Showing 132001 words to 135000 words out of 227321 words

Chapter 45 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1535

dai minene mahaifiyata ta fitar da ni daga kunyar kayan kitchen sauran na daki da ban saka ran Baba zai yi min ba.

Ni da Umma muna duka kayan domin a lokacin Hana bata gidan tana gurin talla, sai da na gama duba komai sannan ta rika min na kai su dakinmu, ita kuma ta saka hijab dinta ta yi shirin tafiya ba tare da ta sha ruwa ba balle har ta tsaya cin abincin da yanzu ake girkawa, babu wani far'a a fuskarta na san kuma hakan baya rasa nasaba da yadda suke kallon Baba a matsayin ma ci amana kuma marar mutunci a yanzu, daman Mama Jamila ta fi kowa daukar zafi ko a lokacin da Mama take aure Baba balle kuma yanzu da babu alaka sai ta yaya.

Bakin titi na rakata tana ta yi min gargadi na zauna lafiya gidan mijina na san waye mahaifina kuma na san yadda zaman gidan yake a yanzu, har tana addu'ar ita ma Hana Allah ya kawo mata na gari ta yi aurenta ta guta wannan wahala da takaici na gidan uba. Sai da ta shiga Napep din sannan na juyo na nufo gida, ina tafiya na ji karar mota bayana matsawa na yi gefe domin ba mai motar hanya. Kamar haka yake nema sai ya wuce ni ya isa kofar gidamu ya faka, tun kamin ya fito motar zuciyata ya raya min Kareem ne domin motarsa ce gashi kuma ya faka a kofar gidanmu.


Me ya kawo shi? Wanda ya ce mun yi bankwana tun a kwanan baya? Ko dai ya ji ba zai iya jurewa ba ne sai ya gan ni shiyasa ya dawo ko kuma wata matsalar ce? Ta a yanzu da ya rage sauran sati daya a daura mana aure da Abdull. Na fi kyautata zaton matsalar domin ba kasafai Kareem yake zuwa gidanmu da rana ba, kuma bana tunanin marmarin ganina kawai zai kawo shi a gidan ana sauran kwana bakwai na zama matar wani. Wani tunanin aka jefo min na Safeena da alakarsu da kuma fadan da muka yi jiya da ita.

Na karasa gurin na tsaya ina kallonsa ba tare da tsoro ko fargabar wani ya gan ni tare da shi ba a yanxu da zan yi aure na biyu, domin ba alakar soyayya ce tsakaninmu ba balle ace na kula wani, haka kuma Abdull baya garin nan a yanzu ya kuma tabbatar min ba zai dawo ba sai ana gobe daurin aurenmu. Matsalata daya ce kar Baba ya ce zai yi masa fada ko yayi min idan ya tararda mu a tare.

Ko da yake Kareem din mai gidan ansa ne kuma mai yawan yi masa kyautar kudi mai kyautata masa, wata kila hakan ya saka ya daga masa kafa ya ji kunyar yi masa wani abun na cin mutunci ko cin fuska. Sai a lokacin ya rufe motar Motarsa da yake rike da gambun yana kallona har na iso.


https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0


PAID PAGE 2?? 0??


??KhadeejaCandy
????Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______" " " _______

Rumgume hannayena na yi ina kallonsa with my innocent face.

 Besty how are you?

Ya tambaya yana daga kai ya kalli harabar unguwar.

 I'm good and you?

Ya daga gira not happy not sad.

 I'm not fine

Na dan matsa kusa da shi.

 Me ya same ka?

Sauke kai yayi kasa sannan ya ce.

 Bestyna kamar kin taba fada min sunan wanda zaki aura ko?

 Eh Abdull

Ya dago ya kalleni.

 Yana da mata kika ce idan ban mata ba

 Eh da yara uku matarsa ya haihu na hudu

Ina jin sautin hade yawunsa.

 Amman kin taba ganin matarsa?

Na dan kawar da ido daga kallonsa sannan na amsa.

 Eh na taba ganinta ya nuna min hotonta

Ya langwashe halshensa.

 Kin san sunanta?

 Safeena your ex-

Murmushi yayi ya jinjina kai yana juya idanuwansa like na bashi mamaki sosai, kamin ya kalleni.

 Kin san duk wannan kuma kika yarda zaki auri Abdull?

 Ba mutumen kirki ba ne?

 Ban san komai a kansa ba, amman na san komai akan Safeena, ba zaki iya kishi da yarinyar nan ba, she's criminal

Na dan tabe baki.

 Bana jin zata yi kishina, ai kai take so kuma kai take kishi, me zai saka ta yi kishin mutumen da bata so indai har da gaske bata son shi

 Mijinta ne uban yayanta taya ba zata ji kishi ba, kuma ni ban taba fada miki cewar bata son shi ba, taya zata ki mutumen da shi ya tsamota daga ruwa a lokacin da na jefata?

Na daga kafaduna not knowing what to say yanzu kuma. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da murya ya ce.

 Noor me kika fadawa Safeena?

Na kalleshi da sauri daman na san za a zo gurin.

 Me tace na fada mata?

 Sirrin da na yi dake ta zo ta fada min duk abun da kuka yi, saboda me zaki nuna mata cewar kin san abun da yake tsakaninmu

Na ciro wayata daga aljihun rigata na nuna masa sakon da ta turo min, kamin wani abu ya tsikare ni kamar zan yi fada na fara magana.

 Ganin na yi tana neman daga min hankali tun kamin na shiga, ni kuma ba na yi aure ne saboda na je na fito ba, bana son aurena ya sake rabuwa sai idan mutuwa ta raba

 Amman sai ki yi amfani da wata hanyar ba wannan ba, ke yarinya ce, baki gama fahimtar duniya ta mutanen cikinta ba, ba ki san illar abun da kika ba sai bayan ki aikata

 Ba ni da wani weapon na yakarta sai wannan

 Amman wannan sirrina ne, na fada miki ne saboda na yarda dake and i need someone to talk to, taya zaki aikata abun da zai iya janyo matsala ya janyo miki?

Zan yi magana ya daga min hannu ya nuna min yatsa.

 Look Noor ina da yara, mahaifina yana raye ina da yan'uwa da abokaina, ko kadan bana son abun da zai zubar min da mutunci, na fada miki damuwata ne saboda na yarda dake, kuma ina jin kusanci da zuciyata, ba dan ki bayyana ma duniya ba, na san na aikata abun a lokacin da idanuwa suka rufe shekaru suka tsirewa tunani, and now i realize na yi wa kaina babbar barna and i regret it, you shouldn't discuss this with anyone!!

Ya bude motarsa ya shiga ya bar ni a tsaye ina kallonsa hawaye na sauko min, domin be taba rufe da fada irin na yau ba. Har yayi baya sai kuma yayi gaba ya faka a inda ya faka dazun ya sake bude motar ya fito ya tsaya kusa da ni.

 I'm sorry, Na san na kaurara amman Noor ban ji dadin abun da kika yi ba, wannan sirrina ne, be kamata kowa ya ji ba 

 Bana hira da kowa, ban taba fadawa kowa ba, kuma ita wanda ta ji daman ai ita abun ya shafa

Na bashi amsa cikin sautin kuka. Idonsa ya sauke kasa yana sake fuskarsa.

 Bana nufin sakaki kuka ko kara miki damuwa akan wanda kike ciki, amman ni abun da kika aikata yanzu zai daga min hankali ya saka ni a damuwa, waya sani ko zaki sake fadawa wani? Kuma Safeena ba zata zura miki ido hakan nan kawai ki cigaba da rayuwa a free ba, bayan kin san sirrinta, ni da ita duk muna da iyali, ki rika duba wannan kamin ki aikatawa wani abun Noor

Na share hawayena.

 Ta je ta bata ni gurinka ko?

Ya rufe ido yana murmushi sai dai hakan be hana ni fahimtar damuwar dake shimfide a fuskarsa ba. Bude ido yayi yana min magana a hankali.

 Bata iya wannan, babu wanda zai iya wannan ma, just be careful yanzu Safaeena tana kiyayya dake ta kofa uku ne, Allah ya tsareki kuma ya baki zaman lafiya, amman Bestyna Noor ina son ki sani ko mutuwa na yi bana son na tafi na barwa ?a?ana abun kunya

 Ni ma ba zan so haka ba, kuma na maka alkawari daga wannan ba zan kara ba, kuma babu wanda zai ji

Yayi tattausan murmushi da ya kara masa kyau.

 Thank You, Allah ya tabbatar miki da alheri

 Ameen

Ya sake Bude motarsa zai shiga.

 Shikenan tafiya zaka yi?

Ya juyo

 Ko kina da bukatar wani abun ne?

Na girgiza kai.

 I will miss you alot

Yayi murmushi ya sauka kansa.

 Akwai abun da kike bukata na auren Noor? Akwai abun da Baba be miki ba?

Na girgiza masa kai alamar aa. A ganina kamar be kamata na dora masa nauyin komai ba, kuma ai da kunya na bukaci kayan daki a gurinsa, domin su ne kawai nake saka ran Baba ba zai yi min ba, shi ma kuma ba ni da tabbaci.

 An yi komai

Yayi murmushin dake nuna kamar be aminta da ni ba.

 Sai wata rana

Wannan karon be sake kallona ba ya shiga motarsa yayi mata key ina tsaye ina kallonsa har na daina hango shi. Wata kila shi kam ba zai yi marmarina ba kamar yadda anke jin kewarsa tun a yanzu, ba mu wani dade a tare ba amman shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da shi.
Bayan tafiyarsa ne fahimci na yi katobara na bayyana ma Safeena na san komai a tsakaninsu ba dan ita ba, sai dan shi wata kila hakan zai iya haifar masa da matsala, sai dai iya abun da na sani shi ne, Safeena ba zata yarda asirinta ya tonu ba, domin tana da aure da yara kamar yadda ya fada, ni kuma ba zan sake tattaunawa da kowa akan matsalar ba.

Hakan da na yi ya saka na samu yanci gurin Safeena, mijinta ma ya samu kwanciyar hankali domin ana sauran kwana biyu a daura aure nake tambayarsa ya Safeena sai yake cin yanzu ai ta fahimci, tashin hankalinta ba zai hana aurenmu ba ta shafa masa lafiya. A raina na ce ko dai ta fahimci Ni din ba kanwar lasa ba ce ta bawa kanta lafiya da ni.

A daren ne yayi ta damuna da maganganu da be sana yi min ba, hakan kuma ya raunata yarda ta ya haifar min da tsoro akansa, sai dai na lura shi kam sam baya kunyar fadar haka, wata kila saboda ya taba auren ne, ko kuma yayi zaton a aurena na farko na san komai kamar shi. A yadda na lura Abdull irin mutanen nan masu masara kunyar ido da furta komai a take. Ni dai bana iya cewa komai idan ya jefeni da wani kalamin, na kan ji kaina yayi girma kunya ta rufe ni.

Washe gari gidanmu ya cika da yan'uwa mahaifina wadanda suka zo shirye shiryen abubuwan da za'ayi, ta hirar da Baba yake da su ne na ji yana fadar mai gidan Nabil wato Kareem yana da kirki da mutumci sosai.

 Yanzu bayan daukar nauyin karatun yaron nan da yayi, auren nan da za'ayi sai da ya same ni a majalisa ya damka min kudi mai yawa wai na kara na yi hidima, Allah dai yayi masa albarka ya yara masa yaransa, wutar nan ma da ta taso tsakanina da yan'uwan Hafizu shi ya kashe ta

 Ai wasu masu gida haka suke da taimako da kirki, musamman idan sun san baka da shi, wasu kuma suna bakincikin abun da zaka samu ma

Cewar Baba Garba.

 Haka ne, ni farko ma na dauka shi zai ce yana son Noor ne, kuma na ga kamar ba haka ba ne, ai ba dan kar ta ba ni kunya irin na wacan karon ba, Wallahi da sai na aura masa ita saboda kunyar abun da yake min, ya rike amanar abota

Jin hakan a gurin Baba ya saka na ji Kareem ya kara kima a idona, tabbas shi din mutumen kirki mai son taimako, babu ruwansa da duba matsayi ko girma. Haka dai na yi ta jin suna ta hirarsu ta yan'uwa yana fadin mutanen da suka taimaka masa a yanzu da kuma aurena na farko. A lokacin da suka dauko zancen abubuwan da zai kai na ji Baba Garba yana tambayar Baba.

 Toh yanzu kai Magaji ka siyo mata kayan dakin ne?

 Ni babu abun da na siya kuma babu abun da zan siya, ai ya fada mana da zarar an daura aure za su wuce can Lagos din da ita, to taya za a tsaya wani siyen kaya nan tun da nan za su zauna ba? Dubu hansin zan bashi a cikin kudin sadakinta idan sun je can ya siya mata abun da ya kamata

Anty Larai ta ce

 Aa gaskiya be dace ka yi haka ba, ai ana son ka siyama yarka girma, ko dai ba mai tsada ba kowa ya san karfi ba daya ba, sai ka mata na iya karfinka saboda Allah magaji

 To wai me za'a siya ma? Uwarta ta aiko mata da kaya, kuma ba a nan za su zauna ba, ai kayan sun isheta komai

 Kayan da ta aiko mata kayan kitchen ne, kai kuma naka kayan daki ne da dan wani abu da za aka bawa ango

 Aa aa aa karya haram ba zan iya kashe kaina ba, yarinya suka ce suna so ita za a ba su, ita da Allah yayi jininta jinin masu kudi me zai kai ni wahalar da kai na siye wasu kayan daki? Hafizu ma Allah ya masa rahama da kansa yace ba zai na yi komai ba ya dauke min komai

 Toh shi wannan ai be ce ba, gaskiy...

Bata karasa ba Baba ta tari numfashinta.

 Ni fa dan abun da na samu, gyaran gidana zan yi na kuna kallon yadda gidan nan gaba daya ya canja babu wani taimako da na samu, sauran kuma sai na bude shago na zuba kayan masarufi

Jin cewar Baba ba zai yi min furniture ba ya disashe farinciki dake zuciyata, wata kila shi din ba kamar Hafiz ba ne da zai ce ya yafe komai, hakan kuma wani abun gori ne a gurina da danginsa da ma kishiyata. A ranar aka yi min kunshi mai kyau mai ja sosai, da dare kuma Hana da kawata Zainab suka raka ni na tafi gurin gyaran gashi domin ni ba mace ce ma'abociyar son kitso ba. A nan na samu damar fada musu damuwata, Hana ta nuna damuwata da jin cewar Baba ba zai siya min komai ba har ma take cewa.

 Yanzu da ace Mama bata aiko da wannan ba haka za'a kai ki ko spoon din aiki ba ki da shi?

Na sake jin babu dadi domin Baba baya kyautata min a rayuwa, wasu hakokan da ya kamata uba ya saukewa yarsa shi baya sauke min su.

 Noor kar hakan ya daga miki hankali, Baba ya fadi gaskiya idan ba nan za su zauna ba, babu amfanin siyen kaya, daukar kaya daga Kano zuwa Lagos wani aiki ne babba, kuma kin ga yace ba a nan za su tare ba

Zainab ta shiga kwantar min da hankali, na dube ta na ce.

 Amman wasu ko ba a garin za su zauna ba, ana yi komai Zainab a garin da miji yake, saboda can aiki yake yi ai, wata rana zai iya dawowa mahaifarsa

 Ki gode Allah Noor, idan mijinki mai sonki ne duk ba zai ga wannan ba, kuma zai rike ki amana, idan ma Baba bai miki ba ke zaki iya yi ma kanki ko kuma shi mijinki yayi miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki Noor

Duk yadda zata karfafa min guiwa sai da ta yi har ta yi nasarar kwantar min da hankali na dan sake raina. A napep muke ta labarin Zafeer da sabon auren da aka ce yayi a gurinta nake jin labarin irin hidimar da aka yi na bikin auren domin Zainab tana abota da kanwar Zafeer sosai, shi ma kuma yana good time da ita ko a lokacin da muka samu matsala ita yake aikowa gurina.

 Amman kin ga yana dariya?

Na tambaya ina jin bakinciki marar misaltuwa kamar ba ni na fara guje masa.

 To zai ki dariya ne Noor? Ai dole yayi farinciki ko yaya ne, wata kila ma yanzu ya manta da soyayyarki, domin yar masu kudi ya aura ance mahaifinsa ma shi zai sama masa aiki, daman ita yarinyar tana aikinta, ance ta girme shi da shekara uku

 Allah ya saka masa tun ba ayi nisa ba, ya samu wadda ta fi ni komai

Na fada hawaye na sauko min, Zainab ta dube ni.

 Noor har yanzu kina son Zafeer wai?

 Unconditionally, har abada zuciyata ba zata daina son Zafeer ba, ba zan taba son kowa kamar yadda na so shi ba

Shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa Uffan daga ni har su. Har muka isa gida hawaye nake, haka na shiga gida rai babu dadi zuciya na kuna, kiran da Abdull yayi ta min ma kasa dagwa na yi saboda damuwar data haifar min da ciwon kai.
Washe gari ya Friday gidanmu ya cika da makota da yan'uwa na kusa da nesa maza da mata, kusan wannan bikin ma kamar ya fi wacan yawan jama'a.

Bayan saukowa daga Massallaci na fita waje na yi alwala na shigo dakinmu kenan wayata ta yi kara, dubarwa da zan yi sai na yi arba da number Abdull, a take na amsa kiran na kara wayar a kunnena.

 Hello...

 Congratulations an daura aurenmu, Alhamdullahi

Gabana ya fadi har sai da kaina ya sara, kai kace ban tsammaci zuwan wannan ranar ba.

 Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login