Showing 81001 words to 84000 words out of 227321 words

Chapter 28 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1568

kamar zata cire, murmushi yayi min ya juya ya fice. Da gudu na tashi na shiga bandaki na fara korawa bakina ruwa na wanke shi tasss sannan na saka mai goge baki da buroshi na fara goge bakin ina jin kyankyami. Kamar daga sama na ga an turo kofar dakin ta jikin madubi nake kallonsa har ya fito murmushi yake kamin ya kai hannunsa ya cire brush din ya debo ruwa ya wanke min bakin sannan ya sake hade bakinsa da nawa wannan karon da ya cire sai da ya cilasta min hade yawun bakina.

 Na hade

 Toh muje ki kwata, kar na sake kissing dinki ki wanke baki daga yau

Na kalleshi kamar na ce wani abu sai kuma na kyale na bi umarninsa. Saman gadon na hau na kwanta ya lullube ni sannan ya fita be jima ba Ikram da Walida suka shigo suka hauro gadon suka kwanta tare da ni. Bachin yayi min dadi sosai domin ban kwanta tare da shi ba, babu fargaba ko tsoro a kusa da ni. Washe gari bayan na yi sallah ban koma bachi ba na fita falon na gyara kitchen na gyara falon na wanke na wanke na goge na goge sannan na dawo na zauna. Zamana babu wuya Aisha ta shigo falon kiran yaranta da sai a lokacin suka tashi bachi.

 Amarya ya kwanan kadaici?

Na yi murmushi.

 Yara na zo kira, ko sun tashi

 Eh sun tashi bari na kira su

Haka ta bini da kallo har na shiga dakina na taso yaran suka fito, ta kama hannunsu suka fice tare. Dakin na gyara sannan na shiga na yi wanka na fito jikina na ciwo domin ban saba aikin wahala haka ba, mai na shafa na dauki riga da skirt material na saka sannan na shiga kitchen din na dafa shayi da gass na soya kwai biyar na soya dankali na fito na zauna. Ina tsaka da ci Hafiz ya shigo falon rike da biredi ya aje min.

 Good Morning

Na amsa da murmushi sai ya gutsuri kwain dake gabana ya ci.

 Ashe kin iya soya kwai

Na yi murmushi, ya mayar min da murmushin sannan ya tashi ya fice. Ina gama karyawa na hau bachin wahala idona cike da kwalla indai haka auren yake ba shi da dadi ni dai a gurin, ba zan fita ba ga aiki kullum ga wahalar kyautatawa miji ko baka so... Na yi wannan tunanin na yi wacan har bachi yayi gaba da ni ban farka sai azahar shi ma saboda Aisha ta shigo har dakina ne ta tashe ni daga bachin.

 Ke bachin rana kin yi sallah ma tashi mu yi hira

Na tashi ina murza ido, bayan na yi sallah na dawo muka zauna da ita falo tana min hira mafi yawan hallayar Hafiz take fada min marar kyau, tana kara tsorata ni akan mijinta, sai dai abun da ya bani mamaki kuma ya daure min kai shi ne yadda take zaune da shi lafiya babu wani tashin hankali sai soyyayah da kaunar juna. Ba ita ta bar bangaren ba sai biyar na yamma a lokacin ne na shiga kitchen na sarrafa shimkafa da miya da naman kaza na ci, na bar ragowar kamar yadda na kasa cinye kwan da na soya a dazun. Da dare Hafiz ya shigo ya duba ni sannan Yaransa suka shigo muka kwana tare, washe gari ma haka ya na gyara komai na yi wanka na girka shimkafa da wuri, kamin na kwanta bachin kanwarta ta shigo kirana wai yau tana son na shigo bangarenta mu yi hira.

Kwasar fafauwana na yi na shiga bangarenta tana ta bani labarin irin soyayyar da suka yi, ashe aure ta yi bata dace ba ta fito shi kuma ya ganta ya nuna yana sonta iyayensa suka amince kasancewar ba masu matsala ba ne, shi yayi mata komai kamar yadda yayi min a aurena, a lokacin ne take fada min shi ya saka ta makaranta ta yi karatu har take aiki.

 Amman ban taba ganin kin tafi aikin ba?

Ta yi murmushi.

 Yanzu kin ga ina da ciki wata 6 kuma gaskiya bana sha'awar aiki, na fi sha'awar zama a gida yanzu na kula da mijina da aurena, daman dai babu abun da na rasa kawai ra'ayi ne, yanzu kuma na gane hakan ina son zama a gidana ko ba komai hankalinsa zai fi kwanciya za mu kula da shi tun da ba ni kadai ba ce a yanzu

 Haka ne, amman aiki yana da sha'awa ina son aiki sosai

 Amman ke baki gama karatu ba aka miki aure ko? Na ga ke din yarinya ce sosai har yanxu baki gama wayo ba

Na sauke kaina kasa.

 Haka ma a gidanmu ake cewa wai bana da hankali ba na da wayo, wai kanwata ta fi ni wayo, amman ni bana ganin haka

Ni da ita muka juya muka kalli kofar falon da aka bude Hafiz ne ya shigo ba a irin lokacin da ya saba dawowa ba, har da yar tsabararsa.

 Welcome Barrister

 Yan mata na har biyu, me ake tattaunawa?

 Hira ce kawai ta karatu take fada min tana sha'awar aiki, ni kuma yanzu ya gumshe ni har na aje sai nan gaba kuma idan komai ya daidaita

Yayi murmushi ya miko min ledar hannunsa sai na saka hannu biyu na karba, sai dai na lura kamar hakan be mata dadi ba domin a take fuskarta ta canja.

 Aiki kike sha'awa Noor, ni yanzu bana sha'awar mace ta yi aiki, ita ma saboda ta dage sai ta yi ne, zan saka ki makaranta ki yi karatu mai zurfi saboda gaba, amman zancen aiki ba yanzu ba

Na wara ido baki sake kai kace son karatun nake.

 Da gaske zaka bar ni na yi karatu?

 Me zai hana ni fa dan boko ne, karatu sai kin ture yarinya

Zan yi magana ta cafke ta nuna masa murnarta a fili na jindadin yadda yace zan yi karatu tana ta yabonsa har da masa godiya.

 Ke gani ko ai na fada miki ki kwantar da hankalinki Barr be da matsala ko kadan, shi mai son kyautata ma iyalinsa ba

Annashuwa ta suka fuskarsa.

 Wato gulmana kika yi ko? Na kama ki

Sai ta yi dariya tana kallonsa. Shi kuma ya kalleni.

 Ba zaki bude ledar ki ga miye a ciki ba Noor

Na bude ledar na ciro gasashiyar kaza da kayan ciki mai Onion and vegetable sai kamshi suke. Leda ta uku kuma faranti ne dauke da yar tsutsar nan da na yi sha'awar ci tun ina zuwa restaurants din Kareem.

 Waya fada maka ina son wannan?

 Na taba ji gurin Kareem

 Na gode

Ina fada ina kallonsa gaba daya ya gana faranta min zuciya a yau.

 Me aka dafa?

 Ghanian jollof na yi

 Ku kunci kenan?

 Har kunci kenan?

Ta amsa.

 Eh mun ci

Na mike tsaye rike da leadar.

 Zan tafi bangarena na ci wannan sai na sha tare da tea

 Okay Amarya aci dadi lafiya

Ta fada na fice daga bangaren na dawo bangare na, wanke hannuna ne kawai ya same ni dole na wanke hannun na zauna na fara ci ina jin wani shauki saboda mai da take da shi gashi ta yi laka laka kamar kitsen kilishi. Bayan na gama na wanke hannun na yi alwala na yi sallah ina nade carpet ya shigo rike da plate dake dauke da kayan ciki da kazar da ya siyo dazun.

 Kin manta wannan Noor ko ba ki ci.

 Na ci wannan abun na koshi

 Ki aje wannan anjima sai ki ci

Na karba na juya zan fice sai na ji ya rikoni yana kokarin rumgume.

 Kin yi min kyau yau fiye da kullum, ko dan kin dan sake jiki kin sake fuskar nan ne

Na yi murmushin yake Ina sauraren yadda yake yawo da hancinsa a wuyana. Sallamar Na'ima ce ta katse hanzarinsa a dole ya sake ni da sauri yana amsawa. Ya fice daga dakin da sauri

 Wai Anty tana kiranka

 Okay

Na bi bayansa na shiga kitchen na aje naman sannan na fito na dawo falo na zauna ina kallo. Da zai shigo yi min sai da safe ne yake sanar da ni wai an yi gobara a gidan Baba, hankalina ya tashi sosai jin cewar gidan ya kore gaba daya.

 Amman ba a rasa kowa ba?

 Da an rasa rai da Baba ya fada min, kin san baya boyo, amman dai gobe zamu je mu duba

 Da dare nan aka yi wutar?

 Da yamma

 Dan Allah ko zaka kira min Baba na ji shi?

Na tambaya tare da fatar zai karba bukata sai dai hakan be samu ba.

 Ki yi hakuri gobe zamu je mu duba

 Tohm

Kusan sai da na yi mafarkin wutar saboda na kwanta a abun a zuciyata, washe gari na gyara komai na shirya da wuri ina gama karyawa ya shigo bangarena da shirinsa muka fita, a nan ma na ga rashin jindadin fitar ta mu a tare a fuskar Aisha domin ta kasa saki fuska kamar yadda ta saba sai ce masa take ya dawo ya ci abincin rana.

 Wata kila ba zan samu dawowa ba, ita ma ai zata dawo ta yi girki ko?

Ya kalleni ina zaune a gidan gaba.

 Eh

Ta yi mana Allah ya tsare na rufe motar yaja muka kama hanya. Ba mu yi nisa da fara tafiyar ba ya kama hannuna ya rike yana murzawa a hankali.

 A kwana biyun nan fa ina ta jin sonki yana kama ni, kin san ni ban san dadin auren budurwa ba sai yanzu, Allah yasa na same ki fiye da yadda bake tsammani

Na yi shiru ba dan ba gama fahimtar inda zancensa ya dosa ba. Shi kuma be sake ce min komai ba har muka isa unguwar, ina kallon gidansu Zafeer dai da idona ya cika da kwalla, a nesa da kofar gidanmu ya faka ba tare da ya kashe motar ba ya ce.

 Ki fadawa Baba idan zan zo daukarki xan shigo mu gaisa ina masa jaje

Na kalleshi kadan na dauke kai, wata kila ya fara gajiya da halin Baba ne, ko kuma dai yana jin abun da yake nema a yanzu ya samu shiyasa yake son kaucewa daga jikin Baba. Ko da yake Baba din ne iya masa sai Allah ba kowa ne zai jure ba. Bude motar na yi na fita sai da na isa kofar gidanmu sannan yayi reverse ni kuma na shiga cikin gidan namu da ya kone tun daga waje har cikin gidan. Da gudu na karasa gurin Hana dake kwance tsakar gidan da konuwa a fuskarta zuwa cinyar hannunta.

 Innalillahi Hana

Ta fara yunkurin tashi zaune. A lokacin da Baba ya fito bandakin da sauri yaka aje butar ya kalleni yayi murmushi.

 Aha ahhh wa nakd jin muryarta a gidan kamar Nooriyya yar albarka

Na juya na kalleshi ina hawaye.

 Baba ashe gobara aka yi?

 Kin gani dai haka Allah ya kawo mana, wutar da dare, ina mijin naki? Baki ce ya shigo ba? Kika bar shi a waje? Ba kara ya shigo ya ga yadda gidan yayi ba

Ya fara tafiya sai na dakatar da shi.

 Baba ya tafi yace yana maka jaje za ku gaisa idan zai zo daukata

 Au be tsaya ba? Tohmmm... Toh toh ba matsala ai duk daya ne, kuna dai zaune lafiya ko?

 lafiya Kalau Baba, Baba me yasa ba a kai Hannatu asibiti ba? Kuna ce fa

Na fada ina kallon maganin gargajiya da aka shafa mata.

 Ina kudin yake Noor? Kin san yanzu abun duniya ba zama yake ba, ban da rayuwa ba ni da komai a yanzu, sai kuma wanda ya ga Allah ya ga Annabi ya kyautata mana, kina kallon yadda gida ya zama kamar kango, abun bakin cikin ma sai da na sake masa sabon fenti

Ya fada kamar zai fasa kuka, na daga kai ina kallon bakin wutar da ya rufe ginin ya hana a gani fentin.

 Ai na so Hafiz din ya shigo ya ga yadda gidan ya koma

Na kalli Baba bance komai ba. Kamin ya shiga tambayata ya kishiyata ya zaman gidan Baba wata matsala, na amsa masa da komai lafiya. Ina nan wasu makotan suka shigo jaje suna ta maraba da ganina har suna fadin wai na fara natsuwa saboda na kasa hada ido da su.

 Aure na natsar da mutun, wai Noor ce a haka, Allah ya bada zaman lafiya

A fuskar Baba nake ganin yadda kalamansu suka masa dadi, bayan sun fita shi ma ya fita a nan na samu damar hira da Hana tana fada min yadda wutar ta fara.

 Daga dakin Mama ta fito, kuma bachin ya mana nauyi duk ba mu san ta kama ba sai da hayaki ta cika gidan, Yaya yana dakinsa na zaure Baba kuma a waje ya kwana ni kadai ce a daki

 Ya aka yi ta kai ga jikinki?

 A lokacin da na farka na ga wutar tana ci sosai har kusan kofa ba damar na wuce ta saman kuma ta sauka kan katifa sai ta kama tufafinmu ceiling saman kuma yana ta narkewa yana fado min a jiki kin san na roba ne idan ya digo kamar fatar zata cire nake ji, sai da Alhaji Bashiru ya shigo ya fitar da ni

 Ni ma ban sani ba sai jiya da dare Hafiz yake fada min, amman Hana baki ma Yaya magana ba ya kai asibiti?

 Ba shi da kudi ai kin ga da ya kai ni, Baba kuma ba zai iya kashe kudinsa ba ji yake hasara yayi, ban dan ma gobarar nan ba jibi za a kawo amaryarsa shiyasa kika ji yana fadar yayi fenti

Na gyara zama ina mamaki.

 Auren dai yana nan da gaske?

 Noor to me zai hana? Mama ma aure zata yi?

 Ita ma? Yaushe? A ina?

 Garin nan, wani mai rufin asiri ma kuwa motarsa ma abar kallo ce

Dadi na saka ni murmushi.

 A ina Mama ta hadu da shi?

 A cikin unguwa ya zo gidan wani abikinsa

 Amman shi ne ba a fada min ba? Bani da labarin kowa babu mai zuwa gurina kun bar ni can ni kadai

 Noor ba a kusa kike ba balle nace zan taka da kafa na tafi, ba ni da kudin abun hawa kuma mijinki ma zai gaji idan aka ce kullum zai na je

 Ba zai gaji ba ita ma kanwarta tana yawan zuwa ai, ko jiya ma taje kuma baya cewa komai

 Sai na samu lafiya zan zo

Da kanwata da kusan zan iya cewa tawainiyata ma muka sha hira muka koshi, ina ta sake saken yadda zan saci kafa na tafi na ga Mama babu hali, domin na san Baba zai yi fada idan ya dawo be tarar da ni ba, dole a wayar Yaya na gaisa da ita har nake tambayarta ance zata yi aure.

 Da yardar Allah kuwa Noor, idan lokaci yayi ai dole za a fada muku

 Mama yaushe zaki zo?

 Yaushe aka yi auren ma balle na kwashi kafafuwa na tafi Noor? Ni fa uwace ba zai yiyu na tafi gidanki ba sai da dalili

 Amman Mama kin ji Baba yayi wuta?

 Uhmmm Allah ya kyauta gaba, Noor ki rike aurenki da mutuncinki, idon mutane yana kanki kowa jiran yake wani abu ya faru da ke, kuma kin ga zaman gidanku nan ba shi da dadi, da alama kuma mijinki mai hankali ne da tunani, kishiyarki kuma ki rike ta da mutuncin kuma ki yi taka tsantsan da ita, ki rika kula da rayuwa na san halinki da sakarci, balle kuma an dauke ki an kai ki gurin babbar mace ina yarinya karama, ta fiki wayo ta fiki hankali kuma ta fiki sanin kan mijinku, ki bi a hankali kuma ki rike addu'a kar na ji kar na gaji wani abu ya faru, kuman ko da wasa bana son na ji kin bibiye Zafeer aure ya rabaki da kowa yanzu

 Toh Mama, zan kiyaye, Zafeer ni ba zan taba yin magana da shi ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi masa magana


 Toh sai ki kiyaye, ki zauna lafiya a gidanki kin ji?

 Toh Mama

Sallama muka yi sannan ta kashe wayar na mikawa Yaya.

 Mahaifiyar Kareem ta rasu ko Yaya?

 Eh kwana uku aka yi ai ba a bude restaurant din ba, sai da aka yi sadakan uku duk mun je masa gaisuwa

 Yayi kuka?

 A gabanmu zai yi kuka? Sai dai a boye ko? Kin masa gaisuwa

 Hafiz be bari na tafi ba matarsa kawai ta tafi, wata kila sai nan gaba idan na fara fita

 Kila


Saman sama muke taba hirar Yaya na fada min Kareem din ya rame sosai abun ya taba shi. Na yi zaton Hafiz zai dawo da rana ya dauke ni saboda yayi min zancen girki amnan shiru be zo ba sai bayan Isha'i a lokacin Baba har ya gaji da jiransa. Yana yin sallama Baba ya tarbeshi jiki na rawa suka gaisa sannan ya shiga nuna masa gidan yana fada masa yadda gobarar ta fara.

 In shaa Allah zan kira ka Baba sai mu yi magana na ga abun da ya dace ayi

 Na gode Allah ya saka da alheri ya kara rufa asiri...

Baki har kunne baba yake Fadar haka, sai dai ko kadan ban ga alamar sake fuska a gurin Hafiz ba, yadda yake rawar jiki da Baba ma wannan karon ban ga yayi haka ba. Ba Baba kadai ba ni kadai na yi tsammanin zai bawa Baba kudi ko kuma ya ce akai Hana asibiti amman ba ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login