Showing 57001 words to 60000 words out of 227321 words

Chapter 20 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1567

ba

Ya wuce zai haura stairs sai ta bishi da kallo.

 Na saba idan zan fita rubutu nake na aje maka, idan zaka fita kai ma haka kake min? Me yasa aka samu canji yau? Zargina kake yi?

Ya tsaya cak sai dai be juyo ba.

 Wani abun kake aikatawa da kake ganin kai ma za'a iya aikatawa matarka? Duk yadda duniya ta lalace har gobe akwai na kwarai Wallahi, ni ba zan iya zina ba ko babu aure balle da aure da Yaya, idan ma kana tarayya da matar aure, budurwa ko bazawara wannan kai ya shafa, ni dai ba za'ayi da ni ba, ubana be yi da yar wani ba ba zan aikata ba Wallahi, amman kai ka kuka da yarka kuma Allah ya isa zargin da kake min...


Ta wuce shi ta haura stairs din ta shige dakinta ta rufe kofar da karfi. Shi kuma ya juyo ya sauko yana jin babu dadi wani abu ne ya same shi a yau da be saba samunsa ba, be taba zargin matarsa ba ko sau daya amman yau ya ji rashin natsuwar a fitarta gashi har ta ja masa Allah ya isa. Falon ya koma ya zauna ya rufe ido, yana tunanin wata kila da ba baya aikatawa da duk hakan be faru ba. Wayarsa ya ciro ya kama number Safeena ya saka a blacklist sannan ya goge number yana kallon hoton yarsa dake lake a falon.





NOOR POV.

A zauren da suka tafi suka bar ni a nan Yaya ya shigo ya same ni, ina kuka sai ya rika ni ya shiga da ni cikin gidan ya tambaye ni lafiya.

 Ba komai

 Ko dan an barki ke kadai?

Na daga mishi kai, sai ya tashi ya fita be dade ba ya dawo da fura irin wadda ake siyarwa a titi damammiya ya zuba min a kofi na sha ya debo min ruwa na sha.

 Ina Hannatu?

 Bata dawo ba

Na amsa da muryar kuka.

 Kila ta wuce gurin Mama, Baba kuma be dawo ba?

 Eh ni kadai aka bari

 Shi ne kika yi ta kuka ko? Ni ma oga ne ya kira ni yace na zo aiki kuma na dubaki

 Ina ka ganshi?

Na yi shiru bance komai ba, mintuna da ya kara be wuce talatin ba ya ce min zai tafi aiki ya fita ya bar ni.
Ama daf da kiran Sallah magariba Zainab ta shigo gidanmu sanye da uniform dinta na islamiya, kamar da tsoro ta shigo dakinmu tana tambayar ina mama.

 Bata nan

Ta saka Hannu a jakarta ta dauko takardar da miko min sannan ta tashi da sauri.

 Bari na tafi kamin ta dawo kar tace ni nake kawo miki sako

Ni dai binta kawai na yi da ido har ta fice sannan na maida dubana gurin takardar gabana yana faduwa, na san mai aiken sakon ciki ne dai ban san me ya kunsa ba. Na dade ina kallon takardar cike da fargaba sannan na bude.

 Abu dai kamar wasa Noor ina shirin rasa ki, Wallahi ina sonki Allah ya sani, duk wadda yake son ki be kai ni ba, kuma zasu bata miki lokaci ne kawai su ci amanarki su gudu su barki, za su lalata rayuwarki ne kawai Noor karki aminta da su, babu wadda zan iya dake ya jure sai ni, ni kadai ne mutumen da zai iya zama da ke a kowane hali na rayuwa, amman duk wadda zaki aura Noor sai dai ki je ki yi ki dawo ba zaki taba zaman aure ba matukar ba ni kika aura ba, babu wadda zai iya zama da ke sai ni, kuma ke din tawa ce har abada ba zan daina kaunarki ba Noor har abada, kin manta yadda muka tsara rayuwa? Zaman tare duk kin manta Noor, Amana ta ba zata barki ba, ba zaki taba zaman aure ba, ke je ki yi auren zan jira ki saki dawo, zaki gane kuskurenki Noor a lokacin da zaman auren zai gagareki, ba fata nake miki ba amman ni na san ba zaki taba iya zaman aure ba har abada...! Saboda na san wacece ke Noor, ba zan daina sonki ba, zan mutu da kaunarki Noor Ba zan taba son wata mace kamar ke ba, talauci yayi min illa, ke kuma zaman aure zai zame miki kaya kun ci amanata kuma amana ba zata barku ba, ban yi tunani zan baki umarni ki kauce ba, ban yi zaton zan miki magana ki juya min baya ba... Kin ba ni mamaki Noor... 

Na dunkule takardar a hannuna ina jin tausayin kaina da, gashi ba ni da wata hanya ta wanke kaina daga zargin da Zafeer yake min. Na kwanta a gurin ina kuka. Ban sake ganin kowa ba sai bayan sallah Isha'i da Baba ya dawo da ledar nama. Duk yadda bakina ya saba da kwadayi sai na kasa cin wani abun kirki sai kadan ka ci na bar sauran na shige dakinmu cikin hudu na kwanta har lokacin Yaya da Hana ba su dawo ba, daman Yaya ya saba yin dare a waje shi da Baba Hana ce dai rashin dawowarta ya dame ni domin na koma ni kadai a gidan.

 Wato Hannatu ta zabi uwarta ko? Shi ne daga makarantar ta wuce gurin Hajara ko? To sai ta yi ta zama a can kar ma ta dawo gidan nan

Fada Baba yake sosai inda yake shiga ba nan yake fita ba, tafiyar Hana gurin Mama ta yi masa ciwo sosai. Ni dai ban ce uffan ba sai da yaro ya shigo yace wai ana sallama da Noor inji Hafiz. Sanin Hafiz din yana tare da Kareem ne ya saka na ji bana bukatar zuwa amman ban isa na yi hakan ba saboda Baba yana cikin gidan.

 Je kace tana zuwa

Baba ya amsa masa ni kuma na tashi na dauki hijabina na saka na fito daga dakin Baba na haska min talkamina na saka na fita waje. Nesa kadan da kofar gidan na hango shi ganina ya saka shi fitowa daga motar da already tana bude ya rufe yana kallona. Ni kuma na karasa ina jiran na ga fitowar Kareem.

 Sannu Noor

Ya fada sai na daga mishi kai ina kallon kasa cike da natsuwa.

 Ba tare da Kareem na zo ba, kuma ba matsalar Kareem ce ta kawo ni ba, na zo ne mu yi wata maganar dake mai muhimmanci

 Ina jinka

Na fada a sanyaye. Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce.

 Dazun na so mu yi magana amman na lura kamar baki cikin yanayin da ya kamata na yi maganar

Sai kuma na ji shiru jikina ya bani kallona yake, ina daga kai sai na yi arba da idonsa a kaina.

 Noor Baba ya fada min wata magana a dazun, ba zan ce ba haka ba ne amman abun ya ba ni mamaki

Gabana ya fadi.

 Me ya ce maka?

Ya matsa kusa da ni kadan ya rage muryarsa.

 Ya fada min wai ya tambaye ki fitar da miji sai kika ce ni kike so haka ne? Ko kuma dai Baba be fahimce ki ba ne? Ko kuma dai Kareem kike nufi Baba be fahimta ba yace ni

Kallonsa nake ina ta kokarin hada kalmonin da ban fahimci manufarsu ba, ta dayan bangaren kuma gargadin da Baba yayi min dazun da safe yana dawo min.

 Noor ko ba haka ba ne?

Kiran sunana yake tare da tambayar da bam san taya zan amsa masa ita ba. Ba zan iya karyata Babana ba, bayan duk gargadin da yayi min, idan har na yi haka ban zan me zai biyo baya ni ma zai koreni kamar Mama ne ko kuma zai yi ta dukane ne yace babu ruwansa da ni.

 Ban sani ba tukuna

Na fada da muryar kuka ina kai hannu na na taba zuciyata.

 Hakan yana nufin ba gaskiya ba ne kenan?

Ya sake tambaya ta sai na amsa masa ina fashewa da kuka.

 Gaskiya ne....

Na juyo na shigo cikin gidan da wani irin kuka mai karfi, a tsakar gidan na zube na rushe da kuka ina jin tsanar mahaifina fiye da kowa a duniyar nan. Taya zai yi min haka ta ina zan iya Zaman Aure da Hafiz wane irin abun kunya ne wannan? Baba babu ruwansa da damuwata babu ruwansa da wadda nake so, daman can Hafiz ne yake so na ba Kareem ba ko kuma dai dukansu wasa suke da hankalina ne? Ni kadai ce mai uba irin Baba ko ina da ta biyu..!

 Lafiya wani abu ya faru?

Na daga kai na kalli Baba ina kuka.

 Baba bana son Hafiz kai kace masa ina son shi? Ni Zafeer kawai nake so, ni idan ba Zafeer ba ko an min auren ba zan zauna ba, Baba bana son kowa sai Zafeer

Tsawa ya daka min sai da na zabura.

 Rufe min baki, Wallahi sai kin auri wadda na zaba miki sai idan shi yace ya fasa, kuma idan kika yi sanadin da ya fasa aurenki sai na lahira ya fi jindadi

Yana rufe baki ya hau dukana.

 Karki yi zaman auren idan an kaiki ki fito ki dawo gida ki zauna, daman ai haka uwarki take so haka kike so, ke kin fi son ki yi ta gantali a gari kin zama wawuya to mu zuba ni da ke, Wallahi ko zaki mutu sai kin auri Mutumen nan idan ba ki aure shi sai na tsine miki Noor, ki bi duniya ki lalace daman kin fi son lalatar kin sha'awar ki zama watsatsiya kowa yana miki kallon mahaukaci, ko da yake ba laifinki ba ne, laifin ne da ban zabo uwar da zata koyawa Yayana tarbiya ba, gashi ita Hannatu ta bar gidan ke kuma kina son saka min hawan jini ko? To ba ku isa ba, ai yara da dawo ana musu aure ko basa so amman basa musawa sai ke da babu albarka a tare ke...

Azabar dukan da yake min da hannu bata saka na gane kuskuren yi masa musu ba har sai da ua dauko maburkin Mama na ice yana duka na da shi, a take fara rokon gafararsa ina sosa jikina ta ko'ina ina jin kamar wuta yake watsa min a jiki.

 Na bari Baba na bari, zan aure shi Wallahi zan aure shi Ina son shi ina kaunarsa Baba zan zauna dan Allah ka yi hakuri Baba na bari ba zan sake ba

Rawa jikina yake kamar mazari majina da hawaye sun hade min guri daya, numfashina na fita da karfi...





__________________



A nan muka kawo karshen Book One na litfafin TA KI ZAMAN AURE, sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana zamu dora a book two... A inda littafin zai amsa cikaken sunansa.

Akwai tambayoyi da yawa da kuke bukatar amsoshinsun a tare da Noor da kuma Zafeer da Kareem da ma wasu a gaba.

Anya fitar Mama a gidan Baba zai haifa da da mai ido kuwa?

Wai ina labarin Safeena ne? Ta hakura ko tana kan bakarta?

Kuna Ganin Yusura zata iya juyowa ta kalli Kareem da idon rahama?

Shin Kareem zai iya jurewa Abokinsa ya auri Noor kuwa?

Me. Zafeer yake nufi da cewar ba zata ta Zaman aure ba?

Me yake Hana Noor zaman auren ne? Rashin dace da miji ne ko bakin iyeye ko kuma rashin Hali na gari? Ko kuma daga mahaifin ne?

Akwai wani dunkullen sako a cikin Littafin da nake son isarwa idan Allah ya ara min lokaci kuma ya amince min. Allah yasa mu amfana.



#KhadeejaCandy
+2348036126660
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


WELCOME BACK...
Fatan mun yi Sallah lafiya, Allah ya karbi ibadunmu. AMEEN.


*Book 2 - Chapter 1*


6 -Month Later...
@8:11am

Yana tsaye rike da mug yana kallon harabar gidan aka wuce da motar yaransa zuwa makaranta. Sai da aka rufe gate din sannan ya juyo zai dawo wayarsa ta yi kara alamar shigowar sako. Hannunsa na hagu ya saka ya ciro wayar ya duba, sako ne aka turo da bakuwar number.

 I Love You
I love You Kareem Ina sonka sosai

Haka ya bi sakon yana karanta kalma bayan kalma sai kuma yayi saurin kiran number da sakon ya shigo masa ya kara a kunnensa ya juyo ya sauko daga entrance din...

 Hello... Kareem...

Dakika biyu ce tsakanin amsawa da Hello da kuma kiran sunansa, sai ya lumshe ido ya matse bakinsa domin be ji muryar da yake zaton sakon ya zo daga gurinta ba.

 Safeena What Now?

 Na yi marmarinka Kareem, na san idan na kira da line na zaka iya kin dagawa, ina cikin damuwa rashin saka a ido da na yi, ina sonka Kareem ka sani ina sonka sosai

Ya katse Kiran ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya, sannan ya busar da iskar bakinsa. What he got himself into? Matar aure matar sunna ta tsaya tana fada masa yadda take kaunarsa, ya san ya cutar da Safeena na bin umarnin Momy ya auri Macen da ba ita zuciyarsa take ba, ya cutar da kansa kuma ya cutar da Safeena, gashi yanzu shi da ita sun fada cikin halaka. Ya shafa kansa sannan ya juyo ya nufo kofar falon ya tura ya shiga arba da yayi da Yusura tana mopping ya dada bacin ransa, domin ita ce macen da ta ruguza masa komai a rayuwarsa. Me yasa bata amsawa Mahaifiyarsa cewar ba zata iya zama da shi ba tana da wanda take so? Shi ba zai iya musawa Momy ba, amman ita zata iya fada mata bata sonsa da yanzu duk haka be faru ba, gashi suna da yara har biyu amman wani abu mai suna so be fara shiga tsakaninsu ba.

 Breakfast dinka is ready

Ta fada masa ganin yadda ya tsaya a gurin yana kallonta fuska babu Annuri, ita kanta ba son take ya kalleta ba, yadda yake jin tsanarta haka take jin tsanarsa a zuciyarsa har ma ta fi shi. Ya dauke kai ya bar kofar a bude ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa ya aje mug din ya aje wayarsa a saman gado ya cire tufafin jikinsa ya dauki bathrobe ya saka ya nufi bathroom kamin ya shiga wayarsa ta yi ringing. Juyowa yayi ya dawo ya dauki wayar ganin number mahaifin Hafiz ya saka shi zaunawa sannan ya amsa wayar cike da ladabi.

 Hello Abbah

 Naam Kareem kana lafiya?

 Lafiya Kalau Abbah ya gida?

 Lafiya Kalau

Daga haka Abbah yayi shiru be sake cewa komai ba har sai da Kareem ya tambaya.

 Abbah lafiya?

 Lafiya Amman ni ma ita na kira na ji, na ga duk hidimar auren nan da ake ba ka zo ba Kareem ko last week da aka kai lefen abokinka na yi zaton zan ga domin maza suka kai lefe amman ban ganka ba, ko da yake dai ya ba da izuri cewar aiki ya maka yawa amman ina fatan dai ba matsala kuka samu ba

Kareem yayi murmushi.

 Haba dai Abbah ni da Hafiz ai mun zama yan'uwa dangantakarmu ta wuce abota ina kallon Hafiz a matsayin dan'uwa ne na jini ba aboki ba, babu wani abun da ya shiga tsakaninmu kuma babu abun da zai taba shiga tsakaninmu har abada

 Toh haka nake fatan ji, shi ma kuma haka ya fada min amman zuciya bata natsu ba sai shiyasa na kira da kaina

 Abbah kullum muna tare da Hafiz ma, kasan gurin zamanmu daya, indai ba ina aiki ba kullum muna tare da juna, babu wani abu da ikon Allah

 Tohm Allah ya muku albarka

 Ameen Abbah Sai anjima

Ya aje wayar sannan ya mike tsaye ya shiga bandakin. Ya dauke shi awa daya daga fitowa wanka zuwa shiryawa cikin manyan kaya kasancewar yau Jumma'a. Sai da ya dauki abubuwan bukatarsa sannan ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon yana zuba kamshi kamar shi ne angon. Motarsa ya nufa ya bude ya shiga ya murza key yayi warming din motar sannan ya kwanta ciki yayi relaxing yana murmushin da shi kadai ya san ko na minene. Can kuma ya dago ya ja motar yana danna horn Mai gadin ya bude masa Gate. A minti goma shabiyar ya isa kofar gidan mahaifinsa ya faka a harabar gidan da karin minti uku, ba yabo ba fallasa ya fito motar ya nufi kofar falon da zata sada shi da bangaren mahaifiyarsa. Gidanta gidane dake cike da jikokinta da na dangi domin kuwa ita mace ce mai tsananin son yara da yan'uwa, sai dai kasancewar safiya ce babu ko daya duk sun tafi makaranta. A falo ya sameta tana zaune ta dora kafafuwanta a karamin Center Table hannunta kuma rike da plate din dafaffen nama tana ci. Kusa da ita ya zauna yana fadin.

 Momy ba zaki daina cinye cinye nan ba, mai surga fa baya wannan cinye cinye

Ta kalleshi tana murmushi.

 Yanzu ma Khadija ta yi ta gaji ta tafi ta bar ni, so kuke na mutu da rama ai sai a zagi mahaifinku ma

Ya shafa kansa ya kai hannunsa ya dauki tissue ya dauki nama ya fara ci.

 Momy saboda lafiyarki ake fa, kina fama da BP ga Suga mu lafiyarki muke so ba ciwo ba

 Ai ku likitocin nan haka kuke, idan mutum be cin dadi ku ce ya rika cin kaza da nama da kayan dadi, idan kuma yana ci ku ce za su saka masa ciwo ya daina, ni ba zan bi ba, ku bar ni na ci dadi mutuwa da wahala ba a musu wayo ai

Wannan karon dariya Kareem yayi yana dariya.

 So yanzu laifi muke idan muna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login