Showing 42001 words to 45000 words out of 227321 words

Chapter 15 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1549

taja majina tukuna ta amsa.

 Mun karba, shiyasa kake auren wata macen ni kuma nake auren wani namijin da ba kai ba Kareem

 Idan har zamu cigaba da aikata abun da muke aikatawa kazantar ta yi yawa abun yayi muni, kuma hakan yana nufin ba mu karbi kaddarar ba Safeena

Ta yi dariya da zai iya ji.

 Ba akan mu farau ba Kareem, kuma shi Allah mai yafiya ne a koda yaushe, ba haka za mu dauwama ba, wasu ma suna matsayin budurwa da saurayi suke yi balle mu da muke da aure, wannan abun duk kauna ce ta kawo, karka bari yarinyar nan ta canja min kai

 Babu ruwan Noor a alakata da ke, ni ba soyayya nake da ita ba, kawai dai an yi sara ne akan gaba ne, amman ba aurenta zan yi ba

Fashe masa ta yi da kuka.

 Kana cewa mu rabu kamar abu ne mai sauki Kareem, kana kokarin juya min baya bayan kuma na saba da komai na ka, taya kake son na jidadin rayuwa babu kai a kusa da ni? Wallahi saboda kai bana sha'awar Mijinta yayi sati daya a garin nan, saboda kai bana jindadin duk wata mu'alama da mijina, kullum mafarkina da burina akanka ne Kareem, ka juya min baya a lokacin da na fi bukatarka, yanzu kuma mun sabu da juna kake kokarin guje min a karo na biyu? Ko ka manta wacece Safeena a gurinka Kareem....?

Tif... Ya kashe wayar ya sauke ajiyar zuciya, jin kamar kalamta na kokarin saukar masa da tausayinta kuma suna kokarin kusanto da rauninsa.

 Me na jefa kaina a ciki? Me yasa na bari zuciyata ta yi nesa? Ba zan sake aikatawa ba, ba zan sake ba, ba zan sake cutar da wani ba, ba zan sake bari zuciyata da yaudari da jindadin da ba zai tabbata ba a gareni

Ya saka wayar aljihu sannan ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na Biyu ya juya ya koma ciki. A bude ya samu office din babu kowa a ciki ma'ana dai Hafiz ya fita daga office din. Wayarsa ya fara cirewa daga aljihu ya dora a saman teburinsa sannan ya zauna ya dafe kansa. Abu da yake a bayyane gurin kowa kuma sirri dake aje a zuciyarsa yana son Safeena irin son da yake jin ba sai taba samun mai maye masa gurbinta ba, irin son da ya tabbatar sai dai ya mutu da shi domin ba zai iya aurenta ba a yanzu kuma baya jin zai iya cigaba da mu'alama da ita ta kazamtacciyar hanyar da ya sabawar kansa.? Sai bayan sallah Isha'i Kareem ya koma gidansa, yana shiga falonsa ya samu Yusura zaune tana duba waya, laramin danta dake cinyarta ya zo da gudu ya tare shi.

 Daddy Oyoyo

Kareem ya cillashi sama ya cafke sannan ya sauke shi ya shafa kansa yana murmushi.

 Areef ya kake?

 Lafeeya lau, amman Momy bata da lafiya

Kareem ya daga kai ya kalleta sai ya ga har lokacin idonta yana kan wayar dake hannunta kamar ma bata san da shigowarsa ba. Ya maida dubanshi gurin Areef

 Me ya same ta?

 Jikinta da zafi ta yi amai kuma ta yi kuka...

 To yayi kyau je dakinka ka kwanta gobe akwai makaranta, ina Tine

 She's sleeping

 Okay kai ma je ka kwanta

Ya sumbance shi yaron ma ya mayar masa sannan ya sake shi ya nufi sama da gudu yana waigensa. Sai da ya haye sannan Kareem ya karasa gurin da Yusura take zaune yana daga tsaye zai yi magana ta riga shi ba tare da ta kalleshi ba.

 Ga abincinka a dinning room

Ya kalli dinning area din sannan ya sake dubanta.

 Ai da baki girka ba, tun da baki da lafiya kuma abinci ba wani damuna yayi ba...

Ta tsayar da taba wayar da take ta dago ta kalleshi.

 Idan har ban girka abinci a gidan nan ba, wata kila ina ciwo ne mai tsanani da ba zai bar ni na iya tsayuwa da kafafuwana ba, amman girka abinci, gyara gida, kula da yaranka da kuma tsare mutuncina, wani abu ne da addinin da al'ada suka taru suka samar mana, ina yi ne saboda sauki nauyi na matar aure a gidan Kareem, ba wai ina yi ne saboda Kareem ba, ina jin tsoron tsayawa a gaban mahaliccina ya tambaye ni wani hakki na bawansa na kasa amsa masa, ko Kareem ya ci abinci ko kar ya ci Yusura zata girka, ko ka tsare mutuncinka ko kar ka yi Yusura zata tsare nata, ko ka kula yaranka ko karka kula Yusura zata ba su tarbiya gwargwadon halinta...

Ya hade wani abu da ya ji yana masa yawo na rashin dadi ya danne zuciyarsa ya sake yin furuci a gareta.

 Ya jikin na ki? Me yake damunki?

Ta sake daga kai ta dubeshi.

 Kana da bukatar wani abu?

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wallet dinsa ya cire ATM dinsa ya aje mata a hannun kujerar da take zaune.

 Gashi idan kina bukatar wani abu ki siya, idan kuma kina bukatar ganin Likita ki je ki ganshi, 5885 is the pin

Yana dauke hannunsa daga aje ATM din ta mike tsaye.

 Bana bukatar komai daga gareka, ina da rufin asirin da zai wadace na yi ma kaina komai, sai da safe

Ta bar a gurin tsaye ta nufi stairs. Binta yayi da kallo har sai da ta haye sama sannan ya zauna a inda ta tashi ya ja hular kansa baya ya kai hannunsa yana murza gaban goshinsa dake masa ciwo ya rufe ido.


YUSURA POV.

Tana shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta zauna bakin gadonta hawaye suka sauko mata. Ba burinta ba ne fadawa mijinta bakar magana ba burinta ba ne yin zaman auren da babu farinciki a cikinsa, amman tsananin kiyayyar da take yi ma Kareem ya hana ta mallaka masa ruhinta, daman ita zuciyata ta san ba zai taba samunta ba, domin bata taba jin wani abu akansa ba duk tsawon lokacin da suka dauka a tare, tana kone zuciyarta ne kawai tana azabtar da kanta. Kareem yana da kyau da cikar kamala irin wadda yana da kudi ya shahara a cikin sa'aninsa masu irin aikinsa, amman babu dalili daya da kai ya saka ta so Kareem domin ba shi take so ba tun farko, aure da matar da ta rike ta a matsayin uwa ta hada, a lokacin da ba zata iya ce mata a a ba.

 Har zuwa yaushe zan yi ta zama a cikin wannan yanayin? Sai yaushe zaki tafi Momy? Mutuwarki kadai nake jira, ko kuma ta Kareem na yi takaba na wanke wannan bakincikin, bana fatan mutuwa da aurensa, saboda bana son na tashi tare da shi gobe alkiyama, wata kila dai ba zan iya cin wannan jarabawar ba, kiyayyar da kike ganin kamar zata iya zama soyayya ba zama ba Momy, ta ma kara rura wutar kiyayyar da zata iya hada kasashen dake cikin zuciyoyi yaki da ta yi

Magana take da kanta zuciyarta na mata zafi, abu ne da ta riga ta sani har abada ba zata taba son Kareem ba, ba kuma dan be kai a so shi ba, ba dan yana mata wani abun ba, sai dan bata taba jin tana kaunarsa ba tun farko, shiyasa kullum take jin kamar a kurkuku take ba a gidan aure ba. A hankali ta kwanta gadon tana kallon gefen dakinta tana ta nazarin rayuwa.


NOOR POV.

A wahale na wuni a ranar, daga mama har Ya Nabil babu wadda ya sake bin ta kaina. Hana ce kawai ta taimaka min ta kwashe aman da na yi bayan ta dawo daga makaranta. Ina jin lokacin da Mama take mata fada wai ai da ta bari na kwashe taya zata kwashe min amai ai shagwaba ni da ake ne yasa nake son lalacewa. Wani abun da Mama bata saba min da shi ba shi ta yi min a yau, wato horo da yunwa ta hana ni abinci rana da hana ni na dare ko da wata safiyar ta waye jikina har rawa yake domin na saba ci ba kadan ba gashi kuma na wuni na kwana ban ci ba. Bayan Hana ta wuce makaranta na fito waje ina jin jikina kamar ba nawa ba, na nufi tukunyar dumame na bude na duba babu komai a ciki, sai na lashe tukunyar na dawo dakinmu na zauna ina jin rashin kyauta abun da na aikata tun farko...

Da sannu na sabarwa kaina da zaman daki bana sha'awar fita ko'ina tun a wacan ranar da Zafeer yayi min huduba. Kwana hudu na shafe ko kofar gidanmu ban leka ba, kullum kuma ina sauraren yaron da zai shigo yace Zafeer yana sallama da Noor amman shiru. A ranar da aka cika kwana biyar ne mutumen da yayi ma Baba alkawarin siye masa gida ya zo aka yi maganar gidan da wani abokin Baba amatsayin shi ne mai gidan aka yi ma gidan kudin miliyan uku da yan kai a take ya biya kudin, duk abun da suke ina jin domin ina cikin dakinmu kwance. Ban motsa ba har sai da abokin Baba ya fita tare da shaidun da suka yi shaidar gidan da aka siyarwa Baba. Kareem din da abokinsa suka bukaci ganina. Sannan na saka hijabina na fito daga dakin ban kalli kowa ba har na zauna na natsu sosai kamar ba ni ba, domin ni kaina na san na canja.

 Noor

Kareem ya kira sunana sai na daga kai na kalleshi. Shi ma yayi rama kamar dai ni, Murmushi ya sakar min yana tambayar ya jikina, a madadin na mayar masa da murmushin sai hawaye suka cika ido na ba tare da dalili ba, na yi ta yunkuri kirkiro murmushin na kasa.

 Waya cire miki bandajen?

 Ni na cire

Na amsa ina maida kaina kasa.

 Kina shan maganinki dai ko?

Na daga masa kai, domin bana son dogon zancen ni yanzu babu wadda nafi bukatar gani kamar Zafeer. Ban san me ya hana shi zuwa ba kusan sati daya yau, gashi Yaya Baya shiri da ni balle na ari wayarsa na kira shi na ji ko lafiya.

 Ko dai wani abu aka mata Baba? Na ga ta canja? Kamar ba ita ba kuma ta yi rama

Baba ya juyo ya kalleni yayi dariya.

 Ba abun da aka yi mata, mu kan mu muna mamakin yadda ta zama haka

Abokin Kareem din da ya siyawa Baba gida ya dube ni.

 Duk lokacin da na fada maka wani abu akan yarinyar nan baka yarda ai, she's very simple and easy going cikin kankanen lokaci zata iya canjawa daman

Kareem din yayi kamar be ji shi ba, ya cigaba da magana da Baba ta zuba godiya kamin ya miko min wayarsa

 Duba ki gani irin wannan maganin ne da na rubuta miki kike sha?

Na karbi wayar, a madadin hoton magani ko sunansa wani rubutun ne na gani zube a screen din wayar da Kareem ya miko min.

 Me ya faru Noor? Why the sad face? I Miss the old you, indai damuwarki akan Zafeer zamu taimaka masa, idan kuma akwai wata matsalar bayan ita rubuta min yanzu


Na dago na dube shi sai na ga daga shi har abokinsa idonsa suna kaina, na girgiza masa kai.

 Ba shi ba ne

 Amman dai babu wata matsala ko?

Na daga mishi kai.

 Babu...

Na yi murmushin domin furuncin na cewar zai taimakawa Zafeer ya faranta min rai siye da siyen gidan Baba da suka yi a bisa karya. Ya miko hannu ya karbi wayar ya saka aljihu ni kuma na juya na kalli Mama da ta fito tana musu godiyar siya mana gida da suka yi.

 Ba komai Mama ayi dai cigaba da hakuri da Noor da halinta, wata rana sai labari gashi dai yanzu ta janyo muku alheri

Cewar Hafiz abokin Kareem, sai Baba ya fashe da kuka kamar gaske.

 Haka ne haka ne, Allah dai ya saka muku da alheri, ita kuma Allah ya kara mata hankali, ya kawo mata miji na gari...

 Ameen

Suka amsa ni da Kareem muna kallon juna kasa kasa kamar wadanda suka kula wani munafurci. Wata kila Baba ji yake kamar ba su fahimci zaren addu'ar ba, wata kila kuma sanadi ne da ni ma zan ji halin da ake ciki game da Zafeer domin tsinkayo Baba muka yi yana fadar abun da ban san an yi ba kuma wani be fada min halin da ake ciki ba.

 Shi wannan yace be shirya ba, wai ba shi da hali yanzu, ya turo yan'uwansa sun zo nan kwana uku da suka wuce da dare yana neman a daga har nan da shekara biyu ko daya da rabi, shi ma kuma ya zo da kansa amman ni na fada musu ba zan iya ba, domin so nake na aurar da Noor na huta, ba karatu take ba, kuma ba wani aiki take tare mana ba balle ace za a daga har lokacin ?a mace da ta tasa kyauta dakin miji, balle kuma irin Noor kara na aurar da ita tun ina da rai

Na kalli Baba da sauri hawayen da ban san yaushe suka taru a ido ba suka zubo min. Sai dai wani kyauta da dadi sai na kasa cewa Uffan ba kamar da ba, wata kila da zan iya daka tsalle na rantsewa Baba na kunyata shi ko a gaban waye nace Zafeer nake so domin shi ne zabin raina... Amman a yau sai na kasa furta ko da kalma daya ne.

 Baba Noor tana son saurayin nan nata, kuma shi ma yana sonta, be kamata ka shiga tsakaninsu ba, da dai zaka duba ka ba su damar zai fi, inda aka fito be kai inda za'aje ba

Kareem ya fada sai na juyo ina kallonsa da kamar damuwa a fuskarsa.

 Ba wai bana son ta aure shi ba ne, samarin ne na yanzu sai a hankali ni har na fi sha'awar Noor ta auri mai mata sun fi rikon aure, kuma ita Noor ai ba wani so ta sani ba, ita dai barta ga shirmenta mu lokacin da muna yara ai ba wani soyayya muka sani ba, sai dai kawai ace an maka mata kuma sai ku yi zaman aurenku lafiya lau, zamani ne ya lalace har aka san wani lobe lobe, kuma ita Noor ai kawai dai ayi sha'ani...

Baba ne yake maganar ya karasa da dariya irin wadda ke nufin Noor bata san abun da take ba. Abokin Kareem ya ce.

 Gaskiya, kuma ance abun da Babba ya hango yaro ko hau tsauni ba zai hango shi ba, to Allah yasa hakan ne mafi alheri, kuma kana da gaskiya ba Baba idan yarinya bata karatu babu inda ya fi dacewa da ita irin gidan aure, ko da ma tana karatun balle kuma irin Noor cikin kankanen lokaci zata fara son wani ma

Shi ma dai kallonsa na yi wata kila ya manta da ina zaune a gurin yake wannan zancen, kamar Kareem ya san abun da yake zuciyata sai ya dubi abokin nasa ya ce.

 Hafiz dan Allah karka zuga Baba ya aurawa Noor wadda a shi take so ba, baka san komai game da auren wadda baka so ko baya sonka ba, idan ba zaka lurar ba, to karka lalata

Mama ta tashi ta shige dakinta, ni kuma na mike tsaye ina jin Baba na fadar.

 Ai gaskiya ya fada babu wata zuga, Noor ai tana da saukin kai sosai kowa ya same ta ya zamu mata ba dan tana ?ata ba, sai dai ace bata jin magana amman tana da saurin sabo sosai

Daga haka ban sake juyo me suke tattaunawa ba, har suka ci suka shude suka fita ban san anyi ba, domin hankali ya karkarta a gurin Zafeer ina ta hararon dalilinsa na rashin zuwa, Allah kadai ya san me Baba yace masa ko yan'uwansa, amman me yasa Mama bata fada min hali da ake ciki ba? Shim ba ni da hakkin sani ne? Ko kuma ita ma din bata sani ba? Ko kuma saboda sun mayar da ni wawuya marar hankali da tunani ne? Tun da na yi alwala azahar ban sake fita ba dakin ba har aka yi Isha'i da ita na yi sallah, abinci ma da Mama ta kira tace na zo na dauka na dare sai na kasa fita na ji kamar bana bukatar abincin.

Misalin karfe tara da yan mintuna yaro yayi sallama ya ce Zafeer yana sallama da Noor, kamar ina jira ba tashi da sauri daman akwai hijab a jikina na fito waje na saka talkamina zan nufi kofar sai Baba dake kishingide yana sauraren redio ya ce.

 Ina zaki?

Na yi shiru na rasa me zance, domin na san ya san dalilina na fita a yanzu.

 Na fa fada masa zan miki miji tun da shi be shirya ba, na san halin wasu yaran yan iskan unguwa sai su nemi lalata yarinya ma idan suka ga ba su samu damar aurenta ba, gashi ke ba wayo ba balle na ce

Mama dake zaune gafensa ta ce.

 Haba Malam.. Ai ko da ka fada masa haka be kamata ka hana ta fita ba, baka san me ya zo da shi ba, kuma ba san abun da Allah zai yi a gaba ba, ko rabuwar za'ayi ai ta mutunci tafi, Wallahi Allah kadai yasan zagi da za'ayi maka a unguwar nan saboda kin dagawa yaron nan kafa da ka yi

Baba ya juya ya kalleta a fusace.

 An dade ba a zage ni ba, a cikin masu zagin akwai mai wani mudu daya na shimkafa? Ko akwai mai ba ni dari biyar na kara na yi chefane? Ni fa ban hana shi aurenta ba, amman na fada masa muddi be shirya ba to kar ya batawa yarinya lokaci kuma ni na gaji da halayarta ina son na aurar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login