Showing 111001 words to 114000 words out of 227321 words

Chapter 38 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1530

ba, kuma kar wanda yayi maka a saka maka ido kawai, ita kuma ta so barin gidan ni na hana, saboda na san idan Momynku tana raye Yusura bata da gurin zama sai gidan nan, a nan ta girma nan ta saba yanzu kuma dan Momy bata nan babu wanda zan bari ya dauketa ko kuma ita ta tafi ta bar mu, sai idan na mutu, kai ma dan kana ganin Momy bata nan ya saka kake son ka wulakanta amanar da ta baka, to ka sani Yusura ta fika gata a gidan nan, kuma matukar ina raye ni ce gatanta ba kuma zata wulakanta ba

Kareem yayi gutun murmushi ya girgiza kai, kana ya sake juyawa ya kalli Saurayin Kanensa ya ce.

 Fushi kuke ta yi da ni akan abun da Baku san komai a kai ba

Aaryam ya ce.

 Haba Big Bro ko dai minene ai be kamata ace ta kai ga haka ba, kai fa Namiji ne, kuma ga yara tsakaninku, kawai dai ban maka magana ba ne saboda Daddy yace kowa ya saka maka ido, kuma ina kasa da kai be kamata na tsuma baki a irin wannan ba sai idan ka bukata

 Gaskiya ne

Kareem ya fada tare da aje numfashi sannan ya mike tsaye ya nufi bangaren mahaifinsu, sai a yanzu ya fahimci dalilin da ya saka har yau da suke wata biyu da sati biyu da rabuwa Daddy be taba kiransa ya tambaye shi miye ya faru ba, kuma be taba yi masa maganar ba a duk shigowar da yake gaishe shi a gidan.
A natse ya shiga bangaren kamar yadda ya saba sai bayan da ya zauna sannan ya gaishe da Daddy dake sanye da gilashi yana duba newspaper.

 Lafiya Kalau, Kareem ya gidan ya yaran?

 Lafiya kalau Daddy

 Maa Shaa Allah, yau Monday ko akwai aiki

 Haka ne Daddy

 Allah ya taimaka ya bada nasara

 Ameen

Kareem ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Daddy. Daddyn ma ya kalleshi

 Allah yasa lafiya, akwai wa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ta matsala ne?

Kareem ya hade wani abun da ya tsaya masa a makoshi sannan ya ce.

 Daddy, ban ji kace komai akan dawowa Yusura gidan nan ba

Daddy ya aje newspaper dake hannunsa.

 Oh wai Yusura, Mijinta ne ya sake ta kasan kuma bata da wani gidan da ya wuce nan, bata da gata a duniyar nan sai mu, zamanta a nan ya takura maka ne? So kake a koreta?

Kareem yayi murmushi jin yadda Daddy yake fadar mijinta ne ya saketa kamar be san Kareem din ne mijinta ba.

 Aa Daddy ai ban isa na ce a koreta ba

 Good kara dai da kasan haka

Ya sake yin murmushi, a yanzu ne ya kara tabbatar Daddy fushi yake da shi.

 Kawai dai na yi zaton ko zaka bincike abun da ya faru ne

 Abun da ya faru, tsohuwar budurwarka tana zuwan nemanka, amaryar abokinka tana zuwan nemanka ta yi magana sai ka mareta ka ce ka saketa

Dif Kareem ya dauke wuta kamin ya kalli Daddy ya ce.

 Haka ta fada maka?

 Ba gaskiya ba ne Daddy, Safeena ta zo gaisuwar Momy ne, kuma na gargade kar ta sake zuwa domin babu wata alaka tsakanina da ita, Noor kuma tana zuwa ne saboda tsabanin da suke samu da Hafiz a lokacin

 Zan yarda da wannan, domin ban san ka da wani aiki na assha ba, shi ma wannan saboda Hassana ta matsa ne ya saka ta fadi wannan dalilin, amman bayan haka bata fada mana komai ba, ni kuma na auna abun a ma'aunin kishi ne, sai dai kai kuma ka yi kuskure na aikata saki a take

Kareem yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Daddy ya cigaba.

 Shiyasa na yi shiru na zuba maka ido na gani shin kana da hankali kansan ya kamata ko baka sani ba

Kareem ya sauke numfashi mai nauyi.

 Daddy, akwai abubuwan da ni da ita muka boye ba mu bar kowa ya sani ba, ban san ya zaka fahimta ba gaskiya ce mai matukar nauyi da daure kai, Daddy ni da Yusura ba mu taba son junanmu ba, ban taba jin ina sonta ba ita ma bata taba jin tana so na, wannan sakin ma ta dade tana bukatar na yi mata shi, saboda da nisanta da ni

Daddy yayi murmushi mai sauki ya cire gilashin idonsa.

 Kareem karka maida karamin yaro mana, baka sonta bata sonka aka yi muku aure kuka zauna lafiya har kuka haihu ba a taba jin kanku ba sai yanzu da Mahaifiyarka bata raye zaka ce wai baka sonta? Wannan ba hujja ba ce

Cikin tsananin damuwa Kareem ya ce.

 Wallahi Daddy bana son Yusura ita ma bata so na, kawai dai mun amsawa Momy ne kuma mun zauna saboda ita, ni da ita ba za mu iya bijirewa umarninta ba

 Okay yanzu da bata raye mu ne abokan wasarka? Kai da ita? Ni ba zan ma yarda ba ku son junanku ba. Kareem zan baka shawara karka yarda ka rasa Yusura, na yi aure tun kurciya har yanzu na zauna da mata biyu a lokacin da mahaifiyarka take raye, mu kan samu tsabani mu yi dadi, wani lokacin har iyaye su sani, amman ban taba ganin matar aure da bata taba kuka da mijinta ba sai Yusura, bata fadin sherinka, bata kawo kararka, kai a gurinka ba abun kunya ba ne aji ka saki matarka? Kuna da yara biyu me kake fada musu? Idan aure kake son karawa you're free to do so ba sai ka saki matarka ko ka wulakanta ta ba, idan har kana fadar saboda Mahaifiyarka ka aureta to miye amfanin sakin a lokacin da mahaifiyarka bata raye? Ke nan ganin idonta kake yi ma biyayya ba saboda Allah ba? Yanzu da ban yi magana ba haka zaka zuba ido ta cika idda? Ko saki uku ka yi mata? Domin bata fada mana ko saki nawa ka yi mata ba, kuma ita bata zauna kamar kai ta kalli kwayar idonmu ta fada mana bata son dan mu ba, Kareem idan ka sake ka rasa Yusura ka rasa matar kirki kenan har abada

Kareem yayi shiru be ce komai ba, domin ya fahimci Daddy ba zai yarda da duk wani zancensa ba.

 Saki nawa ka yi mata?

 Daya

Sai a lokacin Daddy ya sassauta muryarsa ya daina yi ma Kareem fada.

 Ka yi hakuri, shi zaman aure dan hakuri ne, duk can talkaminmu suka tsinke, dole sai an kai zuciya nesa, bana son na sake jin wata matsala a tsakaninku, ka maida matarka dakinta ku zauna lafiya dan Allah

Kareem kamar zai fasa kuka ya ce.

 Daddy mai daki shi ya san inda yake masa yoyo...

Be rufe baki ba Daddy ya rufe shi da fada yana masa tsawa.

 Get out Kareem, tashi ka dauki matarka ka aje ta gida sannan ka wuce aiki, wato Momy kake tsoro kana gudun zuciyarta mu kuma ka raina mu ko? Toh ka bari har bayan raina sannan ka saketa idan ka ga dama ka hada har da yayanka ka koresu gaba daya

Da sauri Kareem ya sauko daga kan kujera yana bawa Daddynsa hakuri, domin idan akwai abun da yake gudu da tsoro a rayuwarsa to fushin iyayensa ne.

 Ka yi hakuri Daddy, na maida aurena saboda kai, kuma zan dauke ta mu tafi gida yanzu kamar yadda ka ce ka yafe min dan Allah

Daddy ya dauke kai ya kai hannu ya dauki gilshinsa ya mike tsaye ya shige bedroom dinsa. Kareem ya dafe kansa ya rumtse ido, ya fi karfin minti talatin a haka sannan ya dago ya fito daga bangaren ya dawo bangaren Hajiya Hassana ya zauna a falon ya kasa yin komai har sai da Step mother dinsa ta fito sannan ya gabatar mata da abun da ya maido da shi bangaren nata.

 Na maida aurena Hajiya, a fada mata ta fito mu tafi

Hajiya Hassana ta yi murmushin jindadi.

 Haba yanzu na ji magana, ko kai ba haka ake so, kuma dan Allah ayi ta hakuri karka ce zaka biyewa mace ita mai rauni ce, kuma duk matsala da za a samu a daina saurin saki, muna raye idan ya kamata mu ji sai ka sanar mana mu tsawatar mata yafi ayi ta saki ga yara

 Tohm Hajiya

Ya amsa irin amsawar nan na wanda ya rasa interes da mafaka da kuma gata a lokaci daya, daman tun farko yayi tsammanin haka shi ya hana shi sakinta a lokacin da Momy bata dade da barin duniya ba, da ace kuma ya sake a lokacin da take raye Allah kadai ya san irin fushin da Momy zata yi da shi. Ya mike tsaye yana jin wani fever na rufe shi ya nufi motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna yana jiranta bakinciki cike fal a zuciyarsa.
Ya bata awa daya a haka sannan Aneesah ta fito ta bude motar ta ce masa.

 Big Bro wai Hajiya tace ka tafi zata kawo ta da kanta

 Toh ki fadawa Daddy haka idan na wuce

Cikin tsananin damuwa Kareem yake maganar sannan ya ja motarsa ya fice daga gidan. Wunin ranar aiki kawai yayi dan ya zame masa dole ba dan jikinsa da zuciyarsa suna cikin dadi ba. Bayan ya gama yana kokarin hada kayansa ya wuce wata mate room ta shigo ta kawo masa takardar envelope.

 Maman Khalid miye wannan

 Wallahi ban sani ba, wata ce ta zo dazun bata same ka tace bari ta ba ni na aje maka dan Allah kar na bawa kowa sai kai hand to hand

Ta fada cikin hausarta da bata gama kwarewa ba, kasancewarta bayarabiya. Ya karba fuska ba yabo ba fallasa yayi mata godiya ya hada kayan saukinsa ya fice daga office din. Sai da ya shiga motarsa sannan ya bude envelope din wani kamshi mai dadi ya bugi hancinsa, flower ce farkon abun da ya fara cirewa daga takardar sannan wani sexy chocolate da kuma farar takardar mai rubutu red. Be yi tsammanin ganin romantic abu irin wannan ba sai a Safeena kuma ya canka daidai a lokacin da ya fara karanta sakon na karin shekararsa a yau.

 Happy birthday Love, barka da zagayowar ranar haihuwar mutumen da bana son zama da kowa sai shi, barka da zagayowar ranar haihuwar mai bani farinciki a zuciya da jiki, mai kwantar da min da hankali, mutumen da ke nisantarsa ke haukata ni ta hana ni sukuni, barka da karin shekara My future husband, my partner in crime, the father of my future kids, father to be... I know its your birthday today.. I am sure u will give me treat in a big house like we use to be.. so I shall talk to you in person there, because I don't know to express my feelings in paper, i love you duk yadda kake tsammanin za mu iya rabuwa da junanmu ba zamu iya ba Kareem saboda muna son junanmu, ba zan iya kyaleka a irin wannan yanayin da kake da bukatar wani a kusa da kai ba, i know how painful it's to lost a best friend and Mother. Please take good care of yourself for me...

Ya girgiza after ya gama karantawa, so today is his birthday gaba daya ma ya manta, daman tun kamin su rabu tun tana girlfriend dinsa ita take tunawa da birthday sai kuma Momy, and even after break up bata daina wishing dinsa ba a duk lokacin da ranar zata zo. Wani gurin ya bude a motarsa ya saka takardar ya rufe ya yi ma motarsa key.

Kusan wannan ne karo na farko da yake jin kamar baya sha'awar komawa gidan all his thoughts is Yusura ta koma gidan by that time, hakan ne ya rike shi daga komawa da wuri domin samawa yaransa abun da za su ci da rana wani lokacin daga restaurant yake karbowa ya je musu da shi, wani sa'in kuma da kansa yake girkawa tare da su ko kuma kamin su dawo. He park his car near the entrance ya bude motar ya fito ya shiga falon. To his greatest surprised yaransa suke tarbe shi da wani irin farinciki da murna da ba su taba tarbonsa da shi ba.

 Dady welcome home, Dady Mamy ta dawo

Ya rage tsawonsa yana kallonsa da murmushin da ya ara ya yaba a fuska saboda yaransa.

 Kun jidadi?

 Eh sosai

Babbar ta fada sai ya shafa kanta, ba su taba tambayarsa ina Mamy su tafi ba, yaushe zata dawo me yasa bata gidan, tun da suka dawo daga school ba su same ta ba ba su sake walwala ba, kuma ba su tambaya ina take ba, kai ka ce sun fahimci sakinta aka yi, tun daga lokacin Kareem be sake kai su family house dinsa ba saboda gudun su ganta ko kuma su yi kuka idan zai dawo da su.

 I'm happy too

Ya fada yana kallonsu cike da alfahari, and he's not lie farincikin yaransa farincikinsa ne, hakan kuma ba yana nufin ya jidadin dawowar Yusura ba, idan har akwai abun da yake nadama a yanzu be wuce aurenta ba, me yasa be fadawa Momynsa gaskiya from first place ko da ba zata jidadin haka ba? Yanzu a wa gari ya waya, waye a matsala sama da shi?

 Kun ci abinci?

 Eh munci Mamy ta dafa mun ci, naka yana dinning Dady

 Okay bari na je na yi wanka na shirya sannan na zo na ci, ku je ku yi shirin islamiya

 Okay Dady

Karamin ya amsa, babbar kuma sai da ta sumbance shi sannan ta nufi sama da gudu tana murna. Tsaye yayi yana kallonsu har suka haye suka shige dakin Yusura sannan ya sauke ajiyar zuciya ya haura stairs din ya shiga dakinsa. Bayan yayi wanka ya kwanta a dakin yayi bachi awa daya ya farka, bandakin ya shiga yayi alwala ya fito ya saka ya sauya tufafin jikinsa daga kanana zuwa shadda sannan nufi madubi ya dauki dan'uwansa turare ta feshe jikinsa sannan ya dauki wayarsa ya wallet dinsa then car keys ya fice daga gidan gaba daya.

A hanya ya tsaya yayu sallah la'asar sannan ya karasa restaurant dinsa. Yana shigowa reception din Nabil da ya gama dutysa zai fita ya gaishe shi cike da girmamawa. Kareem ya mika masa hannu suka gaisa.

 Ka gama naka eh?

 Eh na gama ranka ya dade, daman duty safe nake yau, ko akwai abun da zan yi?

 No aa, ka ce ka daina karatu?

Ya gosa kansa cikin jin kunya ya amsa domin abun kunya ne wannan zamanin a kalli matashi kamar shi ace baya karatu a .

 Eh Wallahi, amman dai zan koma nan gaba idan Allah ya yarda

 Me ka taba karanta? Wane course?

 Mass Com na fara, amman dai ina son nan gaba idan zan koma na canja course

Kareem ya cigaba da tafiya yana fadin.

 Why baka son aikin jarida ne?

 Ina son, amman dai yanzu na fi sha'awar Public health

 Karatun health yanzu yayi yawa, why not ka yi political science? Karatun yana da kyau, kuma idan ka dace da gurin aiki kamin an ankaro ka dauke nauyin gidanku

 To da har ka kawo wannan shawarar da yardar Allah shi zan yi ranka ya dade

Kareem yayi murmushi yana jindadin yadda Nabill yake girmamashi.

 Na jidadin haka, ni kuma zan yi kokarin sama maka scholarship, a private ko kuma gov school, ban sani ba ko a samu a nan gida nigeria ko kuma a waje, fatan dai ba zaka ba ni kunya ba

Nabil ya rasa me zai ce ya rika hannun Kareem yana son masa godiya ya kasa domin be taba kawo wani zai dauki nauyin karatunsa ba, wanin ma kuma Kareem.

 Ranka ya dade, na rasa me zan ce ma

 Toh ka aje kalamanka sai idan an samu tukuna, sai ka yi godiya

Cewar Kareem yana dafa kafadarsa sannan ya wuce yana murmushi ya bar Nabil tsaye da mamaki. Be yi taku goma ba ya juyo ya kalli Nabil.

 Nabil ya Noor take?

Nabil ya hade yawun bakinsa da sauri ya matsa yana amsawa.

 Ta.. Tana lafiya ranka ya dade

 Ba wata damuwa babu wata matsala?

 Eh to tana dai cikin damuwa, mutuwarta nan ta dan taba ta gaskiya, domin ta canja gaba daya kamar ba ita ba

Kareem be ce komai ba, ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Office dinsa ya shiga sai da ya zauna sai kuma ya tashi yake yi yanzu a duk lokacin da ya shigo, da zarar ya kalli kujerar da Hafiz yake zama idan ya shigo office din da yamma sai ya ji babu dadi. Har yanzu ya gagara sabawa da rashin abokinsa wannan kawa zucin yana nan tare da shi, shi ke hana shi walwala a duk lokacin da ya shigo office din.

Be wuce minti ashirin a ciki ba, ya mike tsaye ya dauki keys dinsa ya fice da kansa ya shiga ya saka aka zuba masa abincin da yake sha'awar ci yaron gurin ya rika masa har gurin motarsa. Front seat ya bude aka zuba abinci sannan ya rufe ya shiga bangaren tuki yaja motar ya fice daga restaurant din gaba daya.

Tuki yake not knowing what to do or to go, shi dai gashi nan duniyar gaba daya ta ki ta yi masa dadi. Be faka ba sai da ya samu wasu itatuwa dake gefen hanya, ta cikin itatuwan ya ratsa ya faka motarsa sannan ya bude ya dauki abinci yana ci, gurin is so fresh ga wani iska mai dadi babu damuwa ko hayaniyar kowa it's just him and himself.




NOOR POV

A kwana a tashi babu wuya ga Allah, kamar jiya na fara wanka duk dai wasu sukance wankan be wajaba a kaina ba, saboda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login