Showing 108001 words to 111000 words out of 227321 words

Chapter 37 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1534

su, ba iyaye ne suka cilasta ba, duk wani yunkuri da yake saboda ni ne, daga karshe kuma sai abun ya fada kansa, ashe saboda ya tafi ya bar ni da bakinciki kasa cika masa burinsa ne da ban yi ba...

Ya dago ya kalleta yana murmushi.

 Kin san banbancinki da Noor? Ta fi ki wayo ta fi ki imani da yardar da kaddara, ta fi ki tsoron duniya, yarinyar nan bata iya munafurci da pretending ba, tsabar saka shi da ta yi a zuciya na nesan da ta yi na kwana biyu sai da ta yi mafarkin mutuwarsa tun kamin a fada mata ya rasu, a ranar da za a binne Hafiz na ga wani abun da ban yi zato ba gurin yarinyar nan, ta rike karagarsa tana kuka, na tabbatar da ni aka sanar miki na mutu murna zaki yi...

Ta yi murmushi.

 Kasan da hakan kuma kake zaune da ni har yanzu? Idan zaka kwatanta Noor da misalta ta da Safeena mana, ka ce ta fi Safeena wayo, amman ba ni ba, ni din na san abun da nake so da wanda bana so. Ko da yake dole ka yaba Noor ai, saboda kana sonta shiyasa ka cilastawa abokinka aurenta, yanzu kuma ya tafi ya barku sai ku cigaba daga inda kuka tsay....

Tana kai aya yana wanke mata fuska da wani zazzafan mari, har sai da ta ja baya

 Ka mare ni Kareem? How dare you...!!

 Saki kike so? Tafi na sake ki Yusura

A take ta daina jin zafin marin, farinciki furucinsa ya wanke mata damuwarta. Idan ta tace bata ji tausayin Kareem na mutuwar amininsa ba ta yi karfa haka ma idan tace bata yi farinciki da sakin da Kareem yayi mata a yau ba, ta yi babbar karya. A gurin ta yi sujudar godiya sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin.
Slowly ya zauna bakin gadonsa be taba tsammanin kiyayyar da Yusura take masa ta kai haka ba. Be yi tunanin akwai kiyayyar da zata kai irin ta Yusura ba a zaman aure, ba zai yana sonta ba, amman baya ganin rabuwa da ita a yanzu mafita ne saboda yaransu.







Baba yana kallona ne kamar ni na kashe Hafiz saboda, Hafiz ya tafi be samu kyautatawa Baba kamar gyara masa gida ko kuma yi masa wata babbar kyauta da yake tsammani ba tun a bayan aurena.
Ni ma ban fahimci hakan ba sai a ranar da Hafiz ya cika sati daya da barin duniya, Mama ta kira waya tana kara kwantar min da hankali, bayan mun gama wayar ne Baba ya rufe ni da fada wai na ci amanarsa wata kila da na kyautata masa da yanzu Allah kadai ya san yadda rayuwa zata zame mana.

 Daman sai da zuciyata ta raya min ba zaman lafiya kike da yaron nan ba, saboda juya min baya da yayi ko lokacin da gobarar nan ta tashi be zo yayi min jaje ba, be ba ni komai ba, ashe ma ba zai dade duniyar ba, kina ta shuka masa rashin mutunci, in ba shi ba taya za su ce wai ba za ki masa wanka ba? Ta ina aka taba haka so suke su hana miki gadonsa kenan

Ni dai bance komai ba, gaba daya duniyar bata min dadi, ni kaina ina dorawa kaina nauyin da ba zai gogu ba saboda hana mijina hakkinsa da na yi, ya tafi da abun a ransa kuma na daukarwa kaina zunubi.

 Wallahi zan iya kararsu akan haka, domin babu hujjar da tace ba za a baki gado ba, na bincike limin yace kina da hakkin wanka domin an riga da an daura muku aure, kuma sakin da yayi miki ai ba ki cika idda ba

Sai a lokacin na kalleshi cikin wani irin rauni da damuwa na ce.

 Baba dan Allah ko da sun ce ba za su ba ni hakkin wanka ba, dan girman Allah dan Isar Annabi, Baba kar kace zaka yi kara ko fada ko kuma daukar wani mataki, dan Allah ka kyale su, idan ma ina da hakki Allah ya sani zai saka min

 Toh haka za a zuba musu ido su ci su cinye hakkinki Noor? Idan aka karba ai ko wani abun a rage da shi, dubi yadda gidan nan yake fa, ko gyara aka yi ba a rage ba? Allah kadai ya san abun da bawan Allah nan ya bari

 Ko ma dai miye bari Baba mai karewa ne, rayuwar ma ta kare balle kuma abun da rayuwarta ta aje, ni dai da zaka yarda da magana ta Baba da ka yi hakuri ka kyale komai dan Allah

 Ai daman ke sakarya ce baki san komai ba, sai shashanshanci, ba dan kin nuna masa rashin tarbiya da rashin hankali ba yaushe zai sake ki? Allah ya wadarranki Noor, duk yadda nake ganin kamar zaki natsu ko ki yi hankali ba zaki taba yi ba, duk yadda bake ganin kamar sanadinki wata kila zan warke sai kin kunyartar da ni, ke dai har abada va yar arziki ba ce

Ya rufe da fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ni dai kam na san ban yi dacen abubuwa da yawa ba a rayuwa ciki har da uba. Domin ko a labari ban taba jin uba makamancin nawa ba, mai tsananin kwadayi da son abun duniya.
Na sani sarai idan na kara wata maganar zai iya rufe ni da duka, a dole na yi shiru na ina ta sauraren masifarsa har yayi ya gama ya fice daga gidan. Haka na gagara tashi a gurin har Hana ta dawo daga makaranta ta same ni zaune a kofar dakin, ni ba kuka nake ba damuwa karara a fuskata, tunanin yadda rayuwa zata zame min nake, hankali ko tunanin da suke ganin kamar ba ni da shi ina da shi, ni na san ina da shi, idan ma babu a da to yanzu yana tare da ni. Rayuwar gidance nake jin kamar ba zata min dadin zama ba, gashi kuma ba ni da wani gurin rabawa da zan zauna na ji sanyi.

Yunkurawa na yi na tashi na nufi gurin da kayan wanke wankemu suke na wanke komai tass Hana kuma ta dora girki ta girka mana shimkafa da miya, duk da kasancewa white rice and stew are my favorite amman ban iya cin wani abun kirki ba, daman abinci ya daina burge ni. Kamar wani zanenen al'amari a daren da muka yi haka da Baba sai ga kanen margayi ya zo gidanmu, ban san ya aka yi ya gane gidan ba, kusan ni dai zan iya cewa ban taba ganinsa ba, idan ma na ganshi ba zan iya shaidar fuskarsa ba, domin ban jima a gidan ba balle na san duka yan'uwansa balle kuma mazan da be gabatar min da su ba. A zauren gidanmu ya shigo bayan yayi sallama Hana ta yi masa izinin shigowa. Dogon hijab ne a jikina har kasa kaina kuma a kasa na kasa kallonsa ganin nake kowa kallona yake a wani muhalli da Aisha ta saka ni a idonsu.
Bayan mun gaisa ya gyara tsayuwarsa ya ce.

 Ya Hakuri Noor?

 Alhamdullahi

 Haka Allah ya so sai hakuri, shi kuma Allah yayi masa rahama

 Ameen

Na amsa ina jin idanuwa suna cika da kwalla.

 Na san babu dadi, musamman ma ke da kike farkon shiga gidansa ba ki jima ba mutuwa ta yi muku gaggawa, amman duk da haka ki yi hakuri yana cikin jarabawa ne

 Haka ne, na gode

 Na san ba ki san ni sosai ba, ni kane ne a gurin Margayi uwa daya uba daya, ni ne kanensa na biyu, makasodin zuwa na a nan shi ne... Abubuwa marasa dadi sun shiga kuma za su biyo baya na sani, amman dan Allah ina son ku kawar da kanku musamman ma ke, ki yi hakuri da abubuwan da zaki ji ko ki gani

Na yi shiru ina ta sauraren bayaninsa da ban fahimci inda ya dosa ba.

 Na ji wasu abubuwan ne da ba su min dadi a gidanmu, na iya yadda zan iya na taushe abun amman ya gagara saboda haihuwarmu aka yi ba mu muka haife su ba, dole sai hakuri, amman na san ke zan iya neman alfarma a gurinki kuma na roke ki duk kuwa da ba ki san ni ba, amman ina rokon alfarmar dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen margayi akan gadonki, ke ba da kike da shi ba balle ace saboda da gaba, kina gama wanka na san In Shaa Allahu zaki yi aurenki, bana son na ji wata matsala ta taso daga gurinki, ni dai ina kyautata miki zato sosai

 Ni ba zan iya jayaya akan abun da rai ya tara kuma ya tafi ya bari ba, wanda ya tara abun ma ina yake? Toh me zai saka ni yin jayayya? Idan ma ina da hakki abun da za su ba ni ba zai taka kara ya karya ba, ba shi ne gabana ba, kuma na maka alkawari ba zaka taba jin wani abu makamancin wannan daga bangarena ba

Ya sauke ajiyar zuciya yana kallona.

 Na yi farinciki da jin haka, na jidadi sosai Allah ya saka miki da alheri, ya baki wanda zai maye miki gurbin Ya Hafiz har ma ya fi shi

Na yi shiru ban iya amsawa da Ameen ba. Daga haka yayi min sallama ya tafi, ni kuma na dawo cikin gidan ina ta mamaki mi ya ji danginsa ana fada har dauko kafafuwansa ya zo ya tari nawa fadan, ni kan idan gado ne ko nawa ne ba zai daga min hankali ba balle ya saka ni yin magana ko daukar wata dokar tsorona duk na Baba ne.

Ban fadawa Baba wani ya zo ba, sai dai na lura hakan be yanke komai daga hanzarinsa na niyar saka iyayen Hafiz a kotu ba, idan har ba su ba da hakkina na wanka ba, na fahinci hakan ne ta dalilin wayar da na ji yana yi da yayansa wai ya bincika ko'ina ance ina da gado, dan haka ba zai saka musu ido su cinye min hakkin ba. Ban ce komai ba daman kuma ban isa na ce ya rufe da fada ba mamaki ma ya kara min duka. Zaman gidan sam baya min dadi kamar ina zaune a kaya haka nake ji. Ba ka kamar lokacin da sabuwar matar da Baba ya aura ta tare a gidan.

Gaba daya sai gidan ya kara fice min a rai, domin na lura ta shigo da wani salo na hana mu walwala ni da Hana da kuma Yaya, gara ma yaya ba a gidan yake wuni ba, sai dare yake dawowa ni da Hana ne muke ganin rayuwa a gidan. Babu kuma wanda ya isa yayi magana domin mun san halin Baba ba zai taba yarda da mu ba.

Umma bata wuce wata biyu ba a gidan ta cigaba da sana'o'inta da take, daman na ji Hana na fadar wai ance tana siyar da kunun waken soya kuma tana wara tana kosai, domin ba yar garin Kano ba ce asalinta yar riSa ce dake can kusa da zuru ta birnin kebbi amman take zaune a nan Kano gurin Yayarta bayan rasuwar mijinta na farko, tana sana'a har Allah ya kawo mata Baba ya aureta a yanzu.

Bata taba haihuwa ba a wacan auren nata kamar yadda take labarta masa wani lokaci ni da hana, ba wata babbar mace ce be domin Mama ta yi kanwa da ita ta biyu, sai dai tana da irin jikin nan sosai da zata iya daukar Mama da irinta uku ta goya ta gudu, domin ni da Mama jikinmu daya, ita ba kiba ni ma babu kibar, ba mamaki ma kibar ce ta burge Baba ya aurota.

Wani sabon salo da ta kirkira shi ne na dorawa Hana tallar awarar a titi tana siyar mata kullum zata bata 500 naira, ita kuma tana yin kunun waken soyar a gida, ana shigowa ana siya sai dai ba sosai kamar yadda take fada mana ba.

Dole ce ta saka Hana yarda tana soya mana awara a waje ba dan tana so ba, domin ko a lokacin da Mama take gidan kuma muke cikin tsananin shan wahala bata taba gwada dora mana talla ba, amman ita wannan da ba uwarmu ba ta fara dora ma Hana talla daga zuwanta.

Ko da yake ba laifinta babne laifin Baba domin shi ya bata dama Hana kuma bata isa tace ba zata yi ba, duk kuwa da kasancewar bata so ko kadan. Domin fita tallar ya kashe mata tafiya makarantar yamma, ya zama boko kawai take iya tafiya da safe.

Ni kuma aka bar ni da wahalar aikin gidan, shara wanke wanke da hura wuta tun ban iya ba har na iya, girkin ne kawai bata bari na yi domin na gwada girkanwa ta ji be yi mata yadda take ba. Idan zata hada kunun wanken soyan ni nake wanke goruna ni nake mata komai har tacewa, awara kuma ni zan gyara wake da dare da safe taje ta kanta ta kai nika, idan ta dafa a tare zamu natse ni zan yanka idan aka soya be wuce a ba ni da hansin ba ko saba'in.

Wani sabon shafin wahalar rayuwa Umma ta bude mana a idan, ni da Hana saboda sana'ar da take wai ai ba ita zata fita ta yi ba a dole hana zata soya mana wara a waje ni kuma na yi aikin cikin gida. Ta inda nake samun sauki shi ne takaba da nake bana fita, saboda haka duk wani aiki na fita ita zata fita ta yi, da safe kuma Yaya sai ya cika gidan da ruwa sannan yake fita.

Ta inda gurin da ta samu banbancin da Mama a zamanta gidan ita kam Baba yana bata abinci da cefane mai kyau, ba kamar Mama ba da wani lokacin zai ce be da shi ko kuma ya bada abinci ya hana cefane ko ma ya hana gaba daya. Wata kila saboda ita din tana da dan da sauran kurciya ba kamar Mama ba, wata kila kuma dokin amarci ne yake Allah masani.

Idan kuma aka yi girki ba a ba mu wani abun arziki Allah ma ya sa yanzu damuwa bata barina na ci na koshi kamar da, wani lokacin har ragewa nake na bawa Hana a da kam na fi kowa cin abinci a gidan, ranar da Hana ta tafi family house din Mama ta fada musu halin da ake ciki na dora mata talla, washe gari Kawu Garba ya samu Baba yana nuna masa hakan be dace ba, sai Baba yace kar wanda ya sake saka masa baki akan lamarin yaransa shi ya ga damar su yi, kuma babu mai ciyar masa da yara sai su.

A nan yake fadar ai tun kamin auren ya fada mata yaransa za su rika mata wani abun saboda ta fada masa ita fa tana sana'a kuma aure ba zai hana ta yi ba, shi kuma ba zai iya ganin matarsa da aure ta fita waje ta yi sana'ar wara ba, domin haka yarsa zata maye masa gurbi. Ni kam gaba daya na zama kamar ba ni ba duk abun da ake bana iya cewa komai sai ido, wani kalar canji ne ya same ni irin wanda ban yi zato ba.





KAREEM POV.

Da kansa ya shiryawa yaransa abun karyawa ya dauko lunch box dinsu ya raka su har gurin School bus suka shiga sannan ya juyo ya dawo, dakinsa ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito ya shiga motarsa. Family house dinsu ya wuce domin fara gaisawa da iyayensa kamin ya wuce aiki kasancewar yau Monday.

Wani abun da ya sabawa kansa da shi ne, na kin kallon mahaifiyarsa a duk lokacin da ya shiga gidan. Kai tsaye ya wuce bangaren Hajiya Hassana wadda take step mom dinsa. Karyawa ya same ta tana yi tare da Khadija da Aaryam da sauran yaransa Aneesa da Kamla. Kanensa duk suka gaishe shi ya amsa, Yusura dake zaune gefe daya ta mike tsaye ta shige dakin Hajiya Hassana sai a lokacin ma Kareem ya lura da ita. Khadija ta kwashi kayan abincin ta bi bayan Yusura Kamla da Anessa ma haka, sai ya rage daga Step Mom dinsa sai kanensa Aaryam.

 Zaka ci abincin a zuba maka?

Hajiya ta tambaya.

 Aa

 Baka cin abinci yanzu, tun da Momynka bata nan, shigowa nan ma sai monday Monday kake yi ka duba mu, idan Momynka bata nan ni da mahaifinka ai muna nan kuma Kanenka suna nan be kamata kana haka ba

A hankali ya sauke ajiyar zuciya.

 Hajiya Bana jindadin shigowa ne yana yawan tuna min da Momy kuma ina jin babu dadi

 Tohm ya za'ayi haka tsarin Allah yake, kai kanka mutuwa zaka yi balle kuma wasu, sai hakuri rayuwa ta gaji haka, ni kaina yanzu gidan ba dadi yake min ba Wallahi, amman a haka nake daurewa saboda Khadija da Aaryam da kuma Aneesah, dole na yi walwala idan ba haka ba dukanmu sai mu taru mu takura mu yi ta bakinciki da kuka


Yayi shiru be ce komai ba. Hajiya ta dauki tissue ta goge hannunta.

 Likita..

Ta kira shi sai ya kalleta daman haka take kiransa tun Momy na gidan.

 Ni fa ba zan boye maka ba, ban gane manufar abun da ka yi ba, kuma ban gane inda kuka dosa ba

 Na miye ba Hajiya?

 Kai da Yusura mana, ta dawo gida kawai tace mana ka sake ta, saki daya biyu ko uku ba mu sani ba, Daddy ka ma fushi yake da kai shiyasa be maka maganar ba har yau, Khadija da Aaryam ma gashi a zaune kullum haushinka suke ji saboda haka

Kareem ya juya ya kalli Aaryam kyakkyawan saurayi mai jini a jika, sai yayi murmushi.

 Saboda Yusura?

 Eh mana, Daddynka cewa yayi ba zai maka magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login