Showing 63001 words to 66000 words out of 227321 words

Chapter 22 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1516

shigo rayuwata

Na amsa masa ba tare da na kalleshi ba. Wayar na ga ya kashe ya saka aljihunsa.

 Daman na zo ne na tambaya me zaki yi a cikin shirye shiryen da yan mata suke yi?

 Ba zan yi komai ba

Na amsa a takaice.

 Okay, daman dai na zo na ji saboda na bada kudin shirye shirye idan har zaki yi, kuma Balkisu wato uwargidana kenan ta shirya Walima da Kamu, saboda na fada mata daman abu ne mai wahala ki iya shirya wani event, wannan ina fatan zaki je?

 Ba zan je ba

Ya tsaya kallona kamin na ji saukar ajiyar zuciyarsa. Ya gyara tsayuwarsa ya fuskance ni da kyau sannan ya kira sunana kai tsaye da siffar da be taba yi ba.

 Khadija...

Na daga kai na kalleshi duk da kasancewar bana ganin fuskarsa da kyau saboda duhun dare.

 Ina son na yi wata magana dake, na san kina da kiriniya kina da kurciya amman duk da haka kina da hankali kuma kina da tunani irin na mutane domin ke mutum ce. Kin ga tun farko ni da ke ba mu san juna ba, ban san ki ba baki san ni ba, amman da Allah yayi nufin hada wani abu a tsakaninmu sai ya kawo dan'uwanki a gurin kasuwancin abokina, duk da haka kuma be hada ni da ke kai tsaye ba sai ya hada ki da abokina wanda shi ne silar faruwar komai a yanzu

Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya shiga.

 Wallahi Noor ban saka ran aure nan kusa ba, kuma ban yi tsammanin zan aureki ba, ina wani tunani da tsari ne na dabam a rayuwata game da ke ashe abun da Allah yake tsara mana dabam, kuma dai kamar wasa na amsa abun nan gashi ya zame min gaske, ban san zafin rabuwa da masoyi ba, amman na san dadin auren wanda kake so domin matata ta farko auren soyayya muka yi, sai dai ke ina hango miki wani abu a yanzu wadda na kasa gani a baya, kuma ina hangen wani rame da yake shirin fadawa da ni

Ya gyara tsayuwarsa.

 Shiyasa yau nake son mu kai karshe da ke, Noor ko dai mu karbi kaddarar nan ko kuma mu hakura da juna, saboda ina jin tsoron abun da zai je ya dawo, ance idan gemun dan'uwanka ya kama da wuta to ka shafawa naka ruwa, Zan iya samun Mahaifinki na fada masa cewar na sanyi zancen auren nan, domin na lura san baki ra'ayi na, yadda nake tunanin zan iya juya ki kamar hakan sai gagara a gareni

Na kalleshi da sauri ina girgiza kai hawaye na sauko min.

 Fasa aurena ba zai saka Baba ya amince na auri Zafeer ba a yanzu, kawai zai janyo min matsala ne tsakanina da shi, zai tsine zai yi fushi da ni, Kareem ya riga ya kawo ka a rayuwata kun ruguza min komai

 Babu ruwan Kareem a cikin matsalar nan, da kin san yadda yake son farincikinki da baki furta haka ba, abu ne da aka riga da aka tsara tun farko, shiyasa nake son ni da ke mu karbi wannan kaddarar...

Ya jinjina kai alamar gamsuwa ina share hawayen da suke sauka a lebena.

 Na karba Hafiz, na karba...

Na amsa masa sannan na juya ina kuka na shige cikin gidan. Rasa na yi gurin da zan raba na yi kuka dan haka na dauki buta na shige bandaki na rufe baki na dinga kuka kamar raina zai fita. Daga ranar sai kukan ya rubbanya, domin ina jin a zuciyata na rabu da mutumen da shi ne farincikina. Hankali be kara tashi ba har sai da yan'uwan Baba suka fara sauka gidan wasu daga dangin mahaifiyata dake zuwa kullum suna kawo min maganin mata da ya zame min cilas Ina sha ba dan zuciya na so ba.
Ranar Alhamis aka yi kamu a gurin da uwargidan Hafiz din ta kama, sai dai ban samu zuwa ba saboda zazzabin da ya rufe ni ya hana ni ko da bude ido. Mafi akasarin dangin mahaifina suna dorawa Mama laifin damuwa na ne, sai na kasa sakewa ne saboda bata kusa da ni, ta ki ta leko bikin aure, wata kanwar Baba ma cewa take Baba ya fada mata ita ta hure min kunne nake son bijire masa a auren mutumen da ya saya masa gida kuma ya dauke masa komai na aure.

 Ke ni fa ba dan Hajara ita ta haifi yarinyar nan ba, Wallahi sai na ce bakinciki, domin yau mijin da Noor zata aura Miji ne da ko wace uwa take son a aurawa yarta, mutum mai alheri mai son yarka

Cewar Gwaggo Saude, Gwaggo Hasana ta amsa mata da cewar.

 Tohm ke ma dai kya fada, tun ba yau ba fa Yaya yana kuka da Hajara, wasu abubuwan da Noor take ma ni sai nake ganin kamar har da goyon bayanta, domin dai Yaya yana tsaye akan yaransa suna tsoronsa amman ita kam aa sam so take ma su raina shi, yanzu ba gashi ta yi ma kanta ba ina dadi ayi auren yarka kai kuma naka auren ya mutu? Ka koma gida da tsufanka da komai kana zawarci, yaran matasa ma yanzu ya suka kare balle kai da ke da manyan yaya

Gwaggo Saude ta yi kwafa.

 Ai muje dai zuwa nan gaba kadan sai ta yi nadama, gashi babu gyara balle ace za a gyara, kuma Yaya dai aurensa zai yi domin yace ana yin auren Noor shi ma zai yi nasa

 Ai ni Wallahi ban dauka zai kai yanzu ma be yi auren ba

Anty Larai ce ta katse hirarsu tana kanrar da su abun da suka manta.

 Yaran nan fa suna jinku kuna zagin uwarsu babu dadi

 Gaskiya muke fada Anty Larai, da a fada bayan idonsu ai kara a fada gaban idonsu, su ji komai saboda tuwon gobe ake wanke tukunya, ai da gulmarta zamu yi ba zamu yi a inda zasu ji ba

 Toh ban da abinki Saude su kansu yaran ai ba tsoronsu muke ba balle mu kasa fadar abun da yake ranmu, ita gaskiya ai dole a fade ta

Anty Larai ta ce

 Hassana dan Allah a bar zancen nan ai ana barin halak dan kunya, kuma babu kyau cin gira kusa da ido, yara kuma duk da wayonsu kawai suna son dasa ma kanku kiyayyar ku a zuciyar yaran ne idan kuna cin fuskar uwarsu suna saurare, dan Allah kar wanda ya sake tada zancen nan

Daga haka ban sake jin wata maganar nan. Daga ni har kanwata Hana ba mu motsa ba, ba wannan ne karon farko da suke yawan bawa Mama laifi idan wani abun ya faru ba, domin Baba yana zaunawa da yan'uwansa ya zageta ya nuna bata da gaskiya ko da kuwa ita ce mai gaskiya.
A duk lokacin da suka zo ko ta hadu da su suna yawan fada mata maganar da duk ta so bakinsu marar dadi kamar da gatse, ma'ana dai Mama da yan'uwan Baba suna irin zaman nan ne na doya da manya, sai dai ba duka ba.
A yanzu na kara tabbatar da hakan domin daga Baban da ya kasance Miji a gareta da yan'uwansa babu wanda yayi marmarin dawowa ta a gidan ko da a munafurce ne.

Ina cikin dakin kwance Baba ya shigo gidan da dan saurinsa. Yan'uwansa suka amsa sallamar sai ya tambaya ina nake, tun kamin na ji dalilin neman gabana ya fadi.

 Ina tunanin tana daki kasan ba fitowa take son yi ba kamar mai tsoron mutane

Gwaggo Saude ta fada.

 Wai yaron nan ne ya matsa yana son magana da ita, yaje ya same ni cikin mutane sai rokona yake jama'a duk sun saka baki mi Wallahi har kunyata ni yayi a cikin mutane

 Wane yaro kuma Yaya?

 Zafeer mana

Na tashi zaune da sauri kirjina na bugawa da karfi jin Baba ya amsawa Gwaggo Hassana da sunan masoyina.

 Toh Lafiya? Me yake nema

Natsuwa na yi sosai ina saurarem irin amsar da zata fito daga bakin Baba tare da fatan zai amsa mata da cewar ya fasa aurar da ni g Hafix zai aura min Zafeer din da nake so.

 Wallahi gaba ya saka ni da roko da komai yana son zai yi bankwana da Noor

Na tashi da sauri na isa bakin kofar dakin na tsaya ina kallon Anty Larai dake fadin.

 Bankwana kuma? Ikon Allah ban taba ji haka ba...

Gwaggo Saude ta tabe baki.

 Waya sani ko wani sherin ya dauko yake son ya shafa mata? Albashi idan taje ta kasa zaman aure ko kuma ta miJin ya juya mata baya, kai wannan yaro da naci yake

 Gaskiya Yaya karka barshi, tana ina zaka yarda taje su yi bankwana waya sani ma ko sace ta zai yi su gudu

Na kalli Gwaggo Hassana kamar na yi magana amman na kasa domin ban isa ba na yi wata maganar ace wani abun muke shiryawa.

Anty Larai ta juyo ta kalleni sannan ta juya ta kalli Baba.

 Me yasa yake son magana da ita?

 Wai bankwana zai mata

 Bankwana ma auren da zata yi ko kuma na me? Bankwana kamar ya?

Gwaggo Hassana tace.

 Waya sani Anty Larai ko wani abun ya dauko ace da sun hada ido zata ce bata son wacan shi take so, kuma yarinyar da ya rage kwana biyu a daura mata aure ai matar wani ce ta ina za a bar wani da ba mijinta ba ba muharraminta ba ya ganta... Ni dai zuciyata ba ta natsu da wannan ba

Ajiyar zuciya Anty Larai ta sauke sannan ta ce.

 In har ya zama dole to ya shigo nan a gabanmu idan wata maganar ce ya fada mata, amman ba za a fitar da ita waje ba, kuma ba zai kebe da ita ba

 Ni dai kam da za a dauki shawarata ba zai ga ganta ba, ba mu san sherin da ya dauko ba, duk abun da yake son fada mata ya rubuto mata a takardar a kawo mata

 Eh to kuma kin kawo shawara Saude bari ayi haka din a huta kawai zai fi

Baba ya amsa sannan ya juya ya fita, kusan ni da hoto banbancinmu kadan ne a lokacin domin bana iya motsi kuma na kasa cewa komai hawaye ne kawai abun da ke fitowa a idanuwana. Anty Larai ta taso ta dafata ta shigar da ni daki sannan ta fito tana fadin.

 Ni dai kam da dai Yaya be yi wannan abu ba, ina ganin kamar Hajara ta fishi gaskiya a nan domin yaran nan suna son junansu

 Haba Yaya Larai yaron nan fa be tashi aure ba irin masu batawa yan mata lokaci ne kawai ga wanda ya shirya sai kuma ace ba za'ayi da shi ba, kuma kowa yana son ya kai yarsa inda zata huta Yaya yana da gaskiya Wallahi

Haka suka yi ta juya maganar tsakaninsu, ni kuwa na kashe kunne ina ta sauraren dawowar Baba, amman be dawo ba har dare ya fara yi sosai, wasu ma tuni sun fara bachi.

 Yaya sannu da zuwa

 Yauwa Larai baki kwanta ba

Na ji Baba ya amsa yana sauke gajiya.

 Shiru kuma dazun baka dawo ba ka bar mu da tsammani da jira

 Ai ina fada masa cewar ya hakura ba zai samu ganinta ba Gwaggwaninta sun hana sai ya fara gajiya, ni kuma bukaci ya rubuto ko ma minene, da na fada mata sai na wuce tare da Malam Usman daman tare muke, to bayan na koma can majalisa bayan sallah Isha'i ya same ni ya ba ni takardar

A zatona Gwaggo Saude ta yi bacci domin ban ji motsinta ba tun bayan da suka gama tsinewa Zafeer a dazun, ashe ban canka daidai ba sai jin muryarta na yi tana fadin.

 A bude A duba idan ba wani maganin ya saka a ciki ba

 Ni zan karbe ta ma sai da na yi addu'a na yi bismillah sannan na karba kuma na bude tun a can na duba ban ga komai ba, ban san dai abin da ya rubuta ba saboda ba gane karatun zamani nake ba da ma ace ajami ne zan gane

 To a karanta gaban kowa kowa kuma ya ji

Gwaggo Saude ta fada sai Anty Larai ta tari numfashinta.

 Aa wannan kuma be dace ba, sirrinsu ne a bata ita ta duba abunta.. Noor

Ta karasa da kiran sunana sai na tashi jiki na rawa na fita daga dakin na isa inda take na duka, sai ta karbi takardar daga hannun Baba ta mika min.

 Ga sako inji Zafeer yace a baki

Hannu biyu na saka na karba sannan na mike tsaye na koma cikin dakinmu, babu wutar nepa da hasken fitilar da aka kunna mana na yi amfani na bude takardar ina hade yawu zuciya cike da fargaba.

 Wannan kam ta karshe ce, bankwana ne da ban yi tsammanin zuwansa ba, ban taba mafarkin ko tunanin zan rayuwa da wata macen da ba ke ba Noor i love and i will love you unconditionally, wannan wani abu ne da yake tabbatacce a rayuwata. Sai dai kuma ba zai hana na manta da wannan cin amanar ba, ba kuma zai saka na fasa fada miki hakkina zai bibiye ki ba. Noor ana halittar ko wace mace da rib din mijinta ne, kuma ke ce rib dina and I'm yours, zaki gane hakan nan gaba, zaki neme ni a lokacin da nema ba shi da amfani a gareki, zaki yi nadama bayan kurewar lokaci, Noor ba zaki sake ji daga gareni ba, It time to say good bye Ba zan iya zama na ji ko na ga daurin aurenki da wani da ba ni ba, Noor idan kika ce na fasa tafiya zan tsaya, idan kika amsa cewar zaki aureni kin wanke ni daga damuwa, ina kaunarki Noor ba zan daina kaunarki ba har abada... Tafiya ce da ba ta waiwaye ba... but this is not the end...! Wannan be kare ba, Zan jiraki Noor zan jira...

Na karanta na sake karantawa hawaye na sauko. Na rumgume takardar a kirjina ina kuka marar sauti.
Da wane zan ji? Bakincikin auren wanda bana so ko kuma na rabuwa da wanda shi ne sadaukin rayuwata? Ko kuma na dora min laifi da Zafeer yake? Me yasa ya kasa bude ido ya kalli irin kunnar da nake ciki? Shin labari be je masa cewar dole aka min ba? Ko kuma zuciyarsa tana da nauyin karbar gaskiya ne? Yadda na ga rana haka na ga daren babu wani banbanci, saboda kuka da bakinciki mai hana bachi kusantar idanuwa.
Washe garin ranar, rana ce mai tsananin daraja da martaba ga duk musulmi, sai dai ni na ji ta a dabam, saboda???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kusancewar abun da nake aunawa da mutuwa. Bana iya komai sai ance tashi ki yi duk wadda ya kalleni ya san bana farincikin da auren da zan iya cewa Baba siyar da ni yayi aka ba shi kudi. Ko kuma na ce rawar kai ya janyo min na dauko ajalina har gida na kawo. Misalin karfe uku aka zo da motA daga gidan ango aka dauke ni tare da kawata Zainab, zuwa wani shagon kwalliya, ana fente fuskar ina hawaye hakan ya hana kwalliyar. Daya daga cikin matan da aka je dauko ni tare da ita ce ta kama hannuna ta jani zuwa wani guri na dabam da muka kebe daga ni sai ita.
Ta zauna kusa da ni sosai ta kai hannunta ta dago kaina muka fuskanci juna.

 yarinya aure sirri ne, kukan ba shi da amfani a gareki mijina mutum ne mai tsananin tsoron Allah mai kawaici mai adalci, miji ne da ko wace mace mai hankali zata so kasancewa d shi, da ace kin san halinsa na gari da kuma yadda yake taka tsantsan da duniya da baki zubar da wannan hawayen ba, tun da muka yi aure da miji be taba wulakanta ni ba, haihuwata uku da shi ga ciki na hudu, ba zan miki karya ba mu kan samu tsabanin amman babu wanda yake sani, saboda baya bari a san sirrin gidansa

Kallonta nake irin kallon da na gagara yarda da gaske Matarsa ce.

 Wacece ke?

Ta lumshe ido ta bude

 Abokiyar Zamaninki yar'uwarki kuma yayarki...matar mijinki

Na hade yawu mamaki ya saka hawaye yanke min a take, a wacan karon da ya fada min ta shirya Kamu da Walima ban dauka da gaske ba, domin ban yi tunanin akwai wata mace da zata yarda ta shirya wannan wa kishiyarta ba, a yanzu kuma taje ta mota suka dauko ni zuwa gurin kwalliya, hakan duk be wadatar ba har sai ta fada min kyawawan halayyar mijinta anya Hafix mutumen kwarai ne kuwa. Ta dafa hannuna tana murmushi.

 Na san zaki yi mamaki jin furucina, zuciyarki zata raya miki cewar ko dai mutumen da za a daura min aure da shi ba mutumin kirki ba ne? Ko?

Na daga mata kai domin abun da yake shimfide a zuciyata kenan.

 Ko kadan, Wallahi Barrister mutumen kirki ne, kawai ina fada miki gaskiya ne saboda hankalinki ya kwanta, karki ce bana kishi ina yi, amman na yi Kokarin fin karfin zuciyata ne, saboda ina son farinciki Mijina, kuma idan har yana neman goyon baya akan wani abu ina tunanin ni ce ta farko da zan fara bashi wannan goyon bayan, Barrister ya so ni, ya kaunace ni ya nuna min gata, ya sauya lissafina ya banbanta ni a cikin dangina, kuma ya tsaya tsayin daka ganin yan'uwansa sun nuna min girmamawa da kauna, ni kuma ba zan yarda na bata wannan alakar ba, ba zan saka masa da mummunan sakamako ba

Na sake dubanta irin duba na kokarin tantance gaskiyar mutum da akasinta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login