Showing 6001 words to 9000 words out of 227321 words

Chapter 3 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1508

daga kai na kalli Hana dake rike da karamar buta tana dafe da kafadata.

 Hana Abbah yana yawan fadar bani da albarka ko ba ni da sa'a, yana yawan cewa sanadina ya rasa aikinsa sanadina ya fara talauci, idan mutum ya ce miki haka sai kin ji kamar ki kashe kanki, balle kuma mahaifi, kullum kalma sabuwa take zame min

 Haba Noor ke da kike haske? Hake gidan nan hasken zuciyarmu, idan baki nan babu mai sakewa maganar Abbah ta daina damunki, Abbah ba shi da dadi a gurin kowa ke kin sani Mama ma be raga mata ba balle kuma mu, dan Allah karki bata ranki

 Toh

Na amsa ina share hawayena, sannan na cigaba da alwalar. Yaya Nabil be dawo gidan ba sai bayan Sallah Isha'i yana shigowa Mama ta hada mu gaba daya ta yi mana nasiha shi kuma ta ja masa kunne akan zagin da yayi min dazun a gaban Abbah.

 Raina ne ya bace Mama Noor ce ta yi laifin Amman gurinki yake maida laifi, kuma ita ja hakan ya faru, ba wai na zage ta dan yana tsaye a gurin ba ne, Wallahi zuciyata ce ta rufe na yi mata zagin

 Toh ka rika danne zuciyarka dan Allah ka rika kawar da ido akan komai, ka samu ku rabu lafiya da mahaifinku

Yaya amsa da In Shaa Allahu sannan ya tashi ya dauko kayan da ya wanke ya shimfida tabarma a waje ya fara gogewa da dutsen karfe na wuta. Sai da ya gama goge na shi sannan na dauko Abayata ya goge min ya nade min ya kawo min har inda nake zaune ya mika min.

 Na gode Yayana

Murmushi kawai yayi min ya juya ya shige dakinsa na kalli Hana dake sauraren littafi a wayar Mama na ce.

 Kin gani ba irinki ba, ke baki da nasiha ko tufafinki aka taba sai kin fara fada

Uffan bata ce min ba gaba daya hankalinta ya tattara ya koma gurin wayar dake makale a kunnenta. Sai dai sallamar da Abbah yayi ya saka ta yi saurin cire wayar ta tashi zaune ni kuma na amsa sallama??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r na masa sannu da zuwa na shige dakinmu, shigata da mintuna kadan Hana ta shigo. Daga ni har ita babu wanda ya sake fita dakin gar garin Allah ya waye.

Kamar yadda muka saba Hana ce take hada mana abun karyawa saboda ita ce mai zuwa makaranta, saboda haka da wuri take tashi ta dumama mana idan an raga abinci idan kuma koko za a siyo ko a dama duk ita ce take yi. Sai dai yau ni dai bana sha'awar cin dumame dan haka ban fito na karbi nawa ba sai da na ji motsin Yaya Nabil yana magana da Mama a tsakar gida. Fitowa na yi na zauna bakin kofar dakinmu a lokacin Hana ta dade da wuce makarantar boko.

 Yaya ina kwana

 Lafiya Kalau sai yanzu kika tashi

 Tun dazun ta tashi, wai ita yau bata son dumame shi ne taki fitowa ta karba

Mama ta fada tana juyowa ta kalleni. Yaya Yayi murmushi ya girgiza kai.

 Ni dai yau ba ni da ko sisi idan zaki ci dumame ki ci, idan ba zaki ci ba cikinki ne

 Yaya dan Allah ka siya min indomie Wallahi bana son dumeme kullum shi muke ci

Mama ta saka dariya.

 Wuya bata ci ba yarinya, idan kika ji yunwa da kanki zaki nemi tuwon ma

Mama ta tashi ta shige dakinta, Yaya kuma yayi fitarsa aka bar ni a gurin zaune, sai da na ga babu sarki sai Allah na dauki kwano na gutsira tuwon kadan na ci na aje sauran, tsintsiya na dauka na share ko'ina na gyara daman wanki da wanke wanke ko girki ba nawa ba ne, a cikin aikin gidan babu abun da na tsana kamar wanke wanke da wanki, girki kuma Mama ta fi sha'awa ta girka da kanta, ba kasafai take bari muna mata girki ba.

Misalin karfe biyu da mintun Hana ta dawo daga makaranta, ita kam bata tsaya neman wani abincin ba ta saka dumamen da na ce ba zan ci ba ta cinye abunta ta bar ni da yunwa a ciki. Ina tsaka da miyar ta cinye min tuwo kawata Zee ta shigo gidan cikin shirinta na ankon kamu, ba karamin burge ni ta yi ba domin ta yi kyau sosai ankon ya karbe ta gashi ni ban yi ba, sai yabon kyauta nake.

 Mama kin gani sai da na ce Yaya yayi min ankon nan ya ki

 Komai dai Yayanki, ki rika tausaya masa mana Noor abun ai sai ya masa yawa, komai dai shi ne, me yasa baki ce Zafeer yayi miki ba?

Na kalli Mama dake kare danta.

 Shi ai be da kudi

 Shi kuma yayanki banki ne ko?

Na turo baki gabana ina son yi mata kukan shagwaba.

 Yanzu kuma ko sisi ba ni da na tafiya bikin nan fa

 Daina kallona Wallahi ni ma ba ni da ko naira

Zee ta saka mana dariya.

 Ashe kuwa ba za aje da ke ba, ni ma ba ni da kudin tafiya, na san dawowa ba zai yi wahala ba saboda samari

 Bari na tafi gurin Yaya ina binsa kudi 700 ya bani ko 200 na samu na napep

Na tashi na zuba ruwa a bokita na shiga bandaki na yi wanka na fito na shafa mai na dauki hodar Hana na shafa da jan bakinta na yi kwalliya na yi kyau sosai sannan na saka abayata na dora mayafin, na fito daga dakin na bar Zee tana kara gyara fuskarta sa kayan kwalliyar Hana dake ta yi mana masifa wai sai mun biyata ai kwaliyar kudi take ba kyauta ba.

 Daga nan zaki iya tafiya a kafa har gurin aikinsa? Kuma kika sani ko yana da kudin ko babu, wannan tafiyar kamar ta dole Noor?

Mama ta fara kokarin hana ni, aiko take na bata fuska.

 Mama komai fa ban tafi ba na Salwa kuma wannan ne event na karshe ni dai ina son zuwa, kuma Yaya ba zai rasa kudin da zai ba ni

 Allah ya kiyaye ga ki ga hanya, idan be ga dama ba ai ba zai baki ba, ko ma ya hana ki tafiya bikin

Na saka talkamina na high hill na fice daga gidan, ba a kafa na taka ba titi na isa na tari mai adaidaita sahu na fada masa inda zai kai ni yace na bada 200 naira kasancewar babu wani tazara sosai.

 Kadai san Kareem Restaurant ko?

 Hajiya tun da ke kin san guri ai babu wata matsala

Na shiga Napep din ya ina ta rabon ido har muka isa Fancy Restaurant din na fito na shiga ciki domin ba wannan ne zuwana na farko ba, can ciki na wuce na yi magana da wani na fada masa ya kira min Yayana.

 Yana can ciki aiki suke lafiya?

 Lafiya kalau mai Napep zan sallama kuma zan yi magana da shi

 Bari na kira shi a waya amman idan suna girki ba a bari su fita

Ina tsaye a gurin abokinsa yana ta kiransa a waya be amsa ba, hakan ya saka hankali ya dan tashi domin na san halin wasu masu Napep ba su da mutunci. Komawa na yi na leka waje na sake dawowa ganin hankalina ya tashi ya saka Yusuf tambayar nawa ne kudin napep din na fada masa sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro 200 ya ba ni na fita da saurina na kaiwa mai Napep din.
Sannan na dawo na tsaya reception din, ina ta kallon mutane da yadda ake ta sake sabunta gurin, a kullum idan ka zo sai ka ga ya sake zama sabo.

 Noor yayi picking yace ki zauna ki jira shi sai sun gama girkin zai fito

Abokinsa ya fada, na kalli katon agogon dake gurin na ga uku da yan mintuna, na san ya kusan tashi aikin ma gaba daya, saboda haka na nemi guri a teburin da mutane suke zama na zauna ni kadai ina ta jin rashin sakewa saboda akwai mutane da yawa a gurin, duk kuwa da kasancewar kowa sha'anin gabansa yake. Ta dayan bangaren kuma ina jin dadin yadda sanyin Ac ke ratsa jikina, rabon da na ji sanyi ac har na manta.



https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx


Assalamu Alaikum...
Ina talata muku
KHADEEJA CANDY STORE >?p?=?L?
Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo.

''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -3

Ina zaune a gurin wasu iyalai suka shigo, ba zan iya fadar cewar masu kudi ne sosai ko akasin haka ba. Sai dai alama ta nuna suna da rufin asiri. Teburin sake gabana suka kama yan mata hudu ne sai maza uku da kuma magidancin da zan iya shaidar cewar mahaifinsu saboda kama da tsufan da yayi. Wadda ta zauna a gefensa kuma bana bukatar a fada min cewar ita din uwace domin alamu ya nuna haka. Hannu biyu na saka na yi tagumi ina kallon yadda uban yake handling yayansa mazan suka koma a dayan teburin suka zauna matan kuma suka zauna tare shi.

Sai da suka fara daukar littafin dake teburin suka duba kalar abincin da suke so, tukuna daya daga cikin ma'aikatan gurin ya zo yayi taking orders. Ni kam sai kallonsu nake cike da burge, ba kudin ne abun burgewa ba, ba zuwa restaurants ko order abinci, soyayyar ce ta shiga zuciyata yadda uba yake nunawa yayansa soyayya da kauna yana ta hira da matan suna dariya mazan kuma suna jefo na su hirar daga can inda suke zaune. Wani abu ne da ni na rasa tun tashina, ban tana zama da mahaifina ya tambaye damuwata ko dadi ba, wata hirar farincikin bata taba hada ni da shi ba, ban taba aikata wani abu ya nuna jindadinsa.

 Noor....

Na juyo dama da ni sai na yi arba da Yayana, hannayensa na ji a fuskata yana share min hawayen da ban san sun zubo ba.

 Kuka kike yi? Saboda na dade?

Ya tambaya saboda ya san ni da kukan shagwaba kamar wata wadda ta tashi cikin gata. Sai na girgiza masa kai na juya na kalli mutanen

 Wani abu da na rasa nake kallon wasu da suke da shi, kalli yadda suke cin abinci tare da Babansu be burge ka ba Yaya?

Ya daga kai ya kalli gurin kamin ya dube yana sauke ajiyar zuciya.

 Wata rana ina jin kamar hakan zai faru amman na san ba zai taba faruwa ba

 Kin cika tunani da yawa, a kawo miki wani abu zaki ci?

Na saka hannuna da kaina na share hawayen da suka sake zubo min na dubi Yaya dake sanye da uniform din gurin sai tausayinsa ya kama ni, na san yayana ba mutum ne mai son zaman banza ba, yana da kokarin nema, saboda dukanmu mun taso a rayuwar talauci mun san babu kuma mun saba da hakan. A aljihunsa ake samun kudin chefane gidanmu a kullum kuma da kudinshi Mama take zuba adashe tana mana tanadin kayan aure.

 Wa zai biya? Ni ba ruwana bana da ko shishi...

Yayi dariya domin ya san kadan daga halina ne zan iya komai ko bana da ko sisi sai dai duk abun da zai faru ya faru.

 Za a cire salary

 Toh a kawo, daman Yaya ban ci komai ba tun safe, kuma ban taba cin abinci a Restaurant ba

 Me kika so?

 Akawo naman kaza da na kayan ciki da shawarma da pizza da...

Ban gama zanawa ba ya katsene.

 Ke fa baki da hankali, duk plate daya a nan 5k plate nawa zaki ci?

Na bude baki na kalli mutanen gabana na kirga si na kirga kudin da za su kashe.

 Tab toh Yaya a kawo kaza

 Kaza 10k ne ke kuma abun da zaki ci ba zai wuce 2k

 Toh ai ka ce 5k ne plate

 Rabi zan kawo miki

Be jira abun da zan ce ba ya juya ya bar ni a gurin zaune. Babu jimawa ya dawo rike da plate wata yar shimkafa ce kamar na roka sai wani kofin lemu da gorar ruwa mai yawa.

 Yaya wannan ba zai ce min komai ba, iya halshe zai tsaya

 Masu kudi kadan suke ci ki yi cin masu kudi, ko baki ga yadda Restaurant din yake ba?

Ya zare min ido sannan ya tafi ya bar ni a gurin. Ba dan kar nutane su kalle ni da ba zan ci wannan abinci ba, wannan ai rowa Yaya yake min a gurin aikinsa. Na daure na kai zuciyata nesa na cinye abincin nan tass ko shimkafa daya ban bari a gurin ba, lemun ma duka na shanye sannan na dauki ruwan na sha. Kamin na mike tsaye sai ga Yaya ya zo yana kokarin dauke kayan har da ruwan aiko na saka hannu na dauke ruwana, gudun siyar da hali yasa be ce min komai ba ya shiga ciki da kayan, babu jimawa ya fito sanye da kayansa na gida ya rika hannuna muka kama hanyar fita.

 Mi zaki yi da gorar ruwa wane irin kauyanci ne wannan Noor dan Allah ki aje

 Wallahi ba zan jefar ba, ai ba kyau wulakanta ruwa, kuma ai siya muka yi ba sata ba

Ina jinsa yana jan tsaki amman ban jefar da ruwana ba, ko ba komai kowa ya gani zai san na ci abinci a gurin, masu kudi ma haka nake ganin suna yi ai, suna rike gorar ruwa a hannu idan suna yawa. Sai da muka fita gate din gurin gaba daya sannan yake tambaya me ya kawo ni ma.

 Yaya kudina zaka ba ni, bikin salwa zan je, dari bakwai daka ara zaka ba ni abuna

Ya daka min tsawa.

 Ba salwa ba kwai, yanxu saboda bikin wata Salwa kika kwaso kafa kika zo har gurin da nake aiki har da aron na Napep, kuma sau nawa zan biyaki bashinki ne Noor shekarab jiya kin karbi dari biyu last week na baki dari uku dari biyu kawai kika biyo ni, kuma yanzu kin hau Napep da ita, gashi nan kin saka ni siyen plate daya 5k sakaryar yarinya kawai

Ban san lokacin da na tsayar da tafiyar da nake na dube shi.

 Yaya wannan abincin da naman kahirar ne 5k? Kam bala'i Wallahi a ana zalimci duniya, kuma ni kudina 700 ne

 Da yardar Allah ba zan sake rantar kudinki ba, ke idan an ari kudinki babu zaman lafiya, kuma sai ki rika kari saboda baki tsoron Allah

Yana masifar yana tare mai adaidaita, yadda fuskarsa ta hade sai ka rantse da Allah ba shi ne yake tarairayata a cikin restaurant din ba.

 Kuma wannan abincin da kika ci bashi ne sai kin biya. Malam Wurno Road

Ya karasa yana magana da mai adaidaita sahun.

 Yaya ba gida zamu je ba?

 Ban sani ba, kuma Allah yasa mu je kin zubar min da mutunci mu koma gida ki ga yadda zan miki wulakanci

 Toh wai ni nace ka kawo min abinci? Ba kai ka ba ni ba dan kanka to miye na masifa kuma

 Saboda dari bakwai kika zo har gurin aikina, kuma idan ban kawo miki wani abu abokan aikina ai za su min gulma, kuma kin ba ni tausayi da farko

Ban yarda na sake cewa komai ba, domin abu ne mai sauke ya sauke ni a hanyar ya tafi ya bar ni, na lura ba karamin hawa yayi wannan masifar da yake ta min kamar na ce ya ba ni abinci a dole. Tun da muka shigo unguwar mai adaidaita be tsaya ko'ina ba har sai da Yaya ya bukaci haka. Gaban wani katon gida ya faka Yaya ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya bawa mai adaidainta.

 Zai wuce da ke gida

Ina jin haka na yi saurin fita cikin Napep din na fara yi masa magiya ina kuka. Har ga Allah ba zan yarda ya shiga wannan katon gidan ba tare da ni ba, ko ba komai ai zan bawa idanuwana abinci.

 Yaya ka yi hakuri dan Allah karka ce ya wuce da ni gida, tare da kai zan tafi dan Allah Yaya ka yi hakuri, na yafe maka 700 din ka yi hakuri Yaya dan Allah

 Ba biki zaki ba?

 Na fasa

Ya tsaya yana kallona kamar wadda ya rasa ya zai yi da ni. Ni ko sai rokonsa nake ina magiya kamar wadda za a saka a cikin wata ni'ima. Ganin haka ya saka ya sallami mai Napep din ya nufi gate din gidan dake rufe. Kwankwasa yayi aka bude masa farin gate din muka shiga ciki yana gaisawa da masu tsaron kofar.
Galala na yi ina tafiya ina kallon yadda gidan ya tsaru da abubuwa gidan sama har hawa biyu, gashi komai na gidan fari ne tun daga motoci har fentin gidan, wata babbar kofar ya nufa ya danna door bell sannan yaja ya tsaya, kallo daya yayi min na natsu sa kyau na sauke kaina kasa, ba sai ya tuna min ba, ni ma ai ina ganin yadda komai yake tsare na san gidan masu alfarma ne.

Wata yar lukutar yarinya ce ta bude mana kofar, fara ce sosai babu alamar kashi a jikinta tsokoki ne suke ta rawa kamar wata tufa.

 Tine babanki na nan?

 Eh ku shigo

Yaya ne ya fara wuce sannan na shiga ina maimaita sunan nata da yayi min kama da ba kafirai. Suuuuuu na fara jin sanyin ac na ratsani irin tsarin nan na musamman, wannan sanyin ya ci uban na wanda na ji a Restaurant. Da katon Tv na fara arba indiawa dake ciki suna magana kai kace fasa tv za su yi su fito, ga wani kamshin turare da ke tashi kamar dakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login