Showing 114001 words to 117000 words out of 227321 words

Chapter 39 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1529

sake ni, sai dai zancen da ya fi karfi shi ne na yin zaman takaba domin akwai gyara a auren kuma ban kai ga cika idda ba ne ya rasu. A ranar da na yi wata hudu da kwana goma Mama ta aiko da waina da fanke aka raba sadaka yan'uwanta suka zo tare da yan'uwan Baba aka saka ni na yi wanka na saka sabuwar atamfar, a ranar kuma mutuwar Hafiz ta dawo min sabuwa kai kace mun yi shekara aru aru da shi ba yan watanni ba, sai dai abun da ya daure min kai shi ne na rashin zuwan dangi ko yan'uwansa a gurin tun a ranar da na dawo gida har zuwa yau babu wanda ya leko ni ko ya bincika lafiyata, abincin da ake cewa dangin miji ma suna kawowa matarsa idan tana takama basu kawo min ba. Wata kila Aisha ta shafa min bakin fenti a idonsu domin na lura har bayan mutuwar Hafiz kishi take da ni.

Bayan sallah Isha'i, a lokacin da kowa ya watse, ina zaune ina gyara wake soya Yaya ya shigo cikin gidan da kuzarinsa ya ce.

 Noor oga Kareem ne a waje yace na kira ki

Na yi shiru na wasu dakiku sannan na mike tsaye kamin na cira kafa na ji Umma ta tabe baki tana fadin.

 Wannan ai ba mutunci ba ne, ace ana maka sallama ka mike kai tsaye ka fice ba tare da tunanin fadawa mahaifi ba, kai ma ai ba ita ya kamata ka samu kai tsaye ka fada mata ba mahaifinku ya kamata ka fadawa

 Ba kisan waye oga Kareem ba Umma, oganmu ne na gurin aiki kuma abokin mijinta nw Hafiz ya saba zuwa nan akai akai

Ya Nabil ya bata amsa.

 Tohm Allah ya kyauta, tashi ki tafi, amman gaskiya idan haka mahaifiyarku ta koya muku ba abun kirki ba ne, ai sai uba ya aminta ake fita domin shi yake aurar da yarinya

A kam ban iya rike kaina ba sai da na mayar mata da martani.

 Baki san komai akan uwarmu ba, karki sake fadin wata mummunar kalma akanta

Kallona ta yi ta dauke kai bata ce komai ba, ta cigaba da dakan yajin da take. Ni kuma na shiga ciki na dauko hijab dina na saka na fito kofar gidanmu. Sai na same shi a gurin da suka saba tsayuwa shi da Hafiz idan sun zo, ko kuma idan ya zo shi kadai.

Ganinsa ya tuna min da Hafiz sosai sai zuciyata ta yi min babu dadi, shi kuma na lura baya cikin walwala da farinciki, gashi ya rame kamar ni yayi hudu haskensa ya rage. Gambun motar dake bude ya rufe sannan ya jingina da motar yana kallona kamar wanda be taba gani na ba.

 Noor how are you now?

Tambayar yake ya nake, amman sai na ji kamar yace na fada masa damuwata ta hanyar kukana. Kawai sai na fara hawaye ina kallonsa, i miss him i miss his friend i miss my previous life.

 Kina cikin damuwa ko?

Na daga mishi kai, sai na ji ya sauke ajiyar zuciya.

 Duk yadda kike tsammanin abun ya wuce nan Noor, na fi ki shiga damuwa yanzu, i loss hope, kawai ina rayuwa da kokarin tsayawa saboda Yayana, a yanzu babu wani daki da zan iya rufe kaina na ji sanyi, duka dakunan zafi ne da su kamar wuta

Na share hawayena.

 Da zan iya komawa na gyara rayuwata ta a baya...

Na ji ya fada sai kuma yayi shiru be cigaba ba. Ni kuma na kalleshi na ce.

 Da ka goge shafina a rayuwarka

Ya girgiza min kai.

 Ba zan iya goge ki a rayuwata ba Noor ko da kuwa ace ina da wannan damar, ba ki min komai ba, babu dalilin da zai saka na natsane ki, you're just innocent, precious soul, and Hafiz was right akan abubuwa da yawa akanki

 toh me zaka gyara?

Yayi murmushi ya gyara tsayuwarsa.

 Ba wannan ya kawo ni, na zo nan ne saboda na yi magana da ke da kuma Baba, amman kamin nan fada min ya kike?

 Ina lafiya, amman mutuwa bata da dadi Kareem, shiyasa lokacin da Hafiz ya fada min mahaifiyarka ta rasu, na yi kuka sosai na tausaya maka yanzu kuma na ji yadda ake ji

Murmushi yayi ya daga kansa sama sai kuma ya sake kallona.

 Noor... Kamin na manta, na zo nan ne saboda maganar gadonki da kuma kayan dakinki

Na cigaba da kallonsa ina sauraren abun da yake fada.

 Noor dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen Hafiz akan gado ko wani abu, sun ce baki da gado kanensa ya kira ya fada min kuma na je na same su na yi musu magana na fahimtar da su, amman ba su yarda ba, iyakar hujjarsu wai Hafiz ya sake ki kamin ya rasu, kuma kamin ya sake ki wai be taba tarayya dake ba haka ne?

A nan na sauke kaina kasa na dan bata rai.

 Aisha ta bata ni a gurin kowa, kuma ita ce silar duk faruwar haka

 Babu wanda zai iya bata ki a gurina, kuma mutuwar aure abu ne da Allah ya kaddara, kuma ba dan Allah ya rubuta haka ba, na yi magana da Hafiz kuma yayi alkawarin yana dawowa zai zo ya dauke ki ku tafi gidan tare, sai dai kamin ya iso Allah yayi ikonsa

 Da gaske?

Ya daga min kai.

 Yes Noor na lura kina cikin damuwa a lokacin kuma kin fada min kina son komawa ai, babu wani abun da zaki roka ban miki shi ba Noor sai idan ba zan iya ba

 Na dauka ina takura maka ne, na ga har baka son zuwana gurinka, na san ni ina da takura ai

Yayi murmushi.

 To ki yi hakuri, idan Baba yana ciki shiga ki masa magana

 Baya nan yana majalisa

 Shiga ciki zan je can na same shi, ki kwantar da hankalinki Allah zai baki abun da ba su ba ki ba, kayan dakin ma sun ce ba za su baki ba ai saboda shi yayi komai

 Ni fa ba abun da ya dame ni da wani gado, su je su yi ta riko, amman ka yi magana da Baba shi ne dai na ji yana zancen zai yi kara idan ba a bada ba

 Okay

Kallona yake har na shige cikin gidan, ina shigowa Ya Nabil ya fita waje.


Duk wata maganar da zai yi da Baba na san ba zai saurare shi, amman kudi za su iya sakawa ya fahimci komai kuma ya sassauto. Da alaka kuma Kareem yayi amfani da su ne domin babu ya shigo da far'a har da tsarabar nama yayi ma Umma. Cewa yake a yanzu ya hakura zai kyalesu amman saboda Kareem be kawai ba dan haka ba da babu abun da zai hana shi jan min hakkina. Yanka biyu aka ba mu, sai da muka cinye sannan yayi mana albishir wai Kareem ya fada masa ya nemawa Ya Nabil karanta a Sudan. Farinciki ya cika ni a lokacin da Baba yake fada min Kareem yana neman izininsa idan ya aminta sai ya fadawa Ya Nabil din ya kai masa takardunsa na SSCE.

Sanin da na yi ba karamin dadi Ya Nabil zai ji ba, ya saka ni farincikin da na kwana biyu ban yi ba. Hakan kuma ya karantar da ni cewar Kareem yana da kirki ta wani bangaren, domin gashi ya danne kudirin mahaifina kuma yana kokarin nemawa dan'uwana karatu alhalin be hada komai da mu ba. Farinciki a gurin Yaya Nabil ba a magana kamar zai zuba ruwa kasa ya sha domin murna, daman abun da yake nema ne yana son karatu shi da Hana ba kamar ni ba.

Washe gari da safe Kanen Hafiz ya sake kawo min ziyara sai dai wannan karon ba, maganar gado ce ta kawo shi ba, ya zo min ne da tsaraba ta atamfa biyu da kuma turare sai sabulu da talkami da kudi 10k wai yana taya ni murna fita waka, kuma na yi hakuri da yadda yan'uwansa suka nuna min halin ko'ina kula. Na karba na yi masa godiya muka yi sallama na shiga ciki, bana tunanin ina da wata bukata ta kudi a yanzu wannan ya saka na dauki kudin na bawa Hana na ce ta kaiwa Mama idan ta tafi gidan, domin ita ce mai yawan zuwa ni ban taba zuwa ba domin an yi auren ne a lokacin da ba ni da halin yawo.

Abu kamar wasa, shiryen shiryen tafiyar Yaya Nabil Sudan ya fara, duk wani abu da za'ayi Kareem ne yake ba shi kudi yayi, har aka kammala komai within three months. Ranar da zai je yi ma Mama bankwana na bi shi muka tafi tare, ni da shi sai a ranar muka fara zuwa gidan.

Babba gida ne mai bangare kusan hudu, gida ne mai kyau da tsari Mama da kanta na san ba ta taba mafarkin aure irin wannan gidan ba.
Da muka shiga ciki sai ta zame mana kamar wata bakuwarmu saboda yadda rayuwa ta canja mata, ta yi kiba ta kara haske ga tufafi masu tsada kayan kallo kai har da dinning da ac kamar daman can Mama bata taba auren talaka ba, duk inda ta wulga kallonta nake kamar wata bakauya.

 Noor na zame miki sabuwa yanzu ko?

Na yi dariya ina kallon plate din taliyar da ta aje min nama batsa batsa kamar wanke.

 Mama ina ta mamaki ne, ina kika hadu da wannan mutumen ne?

Ta dan hade rai.

 Mutume? Toh idan ba zaki iya kiransa da Baba ba, ki kirashi da suna Alhaji kamar yadda kowa yake kiransa a gidan nan, wato ke dai sakarcin ki ba zai canja ba ko?

Na yi shiru ina kallon Yaya dake cin taliyar, sannan na soma cin tawa. Rabin abincin kawai Yaya ya ci ya sha ruwa yace zai tafi.

 Da wuri Nabil na yi zaton sai dare, saboda Alhaji ya dawo ku gaisa, yana ta fadar ban taba gabatar masa da sauran yarana ba, be san kowa a cikinku ba sai Hana da ke yawana zuwa

 Bana son na kai dare Mama, akwai guraren da ya kamata na tafi kamin ba bar garin nan, kuma kin ga kwana biyu ya rage min

 To sai dai kai ka tafi Noor kuma zata tsaya sai ya dawo kun gaisa tukuna ta wuce

Mama ta shiga dakinta ta dauko masa babbar leda cike da kaya sannan ta danka masa 20k tana ta sakawa Kareem albarka wai daman a yanzu tana ta tunanin wace makaranta zata nemawa tarin kudin da take shi take yi ma, amman gashi ya dauke mata nauyi. Bayan Ya Nabil ya wuce muka zauna da Mama muna hira take tambaya ko Zafeer ya ji rayuwar Mijina.

 Zai iya ji tun da iyayensa suna cikin unguwar, ko basa nan ma ai yan gulma suna nan, fitowar nan ma cewa suke ta yi hakkinsa ne

 Zafeer yana sonki sosai, zai iya dawowa yanzu ma, wata kila kuma iyayensa su hana shi, ko da yake a can baya ma sun yi ta kokarin hana amman ya nace sai ke, gashi kuma an watsa masa a ido, Wallahi mahaifinku be kyauta ba

 Baba ma da yace be yafe ba idan na sake masa magana, shi ne abun da ya fi damuna

 Wai har yanzu? Toh ai Hafiz din baya raye kuma, yanzu idan Zafeer ya dawo ba zai bari ya aureki ba?

 Ban sani ba, amman da kamar wahala saboda yana ganin Zafeer talaka ne

 Haka ne, ubanki be ji wani yare sai na kudi, gashi babu mai iya ja masa liyi a dangi komai yayi daidai ne a idonsu

Na daga kai ina kallon POP din falon.

 Taso mu tafi ki gaisa da mutanen gidan, suna ta tambayar, da kika fita wanka ma sai da matarsa tace zata tafi ta duba ki kuma Allah be yi ba

 Ita bata kishi ne Mama?

 Ana tabawa mana ayi mace babu kishi, amman boyewa ake na ciki na ciki, ita dai tana da kirki ba kamar wasu ba

 Ko dai irin na Aisha take miki ba, haka take nuna min ba komai ashe wayo take min

 Ke dai da halinki Noor, na san ki ba, kuma zamanmu a nan Alhaji ya fada mace kamar riga take a wuyansa duk wanda ta daga masa hankali cire ta kawai zai yi ya aje, duk tarin yaransa babu wanda uwarsu take cikin gidan nan, sai wannan matar da yaranta uku, sauran duk iyayensu sun fita, ni ma sai bayan auren nake ji, wata kila shiyasa ta kama kanta

Ina jin haka na san an gudu ba a tsira ba ne, kenan ita ma idan ta yi masa ba daidai ba zai iya sakinta. Daga bangaren Mama muka fito muka shiga bangaren matar da take gidan a yanzu. A cike muka samu falon da mata da maza, Mama ta yi sallama suka amsa suna gaisheta da mutunci.

 Noor Ya hakuri?

Wata budurwar da ban waye ta ba ta fada sai na amsa da Alhamdullahi na gaishe da Hajiyar.

 Lafiya Kalau Noor, an fita wanka ko? Tohm Allah ya bada hakuri ya kawo na gari

Mama ta amsa da Ameen.

 Alhaji ne be santa ba sai mita yake ina boye masa yara, tare da yayanta take jibi zai wuce Sudan gurin karatu, ya zo bankwana amman be tsaya ba, ita kuma ba ce ya tsaya ta gaisa da yan gida

 Ta kyauta gaskiya, da ma dai kin maido nan kila zata fi jin sanyi kin san gidan na mu cike yake da mutane

 Mahaifinta ne ai be yarda ba, ko takaba a nan ya so ta yi amman uban yace ba zata yi ba

 Kin san wasu mazan akwai kishi

Haka dai suke ta hirarsu ni dai kaina na kasa ban dago har sai da na ji an bude kofar falo alamar mutum ya shigo. Dagowar da na yi sai muka yi ido hudu da Safeena tana dauke da cikinta da be gama girma ba. Bata kallon kowa sai ni ni ma kuma bana kallon kowa sai ita muka rika kallon kallo wata kila ita ma tana mamakin ganina ne kamar yadda nake mamakin ganinta. Gidansu ne? Ko kuma zuwa ta yi? Ko kuma dai tana da wata alaka ce da mutanen gidan?

 Kin dawo Safeena?

Hajiyar ta fada sai Safeena ta amsa mata ba tare da ta kalleni ba, har lokacin ni take kallo.

 Na dawo Hajiya, na karbo files din gobe zan tafi asibitin na kai

 Toh Allah ya taimaka ya raba lafiya

 Ameen

Ta amsa sannan ta dauke idonta ta zauna a kujerar dake facing dina, sai kuma ta sake dasawa daga inda ta tsaya.

 Anty Safeena kin santa ne?

Na kalli mai tambayar wata kila su ma sun lura da kallon da take min yayi yawa. Ga mamakina sai ta amsa da cewar

 Aa ban san ta ba, wacece hala? Ta yi min kama da wata kawata ce ta yarinya

 Noor ce yar wajen Anty Amarya, wanda mijinta ya rasu

 Allah sarki Allah ya masa rahama

Ya juya tana kallon Mama dake amsawa da Ameen sannan ta sake kallona. Har muka baro bangaren babu abun da take sai kallona kamar wata bakuwarta. Ban kuma san dalilinta na boye cewar ta san ni ba. A bangaren Mama na koma na zauna har dare ina jiran dawowar mijinta saboda mu gaisa, be shigo ba sai bayan Magariba a lokacin da ake hada hadar Sallah Isha'i.

Na yi mamakin yadda yayi murna da farinciki ganina babu wata kyama, har na na yi sha'awar ina ma ace shi ne mahaifina ba Baba ba, zaunawa yayi a falon yana ta min nasiha akan hakuri da rayuwa na halin da na samu kaina da kananan shekaru, na yi masa godiya ya saka hannunsa aljihu ya ciro 10k ya ba ni.

 Aa na gode

A bakin gaskiya ta ba zan karba ba, domin ko na karba ban san miye zan yi da su ba a yanzu. Sai dai na lura hakan be masa dadi ba domin rufe ni yayi da fada a dole na karba na yi masa godiya.

 Tafi bangaren Hajiya ki ce na ce cikin yaran nan duk wanda yake nan ya sauke ki gida

 Tohm

Na mike tsaye na yi ma Mama sallama sannan na fice daga falon yana ta kallona. Bangaren Hajiyar na dawo na sanar mata abun da Alhaji ya fada sai mutumen dake tsaye a gabanta yayinda take zaune ya juyo ya kalleni. A nan ma wani mamakin ya kara kama ni, mutumen nan da ya taba yunkurin biya min kudin siyayyar da na yi a wani dare da muka fita tare da Hafiz.

 Kamar na sanki?

Na bude baki kamar zan yi magana sai kuma na yi shiru, ban san me zan ce ba, ni dai ina da saurin gane mutane shiyasa na gane shi.

 Noor ce Yar wajen Anty Amarya ce, ita ce wadda mijinta ya rasu

 Ai ban sani ba, Allah ya jikanshi da Rahama

 Ameen, ku tafi tare sai ka sauke ta ka wuce, Noor bari ga Abdull zai fita yanzu sai sai ya wuce da ke, ki jira shi a waje

 Okay

Na juya na fito daga ciki, ban san wacece motarsa a cikin motocin gidan ba dan haka zauna a balcony har ya fito.

 Kika zauna a kasa?

Bance komai na na mike tsaye na bi bayansa muka isa gurin wata sabuwar mota, sai da ya fara shiga sannan na bude na shiga front seat. Ba tare da yace min komai ba yayi reverse ya fice daga gidan.

 Ina ne unguwarku?

A lokacin da na dago sai na ga idonsa akaina suke. Na fada masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login