Showing 120001 words to 123000 words out of 227321 words

Chapter 41 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1557

da muka zama kawaye ko abokai ni da shi ba. Da alama kuma tambayar tawa ta ba shi dariya har sai da ya bayyana hakoransa.

 Uhm ba ma bukatar request ai, idan ba mu zama abokai ba mun zama yan'uwa saboda Mama ko?

 Maybe

Na fada ina dan wara ido.

 Not maybe, pretty gal ban da jan aji, ko da yake kamata yayi na gabatar da kai ne, taya za ayi abota ba a san juna ba

Ya miko min hannunsa.

 I'm Abdull by name, engineer ne ina zama a Lagos for now, ko da yake ni dan garin Kano ne haifaffen garin kano aiki ne ya kai ni Lagos kuma idan na tafi na kan yi wata biyar hudu uku har fi a can, am ina da mata da yara uku a yanzu

Kallon hannuna nake wata kila dai ya manta da cewar ni da shi hausawa ne kuma musulmai, idan ba haka ba miye na miko min hannu mu gaisa. Kareem ne kadai ya taba yi min haka bayan shi kuma bana jin akwai wanda zai sake miko min hannu na karba.

 Nice to meet you Abdull

Na amsa ba tare da na ba shi hannun nawa ba.

 Ba zaki gaisa da ni ba?

 Ba ayi min wannan hallacin ba tukuna

Yayi murmushi tare da maida hannun nasa.

 Daman dai na zo na gaishe ki ne, hallaci kuma za'ayi miki nan gaba kadan, abu na karshe bana bukatar ki fada min komai a kanki na tambayi Mama wacece ke ta fada min yadda kike da kafiya da rashin magana, ban yi mamaki ba kuma saboda kina da kyau kin san mata masu kyau suna da rashin magana sosai

Na yi murmushi kadan, sai ya bude motarsa ya dauko leda ya mika min.

 Ga tsaraba ki shiga da shi gida

 Aa na gode

 Mu ai ba ma yin kyauta a mayar mana, ko dai ki karba ko na aje miki na tafi

Jin haka ya saka na kai hannu na karba, na yi masa godiya na juya sai na ji ya kira sunana.

 Noo oor

Na juyo.

 Yaushe zaki je ganin Mama?

Sai da na yi nazari kamin na amsa masa.

 Friday

 Okay see yeh '

Ya sara min da yatsu biyu sannan na yi masa murmushi as responsed sannan na juya na shiga gida. Gudun laifi ya saka na aje ma Umma ledar da ya ba ni ba tare da na bude ba.

 Shi ne abokin mijinki?

Bana son dogon zance dan haka na amsa mata da eh ina kallon turaran da take fitarwa da man shafi masu kyau.

 Ko dai son ki yake?

 Aa daman tun kamin na san Hafiz din na san Kareem

 Toh bari a aje idan mahaifinki ya dawo sai a nuna masa

Akan haka muka rabu, ban sake ganin ledar kayan ba sai washe gari bayan Baba ya fita ta miko min ledar wai ita ta dauki turare daya Baba ya dauki biyu sun dauki man shafi biyu suka bar min daya. Ban ce komai ba na karba na shiga da shi dakinmu na aje ma Hana man shafin da turare daya na dauki dayan da ya rage.

Sai da na dan kimtsa sannan na fito sanye da hijabina, kamshi kam kai kace gidanmu ake kamfanin turare na fesa wanda Abdull ya kawo min sosai saboda yana da dadi da saka sanyi zuciya.

Tsakar gidan na fito na dauki bokiti uku da nake deban ruwa da su na fice daga gidan domin yin abun da ya zame min wajibi. Fanfon da muke dibar ruwa irin wannan ne mai tuka tuka sai ka yi ta bugawa kamin ya cika, haka na yi ta wahala ni kadai ina jan karfen yana jana har na cika. Da kuduri biyu na fito daga gida, kudirin debo ruwa da kuma ziyarar gurin da na san Zafeer yana aiki, domin ban isa na tunkari gidansu da bukatar ganinsa ba.

Idanuwa kaikaiyin ganinsa suke, zuciyata tana ta muradin mai sakata farinciki, na san ba zai kalleni ba idan ma yana gurin ba lallai ya sake kaunata ba, amman ni zan ji sanyi idan na yi magana da shi ko da kuwa zagina yake. Tafiya ce mai dan nisa haka na kama hanya ina tafe ina ta sake saken yadda zan fara masa magana idan ma na sameshi a gurin.

Na tarar da Ogansa a gurin muka gaisa yayi min gaisuwar Hafiz, kana kuma ya sokeni da wata kalma mai daci.

 Noor kin guje mana ko? Duk soyayyar nan da muka nuna miki sai da kika butulci mana, gaskiya ban jidadi ba kuma na yi mamaki sosai, Wallahi ba karamin damuwa kika jefa Zafeer ba

Na aje numfashi a muhallinsa ina jin yadda bakinciki ya fara yawo a zuciyata.

 Gurinsa na zo ko yana nan?

 Kai ai Zafeer ya bar nan, tun a lokacin da kika yi aure yace ba zai iya zama garin nan ba, kwanan baya dai ya zo, amman ya koma gaba daya ya kwashe komai nasa a nan, shi ma kuma Allah yayi masa sakamako na alheri yar wani babban mutum zai aura karshen watan nan In Allah ya yarda

Indai abun da nake ji a yanxu, irinsa Zafeer ya ji a lokacin da na yi aure na bar shi, tabbas ya shiga tashin hankali, kasa rike kaina na yi har sai da na fasa kuka sai kuma na yi hanzarin rufe bakina, hawaye suke Noor yau ma muna sha'awar yin ado a fuskarki.

 Haka daman abun Allah yake, lokacin da wani ya ?i ka da wuni, wani zai ya so ka da kwana, yadda kika guje masa kika auri mai kudi, shi ma Allah ya ba shi yar masu hannu da shune, yar babban mutu kuma babbar ma'aikaciyar banki, an yi lokacin da take kawo gyara a nan, bata duba talaucinsa ko kaskancinsa ba ta aure shi

 Baka san komai akaina ba oga Lawal dan Allah karka yanke min hukunci

Na fada ina hawaye, na cira kafa daker ina tafiya kamar wata tsohuwa. Har na iso gurin bohol din hawaye nake, zuciyata zafi take wasu abubuwa nake ji a cikin kaina suna min yawo. Ban tarar da ruwan da bokitan da na kawo ba, daga ruwan har bokitin wanda ya fi ni so yayi awon gaba da su, wani mai dan hali mai son biya lahira.

Bana cikin yanayin da zan iya shiga gidajen da suke kusa da Bohol din balle na tambaya ko sun ga wanda ya dauka ko kuma sun dauko. Sai kawai na nufo gida ina tafe ina hawaye har na iso.

 Ina ruwan?

Umma ta tambaya tana daura dankwalinta.

 An dauke kayan

 Garin ya? Taya kika yi sake har aka dauke kayan? Sai kuma ki dawo min gida kina kuka, Wallahi ko kije ki nemo min kayana ko kuma na fadawa mahaifinki idan ya dawo wannan ai keta ce da sheri, kamar ya an dauke kayan kina aikin me aka dauke? Kukanki ba zai kwace ki ba

A zatonta ina kuka ne saboda an dauke kayan, bata kukan bakinciki nake ba wanda ya fi na sata ciwo. Dakinmu na shiga na dauko dubu goma da Alhaji ya ba ni a lokacin da na tafi gurin Mama na cire 1k na mika mata saura.

 Ga kudi ki siya wasu

Sai da ta gama kallon kudin baki sake sannan ta karba bata ce min komai ba ta shige dakin Mama wanda ya zama dakinta a yanzu. Ni kuma na sa kai na fice daga gidan, bana iya daga kai saboda bana son kowa ya ga idanuwa. Ina isa titi na tari Napep na hau na fada masa inda zai kai ni, domin ba ni da gurin zuwa yanzu da ya wuce can.

Ko da yake idan ma na tafi ban san me zan fada mata ba, ba lallai ne ta ji yadda nake ji ba, ni kadai nake iya fahimtar kaina.
Bayan na sauka na ba shi dubu daya ya ba ni canji na nufi gate din dake bude na shiga, a lokacin ne wata motar ta iso kusa da gate din zata fice. Daidai saitin da nake tafiya mai motar ya tsayar ya sauke gilashin kasa.

 Noor kika ce min sai friday?

Na kalleshi Abdull ne a cikin motar yana sanye da facing cap. Ban ce masa komai ba na nufi bangaren da Mama take. Ina tana kofar na jita a rufe na fara kwankwasawa.

 Bata nan fa ta fita

Na juyo na kalleshi sai ya saka hannayensa aljihu ya cire hular kansa yana kallona.

 Sai dai ki shiga bangaren Hajiya

 Aa ba sai na shiga ba, zan koma gida kawai

Na fada ina mamakin Hajiyar mahaifiyarsa ce ta Safeena tsakanin shi da Safeena gidansu waye ne? Ko kuma shi da ita Yaya da kanwa ne oho.

 Okay Let me drop you off Girly

Ban masa musu ba ya wuce gaba na bi bayansa har muka isa gurin motar na bude na shiga, shi ma ya shiga yaja motar muka fice daga gidan. Tafiyar kamar ta kurame haka ta zama bana cewa komai sai tunanin Zafeer nake da irin rayuwar da yake ta fada min zamu yi. Ban ankaro ba na ji hannunsa a cinyata yana shafa ni.

 Kin yi shiru baki cewa komai Noor

Na yi saurin buge masa hannu.

 Miye haka?

Sai yayi murmushi.

 I'm sorry daman ina gwadaki ne kawai

 Gwada ni kamar yaya to see what?

Asking with little bit of confuse.

 To see if you're wife material...

 Sauke ni a nan

Ya dube ni da sauri.

 A nan?

 Eh a nan zan sauka

 Ba gidanku ba ne ai

 Na ce ka sauke ni a nan zan sauka

Wata kila bakin hadarin da na hada a fuskata ya firgita, domin na daure fuskar sosai babu alamar wasa. A dole ya faka gefen titi ni kuma na bude na fita na bar masa motar a bude.

 Kin ga ni fa gwadaki ne kawai nake ba wani abu ba...

Ban kula shi ba na cigaba da tafiya a kafa, ya so gwada bina a motar yana min magana da ya lura ba zan saurare shi ba kuma ba ni da niyar shiga motar sai ya motarsa yayi gaba. Tsaye nake ina jin kamar na fasa ihu na fadi na yi birgima a guri. Kusa da ni wata motar ta tsaya wannan karon ina ganin wanda ya fito motar sai na ji sabon kuka ya taso ni gaba, wani irin shagwaba da narkewa na fara yi kamar wata yar baby.

 Me ya faru? Me kike yi a nan?

Ya tambaya tun kamin ya karasa fitowa daga motar, matsawa na yi kusa da inda ya faka motar ina kuka har da shessheka.

 Kareem...

Ya kalleni hankali a tashe.

 Me ya kawo ki nan Noor waya taba ki?

 Kowa ma taba ni yake...

Ya kama hannuna ya ratsa da ni ta cikin wasu itatuwa da ke gurin muka shiga ta can ciki gurin da ke da sanyi da iska mai dadi, sakin hannuna yayi.

 Fada min me ya faru?

Na daga kai na kalleshi kawai hawaye na sauko min. Cikin kwantar da murya da lallabawa ya ce

 Can i be your best friend?

Na daga mishi kai.

 Okay daga yanzu na zama best friend dinki, yanzu fada min damuwarki

I don't know why, how and when, i just find myself laying on his chest idanuwa na zubar da kwalla.

 Zafeer zai yi aure Kareem...

Mun dauki 12-seconds a haka, ni da shi babu mai motsi kamar mun mutu, but zuciyata na bugawa da wani irin karfi kamar yadda nake jin tasa ma tana bugawa, sannan ya matsa baya hakan ya saka dole na dago daga jikinsa, he look straight into my eye ball ya ce.

 Noor ki daina saka turare mai yawa haka idan zaki fita, Haramun ne

 Kai turaren ne damuwarka?

 Saboda yana dagawa mutane irina hankali turare is my weakness, my weak point

Ban gama fahimtar abun da yake fada ba, na ganshi slowly yayi kasa ya zauna akan turbaya ya nade kafafuwansa ya dago yana kallona.

 Zauna karanta min damuwarki, maybe zamu iya solving matsalar...

Na zauna a gurin ina fuskantarsa da irin zaman da yayi.....

Na maida idanuwana kasa ina jin wani sabon kuka na tunkaro ni, ban sani ba raini ne ko kuma yarda ce ta saka nafi sakewa a kusa da Kareem ne kamar yadda nake sakewa da Zafeer sosai ko ma fiye da haka. Ina jin son fada masa damuwata ko da kuwa ba zai saurare ni ba, na kan ji kuka sosai idan ina kusa da shi musamman idan damuwa ta yi min yawa, tsabanin sauran mutane.

 Noor...

Wata kila yanayin yadda ya kira sunana ne ya kara masa kwarjini a idona lokacin da na kalleshi.

 Ka rame, Kareem

 Ke ma kin rame, ni da ke duk muna cikin damuwa mabanbanta, fada min taki

 Ya aka yi kasan ina nan?

Ya kalli gurin ya sake kallon ya sauke ajiyar zuciya.

 Na kan gwada zuwa nan yanzu, saboda ina jindadin gurin, bana son zaman office a yanzu saboda zaman yana tuna min da Hafiz, na kan zauna a nan na yi tunanin rayuwa, mafita, da kuma nazarin rayuwa

Na sauke kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna.

 Ke waya kawo ki nan?

 Wan...

Sai kuma na kalleshi da saurin ina jin kamar na yi barin zance.

 Wani...? Wani? Har kin fara samari?

 Ba saurayina ba ne...

Na fada masa yadda alakar take.

 To me ya sa ya sauke ki a nan?

 Taba ni yayi sai na ce ya sauke ni a nan

 Taba ki?

Na daga mishi kai.

 Ki yi taka tsantsan da zaman yanzu, okay

Na daga mishi kai sannan na fara karanta masa damuwata. Na yi tsammanin zai taya ni bakinciki ne amman sai na ga mamaki karara a fuskarki.

 Amman Noor ke kika fara gudunsa, yanzu kuma ya samu mai son shi, so kishi kike ko kuma kina ganin kamar ya ci amanarki ba

 Ban sani ba ina dai jin babu dadi, kuma hakan yana nuna kamar ya daina so na, zai yi rayuwa da wata ba ni ba

 Sai hakuri, wata soyayyar bata nufin daurewa har abada, wata alakar kuma mai daurewa ce, ke dai ki yi addu'a duk abun da yake na kwarai mai alheri a gareki Allah ya tabbatar miki

 Tohm

Idona ya cika da hawaye, sai ya leko fuskata.

 Bayan wannan akwai wata damuwar?

Na daga mishi kai, na fara fada masa yadda zaman gidamu ya dawo yanzu ni da Hana duk ba ma jindadinsa.

 So yanzu so kike na yi ma mahaifinku magana ko kuma Yaya?

 Aa kawai dai na fada maka ne

Yayi min murmushi yana kallona.

 Kin san na zama best friend dinki a yanzu zski fada min damuwar da bukatunki a duk lokacin da hakan ya taso, hakan ya miki?

Na rausayar da kai Ina zane a kasa.

 Toh kai fada min damuwar kai ma a kana cikin matsaloli

A take na ga murmushin dake fuskarsa ya gushe damuwata ta bayyana karara.

 I don't want to talk about this da ke? Ba zaki fahimta ba Noor

 Zan fahimta mana, gashi kai ma ka fahimce ni kuma ina ganewa idan kana cikin damuwa

Wannan karon dariya yayi.

 Tun mutuwar abokina ban yi hirar damuwata da kowa ba, kuma ban nemi shawarar kowa ba hakan kuma yana kara jefani a matsala

 Toh fada min damuwarka a yanzu

Na fada ina kallonsa da idanuwa kamar na yan fari. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.

 Wasu abubuwa na aikata da nake tsananin nadamarsu a yanzu, sai dai kuma na fi nadamar babban wanda shi ne silar dukan ukun

 Fara fada min babban

 Amincewa na auri macen da bana so bata so na, shi ne babban domin shi ya janyo kananan matsalolin

Na kalleshi da duba mai kyau.

 Kana nufin ko da ka auri Yusura baka sonta bata sonka?

Da mamaki yake kallona.

 Why Yusura kika sani ko na taba aure kamin ita?

 Ban sani ba, amman ai ita ce na lura ba ku zaman lafiya, bata son ka, ko shiyasa kake cewa bata kishinka a baya?

 Ashe kina da hankali Noor har kanki ya kawo wuta haka?

Na yi murmushi.

 To miyasa ka aminta

 Saboda Momy na ne, akwai wata budurwa da na yi a lokacin baya, mun so juna amman Momy ta ce ba zan aureta ba, saboda bata yarda da tarbiyarta ba, ita kuma a lokacin akwai wanda take so, amman a haka Momy ta gabatar mana da matsayarta, ni kuma ina tunanin babu hanyar sakawa iyaye sai biyayya a garesu, na amsa mata da na amince, ita kuma ta amsa da hakan saboda tana tsoron kar ace ta yi butulci bayan irin rikon da Momy ta yi mata tun tana karama har girma

Ya dan yi shiru yana kallon wani gefe.

 A haka muke ta rayuwa a haka muka haihuwa haka muke har yau, kuma a haka zamu rayu a nan gaba, amman a yanzu abun yana ci na sosai

 Ka fada min daya sauran uku..

Ya dube ni with seriousness ya ce.

 Na aikata wani abun da yake hana ni sukuni a yanzu, zunubi ne mai girma

Jin haka ya saka ni mamaki.

 Shirka kai yi?

Ya girgiza kai alamar AA.

 Wani ka kashe?

Ya girgiza min kai.

 Ko dan kana zubar da ciki?

Nan ma kan ya sake girgizawa.

 Zina ka yi?

Ya kalleni.

 Me yasa Zina ta zo miki a kai?

 Saboda tana cikin manyan zunubai

 Haka ne, gashi dafinta yana ta bibiyata

 Ita ma Allah yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login