Showing 189001 words to 192000 words out of 227321 words

Chapter 64 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1543

so ta yi tun auren farko amman be samu ba sai yanzu.

Sallama suka min suka Zainab na rada min lalata a kunne tana dariya sannan suka tafi tare da abokansa da za su sauke su gida, bayan sun yi mana addu'a tare da fatan alheri. Zafeer ya saka hannu ya yaye mayafina gaba daya ya kalleni, ni ma kallonsa na yi cike da farinciki duka auren da na yi ko wane ina tafiya da soyayyarsa da tunaninsa ne a gidan wasu, amman yau a gidansa na tare, tare da soyayyarsa to mi yafi wannan, ni ma dai na ji farincikin da masoya suke ji.

 Alhamdullahi, shekara da shekaru sai yanzu Allah ya cika mana burinmu, ko ma nace burina domin ni cutar ta fi kamawa

Ya shafa fuskata da hawaye ke zuba.

 Ranar da aka daura aurenki da Abokin Kareem Hafiz ko? Na yi kamar na mutu na ji kamar ban taba samun farinciki a rayuwata ba, na wahala sosai domin ban yi zaton soyayya zata kai mu ga haka ba, ban yi zaton rashin imanin mutanen ya kai haka ba, musamman ma Kareem ya raba ni da ke ne kawai saboda yana jin cewar ya isa kuma yana da kudi, ba dan zai aureki ba, aurenki na biyu ma ba zan iya misalta bakinciki ba, har sai da na tambayi kaina miyasa kaddara take hada ni da ke bayan ko wane aure na ki, ashe akwai abun da kaddara take saka mana da ba mu sani ba

 Wani abun a nesa yake, kamin a samu cikar buri akan wahala wani lokacin

 Haka ne, domin na wahala kamin na same ki Noor, talauci ya cutar da ni ya nesanta ni da ke, amman Alhamdullahi gashi a yanzu arziki ya sadamu

 Kaddara ce ta raba kuma ita ta sake hadawa yanzu, ba talauci ba, ba Kareem ba, kuma ba arziki ba

Yayi murmushi mai sauti, da alama amsata bata gamsar da shi ba, tun a daren na san zama ba zai mana dadi a gidan ba, domin yana kallon na guje shi ne saboda talauci yanzu kuma na aure shi saboda arziki. Shi kadai yayi alwala domin ni na yi tawa tun a gida, raka'a biyu muka yi muka gode Allah muka yi addu'a sannan ya juyo ya rike goshina yayi min addu'a. Sai da na cire tufafin jikina an saka na bachi kamar yadda ya bukata kuma ya saka sannan ya dauko mana abun tabawa. He feed me, i feed him cikin soyayya da kauna, sannan kwashe kayan ya rufe kofofin gidan ya rage hasken dakin ya kwanta bayana.

A wannan daren na tsammaci abubuwa da yawa daga gurin Zafeer, kamar hugging, kissing romanced, da ma uban gayyar, ba dan ina da bukata a sai dan sani ba, kowane masoya suna raya darensu da soyayya ne. Wata kila akwai gajiya a tare da shi, domin be dade da kwanciyar ba na ji bachi ya dauke shi sai ninshari yake irin na wanda bachi yayi masa dadi. A haka muka kwana ni a karshen gado shi kuma a farkon gado fili mai yawa a tsakaninmu.

A tare muka yi sallah asuba, bayan mun gama na gaishe shi na kwantar da kaina a
cinyarsa, sai ya dora hannunsa a fuskata yana shafa fuskar a hankali.

 My beautiful Wife Good Morning, how was your night

 Alhamdullahi ya naka daren

 Alhamdullahi ni ma na kwana cikin farinciki, wannan ne karo na uku da abun farinciki mai girma ya same ni

Na juyo kaina da kyau saitin fuskarsa na kalleshi.

 Fada min biyu, na san na uku

Yayi murmushi ya lakaci hancina.

 Na farko, Auren Fanna, yarinyar nan ta yi kokarin ganin ta dawo da ni hayyacina a lokacin da kika guje ni, ta nuna min kauna ita da iyayenta, na jidadin da Allah ya hada ni da ita, a daren da aka daura aurenmu ta mantar da ni dukan wata damuwa

 Ta ya aka yi ta san mun raba?

Na tambaya ina jin kishi a raina, domin a yanzu na sani ba ni kadai ba ce a zuciyar Zafeer.

 Waye ma be sani ba, gaba daya fa rayuwara ta canja Noor da na rasa ki, na kusan na yi hauka, Allah ya sani na kaunace ki sosai a lokacin, kin san tana kawo gyara ta zo ta same ni wani iri ta tambaye ni me ya same ni na sauya haka, ban fada mata ba amman oga ya fada mata, a lokacin da ta sake zuwa na bar garin nan ne saboda ina jin ba zan iya zama idan ba same ki ba, a lokacin ina jin kamar ba zan iya rayuwa idan babu ke ba Noor

Ya sauke ajiyar zuciya.

 Ta samu number wayata ta gurin oga, ta kira ni ta min nasiha sosai kuma tunatar da ni abun da na manta iyeyena da karatu wanda su suka fi muhimmanci sama da soyayyata da bata samu cikar buri ba, na fada mata ba zan iya zama a garin ba saboda makiya za su min dariya kin yi aure kin bar ni, sai ta bukaci na tafi Sokoto gurin wani dan'uwan mahaifinta na zauna a can, na zauna a can har sai da na samu sukuni na dawo hayyacina ni da mazan gidan muka zama kamar abokai, a lokacin da na dawo sai ta yi min ta yin kaunarta bayan ta ba ni gata na kwantar min da hankali da yin magana da iyeyena, kuma ta gabatar da ni a gurin iyayenta suka min nasiha. Na amsa soyayyarta amman bata bar ni na kashe naira ba, bayan sadakinta da na biya ban san wani abun wahala da na yi ba su ma kuma kudin sadakin ta gurinta na same su, bayan aure kuma takarduna suka fito na yi service sai mahaifinta ya ba ni babban gurbi a ma'aikatarsa

Na tabe baki ina jin zafi a zuciyata.

 Mai arhace ma, ashe ita ta yi maka tayin kanta, kuma ta yi maka komai, wata kila dan bata da masoyi ne

Da gatse na yi maganar domin na lura bara mana soyayya yake, a cikin labarinta da yake ba ni akwai kauna da soyayyarta a zuciyarsa, sai dai ina da tabbacin be kai nawa ba, wata kila ma dai kimarta ne kawai yake gani domin ta cancanci a yaba mata.

 Noor duk zaman da zamu yi dake karki yarda ki fadi wata magana marar dadi akan Fanna, ban ji babu dadi kuma bana son abun da zai kawo tsabani a tsakaninmu, idan Allah ya hada ku ina son ki yi mata biyayya fiye da yadda zaki yi min

 Zan dai maka biyayya kai da kake mijina domin kai na aura kuma kai nake aure ba ita ba, ita dai matsayinta ba zai canja a matsayin matar ka ba, kuma abokiyar zamana

Yayi murmushi ya dauke idonsa akaina.

 Na ji farko fada na biyu

 Na biyun aikin da mahaifinta ya ba ni, already na fada a cikin na dayan ai, daren fa ban iya bachi ba, saboda farinciki, gashi ya sake ma iyayena muhalli kuma bana da su za ayi hajji da yardar Allah, na ukun dai nw baki sani ba

 Na sani mana aurena ko?

Yayi shiru for seconds tare da kai hannunsa a kunnena.

 Eh haka ne, aurenki ne farinciki na uku amman makasudin jiyar da wanda ya jiyar da ni bakinciki ne

Kamar ya san zan tambaya waye sai ya ba ni amsa tun kamin na bukata.

 Na ji farinciki jiya na kwana a farinciki, yau kuma na farka a farinciki wanda ya raba ni da ke kuma na san jiya ya kwana da bakinciki ya farka da shi, zai ji kwatankwacin abun da na ji a lokacin da ya raba ni da ke saboda kawai yana jin yana takama da kudi, kuma ba ma aurenki zai yi ba ya aurawa abokinsa, manufarsa ta yin hakan ne ban gane ba har yau

Gaba daya sai jikina yayi sanyi, zuciyata ta karaya saboda me Zafeer zai aikata abun da zai hana Kareem farinciki? A da can ni ma ban fahimce shi ba, amman a yanzu na sani ba shi da burin da ya wuce ganin farincikina. Na tashi zaune daga kan cinyar Zafeer na kalleshi.

 Bana jin ya raba mu ne saboda isa ta kudi, kuma abokinsa shi ya amsa cewar yana sona a lokacin da alakarmu ta lalace, Baba ne silar komai na sani Allah ka yafe masa

 Me yasa shi be aure ki ba idan har sonki yake?

 Saboda na fada masa na sake nanata masa cewar kai nake so, shi kuma yana tsoron ya auri macen da bata son shi

 A yanzu ya fahimci kina son shi ne shiyasa yake ta shirye shiryen aurenki ko kuma dai yana son ya aureki a haka ne ko da baki son shi, ko kuma dai yana son ya maida ki kamar tsohuwar budurwarsa ne saboda yana ganin kamar baki da wayo...!!

Na kasa sake furta komai na kasa fahimtar gurin da kalaman Zafeer suka dosa, maganar sai ta juye min upside down. Daga haka kuma wata maganar bata sake fitowa daga bakina ba. Shi ma kuma tashi yayi ya fita waje yana amsa wayar matarsa ko ma na ce uwar dakinsa.

Tea ya hada mana daman tun da dare ya siyo kayan tea da komai, ni dai ban ma iya cin biredi ba sai tea kawai na sha, duk inda ya juya kallonsa nake kalamansa nake tunani, na kasa hadewa har sai da na tambaye shi.

 Zafeer idan na canka daidai k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????amar ka aure ni ne saboda Kareem ya ji babu dadi ba dan kana so na ba?

Ya kalleni.

 Idan na ce bana sonki zaki yarda? Ina sonki mana Noor har gobe, amman dai makasudin na dandana masa abun da ya dandana min ne

Tun a kalamin na yi kuskure, ban kuma sake sakin jikina ba, farinciki da ya kamata na samu a gidansa sai na gagara samunsa. Wata kila ni dai kam ba ni da rabon dacewa a cikin aure wata kila tawa kaddarar a cikin aure take.

Har na gama cin amarci yan'uwan Zafeer ba su taba takowa gidana ba, duk wanda zai zo ko ya zo to daga dangin mahaifiyata ne ko mahaifina ko yan unguwa. A tsawon sati biyu da na kwashe a gidan Zafeer be taba kissing dina ba, be taba kai hannunsa a jikina da nufin jiyar da ni jindadi ba, idan har jikina ya hadu da nashi, to ni na kwnatar da kaina ko jikina a nasa, ko kuma na shiga jikinsa da dare idan zamu kwanta sai ya rumgume ni mu yi bachi, hana rantsuwa idan ya dawo daga aiki yana taba fuskata ko hannuna ya tambayi ya nake.

Tun ina hakuri har zuciyata ta fara raya min ba daidai ba, ko dai Zafeer yana kyamata ne ko kuma yana ganin kamar na yi tarayya da Kareem ne, ta ina ma ya san Kareem yana da tsohuwar budurwa? Ta ina ya san Kareem yana shirye shiryen aurena? A duk lokacin da zai amsa wayar matarsa sai ya tashi ya fita a falon ko dakin, idan kuma yana jin kuiyar fita ya kan umarce ni da na yi shiru ne ko kwararan motsi baya son na yi. Yau ma kamar jiya tana kira yayi min alama da na yi shiru sai na tashi na fice daga dakin na shiga kitchen dina domin duba girkina.

Shimkafa da miya na girka domin ita na fi kwarewa kuma ita ce favorite dina. A plate daya na zuba mana na kawo na aje a gabansa sannan koma na dauko mana lemu da ruwa da spoon na dawo na zauna ina facing dinsa, a rayuwata ban taba tunanin zan auri Zafeer na yi irin wannan zaman auren da babu soyayya a ciki ba.

 Ruwan miyar nan be tsane ba Noor kuma gishiri yayi yawa a miyar nan

 Hannuna ne ya subuce

Na amsa cikin rashin jindadi daman na san ban iya ba, kuma abu ne da na cutar da kaina da shi tun a kurciya hauka da rashin natsuwa ba su bar ni na tsaya na koyi girki kamar kanwata Hana ba.

 Ki maida hankali mana, babu abun da namiji yake so irin mace da ta iya girki, haka jiya kika girka tuwo be tuku ba shimkafa a tsaye a ganinta. Kin ga Fanna Wallahi duk gatan ubanta ta iya girki, ban tana siyen abinci ba tun da na aure ta, komai fa maida hankali ne aurenki biyu kina nufin kullum siyen abinci suke ba zaki girka ba? Idan baki iya ba sai yaushe zaki iya Noor?

Ba da fada yayi min maganar ba, amman ambatar Fanna ta fini iya girki ya saka na ji raina ya bace.

 To ka kirata ta zo ta girka maka mana, ai ni ka san ni tun kamin ka aure ni, kuma a haka ka ji zaka iya zama da ni, ba kai kace babu wanda zai iya da ni sai kai ba? Me yasa tun yanzu ka kasa?

Kallona kawai yake har na ci na tsude be ce uffan ba. Sai ma tashi da yayi ya dauki wayaarsa da makullin motarsa ya fice daga gidan. Ni kuma na kwanta a gurin ina hawaye, a yanzu kam na yarda 100% rayuwa bata nufin jindadi a gareni, indai har Zafeer zai aureni na kasa samun farinciki to ba zan same shi ba har abada. A dole kuma haka zan yi hakuri domin ba ni na tsarawa kaina komai ba.

Ni ma ban iya cin abinci ba saboda kuka da bakinciki, bayan fitarsa sai fargaba da tsoro suka kama ni, idan na cigaba da fusata akan wata zan yi ta samun matsala da mijina ne, wata kila har hakan ya zama silar mutuwar aurena wanda bana fata, domin mutane sun min shaidan bana zaman aure, alhalin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Be dawo ba sai dare a lokacin kuka har ya sauya kamanin fuskata, abu ne da ya kamata ace idan da sabo na saba da shi kukan amman na kasa a lokacin da ya kwankwasa kofa sao na bude.

 Sannu da zuwa

 Sannu amayar ya kike fatan an gama fushin yanzu

Yana cire rigarsa yana amsa min, sai na shiga gabansa na durkusa har kasa na bashi hakurin abun da na yi masa a dazun kuma na roki yafiyarsa. Da sauri ya rika ni ya mikar da ni tsaye

 Haba Haba Baby Noor, ki daina wannan dan za ki ba ni hakuri har sai kin kai kasa? Nooo na yafe miki, amman duk abun da nake miki magana akai ina miki ne saboda ki gyara

For the first time ya kai bakinsa ya sumbanci goshina ya sumbanci wuyana, ina jin lokacin da ya fara wasa da gabobin jikina har ta kai mu ga kwanciya saman gadon, sai kuma yayi zumut ya zare hannunsa da jikin da sauri ya sauka bakin gadon ya sauke kai kasa yana sauke ajiyar zuciya. Kwakkwaran motsi ban yi ba har safe tunani ya rufe ni, kyamata Zafeer yake ko kuma dai akwai abun da baya son fada min. A tare muka shirya abun karyawa, a duk lokacin da na kalleshi sai na yi ta tuna kalamansa na baya, idan na tuna yadda ya fada min zamu shimfida soyayya sai na tambayi kaina to yanzu me yake jira?

Zuciyata ta kan tunatar da ni cewar a yanzu ba ni kadai ba ce a zuciyar Zafeer, kuma na san baya kallona a wacan matsayin na da, a dole na shafa kaina lafiya. Wata rana da muka fita tare da shi muna zaga gari yana ta nuna min gurare ciki har da gidan da yake zaune da matarsa gidan sama ne mai hawa biyu ba ko daya ba, wajen gidan kadai ya wadatar da mai kallo, dan haka bana bukatar aban labarin cikinsa. Ya kai ni gidansu gurin iyayensa su ma gidan mai kyau suke zaune ba laifi Mahaifin Fanna yayi kokari gurin sama masa ingantacciya rayuwa shi da iyayensa.

Tun da muka gaisa da mahaifiyarsa ta fice ta bar ni a dakin, kanensa ma kamar an musu dole haka suka gaishe ni, suka fice daga dakin kai kace wani na kashe musu, ko da yake suna da hujja na guji dansu a da can sai a yanzu na aureshi. Sai da za mu fita na sake yi mata sallama a tsakar gida na wuce ko Allah ya kiyaye hanya bata ce ba, balle ta yi godiyar abinci da na kawo musu. Daga gidansu ya sauke ni gurin Mama ta yi farincikin ganina tun da yake zuwana na biyu ne bayan auren, ni ma jidadi ganinta na same ta tana ta shawarar maka Alhaji a kotu wai so take ya sake ta ta huta shi kuma yace ba zai sake ta ba.

 Amman Mama ba ke kika ce mace kamar riga take a wuyansa ba? Me yasa ba zai sake ki ba?

 Shi da kansa haka ya fada min kuma haka mutane suka shaida amman na yi kida na yi rawa na yi yakin duniyar bawan Allah nan ya ki yarda ya ba ni takardar sakina, shi kokarin ma yake ya ga na koma

Ba zan bata shawarar komawa ba, domin duk wani abu da ya shafi Abdull bana kaunarsa a yanzu, kuma ba zan karfafa mata guiwar kashe auren ba domin ban san abun da Allah zai shirya a gaba ba. Mun yi hira ta saka min albarka domin ita ma na kai mata abinci da dan alheri da zan iya. A lokacin da Zafeer ya dawo daukata ya shigo suka gaisa sannan ya fito tana saka min albarka muka dawo gida tare. A daren na kwana da ciwon mara sosai washe gari na tashi da period.

Kwana uku na yi sannan yi tsarki, kamar yadda na tsammata Zafeer ba neme ni ba, sai ma ya zo min da albishir wai Fanna zata dawo wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login