Showing 183001 words to 186000 words out of 227321 words

Chapter 62 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1539

ita, ni ce amaryar da Hafiz ya aura kamin ya rasu

 Ahhhhhh.... Ikon Allah da gaske

 Ka tambaye ta ka ji ta san Noor zata fada maka?

 Amman ke kin san ni mahaifin Aisha ne daman?

 Na sani yanzu saboda ta fada min, har abun da ban sani ba

 Khadija kar dai ace yarinyar ta zo ta miki cin mutunci ne

 Hmmmm sai anjima, ni dai na fada maka daman ina da wanda zan aura, Allah ya baka wata

Na kashe wayar ba tare da na saurari abun da zai sake fada ba, kamar zai haukace haka ya fara kiran wayata na ki na daga daga karshe ma sai na saka shi a blacklist.

Bayan saukowa daga salla magariba yaro ya shigo kirana, a lokacin ina daga kwance ina chatting da Kareem domin babu damar yin video Mama tana dakin.

 Je ka ce waye

 Mama ki ce kawai bana nan ba zai wuce Ustazun nan ba ya zo yayi ta takura min, kuma ai kin ce na daina tsayuwa da maza barkatai, ni da na sani ma ba zan fada masa kofar gidan nan ba

 Ai kya bari mu ji ko waye ko? Ke kin fi son maza yan duniya ko? Su sauran da suke kiranki a waya suna zuwa fada min kike ne?

Na yi shiru na cigaba da chatting din da nake ina murmushi, fada min yake irin rayuwar da zamu idan muka yi aure.

 Wai ya ce Zafeer ne...

Na dauke kaina daga screen din wayar na kalli Mama dake kallona.

 Zafeer kuma? Tohm...

Mama ta fada ni kuma sai na ce.

 Me zan masa?

 Ai sai ki je ki ko? Ki san dai Zafeer ya wuce wulakanci a gurinki, duk mutumen da zai so ka farko kuma ya sake dawowa ba karamin masoyinka ba ne

 Ba fa so nake ba Mama! Abu ne mai wahala Zafeer ya so ni yanzu, bayan duk abun da ya faru

 Ba sonki yake ba zai yi ta zuwa kofar gidanku ne? Ke ni bana son shashanci tashi ko tafi

Na aje wayar na dauki hijab dina na saka na fita da tunanin kalaman Mama, ni kam a nawa haukar da tunanin Zafeer ba zai sake kula mai irin sunana ba balle kuma ni fin kaina. Ashe na yi kuskure fahimta domin shi yana nufin maida hannu a miya ba. Ban tabbatar da sai bayan na gama kwance masa ciki na labarta masa halin da na tsinci kaina a duka auren da na yi, yayi min tambayoyi da dama kuma na amsa masa da gaskiya babu boye komai.

 Mutum kamar Abdull be kamata ace yana aiki a kamfanin nan ba 

 Ba lallai ne su sani ba ai, ni ma da be aikata hakan ba ba zan sani ba

 Haka ne, amman za su sani yanzu kamfanin na mahaifin Matata ne, ni da na taba aiki da shi a Lagos din na ga halinsa, yana shigewa mata sosai shiyasa na raya cewar ba zaki iya zama da shi ba, ko ba shi ba ma Noor babu wanda zai iya rike ki sai ni

Na daga ido na kalleshi sai kuma na sauke kai a sanyeyye. Ya gyara tsayuwarsa yana sauke numfashi.

 Noor na zo nan ne, saboda wani abu mai muhimmanci

 Wani abun ne ya faru?

 Babu abun da ya faru, a yanzu dai nake fatan faruwarsa tsakanina da ke, hausawa suka ce fa tsohuwar zuma ake magani kuma na yarda, domin na yi yadda zan yi na ga baki fili ki yi iya wasanki, amman na kasa saboda akwai wani abun da Allah yake nufin shiryawa a tsakaninmu, na so ki da farko na yi iya yadda zan iya na ganin na aureki amman ya gagara, amman har yau har gobe bana son kowa yadda nake son ki Noor, na ce zan jira kuma na jira, ina tunanin lokaci yayi da ya kamata ace mun zama ma'aurata ni da ke, burin da muka kasa cin ma a baya wata kila zamu iya cin masa a yanzu, a tsawon lokacin nan ina ta kallon tafiyar rayuwarki ne Noor babu wanda zai fahimce ki ko ya zauna da ke a yadda zan iya, daga Kareem din da yayi kokarin raba ni da ke, har zuwa wanda duk zai ganki ya aureki babu mai iya zama da ke sai ni Noor

Yana maganar jikina ya fara shocking hawaye suka cika idona, ashe ina da kima da daraja a gurin Zafeer har haka? Ashe soyayyata ta kai ya sake dawowa neman aurena duk bayan abun da ya faru?

 Baby Noor...

Na daga na kalleshi ta cikin hasken farin wata.

 Shim zaki iya aurena a yanzu? A yanzu na shirya ko gobe za a iya daura mana aure, zaki aure ni?

Kallonsa nake hawaye na sauko min.

 Ko kuma dai har yanzu wani ya rigani? A yanzu din ma wani zai min kutse kamar yadda aka min a baya? bayan na gina soyayyata? Har yanzu kina jin ba zan iya kula da ke ba Noor? Ina da kudi enough zan baki duk wani jindadi da kuma rayuwar da kike mafarki. Shin zaki aure ni?

Na girgiza masa kai na yi baya baya.

 Aa aa ba zan iya ba...

Na juya na shige gida ina hawaye a kofar dakin Mama na tsaya na dafe zuciyata har sai da na samu sa'ida sannan na shiga dakin ba tare da na share hawayen ba. Kan karamar kujerar da nake kwance a dazun na zauna.

 Lafiya?

Ta dauki fitilarta ta haska fuskata.

 Ba komai kike kuka?

Ban ce mata uffan ba na sakw fita dakin na yi alwala na dawo na gabatar da sallah Isha'i da aka gama tun 8:10pm, sannan na janyo wayata, ashe ban fita daga chatting din da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nake da Kareem ba, hoton tsayuwata da Zafeer na gani fitar da na yi dazun nan da magariba.

 Zan sake rasaki a karo na uku Noor, na sani indai Zafeer zai dawo ba zaki yarda ki aure ni ba

Shi ne sakon dake biye da hoton.

 Ba zan aure shi ba Kareem ba zan iya aurenshi ba

Na rubuta masa a matsayin amsa ashe har a fili na fada, ban hakara ba sai da Mama ta taba ni.

 Ke mi ya faru?

Na aje wayar na fuskanceta.

 Mama Zafeer sake dawowa wai yana son ya aure ni

Fuskar mamaki Mama ta yi ta zauna kan kujerar dake kusa da ni tana kallona ba tare da tace komai ba.





 Me yasa kika ce ba zaki iya aurensa ba? Saboda Kareem?

Na kalleta na yi zaton zata fahimci abun da na fahimta ne kamar ni, ashe fahimtarmu ta sha banban.

 Mama idan na yarda na aure shi a yanzu, zaman ba zai mana dadi ba, saboda zai rika kallona a matsayin macen da ta guje shi a lokacin da yake cikin talauci yanzu kuma na aure shi saboda yayi kudi, wannan uzurin Zafeer ya kasa yi min shi ko a can dama, ganin yake saboda ba shi da kudi na guje masa

 Toh ai ba karya ba ne, na sani da yana da kudi mahaifinki ba zai zabi Hafiz ya bar shi ba, bayan tsawon shekarun da kuka yi a tare

 Amman shi be fahimta ba, saboda Baba ya hana na yi masa magana ban fahimtar da shi

 Sai ki fahimtar da shi yanzu mana, Noor karki zama shashasha mana, yaron ya so ki kuma na san kina son shi, saboda rashin aurensa mahaifinki ya sake ni, babu irin yakin da ba mu yi ba ni da ke na ganin auren ya tabbata amman hakan be samu ba, yanzu kuma bayan aure biyu ya dawo yana son ya aure ki ki amsa da cewar ba zaki iya aurensa ba, anya ba ki ji kunya ba?

 Ji nake kamar...

 Kamar me? Ki rika yi ma kanki fatan alheri, ni dai na san kina son Zafeer kuma ina da tabbacin zai rike ki amana sosai, domin yaro ne mai kirki kuma mai tsananin sonki, kuma mun san iyayensa tarbiyarsa da komai ba mu da haufi a kai, ba ina son ki aure shi saboda yana da kudi ba, aa sai dan ina hango miki jindadi irin na mai hankali d sanin ya kamata

Na sauke idona kasa hawaye nake for no reason.

 Ni dai idan har zaki yarda da ni da kuma abun da nake so, to ki auri Zafeer

 Mama Kareem...

 Kina son Zafeer yadda kike son k
Kareem?

Na girgiza kai ko kadan ba za a hada soyayyar da nake yi ma Zafeer da wadda nake yi ma Kareem ba.

 Ko kuma kina da tabbacin Kareem din zai rike ki amana? Bana fatan ki sake aure ki fito Noor, shi ma Kareem din ba natsentse ba ne, kina masa kallon mutumen kirki ne kawai amman ba haka yake a zuciyarsa ba, domin mutumen kirki ba zai yi tarayya da matar aure ba har ta kai ga haihuwa, shiyasa kullum yana shiga cikin lamarin gidanmu yana kyautata mana, na yi zaton sonki yake da farko, amman bayan aurenki na farko da na biyu na gane so yake ya bata miki lokaci ko rayuwa

Na kalli Mama da sauri ina mamakin a gurin da ta ji wannan maganar.

 Mama a ina kika ji wannan? Kazafi ake masa Kareem mutumen kirki ne

Na yi hanzarin dora ginin da zai tare zubewar mutuncin Kareem a idon Mama, na san duk abun da ta ji ko aka fada masa a kansa gaskiya, but i know yana da kirki kuma ya fahimci kuskurensa, ba zan taba iya tona masa asiri ba, ba zan iya kara masa bakinciki bayan wanda yake ciki ba, mutumcinsa yana da muhimmanci a gurin Iyayensa kanensa da Yayansa.

 Ke yarinya ce Noor baki san komai akan rayuwar duniya da mutanen cikinta ba, har yanzu baki gama wayewa ba, baki da zurfin tunani da fahimtar rayuwa

 Waya fada miki wannan Mama?

 Safeena, kishiyarki kuma abokiyar shedancinsa, har hotunansu ta nuna min wani gurin tana kwance a jikinsa, ita ma yaudararta yayi kamar yadda yake son ya yaudareki, abu ne da kika sani, domin ta fada min kin fadawa mijinta an da ta haifa yanzu ba jininsa ba ne kuma mijinta yayi bincike ya gane gaskiyar hakan har ya dauke kafarsa daga gidan yanzu hana tace kayanta a hade suke domin ta san zai iya bata takardar saki a duk lokacin da ya tashi

Na hade yawu da karfi na sauke kaina kasa a yanzu kam ba ni da wani kuzarin furta wani abu, amman yaushe Safeena ta zo nan? Yaushe ta fadawa Mama haka.? Kamar Mama ta san abun da nake tunani sai na ji ta ce

 Ranar da kika tafi ganinsa Asibiti ita ma ta fito asibitin daga ganinsa ba, ta fada min ta ganki, saboda haka ki kwantar da hankalinki ki daina biyewa Kareem ko da ba aure ba ni bana son alakarku, idan har Zafeer da gaske yake ko kuma mutanen da suke zuwa zance gurinki da gaske suke kawai su fito ayi auren a huta, ki samu gurin da kika zauna kowa ya samu kwanciyar hankali

 Tohm Mama

Babu wani abun da zan iya fada, kalamaina ba su isa su kare aikin da Kareem ya aikata ba, da ace be kusanci Zina ba tun farko da abubuwa ba zu masa a haka ba. Na sani idan Mama ta san na amsa masa cewar zan rike yaron da suka haifa ma zai kara sakawa ta tsani Kareem din ko ta rufe ni da duka ma. But deep down i feel something about ina jin tausayinsa fiye da yadda na ji tausayin kaina a lokacin da aka raba ni da Zafeer.

Tun a wannan daren na san ba zan auri Kareem ba domin Mama bata yi maraba da shi ba, kuma tana da gaskiya kowa yana son suruki na gari, kowa yana fatan yarsa ta yi aure a inda za'aji dadi babu fargaba. Na raye daren da sallah da kuma rokon Allah ya bawa Kareem lafiya, ina jin kamar ba zan iya rama masa abun da yayi min ba a ko'ina sai ta nan. Washe gari misalin karfe takwas Aisha ta fado family house din su Mama da zan iya kira da gidanmu a yanzu, ita da kanenta biyu da wata macen da ban san ta ba.

Bangaren mu aka kawota har kofar dakinmu domin ta fada musu ni take nema, ko ya aka yi ta gane gidanmu ma oho, ni dai na sha mamakin ganinta har na rasa taya zan tarbiya, duk kuwa da na san ba lallai ne alheri ya kawo ta ba, bayan abun da na fadawa mahaifinta ta aikata akan karya. Dan haka ban yi gaggawar yi mata maraba ba na daga kai kawai ina kallonta kamar wadda bata wayeta ba. Mama dake hada tea ta mike tsaye ta fito daga dakin tana kallonsu.

 Toh Allah yasa Lafiya

 Lafiya amman ba kalau ba

Kanwar ta amsa, Aisha kuma ta juyo ta kalli Saitin da nake zaune tana cin magani ta ce

 Noor ashe wuyanki yayi kauri, ashe kin zama tantiyar yar bariki Kareem ya lakawa Hafiz kin kashe shi da bakinciki, domin na san tunanin abun da kika masa ne ya saka shi hatsari, kika maida ni bazawar karfi da yaji kika maida yarana marayu duk hakan be miki ba sai kin kulla soyayya da ubana? So kike yi ki karashe shi ma? Kuma ki shirya masa karya

Na mike tsaye ina murmushi.

 Na yi kishi da ya na ji yadda ake ji, shiyasa yanzu nake son na yi kishi da uwarta, kuma dole ace da mijin Iya Baba

 Karya kike Wallahi, kin yi kadan ke a su wa? Har abada ba zaki taba wannan matsayin ba Wallahi, kuma ubana matansa hudu cif ba shi da gurin saka ki

 Zaki gani idan zan yi matsayin ko akasin haka, mata hudu kuma ba matsala ta ba ne, uwargidan zai fitar ya saka ni, kuma da kike zance na saka ki a zawarci ai kin saba zawarci domin Hafiz ba budurwar ya aureki ba, shiyasa kika yi duk yadda zaki yi dan ki hana mu zaman lafiya saboda kar ya san banbancin dake tsakanin auren budurwar da kuma bazawara, ni ba ni na ga mahaifinki na ce ina so ba, ubanki ne ya ga abun da yayi masa ya biyo sawu kamar yadda mijinki ya biyo

Farat kanwar ta yi ta fado dakin ta rufe ni da duka sai Aisha da dayar kanwarta da matar da suke tare suka fado suma suka fara min duka sai ihu nake ina maida martani a duk inda na samu, abun da ban sani ba ashe Mama ma tana nan tana min yaki a waje dukansu take ta ko'ina, wata cousin dita yar sister Mama ma ta shiga aka yi ta fafatawa da ita, sai da manyan gida suka ankara aka kawo mana dauki aka raba fadan. Kawu ya rufe Mama da fada wai madadin ta raba sai ta shiga ana yi da ita.

 Yaya ta ina zan tsaya su kashe min ita? Daga ita sai Nabil suke rage min, ina zan yarda su yi mata illa su bar ni da jinya da hannu a kai, kana ganinsu manyan mata da su sun fi karfinta ta ina zan tsaya raba su?

Mama na fadan tana rika ni da duba hannuna da suka kusa karyawa.

 Wai ke ina kika janyo wadannan mutanen? Ke dai Noor Allah yayi ki da rashin jin magana Wallahi, ya aka yi suka san gidan nan kuma su waye su?

Kawu ya rufe ni fada shi ma kamar zai min duka. Mama ta ce

 Aisha ce fa da kanenta Aisha matar margayi Hafiz

Kawu ya rike baki, Mama Asiya ma mamaki ya shaki wuyanta.

 Ai ni ban gane ta ba, ya aka yi ta san gidan nan kuma me ya kawo ta? Ina ce mai rabawa ta raba? To miye na duka kuma?

Mama ta fada musu komai kamar yadda na fada matan tun farkon fara zuwan Alhaji Sule unguwa uku a gidan. Kawu ya nuna ni da tsaya hannunsa na rawa kamar zai dakeni

 Ke yanzu ina ke ina tsoho? Ina ke ina kishi da uwarta? Ashe ke ce marar gaskiyar ma, kina girma hauka na shiga kanki? Ai duk abun da suka miki ke kika ja

 Kawu ba fa ni na janyo shi ba, shi ya tare ni a hanya ya karbi number wayata kuma ban san mahaifinta ba ne sai daga baya, kuma Wallahi na yi blocking number shi ma

Na fada cikin kuka Mama na ja min hannun. Sai bayan da komai ya laba sannan na dauki wayata na cire number shi daga blacklist na fita daga gidan gaba daya na shiga makota na kira wayarsa, ringing daya ya daga sai na fashe masa da kuka sosai.

 Ni ban ce ka je ka fadawa uwargidanka abun da yarka ta fada min ba, shiyasa na ce ba zan aureka ba saboda gidanka ya fi karfinka

Yayi shiru irin na manya masu nazari, ina jin haka sai na kashe wayar. Ga ayi second biyu ba kiransa ya shigo na ki na daga, sai da ya sake kira sannan na daga na kara fashewa da kuka.

 Me ya faru Khadija?

 Matakar ta aiko yarka Aisha da kanenta biyu sun zo har gida sun min duka, ni Mamana har Aisha na fadar wai ba Mamansu ta ce a fada min ba zaka taba aurena ba matanka hudu baka da gurin jefani, wai kuma so nake na koya maka zaman banza domin ba ta inda zaka aure ni daman na san ba aurena zaka yi, gashi ma ashe gidanka sun fi karfinka akan me uwargidanka zata aiko ayi min duka? Mi miye nawa a ciki? Ai kai ka gan ni kace kana so na ko?

 Khadija

Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login