Showing 66001 words to 69000 words out of 227321 words

Chapter 23 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1549



 Baki kishi ne?

Kamar jira take na yi mata tambayar sai hawayen da ke makalle a idonta suka zubo mata.

 Ina yi mana, musamman da na san ke din budurwa ce yanzu ne MiJina zai yi auren budurwar da saurayi, domin ni a bazawara ya aureni, Wallahi Noor Barrister mutumen kirki ne idan kika yi rasa shi kin yi babbar hasara...

Ta share hawayenta, ta dafa kafaduna duka biyu.

 Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa, damuwarki tana saka shi a cikin damuwa shiyasa ana dag da auren nan yake ta nanata min yana son ya janye, babu amfani kuka a public place kamar wannan, idan ma zaki yi ki bari sai kin kebanta kinji

Na daga mata kai daman tuni hawayen suka tsaya min saboda mamakinta. Kalamanta kuma sun karfafa min guiwa duk kuwa da kasancewar zuciyata bata yarda 100% mijinta mutumen kirki ba ne. Wata kila dai zagon kasa take min. Anyi kwalliya cikin nasara saboda na bada hadin kai, bayan an gama ta dauko min wani farin lace na saka rigar ta yi min yawa sosai saboda jikin nawa ba na irin sauran yan mata bana daman ni duk abun da na saka sai ya min yawa, ta saka na cire tufafin aka fita da su aka rage sannan aka dawo min da su na saka suka min cif. Kowa yabon kyau na yake a falon na kwalliya saboda yadda na yi kyau daurin dankwalin ma kansa abun kallo ne saboda yadda ya tsaru akaina. Gurin da muka boya dazun ta sake boya da ni ta kira mijinta facetime.

 Madam...

 Barrister ka iya zabi

 Da na zabo ki ko?

Ta kauce fuskarta ta kara masa tawa fuskarka. Natsuwa yayi na wasu dakiku ya dauke wuta yana kallon fuskata kamin yayi murmushi.

 Noor...

Na kalleta sai ta yi min alama da na amsa. Sai dai ban amsa din ba kuma ban mayar masa da murmushin ba.

 Please Smile

Ya fada yana cigaba da kallona, sai na lake masa kafada alamar ba zan yi ba. Sai na ga murmushin dake fuskarsa ya kara fadada.

 Noor kin yi kyau Maa Shaa Allah, Allah ya muku albarka ke da ita

Ban ce masa komai ba, amman a raina na amsa da ba Ameen ba domin bana bukatar addu'arsa.

 Madam...

Ya kira sunanta sai ta amsa ta yi facing dinsa.

 Ke ba a miki kwalliyar ba?

 Yanzu za a min an fara kwalliya wa a amaryar ka ne, na ce bari na nuna maka kamin masu hoto su daukar maka

 Kin kyauta Allah ya miki albarka

 Ameen sai ka dawo

Ta kashe wayar sannan ta kama hannuna muka fito. Sai da aka mata kwalliyar sannan muka wuce a tare zuwa gurin walimar da sun riga da sun shirya komai. Na yi mamakin da na samu dangin mahaifina da wasu daga dangin mahaifiyata har an dauko su an kawo su gurin. A guri na musamman aka zaunar da ni masu manyan wayoyi suka fara wani flash na wayarsu musamman dangin da nake kyautata zaton na Hafis ne ba kuma dan na san su ba sai dan ankon da na ga sun yi kala daya wasu kuma suna kama da shi sosai. Na ga kauna na ga soyayya na ga haba haba na ga marhabun daga dangin Hafix da kuma matarsa na yi mamakin yadda suke ririta ni kamar nice matarsa ta farko, kuma na yi mamakin yadda matarsa ta aje kishi a gefe ta mu'amalanceni kamar kanwarta ba kishiyarta ba.

Jikina yayi sanyi sosai na tsorota da yadda na same su. Sai bayan sallah Isha'i suka dawo da ni gida domin daga gurin Walimar gidan wata kanwarsa aka wuce da ni na huta na yi wanka aka min gyaran kai sannan suka dawo da ni gida. A gidan na tarar kowa sai yabon halin matar yake da yan'uwan Hafiz har wasu na cewa na dace, indai abun ya bi haka.













I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne. If you want to subscribe Pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

Or

6484787074
Khadeeja Candy
Moneypoint

And send the evidence of payment to 08036126660

See you>?p? ' #KhadeejaCandy

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Book 2 - Chapter 3*

Ni dai tsoro ya kamani zuciyata na raya min ko dai cewa aka yi a samo mai irin soffofina. Sam zuciyata bata natsu da wannan ba. Saboda haka na yi amfani da Hana na saka ta ari wayar Ya Nabil da sunan wata yi ma kawarta flashing ta kawo min.

 Noor Allah yasa ba wani abun zaki yi ba

Na karbi wayar ina dan turo baki.

 Ni me zan yi ba Hafix ne yace na ari wayar na kira shi ba, kuma kin san idan ni ce ba zai bani ba

 To kina da numbershi a kai ne

 Ina da shi a littafi dai

 Kin san halin Yaya dai dan ana bikinki ba zai hana yayi miki dukan tsiya ba, kuma dan Allah karki kira Zafeer

Na mata banza na tashi na dauko littafin na zauna a gafe daya kamar ina saka number alhalin number Kareem dake cikin wayar Yaya nake dauka. Sai da na gama na mika mata wayar

 Gashi na ma fasa kiran

Ta karba ta duba sashen kiran ta ga ban kira ba ta sake miko min.

 Ni ban hana ko kira ba amman karki kira Zafeer da wayar Yaya kin san abu mai sauki ya hada mu yayi mana duka, kuma kowa ya ji ya san baki yi daidai ba

 Ni fa ba Zafeer zan kira ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi magana da shi Wallahi ba shi zan kira ba, kuma ki bar shi zan ari wayar Gwaggo na kira da ita

Duk yadda ta so na karbi wayar sai na ki saboda sanin halin Yaya da na yi kamar yadda ta fada. Sai da ta fita azuwan mayar masa da wayar sannan na fito na tsaya daga jikin kofa na ari wayar Anty Larai domin ita ce mai lafiya a cikin yan'uwan mahaifina. Har ta ba ni na juya sai kuma ta kira na juyo bata ce min komai ba sai da na matsa kusa da ita.

 Noor Allah yasa dai ba tsohon saurayinki zaki kira ba?

 Wallahi ba shi zan kira ba Anty Larai ai Baba yace be yafe min ba idan na sake magana da shi

 Toh, na san ai kina da hankali ba kamar yadda suke fada ba tafi ciki ki yi wayar

Na shiga dakin na nufi littafin da na rubuta number Kareem jiki na kwashi number na saka a wayar Anty Larai sannan na fito daga dakin na faki idon mutane na shige bandaki na rufe sannan na aika masa da kira.




KAREEM POV.

Jikin Momy ne babu dadi kwana biyu, ciwon da take yawan fadar rayuwarta yake nema ya sake sallamo mata sai dai wannan zuwan be tsanannta kamar yadda yake tsanani idan aka bude file dinta ba. Tun daga ranar da take jin fever din yana zagoyo mata Yusura take ta zirga-zirga na zuwa dubata, idan ta gama abun da take Kareem zai wuce da ita ya sauke ta gidan Momy sai dare zai dauko ta. Kasancewar yau Jumma'a babu makarantar Allo da Yamma washe gari kuma Weekend ne babu boko sai ya kwasa har da yaransa suka tafi duba Momy, ba sabon abu ne ba a gurin yaran kusan ko wane yana kai su su wuni sai dare ya dawo da su domin Momy mace ce mai son yara kuma gidansa ma yana cike da yara a duk ranaku hutu na yayan da ta raina ta aurar ko na Abokiyar zamanta ko kuma na yan'uwana.

Kamar kullum yau ma sun tarar da jikokin dangi da kuma na kanwar Kareem dake aure a garin. Hakan kuma ba karamin dadi yayi ma yaransa ba domin suna fama da kadaici a gidansu da babu kowa sai kayan kallo. Yusura ta shiga dakin Momy da lullubinta da far'a tana yi mata ya jiki. Kareem ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana sauraren yadda take amsawa Yusura tana shi mata albarka.
Yusura ta kalli Mijinta fuska a sake kamar ba ita ba, ta ce.

 Abban Tine ba zaka matsa Momy ta koma asibitin nan ba? Yau kwana biyu jiki ya ki dadi fa

 Akwai wasu magani da muka dora ta akai, kin san ciwon ya kan taso wani lokacin kwana biyu sai ya tafi, to daga yau zuwa gobe dai idan ba a samu sauyi ba dole asibiti zamu koma

Ya fada ba tare da ya kalleta ba. Momy ta tashi zaune tana mika hannu ta dauko plate din zogalen da Khadija ta gyara mata.

 Ko zan koma asibiti ba ta garin nan zan zauna, ba zan sake fita wajen nan ba, na gaji da yawo nan na gaji da shan maganin nan, ko mutuwa ce dai kara na mutu cikin iyalina

Zancen mutu ya daga hankalin Yusura sosai a take idanuwanta da fuskarta suka sauya.

 Momy kullum baki da magana sai ta mutuwa, mu kike karyawa guiwa musamman da ba ni da gata sai ke a duniyar nan, cuta ai ba mutuwa ba ce

 Masu lafiyar ma tafiya suke balle kuma mu, kuma idan ka ga ciwo yaki ci ya ki cinye ko yana tafiya yana dawowa rayuwa yake nema, kuma karki sake fadin baki da gata a duniyar nan kina da gatan da ya wuce na mijinki? Ko bana raye Kareem ba sai bari ki yi kuka ba ina da wannan tabbacin

Yusura ta daga ta kalleshi shi ma ya kalleta kamin ta yi saurin kawar da kanta.

 Haka ne, Allah ya ba ni ikon cigaba da yi masa biyayya

 Ameen Allah ya miki albarka

Kareem ya sauke ajiyar zuciya sannan shi ma ya amsa da Ameen a addu'ar da Momy ta yi musu. Sannan ya kai hannunsa fuskar Momy yana fadin.

 Ba za ki tafi yanzu ba, sai nan da shekaru dari da hansin Momy na farincikina

Sanin hancinta zai taba ya saka ta buge hannun

 Wai Kareem ka mayar da ni abokiyar wasar ka, gaba daya ka mayar da ni wata kakarka

 Toh ya za'ayi babu kakar Momy ke ce makwafinsu, idan ban yi wasa da ke ba da waye zan yi a gurinki kadai nake samun farinciki

Yusura ta kalleshi tana Fake dariya kamar yadda ta saba idan suka shiga mutane musamman ace gidan Momy ne.

 Abban Tine ka ji tsoron Allah, idan kana fadin haka ai Hajiya sai ta dauka ko wahalar da kai ba ne bana baka kulawa

Kareem ya kalleta irin kallon da su kadai suka san manufarsa and then he smile.

 Duk farin da zaki ba ni ai be kai wanda Mahaifiya zata bawa danta ba

Momy ta aje plate din zogalen da spoon biyu kawai ta yi ta kama kunnen Kareem ta ja da karfi.

 Kai ne babba amman kullum idan ka gan ni sai ka maida kanka wani karamin yaro, ka maida ni kakarka Shiyasa Hajiya Na'eema take cewa ita kullum ganin take kamar ba ni na haife ka ba, gaba daya ka maida ni abokiyar wasar ka sai idan bana kusa

Yusura ta yi murmushi.

 Wannan kuma Momy wani abu ne da kuka saba yi tun kurciya, ko dai ko da na bude ido a gidan nan na yi wayo na san baki da abokin shawara abokin wasa kamar Kareem, Kareem kuma ba shi da abokiyar wasa irinki, yadda kuke mu'alama babu wanda zai zaci ke da shi uwa da a ne, kum fi kama da Yaya da kanwa ko Kaka da jikanta, kin fi shakuwa da Kareem fiye da sauran Yayanki, shi ma ya fi shakuwa da ke fiye da Daddy

Momy ta saki kunnensa tana murmushi.

 Ni kaina na kan yi mamaki yadda kunyar nan ma ta uwa da da Allah be dora min ba tsakanina da Kareem tun ana gulma har an gaji an saka mana ido, kuma kin ga yadda nake wasa da Kareem bana iya sake jiki na yi da Aryam haka shi ma da yake na biyu bana fari ba, wata kila hakan yana da nasaba da yadda yake da tsakanin tausayina da so na tun yana karami

Kareem ya mike tsaye yana murmushi.

 Haka Barrister Hafiz yake ce min wani lokacin, wai Momy ko dai tsinto ka ta yi, ki ji dan iska...

Duk suka yi dariya har Yusura.

 Allah ya tsare a dawo lafiya

Daf da zai fice Yusura ta yi masa addu'ar da bata saba yi masa ba idan suna gida, juyowa yayi ya kalleta ya san tana yin duk abun da take ne saboda suna a gaban Momy ne.

 Ameen

Ya juya ya fice. Be dawo gidan ba sai bayan Sallah Isha'i exact time din da ya zaba zuwa daukar Yusura. Babu fadan da be yi ba a lokacin da shiga falon ya samu Aryam da Khadija ga Yusura suna kallon Momy na cin gassashiyar kaza.

 Miye amfanin zamanku a nan toh? Kun san matsalar da take ciki ba, shiyasa ciwon ko ya tafi yake dawowa

 Doctor kamar baka san halin Momy ba, karamin abu ne ta fara fada idan muka hana ta cin abun da yake so

Cewar Aryam, Kareem ya tashi daga inda yake zaune ya karasa ya dauke plate din ya koma ya zauna.

 Wallahi ku bar ni na ci dadi na tun ina da rayuwa, kar sai na tafi ku yi ta nadama, musamman kai Kareem kana bakinciki ka ga ina cin nama ko wani abun dadi

Kareem yayi dariya ya tashi ya shiga kitchen ya wanke hannunsa ya fito ya dauki naman ya fara ci, taunawa yake a hankali zuciyarsa na wani gurin hana tuna masa da wani abun da ya wanzar da murmushi da nishadi a fuskarsa.

 Momy halinku yayi kama da Noor, da ace ban san iyeyenta ba sai na ce ke kika haife ta, yarinyar nan Allah yayi mata rigima

 Wace Noor?

Momy ta tambaya yana murmushi. Sai ya kalleni Momy kamar dai ya manta da Momy ce kadai a falon ba. Sai dai hakan kuma ba zai hana shi karasa mata labarin da shaukin Zuciya ya debe shi ya fara furtawa ba.

 Yarinyar da Hafix zai aura yanzu...

 Au Noor ne sunanta?

 Eh... Noor

Kusan sautin muryarsa da sautin shigowar kira a wayarsa a tare suka fita. Yarsa Tine ta zo da sauri ta ciro masa wayar daga aljihunsa ya amsa kiran ba tare da ya saka ta ba kuma ta saka hands-free saboda yayi masa sauki ganin ya bata hannayensa da maikon ferfesun kazar Momy da ya karbe. Ta matsa masa da wayar kusa da fuskarsa yana kallon bakuwar number ya furta.

 Hello

 Kareem... Noor ce....

Ta fashe masa da kuka, sai ya dago da sauri ya kalli Momy dake kallonsa ya kalli Aryam ya kalli Khadija ya Yusura ce ta karshe da ya kai dubansa a gareta kamar wani marar gaskiya gabansa sai bugawa yake da karfi.

 Kareem ni dai Wallahi bana son Hafiz din nan ko kadan ni dai ban taba jin ina son shi ba...

Yayi saurin aje naman dake hannunsa ya taba wayar da maikom ya cire hands-free din ya mike tsaye ya fice daga falon da sauri kamar zai hada da gudu. Harabar gidan ya fita sai ga ya juya ko'ina ya ga babu mai ganinsa sannan ya kara wayar a kunnensa.

 Noor me yasa kika kirani? Ina kika samu Number? Wayar waye?

Ta yi shiru.

 Wane zan fara amsawa?

Ya juya ya kalli kofar falon Momy dake bude sannan ya juyo ya kalli gate din ya sauke ajiyar zuciya.

 Me kike yi ma kuka?

Ta sake fashewa da kukan.

 Wallahi ni dai Allah ya gani bana son Hafiz din nan, kuma waya sani ko wani manufa yake da ita akaina ma? Duk kaine sila kuma

 Me ya faru me Hafiz din yayi?

 Matarshi ta yi min kirki da yawa ni abun ya ba ni tsoro shiyasa na kira na tambaya tsakani da Allah Hafiz mutumen kirki ne?

Ya kai hannunsa ya rike goshinsa.

 Noor idan Hafiz ba mutumen kirki ba ne, ai ba zai aure ki ba, ya fi ni zama mutumen kirki, matarsa kuma halinta ne ni ma tana kyautata idan na je gidan

 Na ji tsoro waya sani ko cewa aka a samo wata yarinya mai wadda ta rabu da saurayinta marar jiki fara mai saurin kuka ayi wani tsafin da ita? Taya za'ace mace bata kishin mijinta? Sai idan hada kai suka yi waya sani ko kudin da yake ta kashewa ni aka siye

Murmushi yayi ya lumshe ido.

 Babu wani hadin kai, Wallahi Hafiz mutunen Kirki ne mai nagarta ba shi da matsala, wayar waye wannan?

 Ta Gwaggo na ce

 Ina kika samu number na?

 Na sata a wayar Yaya Nabil

Ya bude idonsa ya daure fuska kamar ance masa tana gabansa.

 Okay daga yau sai yau karki sake kira number na, karki sake tambaya wani abu game d Hafiz ko wani dabam duk abun da kike son sani ki bincike shi, gargadi ne wannan na karshe, kuma zan fadawa Nabik kin kira ni shi ma kuma zan gargade shi

 Ai dole na kiraka kai ne ka yi ruwa ka yi tsaki ka kawo min abokinka ka raba ni da Zafeer, kuma yanzu kace na daina damuwa dole ne mu yi damuwa tare

Ya yanke kiran ya saka number a blacklist.

 Da gaske fa yarinyar nan bata da hankali...!!!

Yana rufe baki wani kiran ya shigo da wata number dabam ba wacan ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login