Showing 198001 words to 201000 words out of 227321 words

Chapter 67 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1559

take saboda lamarin da ya faru. A madadin yin shiru sai Yaya ya fara nasa fadan.

 Abun haushi yanzu Zafeer din ne zai daga hannu da kansa ya dake ki? Saboda yana jin ya kai? Ai kara da aka masa wannan daukan ma ko waye yayi masa dukan nan Allah ya saka musu da alheri, amanarki ce ta fita

 Ina zaton mahaifin Fanna ne suka aiko ayi masa duka saboda ya boye musu aure

 Idan tsoron matarsa yake tun farko saboda me zai aureki?

Mama ta fada a fusace, yau kam na ga fushin da ban saba gani a fuskarta ba. Police din sun yi dan rubuce rubuce suka sake min tambayoyi sannan suka tafi bayan sun fada mana wai za su sake daukar statement idan ya farfado, wayar Zafeer dake hannuna Mama ta karba ta mikawa Police din ta ce idan sun tafi su bashi, tun a lokacin na san Mama ba zata je asibitin ba kuma ba zata bar ni na tafi ba, haka kuwa aka yi daga gidan kai tsaye gida ta wuce da ni aka bar police biyu tare da Yaya saboda gudun barayin unguwa kar su shigo su kwashe kayan dake gidan, domin gate din a balle yake kamar dai kofar falona.




KAREEM POV.


Ya rufe motar ya matsa remote din dake hannunsa ya tabbatar motar ta rufe sannan ya nufi gurin da ya zame masa kamar dole sai yaje, baya son zaman restaurant dinsa a yanzu shiyasa ya saka wani a matsayin manajan gurin ya rika kula da komai a matsayinsa. Zama a restaurant yana tuna masa da abubuwa da yawa na rayuwa da baya son tunawa, and he has nowhere to go now daman can shi ba ma'aboci yawo ba ne haka ma ba shi da kwashe kwashen abokai, iyakanci ayi zumunci sai kuma idan wani abu ya taso.

Yana rike da gorar ruwansa ya ratsa ya shiga gurin, kusan tun da ya dawo ba daga jinya ba ya da wani gurin zama sai nan, yanayin gurin yana masa dadi, kuma yana tuna masa da abar kaunarsa. Yayi mamakin hango mutum kwance a gurin timinti da ya saka aka gina a gurin saboda da zama, karasa yayi gurin sanye da facing Cap dinsa ya leka fuskar wadda take kwance ga mamaki sai ya ga Noor....

Yanayinta furucinta da kuma acting dinta ya karantar da shi bata san me take ba, ko me ya faru da ita abu ne da ya taba ta sosai ga jikinta na nuna duka, ga shi kuma ta furta da bakinta, yayi duk abun da zai iya na dawo da ita hayyacinta na zuba mata ruwa a kai da hura mata iska kuma yayi nasara ta dawo hayyacin nata. Binta yayi da kallo har ta fice gurin, sai da ya tabbatar ta yi nisa, sannan ya bi bayanta da motar, a lokacin hankali ya rika bin Napep din har zuwa gurin da aka sauketa. a zauna a motarsa ya jira har ta shiga Napep.


Nesa sosai da gate din gidan ya faka amman haka be hana shi hango lokacin da ta fito ta bawa mai napep din kudinshi ta koma ciki, kwafa yayi, sannan yayi reverse ya juya da motarsa ya dauki hanyar family house dinsu, dagawa yayi kadan ya ciro wayarsa dake aljihun wandonsa ya duba time sannan ya aje wayar ya cigaba da tukinsa har ya isa umguwarsu, ba kofar gidansu ya faka ba sai ya faka kofar wani matsakacin gida, dauki mask dinsa dake motar ya saka ya daidaita zaman facing cap dinsa sannan ya dauki wayarsa ya bude motar ya fita.

Bakin kofar gidan ya karasa ya kwankwansa yaran da ke guje guje suka fito da gudu sai ya rike daya.

 Kai Yellow yana nan?

 Aa baya nan ya fita tun dazun

 Kasan inda yake yanzu?

 Aa

 Akwai number wayarsa?

 Ba shi da waya amman dai yana da number

 Ai ka ji matsalar

Ya juya ya nufi motarsa kamin ya bude ya ji ana aika masa da gaisuwar manyan arna. Har hada hannu da hannu yake yana masa gaisuwar yan sara suka.

 Sai oga, kowa ya taba ka mu ci bantan ubansa, hayya hayya oga

Kareem ya juyo cire janye mask dinsa yana kallonsa yayi murmushi.

 Kanena ya kake?

 Hayya Babban Yaya lafiya ne, babban yayan lafiya kalau ne sai yunwa

 Karka zan faka motata a farkon layi ka same ni a can zamu yi magana yanzu nan

 Angama Babban Yaya

Kareem ya shiga motarsa yayi reverse sannan ya juya motarsa can ya koma karshen layin ya faka motarsa gefen titi. Be dade da fakin din ba Yellow ya iso da gudunsa domin ya san waye Kareem yana kyautata masa iya gwargwadon hali a duk lokacin da ya shigo unguwar ko kuma suka hadu. Kareem ya bude masa mota ya shiga, sai kawai ya kyalkyale da dariya jin sanyin ac ya ratsa shi.

 Ya aka yi ka gane ni?

 Haba Babban Yaya ai mutuwa ma ta san mai rai, kowa ya san mai bashi, ina farkon layi na hango motarka shiyasa na biyo da gudu ashe ma gidanmu zaka je?

Kareem yayi murmushi sannan ya gabatar masa da bukatarsa.

 To yanzu so kake ayi masa duka, ko ma aika shi barzahu

 Aa duka dai nake son yi masa, ban ce a kashe shi ba ban ce a karya shi ba, just duk kawai kamar yadda yayi mata, so nake ya ji a jikinsa idan akwai dadi, saboda kawai ya mayar da ita marar gata zai mata duka har ya bayyana a jikinta, shi ma ku masa dukan da zai ji a jikinsa, amman ba ban ce ku kashe shi ba, kuma ban ce ku bar wata shaida da za a gane ku ko wanda ya aiko ku ba, abu na biyu kuma karku kuskura ko harar matarsa ku yi, domin kanwata ce, idan kuma baya gidan ku nemi ta fada muku inda yake ku far masa

Kareem na kaiwa karshe ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya dauko 200k ya dora masa a cinya, a take yellow ya saka ihu.

 Kai Wallahi sai mun ci uwarta, yanzu nan ma zan far masa

 Aa aa sai dare, kuma ba kai kadai zaka tafi ba, ka nemi yan'uwa mana, kamar dai kai ma ba dan gari ba

 An gama Yaya, yanzu ina zan same shi?

 Muje na nuna maka gidan, kuma idan kun yi aiki yadda nace zan kara muku wani abu

 Ayya Sa Ayya sa Babban Yaya godiya nake, nuna min gurin naje an dauko abokan aiki mu duba ta inda zamu shiga gidan

Sai da Kareem ya sake komawa unguwar tare da Yellow ya nuna masa gidan sannan ya dawo da shi. A nan suka rabu Yellow ya wuce gurin neman abokan aikinsa shi kuma ya nufo family house dinsu. Ana bude masa gate gidan ya hango Yusura tsaye sanye da hijab tana dariya, Ex Boyfriend dinta yana tsaye suna facing din juna shi ma murmushi yake. Kallo daya Kareem yayi musu ya dauke kai ya faka kusa da su ya bude motarsa ya fita ya shiga cikin gidan.

Ya gaisa da Hajiya Hassana only domin ita ce kadai a gidan yaransa suna islamiya, kannensa ma haka Aaryam ma baya gidan Balle kuma Daddy da ba kasafai yake zama gidan da yamma ba. Be wuce 30min ba ya fito a lokacin Yusura ta sallami masoyin nata ta shiga bangarenta. Motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansa, tukin yake yana ta ganin dukan da Zafeer yayi ma Noor, har yake jin idan be saka an masa duka ba, ba zai samu peace of mind ba.

Taya kato kamar Zafeer zai rufe yarinyar da yake ikirarin yana kauna da duka? Bayan dukan ma Allah kadai ya san me yake mata a gidan na bakinciki. Yana son a koya masa darasi ne not because of yana son Noor sai dan yana jin a yanzu ya zame mata dan'uwa, ta shiga damuwa kala kala maza biyu bata dace ba shi da ake kyautata ma zato sai kuma ya zo da haka? Or maybe saboda yana jin yanzu yana da kudi ne he don't know.

 Wasu daman talauchi ne ke boye halinsu, maybe kuma he marry her saboda ya dauki fansa, sakarai kawai wawa

Ji yake kamar ya shiga gidan da kansa ma yayi masa dukan. Yayi fakin a bakin gate din gidansa a gefe saboda Safeena ta faka a inda zai fi ya shiga da motarsa cikin gidan. Sauke gilashin motar yayi yana kallonta kamar yadda take kallonsa, ta rame sosai kana kallonta ka san tana cikin damuwa domin babu kuzari a tare da ita. Ta bude matarta ta fito ta iso inda yake.

 Na je restaurant dinka ban same ka ba, na zo nan kuma Mai gadi ya hana ni shiga, kuma ka yi blocking dina ta ko'ina idan kuma na kira da wani layin baka dagawa shi ma sai ka yi blocking

 Neman na minene?

 Ina son na yi magana mai muhimmanci da kai Kareem

 Ina jinki

 Maganar ba zata yi a tsaye ba, dan Allah ka saurare ni Kareem, ka ba ni lokaci ka saurari abun da zan fada maka

 Ba ni da wannan lokacin, ki dauke motarki zan shiga gidana, kuma mutanen unguwar nan sun san bana da mata a yanzu ki daina zuwa nemana please, karki zubar min da mutunci

 Kana tsoron kar mutuncinka ya zube ne? To ka aure ni...

Kallonta yake a tsanake sannan yayi murmushi ya kwanta a jikin kujerar motar.

 Aure kike son mu yi?

Ta daga mishi kai.

 Zan aure ki only on one condition

 Minene?

Ta tambaya da sauri zuciyarta na raya mata abubuwa da yawa. Kareem ya danna horn mai gadinsa ya fito.

 Bude mata ta shiga

Mai gadin ya koma ciki da sauri domin duka umarnin da aka ba shi ya bude gate din, ita kuma ta koma motarta ta shiga ta tuka har cikin gidan, sannan Kareem ma ya shiga...
Ya zauna a kujerar dake nesa da ita domin ta riga shi shiga falon. Ta daga kai tana kallon falon.

 Mafarkina a kullum na yarda zan gina rayuwa da kai a karkashin inuwa daya, na ci buri na aurenka Kareem saboda ban saba da soyayya kowa ba sai taka, ba a taba dandana min zaki soyayya kamar yadda ka dandana min ba, abubuwa da yawa sun faru amman yanzu komai ya kau meyasa ba za mu cika burinmu ba? Baka da aure yanzu Kareem balle kace Yusura kake tsoro, ni kuma na san Abdull sakina zai yi soon

 Be sake ki ba kike fadar mu yi aure?

 Zai sake ni, a saboda ya san gaskiyar komai, ya dauke kafarsa a gidan da dadewa, ya daina kula ni, ya dauke yaransa ya bar ni da anka ya koma a dayan gidan da ya bada haya a can yake rayuwa yanzu, saboda an koreshi daga aiki, baya bani komai ni nake yi ma kaina komai, ban san a ina zan kai kukana ba, ba zan iya tunkarar iyayensa ba, ban san ko ya fada musu ba

Hawaye ya zubo mata.

 Kareem ka sha fada min cewar kana kaunata, amman wannan furuci ne, yanzu ne lokacin da zaka nuna min gaskiyar kaunar da kake min, ka aure ni sai mu rumgumi dan da muka haifa

Kareem ya daga kai ya kalli falon nasa sannan ya sake sauke idonsa a kanta.

 Daya daga cikin illar da kika min kika yi ma kanki kuma kika yi ma yaron nan shi ne haihuwarsa, wannan abun kuma zai bibiye rayuwarki fiye da tawa

 Son da nake maka ya fi wanda kake min, shiyasa idona ya rufe burina na aurenka ne kawai da gina tayuwa ta har abada tare da kai

Yayi murmushi kadan

 Hafiz ya taba fada min haka, yace kina son ki haihu da ni ne saboda a gaba ki yi amfani fa hakan ki yake ni, kuma ki aure ni, gashi baya raye amman haka ta tabbata

Ta share hawayenta tana masa wani kallo mai cike da kauna.

 Minene sharadin? Zan iya komai saboda na aureka Kareem, a yanzu kai kadai ne last hope nawa

Ya cire facing cap dinsa ya fuskance da kyau.

 Zaki iya shafe kazantacciyar rayuwar da muka yi a baya? Zaki iya maida yaron nan a cikinki ya zama labarinsa be wanzu ba? Zaki iya zama a gidan mijinki kina masa biyayya da ladabi? Zaki iya kula da yaranki ki ba su lokacinki ki kula da tatbiyarsu? Ki zauna a gidan mijinki har sai wata kaddarar da ba wannan ba ta raba?

 Kana maganar baya ne fa!

Ya amsa mata a tsawace.

 Yes!! Saboda kin bata tarihinki a shinfidar farko, da farko mahaifiyata ta hana na aureki saboda tana ganin wayewarki ta yi yawa Safeena, yadda ya kamata ace ya mace mai tarbiya ta zama baki zama haka ba, amman bayan mun rabu na san idan har wata kaddarar ta fito ke, wata kila zamu iya auren juna, i was stupid as you da farko saboda ina ganin wayewa irin ta wannan zamanin da ta kazanta ita ce soyayya, but then i realize ba son ki nake ba my Heart was young when i fell in love with you, and now kin bata komai

Bata taba zubar da hawaye irin na yau ba, kallonsa take irin kallon da mai yinsa ya rasa ta ina zai aje idonsa.

 Ba a taba fada min wani abu mai daci irin na yau ba, duk wani abun da aka taba fada min a duniyar ko na ji ko ya bata min rai, be kai na yau ba? Kuma duk haukankan da kake akan Noor ne, yarinyar da ta riga ta yi aure ta barka, tun da ta shigo rayuwarka ka sauka min, da bata shigo ba da ka aureni da baka shigo rayuwarka ba da ba zaka guje min ba

 Saboda Shigowarta rayuwata ya farkar da ni daga dagon suman da na yi na son zuciya da shashanci

Ta dafa zuciyarta tana kuka.

 Ta saka ka ka ci amana kai da ita ba zaku ga daidai ba, ta raba ni da kai kuma ra rusa aurena, ta lalata rayuwata, ba zata karewa lafiya ba, sai na lalata rayuwarta

 Me yasa ni ba zaki lalata tawa rayuwar ba? Meyasa kike bibiyar macen da bata damu da ke ba? Ku mata kullum tunaninku na cutar da yan'uwanku mata ne? Idan har ba zan bar mijinta da yake aurenta a yanzu ya duke ta ya kwana lafiya ba, to ba zan kowa ya taba ta ya kwana lafiya ba, ba kisan wahalarda yarinyar nan ta sha ba, domin ina daukar Noor a yanzu kamar yar'uwata ta jini, daga tashinta zuwa yanzu bata san wani abu jindadi ba, wani namiji be taba tsayawa tsayin daka ya nuna mata gata ba, daga uba har zuwa mazan da take aure, ke fa kin samu gata gurin iyayenki da yan'uwansa, a gidan yan'uwan mahaifinki kika hadu da Abdull su ma sun sonki kamar ba gobe, wace kalar soyayya ce ban nuna miki ba? Wane kalar gata da jindadi ne mijinki be baki ba? Ta ina yanzu Noor zata zama silar bakincikinki?

 Har bada ba zata samu farinciki ba, kuma har abada ba zaka aureta ba, kuma ba zata taba zaman aure ba, TA KI ZAMAN AURE sai ta amsa sunan nan da bakinta har karshen rayuwarta, haka zata yi aure tana fitowa shi ma wannan Zafeer din sai ya sake ta, daman be aureta dan yana sonta ba, sai dan ya gwada shaidar da na yi mata, ba dan taimakona ba da yanzu ma be aureta, ya kuma gwada kuma ta tabbata, ba zata taba samu farinciki a gidan ba, domin yar talakawa mai kwacen maza mai kwadayi irin Noor ba zata iya takara da yar mai arziki ba

Kareem ya hade rai ya ci magani kamar be taba dariya ba a rahirin rayuwarsa.

 Tell me you plan all this without telling, you're the reasons behind auren Zafeer da Noor why? Me yarinyar nan ta yi miki? Baki tausayinta da halin da take ciki ne? Karamar yarinya ce da alkamin kaddara yayi mata zane ta kasa tsallakewa

Ta nuna kanta tana hawaye.

 Ni baka ganin tausayina? Har yanzu sonta kake yi Kareem? Ai ta wulakanta ta dauki tsohon saurayinta saboda yayi kudi, kuma na san sai ya nuna mata azaba har wadda bata yi mafarki ba, kuma zai sake saboda aure da saki kaddararta ce, har abada ba zata yi zaman aure ba


 Karya kike baki san komai akan kaddara ba, kuma bari na tabbatar min da wani abu, idan Zafeer yayi wawancin sakin yarinyar nan Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Sai na aureta, ko ana ha maza ha mata, sai na bata gata da kyakkyawar rayuwar da ta rasa, sai na maida ita sarauniyar mata, kuma Wallahi ba zan sake ta ba ko da kuwa zata gasa ni a wuta kullum, idan ba mutuwa ba babu abun da zai raba ni da ita, sai na zame mata gwarzon jarumin da babu irin shi a tarihin rayuwarta, sai na mantar da ita duk wani bakinciki, no one will break her heart again, make my words


Mikewa ta yi tsaye tana haki kamar zata shide.

 Hahh hahh ha ha ha ha ha ha ha haha ha ha ha ha ha

Ta dafe zuciyarta ta koma ta zauna, ta kasa yarda Kareem da take kallo a matsayin farinciki kuma fatanta na karshe ne a yau yake fada mata baya kaunarta kuma ya fi kaunar wata akanta.

 You re dealing with the wrong person, sai na ga bayan yarinyar nan sai na saka kunci da bakinciki fiye da wanda na saka ta, sai na raba ta da duk wani mai kaunarta yadda ta raba ni da farinciki sai na rabata da farinciki, sai dai ta ga murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login