyautata zaton zanje na tarar sai na riske shi a baibai.

Ina shiga na samu Mama na fada mata abun da Kareem ya zo min da shi. Sannan na bayyana mata tsorona, na abun da zai je ya dawo.

 Akwai tsoro ba ke kadai ba, ni kaina ina tsoron abun da zai faru, amman ina ta yi miki addu'a kuma na san Allah zai karba, ko ma ya karba, ga dukan alama idan kika aure shi zaki jidadi, amman halin nan da Safeena...

 Wallahi Mama Safeena ta zo nan ta fada miki duk abun da ta fada saboda kawai ta bata shi a gurinki domin burinta ta aure shi...

Na fada mata abubuwan da Safeena ta yi da kuma halin da take ciki yanzu, kana na jaddada mata cewar Kareem ya canja yayi kuskure amman a yanzu ya tuba, kuma Allah ma yana son bayinsa masu tuba balle kuma mu da muke yan'adam, kuskuren da Kareem ya aikata ba zai zama hujja ta hana ni aurensa ba. Kaddarata kawai nake tsoro kar ta juya bayan auren.

Kamar yadda ya fada haka na dukufa da aikatawa, na kan tashi a tsakiyar dare na yi sallah nafila raka biyu, idan na gama na yi salati ga Annabi Muhammad S A W, na yi daga hannu na yi kirari ga ubangiji sannan na roko zabinsa a cikin auren Kareem ko hakura, ban maida sati ba Allah ya saukar min da natsuwa da aminci akan Kareem tare da hope na jin cewar kamar zan dace.




KAREEM POV.

 Ya Allah ka sani ina son Noor, ina kaunarta, amman Allah ka fimu sanin abun da ya dace da mu, ka fi mu sanin daidai a cikin zabinmu ko akasin haka, Ya Ubangijina ina rokonka idan aurena da Noor akwai Alheri, ya Allah ka saukar mata da natsuwa da gamsuwa akaina, kuma ka hada kan mu cikin sauki, Ya Allah ina rokonka idan ni din ba alheri ba ne a gareta ka sanya min hakuri a zuciyata, kuma ka sassauta min kaunar da nake mata Ya Rahamanin Raheem, Allah idan ni da ita alheri ne ga juna Allah ka ba ni ita, idan kuma ka ba ni Allah ka hana ni cutar da ita, duk wani abun da zai yi sanadin zubar hawaye a idonta ka hana ni aikata shi ya Allah

Ita ce addu'ar da yake a kowane dare, ya san yana tsakanin kaunar Noor kuma baya jin zai iya cutar da ita ko da kan akaifa ne, sai dai be san gaibu ba, domin matsalolin da suka biyo baya har suka shafeta ta bangarensa be yi tsammanin zuwansu ba. Wannan ya saka yake neman zabin Allah kuma yake addu'ar nema tsare daga cutar da ita.

Baya dagawa sai an yi sallah asuba, idan ya gama yake rama bachin da be samu yi ba na yan sa'o'i kadan sannan ya tafi gurin aikinsa. Each and every day kaunar Noor karuwa take a ransa, he miss her so much be dauka zai iya hakuri kamar yadda ya fada mata cewar zai daga mata kafa ba.

A yau ma sai da yayi mafarkinta yayi mafarkin rayuwar aurensu irin yadda yake a kowane dare tsabar saka ta da yayi a ransa. Mika yayi hana hamma sannan ya sauke kafafuwansa ya duba wayarsa Miss call ya gani guda daya da bakuwa Number. Be damu ba ya aje wayar ya shiha bandaki yayi wanka ya wanke bakinsa sannan ya fito ya shirya kansa, daman shi gwanin kamshi ne tutare sai da ya kusa karar da kwalba.

Yana tsaka da murza wani oil perfume a wuyansa wayarsa dake aje ta yi vibrating ya kalli wayar kamar ba zai dauka ba domin baya son picking bakuwar number, ba dan ma gudun uzuri ba zai iya saka wayarsa a bangaren da idan ba shi da number ka ba zaka iya kiransa ba.

 Hello

Ya saka wayar a speaker ya aje ta akana madubin yana cigaba da shirya kansa. Shiru ba a ce komai ba kuma ba a kashe wayar ba. Kallon wayar yayi da dan mamakinsa sai kuma yayi murmushi tunawa da yayi da mutum daya ke iya masa haka ko ma take yi.

 Noor My Love besty, my Beb

 Na'am

Ta amsa a shagwabe da sauri ya aje agogon da yake shirin sakawa ya dauki wayar ya cireta a speaker ya kara a kunnensa.

 Hey Beautiful, how are you?

 Ina tafiya, i just miss you

Ya lumshe ido zuciyarsa ta yalwanta da farincikin da be taba ziyarta sa ba, yayi murmushi mai matukar kayatarwa.

 I miss you more, do you want to see me?

 Uhmm Umm

Ya shafa kansa ya kwanta saman gadon, this is not the first time da Noor tace tana missing dinsa but one hit different.

 Okay your prince will arrived soon

Ya mike tsaye da sauri ya aje wayar ya kalli kansa a madubi, sai ya ji kamar dress din be masa ba.

 Noo nooo nooooo

Ya cire tufafin da sauri ya saka wasu ya dauko wani turaren ya fesa sannan ya dauki keys dinsa da waya ya fice da sauri. Tafiyar minti 35 ya nade hanya yayi ta a minti goma sha biyar. Daf da kofar gidan ya faka ya dauki wayarsa ya kira line da ta kira shi.

 Hey Beautiful na iso

 Okay

Ya sauke wayar yana kallon screen din tsabar kauna heart wallpaper ne a jiki amman fuskar Noor yake gani tana masa murmushi, saboda kaguwa. Bude motar yayi ya fito ya tsaya saitin kofar gate din yana kallon kofar. Cikin natsuwa ta fito gidan tana tafiya a hankali, he count every step nata har ta iso gurin da yake tsaye.

Kyakkyawan murmushin dake a kyakkyawar fuskarta ya sautar da shi kamar be taba ganin mace mai murmushi ba haka yake kallon Noor, ina ma ace zai iya bude cikinsa ya sakata ciki ya rufe.

 Ina kwana...

Sai da ta fada har sau uku sannan ya dawo daga hayyacinsa a rikice ya ce.

 I'm... I'm.. Sorry, Hey Beautiful, Good morning

Sai kuma ta yi shiru kamar wadda ta rasa abun fada. Shi kam kallonta kawai yake kamar ya cinyeta zuciyarta har zalzalza take, be taba jin Noor a yadda take jinta a yau ba, gaba daya ta cika idanuwansa ta cika zuciyarsa da kauna. A hankali ya sauke idonsa kasa yana murmushi he then realize hannayenta duka biyu suna a bayanta a boye.

 Why are you hiding your hands? Me ya faru?

 Lalle aka min bana son kowa ya fara gani sai kai

Ya daga kirjinsa.

 Of course my Queen, i will glad na zama na farkon fara ganin lallenki my Lord

Ta yi murmushin da ya kara mata kyau musamman da ya bayyana fararen hakoranta, and her giggle laugh is something else da ya ba shi pleasure. Ta cire hannun a bayanta ta daga sama saitin fuskarta ta rufe fuskarta da su ta yadda zai iya ganin tafin hannun da kyau..

_Yes i will marry youd'_

Shi ne rubuce a tafin hannunta da jan lalle with symbol of heart. Karantawa yake yana kara karantawa yake ta karantawa yana hada kalmomin a zuciyarsa kai ka ce ya manta yadda ake karatu gaba daya.

Hannayensa ya saka ya rufe idonsa ya girgiza kai sannan ya bude ya sake kallonta ya shafa kansa ya juya ya kwanta jikin motaraa how he wish yana da damar da zai rumgume ya daga ta sama ya juyata just to show her how happy he's.

 Alhamdullahi Alhamdullahi Alhamdullahi

Ya furta har sau uku yana jin farincikin da be taba jin irinsa ba, domin be aure matar da ya zaba da farko ba, auren hadi aka yi masa da Yusura, wannan joy and happiness din be san shi ba sai yau. A yanzu take jin zai yi aure abun da ake kira da aure aure that Worth it. Ya taka ya isa gabanta ya tsaya sai ta sauke hannayen a hankali fuskarta da murmushi mai sanyaya zuciya, bata taba masa kyau irin yau ba, be taba jin yana kaunarta irin yau ba.

Be taba jin yayi sa'a da dacen rayuwa irin yau ba, ashe haka ake ji idan ka samu wanda kake so? Haka felling din yake? Yau Noor ta amince masa Noor ta yarda ta zama matarsa gonarsa mallakinsa. Har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya sauke numfashi ya daga kanshi sama ya sake gode ma Allah, bayan kyautar Yaya da Allah yayi masa idan aka cire lafiya da musulunci be taba samun kyauta mai nauyi mai girma mai faranta rai irin ta yau ba.

 Noor...

Ya furta sai kuma ya jimke hannunsa kalmominsa sun kare, yau Noor ta gama masa komai, godiya zai mata ko kuma zai lissafata mata yadda yake kaunarta ne, domin abun da yake ji a yanzu ya wuce so, kauna ce, hawayen da ya gani yana zuba a idonta yayinda fuskarta take dauke da murmushi ne ya saka jin kamar duniyar ma ta rikice.

 Come on girl, no more tears ever

Ta dafa saitin zuciyarta tana magana cikin kuka mai dauke da farinciki.

 Ban taba amincewa zancen aurena yayi murna ya nuna min jindadinsa kamar yadda ka yi min a yanzu ba, you make me feel special... Allah yasa ka rike ni amana

 But you're special, idan har zan ci amanarki a yanzu ko nan gaba kada Allah ya ba ni ke Noor

Ta share hawayena tana murmushi, mota ya nufa ya bude ya dauko tissue ya bude wani gurin ajiyarsa ya dauko wani tissue da aka yi amfani da shi ya boye a hannunsa sannan ya fito ya mika mata ta karba ta share hawayenta, sai ya mika mata hannu ta bashi ya ciro hannunsa dake baya tsoho tissue da ta taba goge hawaye da shi a gidansa ya dauka ya aje. Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login