Showing 162001 words to 165000 words out of 227321 words

Chapter 55 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1524

da mu ba, jin cewar bata sonsa kuma ba sabu abu ba ne na fahimta tun a zuwana na farko gidan, kamin shi kansa Kareem din ya fada min yadda aka yi auren a wacan ranar da ya fada min sirrinsa.

 To yanzu yaran fa?

 Suna hannunta, idan Kareem yana son ganinsu zai zo ya gansu ne sai ya koma, shi kadai yake rayuwa a gidan yanzu, yana cikin kadaici da ban tausayi sosai, gashi ya rasa yarinyar da ya so ya aura, abun ba dadi, ni ba zan iya biyayyar da Kareem yayi ba, ba zan iya auren macen da bana so ba, auren kiyayya ba shi da dadi shiyasa Yayana yake matukar ba ni tausayi, yana da zuciya da hallaya masu kyau, amman har yanzu be samu farinciki ba

Tausayinsa ya kama ni sosai domin na san yadda rayuwa da wanda baka so take, na gwada na san yadda ake ji.

 Kin san me yasa nake baki labarin nan?

Na amsa masa da alamar ban sani ba.

 I want you to be his best friend, domin yanzu ba shi da abokin shawara ya rasa Hafiz, ya rasa mahaifiya ni kuma tawa safgar nake dabam, na lura da wani abu yayana yana samun farinciki idan kuna tare ko yana zancenki, please idan kin ganshi a cikin damuwa ki yi kokarin cire shi, kuma ki yi iya yadda zaki iya ki ga ya auri wacce yake so take ba shi farinciki yana cikin damuwa sosai...

Aaryam yana maganar ina kallon Kareem dake tsaye hannayensa zube a aljihu yana jiran karasowarmu.

 Kin min alkawari zaki saka shi ya auri wacce yake so? Shi ma ya samu farinciki kamar kowa? Farincikinsa shi ne na mu, and don't tell anyone mun yi maganar nan

Ban iya amsa masa da eh ko aa ba har muka isa gurin da Kareem yake shi kadai yana kallonmu. Da dan zargi yake kallon kanensa sai Aaryam ya daga masa hannu ba tare da ya ce komai ba ya wuce cikin asibiti. Sai da na daina hango shi sannan na juyo na kalli Kareem.

 Me ya fada miki?

 Yadda akan samu Hana

Na amsa kai tsaye.

 Come on karki wasa da ni mana, na san ki fa

Na yi murmushi.

 Ba ka ce ba zaka zo ba?

 Na ji kamar hakan da na fada be miki dadi ba, shiyasa kika yanke wayar maybe you want to see me huh?

Ya daga min gira sai na yi murmushi

 I miss you, i just wanna say thank you, ban taba haduwa da wani mutum mai karamci da sanin ya kamata da kawaici da son farinciki ba sai Kareem, ba alakar uwa ba ta uba amman komai nake so kana yi min, people like you a rare, kai mutumen kirki ne, kai mutum ne mai damuwa da damuwar wani, Allah ya faranta maka ya baka abun da kake nema Kareem

Yayi murmushi mai kyau ya daga kansa yana kallon saman kaina domin yana tsaye ne a matakar dake bawa mutum damar hawa ward din dake cike da mutane, ni kuma ina kasa daman ya fi ni tsayi balle ya hau akan abu.

 Kalamanki sun lashi zuciyata, a duk lokacin da kike bukatar wani abu, ko wani ya taba ki just come to me zan miki duk abin da kike so, if you ever need safe just come to me

 Da me zan saka maka Kareem?

Yayi dariya mai dadin sauraro.

 Thank you, just let me be right beside you in anything you do

Ya fada yana lumshe ido.

Na yi murmushi ina kallon mutane fake ta kai da kawo.

 Mu je ciki ki ganta

Muka jera muna tafiya sai kamshi yake mai kwantar da hankali.

 Kareem

 Uhm mmn

 Ina Yusura?

Ya tsaya cak ya daina tafiyar da yake ya kalleni. Zai yi magana wani mutum ya ba shi hannu suka gaisa, after ya gaisa da shi ya juyo ya kalleni.

 Ina wannan ya fito kuma?

 Kawai ka amsa min mana

 Tana gida family house dinmu, ba ma tare yanzu

 I'm happy for both of you, rayuwa da wanda baka so ba shi da dadi

Ya sauke gutun numfashi.

 Haka ne, rayuwa mutum shi kadai ma bata da dadi, amman dai da sannu zan saba

 Ai ba haka zaka zauna ba, zaka yi aure kai ma ka auri wanda kake so take sonka

 Ba zan taba wani auren ba Noor, yarinya daya nake so kuma na rasa ta, shi ke nan, ba zan sake son wata ba

 Maybe zaka iya son wata, ita ma ai baka san zaka sota ba sai daga baya ko?

 No tun farko haduwa da wannan yarinyar na ji wani akanta, amman ban fahimta sai daga baya, kuma yanzu na yi latti I'm not the one she mean to find, every thing keep us apart, amman ni na san ina kaunarta sosai, i love her so much

Ban san miyasa ba, na dan ji babu dadi da yace yana kaunarta sosai.

 Amman ka yi sanyi ne da baka same ta ba? Kai din nan babu wanda zata ce bata sonka

 Na je ne a makare, wani ya riga ni shiga zuciyarta, kuma ita dai tana jin ban mata ba zata iya aurena ba, har yanzu bata da wayo bata gama fahimtar duniya ba, amman dai zan jira har lokacin da zata yi hankali ta natsu ta fahimce ni, maybe we can rewrite the start...

Na masa duba mai cike da tambayoyi, na ji wani bangare na zuciyata na raya min ko dai da ni yake.?

 Ya sunanta ma?

 Sunanta Hafsat

 Ta yi aure ai ka ce ko?

 Eh

 To tace maka zata fito ne da ka ce zaka jira ta?

 No, tana gidan mijinta har yanzu

Ya bude min kofar dakin yana kallon cikin idanuwa.

 Noor

Kiran da Hana ta yi min ya saka na dauke idona daga kallon Kareem na kalleta, na shiga dakin da farinciki da murna da jindadi sosai ta ji rauni a kai da kai da kuma hannu har an saka mata bandeje an daure. Na rumgume sai ta fashe da kuka sosai.

 Inna a ba su guri su tattauna mana, Aaryam mu tafi ko?

Ina jin lokacin da Kareem yake fadar haka, ban dago ba sai da suka fice gaba daya daga dakin har kanwar Mama.

 Dan Allah ki yi hakuri, da na sani ba zan je na zauna a gidanki ba Wallahi

 Ba laifinki ba ne, halinsa ne daman da ace ba halinsa ba ne ba zai fara ba, ke ya kamata na bawa hakuri na janyo ki a jiki gashi sanadina kin cutu, kuma ban fahimce ki ba sai da kika tafi

 Haka Allah ya tsara min, ban isa na wuce wannan ba, arziki na ma daya an cire cikin

Na dafata.

 An cire? Waya cire? Yaushe?

 Tun a ranar da na dawo yayi min allurar amman sai jiya ya dauke ni ya kai ni wani gida wata nurse ta wanke min marata yace an cire komai?

Farinciki ya lullube ni.

 Amman ta sani amman?

 Eh ta sani, tare muka je da ita yace a bar maganar ne ba sai an fadawa kowa ba, kanensa ma be sani ba

Na sake rumgume ta ina jin kamar Kareem na rumgume tsabar farinciki.

 Amman Kareem din nan son ki yake yi ko Noor?

Na dago daga jikinta

 Aa be taba nuna min ba, be taba fada min ba

 Kyautatawar da yake miki ta wuce misali

 Wata kila saboda ina matar abokinsa ne, kuma yana da tausayi ke ma kin ba shi tausayi shiyasa ya saka aka cire cikin

Na sauke kanta kasa hawaye suka sake idonta.

 Na yi nufin kashe kaina, lokacin da na bar gidanki, ba ni da gurin tafiya, kuma ba zan iya koma gida ba, da kaina na tara kaina a titi mota ta bugu ni, amman ban mutu ba sai na ji ciwo a hannu da kafa da kai, mutumen be tsaya kai ni asibiti ba ya gudu, sai mutane ne suka taimaka min suka kai ni, su ma suna kai ni suka gudu, asibitin kuma suka ce ba za su taba ni ba, sai da dansa kuma sai an siye kati, a gurin aka bar ni wulakance, sai da wahala ta yi min yawa na kunna wayar na ga sakonki, da kuma wani sakon ta wata number yace min shi Aaryam ne idan ina bukatar taimako na fada masa, a madadin na kira ki sai na kira shi, da muka yi magana sai yace kar na kira ki, shi yasa aka dauko ni daga can aka kawo ni Kano. Abdull ba zai gama lafiya ba, kuma na jidadi da baki samu a da shi ba Noor, ni kadai na san me nake ji a raina, kuma shi kenan ya sha a free babu abun da za a masa

 Saboda gudun abun da zai biyo ba ne, Mama ta ce idan wani ya ji ba za a aure ki ba, kuma zai zama abun magana a cikin unguwarmu, amman ki kaiwa Allah kararsa zai saka miki

 Kullum sai na fadawa Allah, ina masa Allaj ya isa, amman wannan abun ba zai taba gogewa ba

Turo kofar dakin da aka yi ne ya saka ta yi saurin share hawayenta ni ma na share nawa. Zainab ce take fadar na tashi mu tafi dare yayi, Mama Talatu ma ta dawo dakin sai na yi mata sallama sannan muka tafi. A napep ma Zainab ta tambaye ni kwatankwacen abun da Hana ta tambaye ni cewa wai Kareem so na yake.

 Be taba fada min ba

 Amman ke baki lura ba, ji yadda yake kallonki fa, kuma yana ta yi min tambayoyi a kanki

 Amman ni be taba cewa yana so na ba, kuma yana ma da wacce yake so sunanta Hafsatu

 Ikon Allah, toh amman dai abun da mamaki wata kila jini ne ya hadu ko kuma ya riga ya fara sonta ne ba yadda zai yi da ke

 Tun kamin ya hadu da ita fa, muke tare ai da ya fada min, kuma ni bana ma son shi

Na yamutsa fuska tunawa da na yi da wani abu. Zainab ta gwalo ido.

 Saboda me?

 Haka nan dai

 Tab Wallahi baki san abun da kike so ba, kamar wannan zaki ce baki son shi? Mutum mai kyau mai kudi mai komai, ko ni za'ayi aurena a watan nan Wallahi yace yana so na zan iya balle auren na aure shi

Na kalleta da mamaki sai kuma na ji haushinta na fadar hakan fa ta yi ban sake cewa komai ba har muka sauka Napep din. Komai ya zamar mana kamar labari, ni na danne ciwon zuciyata Hana ma ta danne nata mun barwa Allah komai muka koma cigaba da rayuwa kamar yadda muka saba, a bayan. Sai wani shakuwa da kaunarnan junanmu da tausayi ya kara shigarmu, Mama kuma tana ta rayuwa a gidan aurenta ba tare da wani tashin hankali ba.


Abun da ya faru da Hana muka haka kasa muka rufe ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai ita sai kuma Mama da Kareem da kuma uban gayyar da yayi aikin.
Ranar da Baba ya saka ni gaba da tambayar dalilin da ya saka Abdull ya daina zuwa gidan na fada masa ya sake ni ne, Baba tsine min ne kawai be yi ba, amman duk wani kalar zagi na duniyar nan sai da yayi min shi. Musamman da na yi masa karyar cewar kawai bana son sa ne ni na bukaci ya sake ni, kuma da ya bincika sai Abdull ya tabbatar masa da cewar ba fada ba zagi kawai na bukaci sakin ne shi kuma ya aiwatar.

Har kusan korata Baba yayi sai da yan'uwansa suka saka baki, Umma ma sai ta koma tana jin haushina domin tallafin da yake bata na sana'ar da Hana bata mata a yanzu ya janye ya daina yi. Sai tace wai bakinciki nake mata saboda ita din ba uwata ba ce, kuma hassada ta bata tsaya kaina ba har da yar'uwata nake yi ma. Ni da Hana ba ma ce mata komai domin mun san abun da bata sani ba.

Hana ta samu sallama a yanzu da bata fita siyar da awara domin Mama tana ta shirye shiryen sakata wata makarantar ne a nan garin Kano, hakan ya saka hankalinta ya dan kwanta, kuma wani abun Allah samari da masu mata sai kawo mata hari suke a yanzu. Sai dai ni ban tsira daga maganar mutane unguwa ba, ganin na yi arba'in amman ban koma gidan mijina ba, ba mutanen unguwar kawai ba har cikin family na ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
samu masu jefa min magana wai na ki zaman aure, Mama ta fada cewar wasu daga familyta sun ce haka za a zuba min ida ina aure ina fitowa na ki zaman aure.

Na kan yi murmushi kawai na bar maganar a bayan kunnena, domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyi, dadi dai ba zai saka mace ta kashe aurenta ta fito domin ta zauna a gidansu ba, ko kuma ta raba a wani guri, ba ni kadai ba mata da yawa al'umma basa musu uzuri, macen bata sakin kanta bata rike kanta amman ba a fahimtar haka, a koda yaushe mutuwar aure yana komawa a bangaren mace idan afku. Ba zan ina cikin jindadi ba, domin zaman gidan ba shi da dadi agaremu. Amman jiki ya dan bude haihuwa ta kara min kyau ta cike min gurbin kasusuwan da na nake da su a wuya, ba wani jiki na yi can sosai ba amman dai jikin ya bude na cika na zama mace.

Bayan bikin Zainab na je gidanta na wuni a can muka sha hira sosai na ji abubuwa da yawa da mutanen unguwa suke fada, wasu su ce hakkin Zafeer ne, wannan kam ba zan yi mamaki ba idan aka ce hakkinsa ne, domin ya cutu, wasu kuma suka ce TA KI ZAMAN AURE, har da masu cewa wai Zafeer asiri yayi min ba zan taba iya zaman aure ba, wasu kuma su ce ina da aljannu ne kawai da basa son aure. Na yi dariya sosai na danne ciwon dake zuciyata na bar sirrina a cikin raina. Ta rakoni bakin kofar gidanta ta koma ni kuma na haka hanya gyale na a kafada, kaina ya sha dauri fuska kuma ta dauki ido kamar wata budurwar kai wata budurwar ma albarka domin gyaran da nake yi a yanzu bana yinsa a lokacin da nake budurwa.

Ina kokarin tare mai Napep wani dattijo ya faka gabana, ya sauke gilashin motar yana kallona fuskarsa da murmushi.

 Ina zuwa?

Na waiga na kalli bayana na kalleshi na yi zaton ko da wata yake magana ba ni ba domin ba yaro ba ne zai haifi kamata da wanda ta fi ni sau goma ma.

 Baba ni?

Na nuna kaina, yayi dariya.

 Yan mata kenan, shigo na rage miki hanya

 Aa na gode

 Ba zaki shigo ba? To saka min number ki a nan

Ya miko min wayarsa.

 Amman lafiya

 Lafiya Kalau Wallahi, kawai na ga ruwan dake min wanka ne, saka min number ki yarinya

Na karbi wayar na saka masa number na, sai ya miko min kudi.

 Rike wannan ki hau napep

Na karba na masa godiya, sai ya wuce na bi matarsa da kallo ina dariya, to ko dai ya ga na yi masa kama da tsofi ne ya tare ni haka har da wani ruwan dake masa wanka, tsab kuwa zan masa wankan kwashe kudi na kara gaba domin ba zan iya da kayan majina ba. Allah ya tsare ni. Na tofar da yawu.
Ina yin gaba kadan wata motar ta faka shi ma dai sauke gilashin yayi yana min magana.

 Hajiya ina zuwa haka?

Na dan taba fuska, yau dai wata kila aljannu sun shafa min maganin farinjini a fuska ko kuma kwaliyar da na yi ce ta dauki hankalin mazan oho.

 Gida

Na amsa sai kawai na ga ya bude motarsa ya zagayo ya bude min front seat.

 Ki min alfarma motana ta samu lada, na sauke ki gida Hajiya, karki ce aa

Ta ina zan ce aa bayan yace kar na musu, shi din ma be yi kama da wanda za a musa masa ba. Na samu kaina da bin umarninsa duk kuwa da na san ba mutuncina ba ne, na zauna a motar ya rufe ya zagaya ya shiga ya tashi motar.

 Sunana Salees

 Noor

 Thank you

Ya fada ba tare da ya kalleni ba, ni kuwa sai satar kallonsa nake baki ne mai dogon hanci ga yalwataccen gashin gemu da zaje gwanin sha'awa.

 A ina unguwar take?

Na fada masa, har lokacin be kalleni ba sai da muka shiga cikin unguwar, nesa da gidanmu na ce ya sauke ni.

 Baki son na ga gidanku ne?

 Ba kasafai ake kawo ni da mota ba, mutane za su iya wani zaton, kuma Baba baya son haka

Ya juya ya kalleni first eye contact da muka yi gabana ya buga da karfi.

 Hakan yana da kyau, tarbiya ce amman da kika san Babanki baya so sai ki kiyaye, abu na biyu ki daina saka veil idan zaki fita, hijab ya fi mutunci, idan kina sha'awar veil ki saka babba wanda zai suturta ki, kina da kyau na zan maza da yawa sun fada miki haka, so ki suturta kyaunki ga wanda yake halalinki haka Allah ya fada

 Na gode zan kiyaye

 Idan kin min izini zan tsaya daga nan har na ga shigarki, saboda zan dawo ko kuma ki saka min number wayarki

Ya miko min wayarsa na karba na saka masa numberta sai ya kira ni.

 Ki yi saving

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login