Showing 147001 words to 150000 words out of 227321 words

Chapter 50 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1564

cin amana Hana?

Ta share hawayenta.

 Ina nufin kamar na guje ki saboda kin min wani laifi, ai kamar na ci amanarki ne a matsayinki na yar'uwata

 To me yasa kike son tafiya gida? Kina karatunki a nan, Abdull ma idan ya ji ai zai yi fada, Mama ma sai ta miki fada tace kin san ba zaki karatu ba kika saka bata kudi aka biya miki har na shekara uku

 Kawai ina yawan mafarkin marar kyau ne, kuma ana baki tsoro a gidan nan ina tunanin akwai aljannu a gidan

 To ki rika addu'a mana Hana, ke da kike fada min yadda zan bi da rayuwa na jidadi yau kuma ke kika rasa ya zaki yi?

Ta yi murmushi

 Gaba daya na rikice mugun mafarkin da na yi ya daga min hankali

Zan sake yin magana Abdull ya kirani.

 Noor kin fasa zuwa awon ne? Karki makara fa

Na dauki ruwan zafi na fice daga kitchen, sai da ta jera mana komai a dinning sannan ta zuba nata ta dauka.

 Lafiya na ga kamar yanayinta ya canja

Abdull ya tambaya she dai shi ma ya lura da yadda take ta hade rai bata son kallon kowa.

 Lafiya kalau

Ta wuce dakinta bayan ta amsa mishi, da kallo na bita sai da ta shige sannan na juyo na kalleshi, kamar na fada masa kudurinta sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na san ba abu ne da zai masa dadi ba, saboda kudin makaranta da ya biya mata ga yawan hidima da yake mata, tafiya makaranta ma kullum sai ya bata kudin bus kuma ya rage mata hanya saboda akwai tazara daga unguwarmu zuwa makaranta kuma babu abun hawa sosai ta gurarenmu sai idan sun kawo Passenger.

 Ina jin bata da lafiya ne

 Me yake damunta? Ko kuma dai mood swings ne

 Yeah

Ko da muka gama karyawa ta yi shirin makaranta da uniform dinta da suke sakawa kullum. Tare muka fita sai da ya fara sauketa sannan ya sauke ni a asibitin ya wuce gurin aikinsa.

Tun daga ranar Hana bata sake yi min maganar komawa gida ba, sai dai na lura da yanayinta gaba daya ya canja kamar zaman gidan ya daina mata dadi a yanzu, domin ko hirar da take zama muna yi tare da Abdull a da yanzu duk ta daina, ko da yake yanzu ba kamar da ba ne, da take gida kullum yanzu kuma idan ta tafi bata dawowa sai yamma idan ta dawo wani sa'in ta hau aikin gida ko da ta gama kuma sai bachi. Sai can ba a rasa ba muke zama muna hira a falo da zarar Abdull ya shigo zata masa sannu da zuwa ta shige dakinta ba zata sake fitowa sai gobe.

Ko wani abun ya siyo sai dai na kai mata nata dakinta, ko kuma shi ya kwankwasa kofar dakin ya aje mata daga bakin kofa, wani sa'in idan ina jin wahalar tashi. Wata kila ta fara haduwa da abokan banza masu hore mata kunne ne, ko kuma dai ta gaji da yin aikin gida ne, ko kuma nata gidan mijin take son tafiya ita ma.
Ko ma dai yaya ne na daure ma zuciyata na zauna da ita a haka, saboda bana son ta lakata karatunta a lokacin da take tsananin bukatarsa, kuma ana yi da kai ya fi ba'ayi, zamanta yana taimaka min ko yaya ne tun da ita take min komai a gidan kuma ina ganinta na san ina da yar'uwa a kusa ina jin sanyi a haka din ma.





KAREEM POV.

Da sauri ya maida idon ya rufe ya kai hannunsa dake sanye da drip ya murza idon sannan ya sake budewa. Hannun ya kai ya cire robar dake bakinsa yana kokarin daga hannunsa daya sai ya ji yayi masa nauyi dubawar da zai yi sai yayi arba kan dansa Areef a hannun. Yunkurawa yayi a haka ya tashi zaune ya saka dayan hannun a hankali ya cire hannunsa. Haka ya cire duk wani abu da aka laka masa sannan ya sauko da kafafuwansa yana tuna abun da ya faru.

Ya san dai yana tsaka da tuki hudu ya sauko masa daga lokacin kuma be sake sanin inda yake ba, maybe ya hadari yayi, ba ma wata kila idan be yi hadarin ba ai ba za a kawo shi nan a aje ba. But why ICU shi da be ji ciwo ko daya a jikinsa ba, domin be ga wani guri da ya ji ciwo bako ya bugu. Hannu ya mika ya janyo files dinsa ya bude ya duba. Daman ya sani zama unconscious or in a critical condition ke saka a aje mutum a gurin. Ya duba ya gani kwanansa biyu a dakin amman be sani ba sai yau da ya farka, babu wata rauni a jikinsa but hankalinsa da numfashi sun yi nisan da an dauka barin duniyar zai yi.

Ko me ua buga oho, ya san dai hakan baya rasa nasara da damuwar da yake ciki, kusan ita ce silar faruwa komai. Ya aje files din ya shafa kan dansa dake sanye da uniform din makaranta yana murmushi ko dan yaran nan yana bukatar rayuwa. Areef ya bude ido sakamakon shafa kansa da Dadynsa yayi.

 Hey young Man

Yaron ya tashi zaune ya matsa ya rumgume mahaifinsa yana murna.

 Dady ka farka

Kareem ya saka hannu ya shafa bayansa yana murmushi kamin wani azababben ciwo ya ratsa zuciyarsa har sai da ya ji ta motsa kamar ta bar muhallinta.

 Oh...

Ya furta Areef ya dago ya kalleshi.

 Dady minene?

Kareem ya murmushi.

 Ba komai ina Tine

 Suna waje bari na kira ta har da Mama ma tana nan, kullum zai mun zo kana bachi, Hajiya tana nan ita da Uncle Aaryan nan yake kwana

Har ya isa kofa sai kuma ya juyo ya kalleshi.

 Daddy ma kullum yana zuwa, yana yin addu'a yana tofa maka, Dady kuma Momy ta kwashe kayanta gaba daya ta koma gurin Hajiya an bata bangare daya tace tare zata zauna da mu

Kareem ya daga mishi kai. Areef ya fita da gudunsa, Kareem kuma ya mike tsaye ya fito daga dakin da kafafuwa normal yake jin kansa kamar be yi hadari ba. Ya san yadda asibitin take fa kuma dokokinta sai ya canja ma kansa daki bayan ya gaisa da ma'aikatan dake ta masa sannu Doctor dake duty yana da tsokarsa yana fadin ya bari yayi aikinsa yanzu shi majinyaci ne ba likita ba

Files din dake dayan dakin likita ya dauko ya dawo da su sabon dakin da Kareem yake, sannan aka bawa visitors damar shiga, yan'uwa na ta shigowa suna masa sannu na nesa kuma suna kira a waya. Duk wani motsi nasa yana kan idon Yusura kallonsa take sosai kamar bata taba ganinsa ba, sau daya ta yi masa ya jiki bata sake ba sai dai duk dagowar da zai yi sai ya ga tana kallonsa. Tun daga ranar kuma bata sake zuwa ba duba shi har aka sallame shi after four day's da yayi a asibitin.

Ranar da zai bar asibitin babu yadda Hajiya bata yi ba akan ya dawo family house ya zauna har sai jikin ya kara warwarewa da kyau saboda a can gidan babu kowa a yanzu amman ya ki, domin baya son zama gidan zai fi sakewa a gida ko da kuwa ba shi da lafiyar balle baya jin ciwon komai a jikinsa. Taya zai saki matarsa ta tare a family house dinsu shi ma ya koma can ya tare kamar mace.

Ba karamin godiya yayi ma Allah ba lokacin da Aaryam ya kai shi gidan ya ga yadda gaban motarsa ya lalace, bayan ma ya bugu ba karamin accident yayi ba amman Allah ya kawo masa sauki tun da be ji rauni a ko'ina ba. Aaryam ya fada masa yadda hadarin ya afko sai da ya cika da tsananin mamaki.

 Babu wanda ya dauka zaka rayu fa, Wallahi duk mun tsorata, babba mota ka buga irin mai zube yashin tefa. Mai motar yace yana ta maka horn domin ya ga yadda ka zo da gudu amman baka tsaya ba sai da ka bugu shi, gashi ita kuma wata motar ta bugi taka a baya, daker aka fito da kai motar babu rauni amman baka numfashi hankali ya bace gaba daya, asibitin ma sai da aka yi da gaske sannan numfashinka ya dawo

Yayi murmushi.

 Kwana ne ba su kare ba, da lokacin yayi da ba zan farka ba, Alhamdullahi

 Gaskiya mun auna arziki, da mun rasa ka rayuwa ba zata yi dadi ba

Kareem ya kalli falon ya mike tsaye.

 Wata rana dole za ku rasa ni Aaryan dole kuma ayi hakuri da rayuwar

 Haka ne, amman ba ma fatan zuwanta yanzu, Allah dai ya kara maka lafiya

 Ameen

Aayam ya sauke ajiyar zuciya.

 Yusura da Khadija sun sha kuka, Hajiya har sai da aka zuba mata ruwa, ban taba ganinta cikin tashin hankali irin na ranar ba, babu wanda be yi kuka ba sai ni

Kareem ya juyo ya kalleshi.

 Eh kai mai zuciyar fir'auna ko?

Aaryam yayi dariya.

 Ai duk abun da zai saka namiji kuka ba karamin abu ba ne, Allah dai ya tsare faruwar hakan

Dinning Kareem ya dafa.

 Yusura bata fada muku abun da ya faru ba?

 Ta fada mana, har ta kwashe kayanta ai Hajiya ta bata bangare daya ta zauna saboda ta samu sakewa ita da yaranta, Khadija da Nana sun koma bangarenta, na yi mamakin kukanta wata kila ita ma ta dauka mutuwa zaka yi

 Daddy be ce komai ba a game da rabuwarmu?

 Ba ka da matsala da shi, tun a lokacin da aka fada min halin da kake ciki sai na same shi na yi masa bayanin komai, saboda mu samu goyon bayansa idan zaka kara aure, ashe Allah da kai ba, amman dai ya sani kuma ya daga maka kafa. Kawai addu'a yayi Allah yasa hakan shi ne mafi alheri

Dogon numfashi Kareem yaja ya sauke ya daga kansa sama.

 Ameen

A gidan Aaryam ya wuni saboda ya ragewa dan'uwansa Zango har sai da yamma ta yi sannan ya tafi bayan sun sha hira sosai. Kareem ya juyo kenan daga rakiyar da yayi ma Aaryan bakin kofar falon sako ya shigo wayarsa.

 Wata kila ni ce silar hadarinka? Shin ka aikata hakan ne da nufin kashe kanka? Ka ji zafin gaskiyar da ka sani ne Kareem? Ni ma daga baya na gane ban kyauta ba na yi kuskure, amman na maka alkwari babu wanda zai ji wannan, ina zuwa dubaka asibiti a kullum amman bana samun damar shiga na ganka saboda yan'uwanka da matarka suna gurin. Yau kuma na tafi aka ce an sallame ka na jidadin haka kuma na ji tausayinka na yi bakinciki abun da ua faru da kai, ina kaunarka Kareem Wallahi ina kaunarka

Ya goge sakon bayan ya gama karantawa, ko ya fada mata yayi hadarin ma oho, falon ya shiga ya kwanta akan kujera ya rufe ido yana maida numfashi a hankali.





NOOR POV.


A lokacin da cikina ya shiga wata bakwai na samu sauki abubuwa da yawa na daina amai da kwadayin sosai, ko zabar abinci. Har ta kai ni nake shirya abun karyawa da safe da kaina. Domin yanzu Hana ce mai tsananin bachin safe idan ta gama sallah ta koma ta kwana sai kace ba yar makaranta ba. Kullum sai ta buga latti saboda bachi, har tausayi take ba ni domin na san wahala ce ta yi mata yawa, na aikin gida da take ga kuma karatu da basa daga kafa.

Abun sai ya zame mana kamar duty ni ce mai saurin bachin dare ita kuma ta yi rankon na safe. Domin da zarar na gama sallah Isha'i Abdull ya kawo lemun juice da yake hada min a kullum, domin likita yace na rika cin yayan itatuwa sosai a yanzu fiye da kayan zafi ko kwadayi irin su madara da danginsu. Saboda kina yana ta girma ne a yanzu, ban yi kasa a guiwa ba na rumgumi kayan marmari, kullum sai na ci da dare kuma sai Abdull ya hada min lemun juice da juicer da ya siya gurin Khadeeja Candy Store, zallar ruwan fruit take matsewa sai dan sukari kadan da yake kasa min ko kuma abar da bana so wato zuma, wani lokacin saboda bakin nawa ya saba da zaki idan babu ba zan sha ba. Da zarar ya hada min na sha sai bachi yayi gaba da ni, ko motsi ba zan yi ba sai safe.

Ina tsaka da shafa face cream ya shigo dakin ya aje min cup din natural orange juice. Sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko kayan bachinsa ya saka.

 Kina bukatar wani abu?

Na kalleshi kamar na ce ina da bukatar ka, yau wata shida kenan ban hada shimfida da mijina ba, tun cikina na wata daya da yan kwanaki ya nade sha'awata ya jefar saboda kawai na ki yarda a zubar da cikin. Sai kuma wata zuciyar tace na daure mana na zuba masa ido tun da haka ya zaba.

 Aa

 Okay to zaki yi kallo?

 Aa bachi zan yi

 Yanzu ai kin lalace da bachin dare, da dare yayi sai bachi kamin tara na dare ta yi har kin kai Morocco, Allah yasa ba raguwa ko rago zaki haifa ba, wannan lalaci yayi yawa

Na yi dariya mai sauti ina masa gwalo.

 Bachin yana min dadi, da na kwanta bana sanin me duniya take ciki sai na farka

 Asha bachi lafiya Mom Unborn

Ya fice ya bar ni na cigaba da shafa face cream din, sai da na gama sannan na dauki lemun juice din na sha kadan sai na ji zakin zumar yayi min yawa gashi ba son zuma nake sosai ba, haka na saka dole na tashi na shiga bathroom na kunna tap na tara lemun na kara ruwa kadan, na kashe juyowar da zan yi santsin tile ya kwashe ni, aiko ba shiri na saki kofin na rike tab din sai kofin ya fadi kasa lemun ya zube.

 Allah ya tsare na auna arziki yau kai...

Na fada ina hakki, da na fadi gurin ba karamin ciwo zan ji ba, waya sani ma ko na karye tun da jikin babu karfi. Ruwa na saka na wanke lemun da ya zube na dauke kofin da ya tsaga na fito na aje shi a inda na saba ajewa na hau gadon na yi addu'a na kwanta, nan da nan kuwa bachi yace wa yake jira ba ni ba, kamar na mutu haka na fara bachin ban san shigowar Abdull dakin ba, kashe wuta da yayi ma duk ban sani ba. Daman bana sanin komai sai safe.

Ina tunanin shan lemun yana taimaka min sosai gurin samun bachi mai dadi kuma mai nauyi da tsayi, domin yau da ban shanye shi gaba daya ba na farka sai dai ban kai ga motsawa ba na ji saukar Abdull daga kan gadon ya nufi bathroom, yana shiga na ji kararar ruwa be jima ba ya fito ina kallonsa ya rufe kofar a hankali ba tare da ya kashe ruwan ba. Mamaki ya cika kwakwalwata ashe har yanzu be daina wannan abun ba, domin tun a wacan lokacin zuciyata take raya min yana biyawa kansa bukata ne a bandakin.

Ina ganin ya dauki wayarsa sai na rufe idona, na yi zaton bandakin zai koma sai gashi ya kunna fitilar wayar ya haska fuskata. Ni kuma na yi kamar bachin nake da gaske har sai da ya kauce sannan na bude ido. Ga mamaki na sai na ga ya nufi kofar fita ya bude a hankali ya fice. Zumut na tashi zaune kamar ledar da iska ya dauka. Na zauna gurin da tsawon minti biyar ban ji ya dawo ba, sai na sauko daga kan gadon na bude bandakin na kunna guluf na duba sannan na kashe na janyo kofar na rufe a yadda take.

Takawa na yi na fita dakin, a tunanin yana falo ne, sai dai kuma ban same shi a falon ba, domin wutar falon ma a kashe take ban ga hasken wayarsa ba kuma ban ga alamar mutum ba ta dan hasken waje da yake shigowa. Na nufi ma kunnun wutar kamar zan kunna sai kuma na fasa na nufi kitchen na leka nan ma baya nan. Na juyowa na nufo dakina da mamaki domin ko kadan zuciyata ba ta raya min abun da kunnuwa za su ji ba. Daf da zan shiga dakina ne na ji karar rufe kofar dakin Hana wata kila kuma na bandakinta ne yayi kara har na ji saboda dare ne, hakan ya saka hankalina ya karkata can, to daman idan baya falo baya kitchen baya dakina ina zai je? Waje? A tsakar daren nan ba zai fita waje ba sai idan da wani babban dalili.

Na taka cikin faduwar gaba na doshi kofar dakin, na kai hannu zan murda da nufin na bude na shiga sai kuma dauke hannuna na matsa kusa na dora kunne na a kofar dakin. Shiruuuu ban ji wani motsi ba, na sauke ajiyar zuciya ina jin kamar hankali ya kwanta, ashe dan'uwansa ne ke tafe da gumurzunsa irin tafiyar da ban yi tsammani ba.

 Sai yaushe za a zubar to?

Na ji muryarta, hakan ya sakan ni kwantar da kunne a jikin kofar sosai na natsu numfashi ma daker nake fitarwa saboda na ji me take fada.

 Kina da matsala ne ke Wallahi, na fada miki ni ai na san lokacin da ya kamata a zubar ko?

 Tsoro nake kar ya girma, kuma ina tsoron na sha wahala

Ta fada cikin muryar kuka.

 Ai na sani idan ban ja lokaci haka ba, ba zan samu hadin kanki ba, yanzu ana zubarwa kuma ba zaki sake yarda da ni ba

Rarararararsssssssaaaa. Gabana ya bugawar da mai sauraren tsawa dake tafe da ruwa.

 Zan yarda,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login