Showing 9001 words to 12000 words out of 227321 words

Chapter 4 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1507

Amarya. Ban raina kaina ba sai da na zauna a kujerar da Yaya ya zauna, wani kalar laushi na ji da ban taba jin na zauna a makamancin abu na ji haka ba. Idanuwa suka ce me muka zo yi ba kallo ba, a nan na fara tantance komai na katon falon da ya kasance fari kamar yadda curtains din da labulaye suke, wata kalar wuta ce a rufin mai blue sai haskowa take.

A hankali na sauke idona gurin stairs da aka kawata kamar ba za a mutu ba, a nan na lura da kasan ba tile ba ne, ba kuma suminti ba, wani abu ne mai tsantsi da daukar ido aka malaya a gaba daya falon har zuwa inda muke zaune, ga wani zare zare da aka saka a ciki kamar maciji.

 Yaya Yaya Yaya

Na kira sunansa na taba shi ya nuna masa wutar sama dake blinking na nuna masa tv na nuna masa tile din sannan na matse hannuna ina masa rada.

 Ac ac ac, sanyi dadi, kujera laushi, kamshi ko'ina ko Yaya?

Da sauri ya kawar da fuskarsa yayi kamar be gan ni, can kuma ban san abun da zuciyarsa ta raya masa ba, sai ganin na yi ya mike tsaye ya kama hannuna na Mike tsaye muka nufi kofa ya bude kofar ya tura ni waje ya rufe. Ba dan ina da zuciya mai kyau ba Wallahi da na nuna masa tijara na koma ciki da karfi, daga zuwa gidan masu arziki sai wulakanci ta biyo baya, miye laifina dan na ga wani abu ya burge ni, ina ce ban taba gani ba sai yau. Kuma gidanmu ai ba ac nake ba fankar dakinmu ma ta lalace kullum a zafi muke bachi.

A raina na yi guntun tsaki, ina jin haushin yadda be bari na ga mutanen gidan ba, wata kila ma su kawo masa wani abu mai dadi ya ci shi kadai ko ma me ya zo yi a gidan oho, ta dayan bangaren kuma ina mamakin Ina Yaya ya san masu arziki haka. Entrance na nufa na tsaya a gurin na rumgume hannayena tare da gorar ruwan sa na yi guzuri, ina kallon kofar falon ko za a bude.

 Who's this?

Wani mutun ne tsaye a gefena rike da laptop a hannuna yana kallona.

 Noor...

Na amsa masa ina dauke kai irin dauke kan dake nuna fushi nake.

 Me kike yi a nan? Can i help you?

 No ina tare da wani ne

 Wani?

 Nabil

 Okay

Har ya wuce sai kuma ya dawo baya kadan ya kalleni.

 Me sa kika tsaya a waje? Ke budurwarsa ce?

Kallonsa nake jin yake yake kokarin kure hakurina da tambayoyi kamar wani dan jarida.

 Me yasa kake ta tambaya haka? Kai ne mai gidan nan ne ko kuma me?

Ya daga kasansa ya Kalli gidan, da alama dai shi ma bako ne domin yanayin kallon da yake ya nuna haka.

 Aa ni yaron mai gidan nan

 Daman ai baka yi kama da mai gidan ba

Ya dan bude ido ya daga gira kadan yana kallona.

 Haka ne, ke budurwar Nabil ce?

 Ni kanwarsa ce, mun fito daga wata Stupid Restaurant ne yace na rakoshi nan

 Stupid Restaurant?

Tambayata yake kamar mai mamaki shi ma dai da alama bakauye ne kamar ni.

 Eh mana idan ba Stupid Restaurant ba, ina za a siyar da abinci haka haka ba wai 5k

Na nuna masa kam akaifata, sai yayi murmushi ya kara juyowa da kyau kamar mai jindadin zancen.

 Abinci akwai tsada ne?

 Sosai ni zan iya cinye plate goma ma ban koshi ba, sai wani munafukin lemu da ake zubawa a cup, da ruwa ka ga ragowar ruwan nan na zo da shi, wai Yaya na jefar na Jefar ni kuwa na ki, har da wani cewa wai masu kudi ai kadan suke ci su koshi, masu kudi dan ba su san darajar naira ba za su je wannan gurin su ci abinci har na 5k wai kazar ma 10k ji fa? Saboda yan raina yan Nigeria, Mtseee

Na ja guntun tsaki.

 Amman da gaske ke za ki iya cinye abincin plate goma?

 Tsab kuwa

Ya kalleni daga kasa zuwa sama kamar mai auna idan zan iya ko ba zan iya ba.

 Haka nake ba kiba sai ci, hahaha

Na yi dariyar kunya kamin ya fara kokarin kare kaina.

 Wasa nake na koshi

Yayi murmushi mai sauti. Sannan ya miko min hannunsa daya.

 Nice to meet you....

 Noor...

Na fada masa, sannan na duba ko'ina na ga babu mai ganina na mika masa hannuna, daman can gaisawa da maza na daga cikin abun da yake matukar burgeni.

 Kai me ye sunanka?

 Kareem, you can call me Kareem

 Nice, nan gidan kake zama?

 Ba sosai ba, mai gidan be cika son ina zama ba

Ya amsa ni, ni kam ban yi mamakin amsar ba.

 Ai dole yayi wulakanci wadanda ba su kai shi kudi ba ma suna wulakanci balle mai wannan gidan, kana gani ka san mai kudi ne sosai

Na fada, sai ya sake daga kamshi yana kallon gidan.

 Not really yana da rufin asiri dai

 Ba wani rufin asiri yana da kudi sosai Wallahi, kai dan Allah wannan gidan be burge ka ba?

Yayi murmushi, a madadin ya amsa ni sai ya jefo min wata tambayar.

 Me yasa kika tsaya a waje? Da kin shiga ciki kin ga yadda cikin yake ai

 Na shiga fa, amman Yaya ya fito da ni kar na masa kauyanci

Be sake ce min komai ba ya nufi kofar ya bude, sai ya juyo ya kalleni yayi alama da na zo na shiga da kai. Abun nema ya samu haka na taka na nufi kofar na shige cikin falon, sai dai wani abun da ya daure min kai kuma ya ba ni mamaki shi ne mikewar da Yaya Nabil na yi zaton ko zai sake korani waje ne sai na ga ya risina yana mikawa mutumen dake baya gaisuwa.

 Ranka ya dade barka da yamma

 Nabil ya gida?

 Lafiya Kalau Oga, ban samu zuwa tare da Coworkers dina na duba ka dazun saboda ina can ciki gurin girki, shi ne na yanke shawara sai na tashi aiki sai na zo na gaishe ka

 Ka kyauta have a seat please

Ya nuna masa kujera sannan shi ma ya zauna, ni dai tsabar mamaki sai na tafi zan zauna a kasa saboda kunya da daurewar kai.

 Karki zauna a kasa mana, ga kujera

Ya nuna min kujerar da Yaya yake zaune. Sai Yaya ya bugu kafadata.

 Ki gaishe shi mana, oganmu ne, shi ne mai Restaurant din da muke aiki

Kulololo na ji cikina yayi wani kuka kamar na yunwa, har sai da ya kalleni hakan kuma be hana ni zubewa kasa na sabunta gaisuwata ba.

 Ina wuni

 Mun gaisa a waje ai, kin tuna? Tashi ki zauna

Na mike tsaye ina juyawa na kalli Yaya Nabil sai ya watsa min wani mugun kallo. Na yi saurin sauke idona kasa ina jin kamar na tsargi kaina.

 Toh ai Yaya baka fada min oganka ba ne, ao ya za'ayi na sani...

Na yi zaton a zuciyata nake maganar ashe ta fito ban sani ba, har sai da ogan da ban gama yarda shi ne mai gidan ba ya amsa ni.

 Toh me kika yi? You're just friendly that's

Da sauri na rufe bakina, wata sabuwar kunya na kara rufeni, kamin na daga kai ina kallon wata mata dake saukowa a stairs, babu wani walwala a tare da ita, shi ma kuma mai gidan na lura da yadda fuskarsa ya sauya daga murmushin da yake min zuwa hade fuska irin na mazan da basa son wasa.

 Nabil

 Hajiya ina wuni?

 Lafiya Kalau ya aiki?

 Alhamdullahi

Ni ma na gaishe ta sai ta amsa min fuska a sake, sai dai bata yarda ko gefen da mijinta yake ta kalla ba, shi ma kuma sai yayi kamar be san da wanzuwarta a cikin falon ba. Har ta nufi wata hanyar da nake kyautata zaton kitchen ne. Yaya Nabil ya mike tsaye ya kalleni ni ma sai na mike tsaye.

 Zamu wuce oga Allah kara lafiya yasa kaffara ne

 Ameen na gode

Ni dai ban ce komai ba, na bi bayan Yaya ina kallon kofar da matar ta shiga.

 Nabil

Yaya ya juyo da sauri yana kallon ogan nasa da ya kirashi.

 Ranka ya dade

 Ka koma da ita Restaurant ta zabi duk abun da take so, Noor sai an jima ko?

Ya karasa yana kallona da Murmushi a fuskarsa kamar ba shi ba, wani kyakkyawan murmushi na aika masa mai kayatarwa sa jan hankali saboda jindadin yace a ba ni duk abun da nake so.

 Amman... Okay Sir mun gode sosai Allah ya kara rufa asiri

 Thank You

Na fada in a low voice gudun kar matarsa ta ji ta fito tace zata min duka, domin na lura matan auren yanzu ba su da hankali akan mazanjesu sai su yi ma mace duka. Hannu ya dago min alamar bye bye sannan na juya muka cire tare da Yaya. Rufe kofar falon ke da wuya Yaya ya fara tambayata me na yi.

 Ban yi komai ba, amman Yaya baka lura ba? Kamar baya zaman lafiya da matarsa ko?

Yaya janyo hannuna da sauri muka sauko daga gurin.

 Wallahi ba dan wani abu ba, da sai na ce masa ina gyaran aure saboda na ci kudi, na ce masa ni mai bada shawarware ni akan aure.... Kuma yana da kyau ko Yaya? Wannan lukutar yarinyar yarsa ce? Matarsa ma kyakkyawa ce ko Yaya?

Muna tafiya ina fadar abun da ke zuciyata a iyakar gaskiyata.

 Ban sani ba, Noor Ban taba sanin baki da hankali ba, sai yau gidansa fa ko'ina camara ne har da wani fadar kina gyaran auren saboda baki da hankali, shiyasa kika nace sai kin biyo saboda ki zubar min da mutunci

Be sake hannuna ba sai da muka fito daga cikin gidan gaba daya. A raina ina ta ayyana irin takeaway da zan yi ma rabin raina Zafeer idan mun koma restaurant din...
https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx

''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -4


KAREEM POV.

After fitarsu, Yusura ta fito daga kitchen rike da cup din ruwa.

 Me za a girka anjima?

Daf da zata wuce shi tambaya. Ba tare da ya kalleta ba ya amsa.

 Ba a gida zan ci abincin dare ba

Ta daga kadunta alamar ko a jikinta sannan ya wuce ta haye sama.

Mike tsaye ya saka hannunsa daya a aljihu dayan kuma rike da wayarsa a hannu ya sake cewa daga falon ya nufi gurin da ya saba zama. Sai da ya isa gurin sannan ya amsa kira na biyu dake shigowa wayarsa.

 Hello

 Darling na yi missing dinka badly

 Toh ya muka iya, tun da mijinki ya ki barin gari? Sai hakuri

 Zamu iya haduwa ko yana gari...

Yayi murmushi ya shafa sajensa.

 aa kar dai mu shiga hakkinsa da yawa, kar zunubin ya mana yawa, kara idan baya gari wannan kina da Hujja

 Wata kila baka yi marmarina yadda na yi marmarinka ba ko?

 Na yi mana, amman dai kar mu wuce gona da iri, kin san ai yadda nake kaunarki

 Ko kirana baka yi Kareem

 Be kamata na kira ki idan mijinki yana gari ba, akwai abubuwan da na iyakancewa kaina aikatasu, Safeena dole muna hakuri da wani abun fa

 Kawai dai baka so na kamar yadda nake son ka shiyasa

Ya shafa kansa yayi murmushi.

 You're the love of my life, ke kadai kika na aikata wani aiki da zai ba ni zunubi mai yawa Safeena, ke kin sani idan bana sonki ba zan yarda wata mu'alama ta hada mu ba haka ne?

 Eh amman...

Sai kuma ta yi shiru kamar wadda ta rasa abin cewa.

 Yau na ga wata yarinya mai yanayi da ke, har ta fiki wauta da sakarci ma

Yana maganar yana murmushi.

 A ina ka ganta?

Ta tambaya daga dayan bangaren.

 Wani yarona na gurin aiki ne ya zo duba ni sai ta biyo shi, ina kallonta ke nake ta tunawa

Shiru ne ya biyo baya har na tsawon lokaci.

 Safeena...

Ya kira sunanta sai ta amsa masa da muryar dake nuna ta damu.

 No wait ba abun da kike tunani ba ne, ke kin cika kishi fa, ba yadda kike zato ba ne, babu wannan a zuciyata har abada ke kadai ce kwallin kwal...

Ta sauke ajiyar zuciyata.

 Duk ranar da ka so wata Kareem zan iya mutuwa

 Ba zaki mutu ba, saboda ba zan so ba, na san yadda kike da tsananin kishi ai, zan kiyaye

 Ina fatan haka

 Ina mijikinki yake?

 Yana daki, ni kuma ina harabar gida ne

 Ni ma ina harabar gidan, amman yanxu zan fita, je ki samu mijinki zamu yi magana anjima

 Okay i love you

 I love you too

Ya sauke wayar yana murmushi. Kana ya busar da iskar bakinsa ya sake shafa kansa ya sauko zuwa sajensa. Sannan ya juyo ya fito daga garden din ya nufo cikin gidan. Ganin kofar falon bude ya fahimtar da shi bako ya shigo gidan, domin daga shi har matarshi da yaransa biyu basa barin kofa a bude. Be karasa ba ya ji sautin kuka da kara mai razanarwa da muryar da be tantance ba. Hakan ya kasa shi cira kafa ya shiga falon da sauri. Yarinyar da ta fita dazun ya gani tsaye kusa da kofar rike da kai tana ihu, Yusura na tsaye gabanta rike da glass cup.

 Me ke faruwa a nan?

Yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri sai ta kara rushewa da kuka.

 Wai daga na shigo ina nemanka sai ta buga min cup din ruwa akai kalla har yayi jini

Ta nuna masa jinin hannunsa. Sai ya juya ya kalli Yusura.

 Why?

 Rashin kunya ta yi min

Ta ba shi amsa babu alamar wasa a fuskarka. Yarinyar ta girgiza kai da sauri.

 Wallahi karya take komai ban ce mata ba, kawai na shigo nace dan Allah ina mai gidan nan, mijinta shi ne kawai ta buga min cup a kai

Kareem ya juya ya kalli Yusura dake tsaye rike da cup din.

 Kishi kike?

 Kishi?

Ta maimaita tana ja baya tare da yin dariyar rainin wayo.

 Kishi dai kishi? Na rasa waye zan yi kishi sai kai? Allah ya tsare gatarina da saran shuka mtscheeeeeeee

Taja dogon tsaki ta juya ya bar musu gurin. Kareem ya kalli yarinyar da jini ke fita a goshinta yace

 Me yasa kika dawo?

 Yaya ya tafi abun shi, wai ba zai koma restaurant din ba, kuma zai buga waya ya fada musu karya nake kar a bani, yana ta min fada a hanya, kuma yace ba zan bishi gida ba sai dai kowa yayi tafiyarsa, shi ne ya saka a Napep yace ya kai ni gida, ni kuma sai da muka yi nisa sai na cewa mai napep din ya dawo da ni nan gidan amman ya biyo wata hanya da Yaya ba zai gani ba, kuma yana waje ban bashi kudi ba

 All this long story ban gane me kike nufi ba

 Ina nufin Yaya so yake na tafi gida ba tare da na karba kyautar da ka ba ni ba, kuma yace ba zai tafi da ni can din ba

Ya rike kunkurunsa yana murmushin da ya kusa zame masa dariya.

 Ammm ya ma sunanki?

 Noor sau uku kenan ina fada maka

 Yanzu ba zan sake mantawa ba, I'm sorry yanzu muje a duba kanki...

Ta juya tana rike da goshin ta fita daga falon, sai ya bi bayanta har sun saka entrance din sun isa gurin motarsa ya tuna keys dinsa basa aljihunsa.

 Noor jira ni a nan zan dauko keys dina

 Toh amman ka yi sauri kar ta fito

Yayi murmushi.

 Ba zata sake fitowa ba

Ya juya ya koma cikin falon, kai tsaye sama ya nufa ya shiga dakinsa ya dauko keys din, ya nufo curtains dinsa dake dage zai sauke kasa sai ya hango Noor tsaye a inda ya barta sai daga hannu take bakinta na motsi da alama masifa take, hakan ya saka shi saurin saukowa domin yayi tunanin ko Yusura ce tsaye jikin kofar falon, saboda ya hango kofar take kallo. Ga mamakin sai ga ita kadai ce take fadan tana kallon kofar falon. Sai da yaja kofar sannan ya nufi Motar ya bude sai da ya fara shiga sannan Noor ta shiga, yayi reverse ya fice gidan, tuki yake a hankali yana kallon yadda Noor ta natsu sam ba zaka ce tana da yawan magana ko kiriniya ba, babu wannan alamar a fuskarta da jikinta natsassiya ce sosai idan bata bude baki ba.



NOOR POV.

Shiga motar alfarma irin wadda ban taba shiga ba, ga wani sanyi ac mai dadi da laushi yana ratsa fatata ya saka natsu sosai ina jin yadda duniyar masu arziki take da dadi, sam na manta da ciwon da mahaukaciyar matar ogan su Yaya ta ji min a goshi har sai da muka isa wata babbar Asibiti, ni da nake zaton chemist zai kai ni domin ciwon ba wani babba ne ba. Fakawa yayi a gaban kofar emergency baya tsoron ma su masa fada.

 Za su maka fada basa bari a faka a nan 

Daf da zai fita na fada masa haka sai ya juyo ya kalleni yayi min murmushi, da alama dai murmushi al'adarsa ce, ko ba komai ai yana masa kyau. Wani abun da ya ba ni mamaki shi ne har muka shiga cikin asibitin gaishe shi ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login