Showing 30001 words to 33000 words out of 227321 words

Chapter 11 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1500

da yace komai ba ya nufi stairs.

 Ga breakfast dinka nan

 Ba a gida zan ci abincin safe ba

Ta tabe baki ta ja kujera ta zauna tana magana a hankali da muryar da ba zai ji ba.

 Ni dai kawai ina ibada, kuma ina jiran ranar takaba

Kareem ya shiga dakinsa ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya fara murza jikinsa har yayi wankan ya gama maganar da Yusura ta jefeshi da ita cewar ta gama yi masa alfarma tun da har ya kasa rike kansa har sai da ya kai ga jikinta tana cin ransa. The part that ita bata san duk kokarin kai kansa da yake gurinta yana yi saboda ya bata hakkinta ba is more painful sama da aurenta. Yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya saka hula ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya saka talkaminsa ya fice daga gidan. Ko da ya sauko tana zaune a dinning din tana cin abinci. Be kulata ba ya fice daga falon motarsa ya shiga ya murza key mai gadin ya bude masa yana mika masa gaisuwar barka da safiya. Hannu kawai Kareem ya daga masa sannan ya kama hanyar da zata kai shi gidan abokinsa. Yana kan hanya kiran Safeena ya shigo wayarsa, duba wayar kawai yayi ya aje be sake daukarta ba sai da ya isa gidan Hafiz sannan ya kira ya sanar masa yana waje.

 Shigo ciki mana

Kareem ya bude motar ya fito ya rike da wayarsa da Safeena ke kara kira. Iskar bakinsa ya busar sannan ya amsa wayar.

 Hello

 Baka kira ka ce ya jikina ba? Baka yi tunanin ko bana jindadi ba? Miscarriage na yi ba jiya, yanzu baka ma damu da lafiyata ba Kareem?

 Safeena ina son za mu yi magana da ke face to face amman bana son mu yi magana yanzu sai idan mijinki baya gari

 Na ji muryarka wani iri, matarka ce ta bata maka rai?

 Me zai saka matata ta bata min rai?

 Ban sani ba, amman dai na san nice mai faranta maka a kodayaushe ba tare da gajiyawa ba

 Ya jikinki.?

Ya tambaya domin ko da yace be damu da Safeena ba ko lafiyatarta ko kuma yace baya sonta yayi karya.

 Da sauki, ina asibiti yanzu haka

 Idan kin dawo zamu yi magana

 Okay i love you

Ba tare da ya amsa mata da i love you too ba ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sannan ya doshi kofar shiga yayi knocking. Hafiz ya bude masa kofar.

 Shigo mana

Ya shiga falon kamar marar lafiya.

 Bismillah ga breakfast na san baka karya ba

Hafiz ya fada yana nuna masa dinning, Kareem ya karasa daman gidan ba bakonsa ba ne. Ya zauna a kujera Hafiz ma yaja kujera ya zauna.

 Yanzu nan ni ma na dawo gida, na sauke madan a gurin aiki

Kareem ya sauke ajiyar zuciyar dakw bayyana damuwarsa sannan ya ce.

 Hafiz ina cikin matsala, ina jin kamar ina daure da sarka, ina jina kamar ina a tsakiyar hanya da ta kasu na rasa wacce zan bi?

 Me ya faru bayan abun da na sani?

Tambayar da Hafiz yayi masa kenan yana zuba madara a cikin tea da already ya saka sugar. Kareem ya fara masa samun cikin Safeena da kuma zubewar wadda shi ya fi damunsa a yanzu. Hafiz ya aje tea cup din dake hannunsa yana kallon abokinsa da mamaki.

 Yanzu abun ya kai jar ciki ya shiga tsakaninku Kareem kuma har ta yi alfahari da haka? Subhanallahi abun ya munana ya kazanta

Kareem ya dauke idonsa daga barin kallon abokinsa saboda kunyarsa da yake ji.

 Baka ji tsoro ba ace cikin ya zube saboda kishina?

 Hakan ya ba ni tsoro sosai kuwa, kuma hakan yana nufin idan baka shata line tun da yanzu ba, Safeena zata wuce gona da iri, kuma zata jan yo maka matsaloli da yawa, a cikin idon yarinyar nan na hango rashin kunya da rashin imani, matukar baka takawa lamarinta burki ba zata janyo maka matsalar da baka isa ka fitar da kanka ba, kuma zata jefa duk wadda yake tare da kai a matsala

Kareem ya sauke ajiyar zuciya.

 Zuciyata na raya min wani abu akan son haihuwa da take da ni, na san tana sona, amman na tsorata da wannan son, idonta yana kokarin rufewa akaina ina jin kamar tana son ta haihu da ni ne a yanzu, saboda a gaba mu kasance tare, ni kuma babu wannan a tsarina ba zan iya auren Safeena ba

 Idan kuma ta gane haka ba karamar illa zata maka ba, shiyasa nake son ka rabu da ita tun yanzu ka tuba ya canja Kareem, karshen cin amanar da zaka yi shi ne ka bari matar nan ta dauki cikin da bana mijinta ba kuma ta haifa masa yaron yayi hidima da shi, kuma da zarar ta haihuwa zata bukaci ka aureta ne ko kuma wani abun dabam, a yadda na lura bata da kunya zata iya lalata rayuwarka saboda idonta a rufe suke, zata iya maka illar da zaka rasa aikinka ka rasa matarka ka rasa girmamawa daga yayanka kuma ka rasa kima a idon mahaifiyarka da yan'uwanka, duk wata kima da martaba da ake ganinka da ita zata iya zubar da ita

Kareem ya dauki tea ya sha yana nazarin kalaman Hafiz. Sai da Hafiz ya motsa tea ya sha ta gutsira biredi sannan ya ce.

 Ina yarinyar nan? Ya hannunta Noor ko?

A take murmushi ya cika fuskar Kareem kamar ba shi ba.

 Ka ma tuna min ya kamata na kira na ji ya jikinta, jiya ta dawo bayan na kaita gida...

Hafiz ya girgiza kai bayan ya gama sauraren labarin da Kareem ya ba shi na abun da ya faru tsakaninsa da Noor da iyayenta a jiya.

 Mahaifinta yana son abun duniya sosai kuma baya tunanin abun da ya dace, miye abun sadaka a nan?

Kareem ya tabe baki.

 Ba dan na bashi kudi ba babu abun da zai hana shi dukanta, yarinyar tana ba ni tausayi ga mahaifiyarta ta kai ga nuna mata wuka

 Kawai tana nuna musu real her ne, su kuma sun ki fahimta

 Shi kansa saurayin da wahala ya iya handling dinta, yana zuwa ya rufe ta ta fada duk sai na ji babu dadi, shiyasa ma na riga su isa na yi magana da Babanta, sun kasa fahimtarta but with time zata daina, yanayin rayuwa ne kowa da yadda yake tashi

Hafiz ya kalleshi yana murmushi.

 She's sweet

 Yeah she's so friendly tana da shiga rai

 More especially when she meet someone like you, kana son wasa da kiriniya a yadda na sanka Kareem kai mutum ne mai son rayuwar aure da nishadi, kai mutum ne mai son shakuwa da mace, kana yawan ba ni labarin yadda kake son ka yi rayuwar aure da matarka irin na soyayya da kaunar juna da taimakona, idan ban manta ba yana daga cikin dalilin da ya saka kake son Safeena sosai

Kareem yayi murmushi ya girgiza kai.

 Wannan duk da ne Hafiz, ban da yanzu

Hafiz ya sake yin murmushi ya cigaba da karyawarsa har sai da Kareem ya ciro wayarsa yana fadin

 Ka tuna min ma, bari na kira Yayanta na ce ya bata na yi mata ya jiki ba mamaki kuma ban siya mata magani ba na manta sam

 Karka kira, tashi muje mu duba ta kawai zai fi mutunci, kuma sai ka rubuta mata maganin nan daga nan ko ba siya ba sai ka bada kudin maganin

Kareem ya kalleshi ba dan yana jin son tafiyar ba.

 Why?

 Zata ta maka complain ne idan baka je ba ai, na lura ita ma tana son kasancewa da kai if not ba zata yi karya tace kai saurayinta ba ne

Kareem yayi dariya.

 Wato wannan yarinyar ko? Idan baka fahimce ba zaka hau sama ka fado ne ka ji rauni, babu wani son kasancewa kawai tsabar iskanci ne da son nuna ita wata ce ai ta fada min gaskiya

Hafiz ya aje cup din ya Mike tsaye.

 Ba mamaki abun da muke fata ya kasance ai, shiyasa na kirata da Amaryarmu a gaban Safeena, kuma na san ba zaka kunyata ni ba, ba za ka zabi bangaren Safeena ka bar bangarena ba, ko ba Noor ba dole zaka yi aure Kareem, saboda ka samu gurin da zaka rika jin sanyi, kuma karin sauren zai nesanta ka da wannan zunubin da kake diba, ina fatar dai Momy ba zata ba mu matsala ba

 Momy bata da matsala da karin aurena, ni din ne dai bana ra'ayin mace fiye da daya

 Ai shi ya cutar da kai har kuka fada tarko kai da Safeena, auren fari baka auri wadda kake so take sonka ba, yanzu zamu nemi mai sonka mu aura maka

 Indai dan haka ne, kar muje gidansu Noor yarinyar nan tana da wadda take so, ba kuma zan sake kuskuren auren macen dake son wani ba, na yi na farko saboda biyayya ba zan yi na biyu ba

 Take so ko dai yake sonta, ai ita bata san so ba a yanzu, kai ka fada min shekarunta fa, kuma kaga yadda rayuwarta take, shi kuma ba lallai yana sonta ba ko kuma zai iya zama da ita, and ba dan wannan zamu je ba, zamu je ne saboda mahaifinta ya maka alfarma idan muka yi haka next time idan ta sake laifi ta gudo gurinka zamu iya ba shi hakuri kuma ya hakura

Kareem ya bishi fa kallo, ya fi gamsuwa da reasons dinsa na karshe dan haka ya mike tsaye ya bi bayansa. A motar Kareem suka dauki hanya, kamin su isa Kareem ya bi ta wani pharmacy ya siya mata magani ciki har da na zafin kafa saboda tafiyar da tace masa ta yi a jiya.



NOOR POV.

Ban kwanta ba sai da na rama sallah magariba da ban samu yi ba saboda tafiyar da na yi a kafa zuwa gidan Kareem sannan na kwanta a dakinmu tare da Hana, washe gari na farka da asuba, da kaina na warware hannuna saboda alwalar da zan yi na ji azaba sosai amman a haka na daure daman karfin hali rayuwata ce, Hana ce dai da bata saba da wahala ba ta tashi da zazzabi saboda dukan da Baba yayi mata. Mama ita ta yi shararta da safe bayan ta gama hada mana abun karyawa. Ina zaune dakinmu ina ji sallamar yaro Mama ta amsa Baba dake daki kwance yana sauraren redio kuma ya kashe radio yana sauraren abun da yaron yana fada.

 Wai Zafeer ya ce a ga sako a abawa Noor kuma yace yana waje yana sallama da ita

 Toh shiga ga dakinta can ka kai mata

Na ji Mama ta fada, sai yaron ya iso bakin kofar dakinmu yayi sallama, na mike tsaye na amsa sai ya shigo rike da katon kwando ya aje min.

 Gashi Wai Zafeer yace a kawo Miki kuma yace yana waje yana sallama

 Toh

Yaron ya juya ya fita ni kuma na dauki hijab dina na saka sannan ya bude kular dake cikin kwandon na duba kwai ne soyayye da plantain sai kamshi suke. Na rufe na fita ina jindadi na nufi waje cikin natsuwa, tsaye na same shi rike da wata ledar da ban san meye a ciki ba.

 Baby Noor ya jikin?

 Alhamdullahi, kai ka aiko min da sako?

 Eh na yi tunanin ko ba zaki iya cin abun da aka girka ba a gidan na saka aka shirya miki wannan

 Na gade

 Never mind, jiya na kwana da tunaninki a raina, na zo Mama tace kin kwanta, jiya ya bani kamar wani abu ya faru dake, sai na kasa natsuwa

 Lafiya Kalau

 Kin ji sauki? Ya hannu mu gani

Na bude masa ya duba cike da tausayawa.

 Noor dan Allah ki daina wannan rashin jin nan bana jindadi yadda abubuwa suke faruwa dake, kuma bana son yadda Mama ko Baba suke miki hukunci, kuma Noor please bana son na sake ganinki da mutumen nan, bana son na sake jin wata alaka tsakaninki da shi

 Bafa komai tsakanina da shi, kawai shi yace abokina ne wai, na fada masa ina da saurayi ina da wadda zan aura

Ya daka min tsawa.

 Wane irin aboki? Abota ake mace da namiji ne? Kar na sake jin sunansa ma na fada miki ko?

 Eh na daina

 Good karbi wannan magani ne na siyo miki na sha da shafa

 Toh na gode Sosai Zafeer ina sonka sosai

 Ina sonki Noor, ina sonki irin son da baki taba tunani ba, irin son da idan na rasa ban san wane hali zan shiga ba

 Ni ma idan ba kai ba ba zan auri kowa ba

 Ko ma kin yi auren ba zaki zauna ba, babu wadda zai iya dawainiya dake Noor sai ni kadai, da zaki auri maza dari Noor ba za su iya dake ba sai Zafeer ke tawa ce har abada!!!

Na yi murmushi ina jindadi shi kuma ya mika min ledar na karba yayi min murmushi sannan yace.

 Allah ya baki lafiya, shiga ciki kar ace kin jima a waje

 Toh

Na masa waving na dawo cikin gidan, a tsawon shekara uku da muka yi tare da Zafeer ba zan iya fadar ranar da kaunarsa bata karuwa a zuciyata ba, kamar yadda ba zan iya bayyana yadda yake kaunata ba. Soyayyarmu da shi wani abu mai rikitarwa, duk yadda iyaye suke gajiya da ni shi be taba gajiya da ni ba. Ko da na shiga dakin na samu Hana ya bude wasu abubuwa tana ci, ban ce mata komai ba na dauka ka kasa na cirewa Mama da Baba na su sannan na zubawa Hana na ta na fara cin biredin kamin na fita waje na dauko kofi na zuba tea dake cikin karamin flask na fara tsomawa kamar mai cin tuwo da miya. Ina gama cinyewa wani yaron ya shigo yana sallama da Baba, ina jin lokacin da ya fita be dade ba na ji ya shigo da baki yana kiran a dauko tabarma. Tashi na yi na fara lekawa waje a hankali ashe sara na yi kan gaba, idona ya sauka akan na Kareem dake kallon kofar dakinmu kamar ya san a nan nake rayuwa. Murmushi ya sako min sai na yi saurin komawa na zauna gudun kar Mama ko Baba su ce na yi laifi.

 Noor... Fito ga Alhaji ya zo ganinki

Na dauki Hijab dina na saka na fito waje n zauna. Na gaishe su cikin natsuwa suka amsa mutumen da ya kira ni da Amarya a office din Kareem ya amsa yana murmushi kamar ya san ni.

 Lafiya Kalau Noor ya jikin?

 Lfy kalau

 Waya ce ki warware?

Kareem ya tambaya cike da kulawa yana kallon hannun nawa kamin ya koma kallon fuskata.

 Idan zan yi sallah ruwa be tabawa

 Noor..

Sai yayi shiru wata kila yana gudun Baba yayi min fada ne. Murmushi yayi min sai na sauke kaina kasa ina murmushi.

 Noor me kika ci haka bakinki duk maiko

Abokinsa ya tambaya sai na kai hannu na taba bakin cike da kunya domin ban san maikon ya bata min baki ba.

 Ai kazamar Budurwa ce nan

Cewar Baba yana kokarin kunyata ni. Abokin da ban san sunansa ba yayi dariya ya ce.

 Aa Baba mantawa ta yi dai da alama, gashi nan ta gyara muku gida ko'ina an share fes

A nan kam na yi sa'a Baba be tona min asiri ba, yayi dariya kawai yayi shiru.

 Ni sai nake ganin kamar na sanka, amman dai ba zan iya tunawa ba ashe nan ne gidanka

 Ikon Allah zai iya yiyuwa ka san ni Wallahi, ai da yake ku masu arziki ba tuna?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? talaka kuke ba, amman na yi mamaki

Mutumen yayi murmushi yana cigaba da fadar.

 Haba Baba wadda ke da irin wannan gidan za a cewa talaka sai dai mai rufin asiri

 Yaro ai haya nake a nan ba gidana ba ne, tukuna na dai

Mamaki ya saka na kalli Baba da sauri jin yana fadar gidan da muke ciki ba gidansa ba ne.

 Allah yayi budi, yanzu kuna biyan nawa a wata kamar wannan?

 Toh da dai talatin ne, amman wannan shekarar na ji yana fadar zai maida shi dubun hansi, saboda halin rayuwa

 Allah ya bada yadda za'ayi

Baba ya amsa da Ameen, duk abub da ake idon Kareem yana kaina, idan muka hada ido sai ya sakar min murmushi. Sai daf da za su tafi sannan ya ba ni ledar magani ya bude ya nuna min yadda komai yake.

 Baba ka bincika, mu ji gidan idan be fi karfinmu ba sai mu siya zai fi biyan haya

Cewar Abokin yayin da ya kai tsaye, Kareem ya kalleshi da sauri ni ma na kalleshi baki sake ina mamaki Baba kuma ya mike tsaye.

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Talla=?G?=?G?=?G?*

KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN S'=?G?=?G?=?G?
To kiyi saving numba ta ki danna wannan link=?G? https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI=?
?ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI=?G?=?G?
1.INFECTION CIWON SANYI =?I?LALACEWAR BREAST=?I?RASHIN HIPS & BUTT=?I?KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING=?I?TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?=?I? AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only =?L?

KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA =?I? KIYI SAVING NUMBER TA DM ME https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1


*Chapter - 10*


 Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login