Showing 141001 words to 144000 words out of 227321 words

Chapter 48 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1541



Na hade takardar da karfi ya yaga ya jefar ya bugu sitiyarin motar da karfi, ya bude motar ya fita ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya dawo ya halbi motar da kafarsa. Ya jingina ya rufe ido ya zai yi? Me yasa ya aikata tun farko? Yaya kenan yanzu? Ya bude motar ya shiga ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ya rufe ido. Be daga ba sai da lokacin sallah magariba yayi, a wani masallaci dake kusa da gurin yayi sallah Magariba ya kasa fitowa masallacin har aka yi sallah Isha'i. Sai kusan Tara da rabi ya doshi gidansa.

Yana driving yana jin kamar kar ya tafi, kunya hada ido da iyalinsa yake duk kuwa da kasancewar ba su san komai akai ba. Harabar gidan ya faka ya kwanta a motar ba bachi yake ba tunanin yadda zai tafi da wasu abubuwa yake. Yana tuna shawarwarin da abokinsa ya ba shi lokacin da yake raye. Da kuma yadda zuciya ta debi shi ta saka idonsa ya rufe a lokacin ya kasa fahimtar illar da Zina zata yi a rayuwarsa.

Ya sani duk wani abu da Allah yace kar a kusance shi, ba abu ne mai kyau ba. Ba ma karku aikata ba kar ma kusanci inda take balle har ku aikata haka Allah ya fada, amman ya take sanin ya murje ido ya aikata, yanzu wa gari ya waya? Kamar zai fadi haka ya bude motar ya fito jikinsa babu kuzari. Sai da ya daga kansa sama ya kalli gidan gabas da yamma sannan ya taka ya isa bakin kofar falon ya shiga.

A hankali yake takawa har ya haura sama, dakin yaransa ya fara turawa sai ya samu suna bachi an kashe wutar dakin an kunna musu ocean, sakin kofar yayi ya shiga cikin dakin dakin ya zauna kusa akan gadon Tine yana kallonta kamin ya juya ya kalli Areef.

 Maybe nan gaba ku ji kun tsane ni, idan ina raye ko a mace, ku yi bakinciki da na kasance ubanku, kuna da yancin yin haka, domin na bar muku abun kunya, bayan ni kuma nawa iyayen ba su bar min abun kunya ba, sun yi kokarin tsare mutuncinsu da na mu

Ya hade yawu.

 Ni dai na san ba zan kashe yaron nan ba, duk wani abun da zan biyo baya dole na karbe shi domin ni na aikata, but no matter what ku sani ina matukar kaunarku kuma ina kokarin na tsare mutuncinku, saboda kar na lalata Future dinku

Ya shafa kan Tine ya sumbance ta, sannan ya tashi ya nufi dayan ma ya shafa kansa ya sumbance shi, ya kallesu cike da bakinciki sannan ya fice daga dakin ya ja musu kofa. Dakinsa ya shiga, yadda ya shigo sanye da talkami da kananan kaya haka ya fada saman gadonsa ya rufe ido, ko agogonsa be iya cirewa ba. Haka ya kwanta har safe ko kadan be yi bachi ba, sai juyi yake idan ya gaji da kwanciyar sai ya sauko kasa ya zauna.

Sai da asuba ya siya motsawa ya cire tufafin jikinsa da talkamin ya shiga bandaki yayi wanka tare da alwala ya shimfida carpet, nafila ya fara yi sannan ya gabatar da farilla. A lokacin da ya daga hannunsa zai roki Allah sai kunya ta kama shi, ba zai iya komai ba sai kuka, to me zai ce Allah yayi masa bayan ya bijirewa umarninsa ya bi son zuciyarsa? Allah ya hana shi kuma ya aikata, yanzu kuma ya roki me? Mafita? Ko yafiya? Shafa hannayensa yayi a fuskarsa ya kwanta a gurin feeling so hopeless.

Kansa har wani nauyi yayi tsabar damuwa da fargaba da suka same shi lokaci daya, ga kuma rashin bachin da be yi ba gaba daya daren jiya. Usually yaransa suna tafiya makaranta ne ba tare da jiran su ganshi ba, wani lokacin ko da za su tafi yana bachi, Yusura kuma ta koya musu idan yana bachi basa tashinsa. But yau sai ya sha banban da sauran ranakun, Areef ya fara shigowa rike da jakar abincinsa Tine na bayansa, Kareem na jin motsinsu sai ya rufe idonsa not like he don't want to see their faces but kunyar kallonsu yake kuma bakinciki zai taso masa ne.

 Bachi yake Areef mu tafi

Areef be ji maganar yayarsa ba sai da ya leka fuskar mahaifinsa ya ga da gaske bachin yake sannan ya juya suka yafi. Suna fita Kareem ya bude idonsa yana kallon ceiling da raunannin idanuwansa. Ya tashi zaune, ya dafe kansa, gaba daya ganin yake kamar ranar jiya ba gaskiya bace mafarki ne. Misalin tara ya shirya cikin kananan kayan babu zancen saka agogo ko shafa mai turare da ya zame masa dole kawai ya tsaya domin baya iya rayuwa babu kamshi.
Gefen gadonsa ya zauna ya bude drawersa ya dauko diary da pen yayi rubutu a kai ya nade ya aje pen din ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya fice daga dakin.

Da dai daya ya rika taka stairs din yana saukowa yana kallon Yusura dake goge dinning kanta babu dankwali. Damuwa ta bayyana karara a fuskarsa kyawawan idanuwansa sun fada sun yi ja sosai irin na wanda be ga bachi ba bachi be ganshi ba. Kusa da ita ya karasa ya aje mata takardar a dinning. For the first time ever ta ji gabanta ya fadi irin faduwar da be taba ba. Ta kalli takardar ta kalleshi.

 Miye a ciki?

Ya kalleta.

 Yancinki ne, yancin da kika dade kina nema

Ta hade abu da karfi.

 Babu amfani Daddy zai sake sakawa ka maida ni

 Wannan yanci ne na har abada, it mean forever...

Ta sake dubansa kamar yadda yake kallonta.

 Ina mai baki hakuri akan duk wani abu da na yi miki, wanda kika sani da wanda baki sani ba Yusura, bankwana ne na har abada

Her heart and body star shaking idanuwanta suka tara hawaye.

 Na gode da kika taya ni aje farinciki mahaifiyata har sai da ta bar duniya. Yanzu kam kina da yancin ki auri wanda kike so ki yi rayuwar da kike so

Ya juya ya fara tafiya, ta juya tana kallonsa? Me yasa yau ta ji dabam? Ta dade tana jiran zuwan ranar amman ta kasa farinciki, wacam karon ta jidadi da ya sake ta amman ta kasa farinciki.

 Yaran fa?

Ya juyo ya kalleta hawaye ya gani suna fitowa daga idonta suna zuba a fuskarta.

 Zan kula da su

 Za su fi jindadin zama a gurina

Ya taka zuwa inda take tsaye.

 Idan haka kike so, zan minta, but only on one condition, no matter how happen a raye ko a mace zaki fadawa yaran nan cewar mahaifinsu yana kaunarsu, duk wani abun bacin rai ko bakinciki da zai biyo baya ko ya biyo i still love them, ki fada musu mahaifinsu yayi kokari ganin ya tsare duka hakkinsu sai abun da ya fi karfinsu

Ya juya ya nufi kofa sai ta risina kasa ta kira sunansa.

 Ka yafe min Kareem, na cutar da kai na sani, kiyayya bata bari na yi biyayya ba

 Komai ya kare yanzu Yusura it over now

Ya amsa mata ba tare fa ya juyo ba ya fice daga falon. Yana shiga motarsa ya murza key mai gadi ya bude masa gate ya dauki hanyar da zata sadashi da gurin aikinsa. Be yi nisa da gida ba hudu ya rufe masa ido kansa ya fara juyawa yana ta kokarin controlling motar amman ya kasa.



NOOR POV.

 Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un

Abun da na fada kenan a lokacin da na farka da karfi, sakamakon mummunan mafarkin da na yi. Wai muna tafiya a jirgi sai ya muka fado kasa ni har da ni ciki, na bugi icce har sai da hankalina ya gushe. Addu'a na yi na neman tsari daga mummunan mafarki. Na yi a'uzubillahi har karshe na tofar dama na sake yi na tofar hagu, sai haki nake kamar wanda ta yi yaki, hannu na kai na lalaba ban ji Abdull ba, sai na sauka daga kan gadon na kunna wuta na nufi bathroom din da nake jin motsin ruwa na tsaya jiran ya fito na shiga.

Da na lura ba shi da niyar fitowa sai na tura kofar na fara lekawa babu kowa a ciki, shiga na yi ciki da mamaki, tab din ne a kunne ruwa na zuba kadan kadan amman babu kowa a ciki. Kashewa na yi na bayan na gama fitsari wata kila ya manta ya bar shi a kunne ne. Sai da na nufo gado na zauna sai kuma wata zuciyar ta tambaye ni ina ya tafi? Bargon na sake yayewa na sauko da kafafuwana ina mikewa tsaye sai gashi ya shigo dakin.

 Ina ka tafi?

 Ruwan na ji na hada tea, ina zaki ke?

 Ai dai ba zan bata ba a gidana ko? Idan bana dakin nan ina falo ko kitchen

Ya hauro saman gadon ya kwanata rai a bace kamar an masa wani abun, har ya manta be kashe wutar ba, wata kila tambaya ta ce ta bata masa rai.
Sauka na yi na kashe wutar na dawo na kwanta.


It's not Free pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.






https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0


PAID PAGE 2?? 0??


??KhadeejaCandy
????Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______" " " _______

Rumgume hannayena na yi ina kallonsa with my innocent face.

 Besty how are you?

Ya tambaya yana daga kai ya kalli harabar unguwar.

 I'm good and you?

Ya daga gira not happy not sad.

 I'm not fine

Na dan matsa kusa da shi.

 Me ya same ka?

Sauke kai yayi kasa sannan ya ce.

 Bestyna kamar kin taba fada min sunan wanda zaki aura ko?

 Eh Abdull

Ya dago ya kalleni.

 Yana da mata kika ce idan ban mata ba

 Eh da yara uku matarsa ya haihu na hudu

Ina jin sautin hade yawunsa.

 Amman kin taba ganin matarsa?

Na dan kawar da ido daga kallonsa sannan na amsa.

 Eh na taba ganinta ya nuna min hotonta

Ya langwashe halshensa.

 Kin san sunanta?

 Safeena your ex-

Murmushi yayi ya jinjina kai yana juya idanuwansa like na bashi mamaki sosai, kamin ya kalleni.

 Kin san duk wannan kuma kika yarda zaki auri Abdull?

 Ba mutumen kirki ba ne?

 Ban san komai a kansa ba, amman na san komai akan Safeena, ba zaki iya kishi da yarinyar nan ba, she's criminal

Na dan tabe baki.

 Bana jin zata yi kishina, ai kai take so kuma kai take kishi, me zai saka ta yi kishin mutumen da bata so indai har da gaske bata son shi

 Mijinta ne uban yayanta taya ba zata ji kishi ba, kuma ni ban taba fada miki cewar bata son shi ba, taya zata ki mutumen da shi ya tsamota daga ruwa a lokacin da na jefata?

Na daga kafaduna not knowing what to say yanzu kuma. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da murya ya ce.

 Noor me kika fadawa Safeena?

Na kalleshi da sauri daman na san za a zo gurin.

 Me tace na fada mata?

 Sirrin da na yi dake ta zo ta fada min duk abun da kuka yi, saboda me zaki nuna mata cewar kin san abun da yake tsakaninmu

Na ciro wayata daga aljihun rigata na nuna masa sakon da ta turo min, kamin wani abu ya tsikare ni kamar zan yi fada na fara magana.

 Ganin na yi tana neman daga min hankali tun kamin na shiga, ni kuma ba na yi aure ne saboda na je na fito ba, bana son aurena ya sake rabuwa sai idan mutuwa ta raba

 Amman sai ki yi amfani da wata hanyar ba wannan ba, ke yarinya ce, baki gama fahimtar duniya ta mutanen cikinta ba, ba ki san illar abun da kika ba sai bayan ki aikata

 Ba ni da wani weapon na yakarta sai wannan

 Amman wannan sirrina ne, na fada miki ne saboda na yarda dake and i need someone to talk to, taya zaki aikata abun da zai iya janyo matsala ya janyo miki?

Zan yi magana ya daga min hannu ya nuna min yatsa.

 Look Noor ina da yara, mahaifina yana raye ina da yan'uwa da abokaina, ko kadan bana son abun da zai zubar min da mutunci, na fada miki damuwata ne saboda na yarda dake, kuma ina jin kusanci da zuciyata, ba dan ki bayyana ma duniya ba, na san na aikata abun a lokacin da idanuwa suka rufe shekaru suka tsirewa tunani, and now i realize na yi wa kaina babbar barna and i regret it, you shouldn't discuss this with anyone!!

Ya bude motarsa ya shiga ya bar ni a tsaye ina kallonsa hawaye na sauko min, domin be taba rufe da fada irin na yau ba. Har yayi baya sai kuma yayi gaba ya faka a inda ya faka dazun ya sake bude motar ya fito ya tsaya kusa da ni.

 I'm sorry, Na san na kaurara amman Noor ban ji dadin abun da kika yi ba, wannan sirrina ne, be kamata kowa ya ji ba 

 Bana hira da kowa, ban taba fadawa kowa ba, kuma ita wanda ta ji daman ai ita abun ya shafa

Na bashi amsa cikin sautin kuka. Idonsa ya sauke kasa yana sake fuskarsa.

 Bana nufin sakaki kuka ko kara miki damuwa akan wanda kike ciki, amman ni abun da kika aikata yanzu zai daga min hankali ya saka ni a damuwa, waya sani ko zaki sake fadawa wani? Kuma Safeena ba zata zura miki ido hakan nan kawai ki cigaba da rayuwa a free ba, bayan kin san sirrinta, ni da ita duk muna da iyali, ki rika duba wannan kamin ki aikatawa wani abun Noor

Na share hawayena.

 Ta je ta bata ni gurinka ko?

Ya rufe ido yana murmushi sai dai hakan be hana ni fahimtar damuwar dake shimfide a fuskarsa ba. Bude ido yayi yana min magana a hankali.

 Bata iya wannan, babu wanda zai iya wannan ma, just be careful yanzu Safaeena tana kiyayya dake ta kofa uku ne, Allah ya tsareki kuma ya baki zaman lafiya, amman Bestyna Noor ina son ki sani ko mutuwa na yi bana son na tafi na barwa ?a?ana abun kunya

 Ni ma ba zan so haka ba, kuma na maka alkawari daga wannan ba zan kara ba, kuma babu wanda zai ji

Yayi tattausan murmushi da ya kara masa kyau.

 Thank You, Allah ya tabbatar miki da alheri

 Ameen

Ya sake Bude motarsa zai shiga.

 Shikenan tafiya zaka yi?

Ya juyo

 Ko kina da bukatar wani abun ne?

Na girgiza kai.

 I will miss you alot

Yayi murmushi ya sauka kansa.

 Akwai abun da kike bukata na auren Noor? Akwai abun da Baba be miki ba?

Na girgiza masa kai alamar aa. A ganina kamar be kamata na dora masa nauyin komai ba, kuma ai da kunya na bukaci kayan daki a gurinsa, domin su ne kawai nake saka ran Baba ba zai yi min ba, shi ma kuma ba ni da tabbaci.

 An yi komai

Yayi murmushin dake nuna kamar be aminta da ni ba.

 Sai wata rana

Wannan karon be sake kallona ba ya shiga motarsa yayi mata key ina tsaye ina kallonsa har na daina hango shi. Wata kila shi kam ba zai yi marmarina ba kamar yadda anke jin kewarsa tun a yanzu, ba mu wani dade a tare ba amman shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da shi.
Bayan tafiyarsa ne fahimci na yi katobara na bayyana ma Safeena na san komai a tsakaninsu ba dan ita ba, sai dan shi wata kila hakan zai iya haifar masa da matsala, sai dai iya abun da na sani shi ne, Safeena ba zata yarda asirinta ya tonu ba, domin tana da aure da yara kamar yadda ya fada, ni kuma ba zan sake tattaunawa da kowa akan matsalar ba.

Hakan da na yi ya saka na samu yanci gurin Safeena, mijinta ma ya samu kwanciyar hankali domin ana sauran kwana biyu a daura aure nake tambayarsa ya Safeena sai yake cin yanzu ai ta fahimci, tashin hankalinta ba zai hana aurenmu ba ta shafa masa lafiya. A raina na ce ko dai ta fahimci Ni din ba kanwar lasa ba ce ta bawa kanta lafiya da ni.

A daren ne yayi ta damuna da maganganu da be sana yi min ba, hakan kuma ya raunata yarda ta ya haifar min da tsoro akansa, sai dai na lura shi kam sam baya kunyar fadar haka, wata kila saboda ya taba auren ne, ko kuma yayi zaton a aurena na farko na san komai kamar shi. A yadda na lura Abdull irin mutanen nan masu masara kunyar ido da furta komai a take. Ni dai bana iya cewa komai idan ya jefeni da wani kalamin, na kan ji kaina yayi girma kunya ta rufe ni.

Washe gari gidanmu ya cika da yan'uwa mahaifina wadanda suka zo shirye shiryen abubuwan da za'ayi, ta hirar da Baba yake da su ne na ji yana fadar mai gidan Nabil wato Kareem yana da kirki da mutumci sosai.

 Yanzu bayan daukar nauyin karatun yaron nan da yayi, auren nan da za'ayi sai da ya same ni a majalisa ya damka min kudi mai yawa wai na kara na yi hidima, Allah dai yayi masa albarka ya yara masa yaransa, wutar nan ma da ta taso tsakanina da yan'uwan Hafizu shi ya kashe ta

 Ai wasu masu gida haka suke da taimako da kirki, musamman idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login