Showing 48001 words to 51000 words out of 227321 words

Chapter 17 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1518

gaba daya bana jindadin yadda Baba yake tafiyar da rayuwar gidan nan, ban taba ganin uba irin na mu ba

Mama ta juyo ta kalleni sai ta miko min hannu.

 Zo nan ki zauna

Na isa kusa da ita na zauna sai ta saka ni a jikinta ta rumgume ni.

 Wai an kama Zafeer

Na daga kai da sauri na kalleta.

 Me yayi?

 Wai ya tafi gurin aikin Ogansu Yayanki yayi masa cin mutunci a cikin mutane shi ne shi kuma ya saka aka kama shi yana can rufe

Na fashe da kuka ina jin kamar na tashi na tafi amman babu dama. Yaya ya kalleni a tausaye ya ce.

 Ni na rasa gane wane irin kalar uba Allah ya ba mu, gaba daya babu ruwansa da damuwarmu, yanzu mutumen ko auri Noor Wallahi ba zai ga mutuncinta ba saboda ya san yadda aka yi ya aureta...

 Jarabawa ce ta rayuwa, sai hakuri Nabil duk yadda zaku ji be kai yadda ni nake ji ba, ku ai ubanku ne ni ko mijina ne, duk jarabawar da za'ayi mace ko yaya ko wace iri ce mai sauki ce idan ba a gidan aurenta ba ne, idan mace tana shan wahalar rayuwa akan ce idan kika yi aure kin huta, amman idan ta tararda kaddarar a gidan aure, to wannan ita ce jarabawa mai girma, domin shi aure yana nufin rayuwa ne ko mutuwa, babu yadda zaka yi, duk yadda kuke jin bakincikin ubanku be kai yadda ni nake ji ba, yara biyu na rasa kamin na haife ku, shekara shirin da uku da aure babu ranar da bana kwana da bakincikin ubanku

Ta karashe zancen cikin kuka Ya Nabil ya sauke kansa kasa rai a bace nikam kuka kawai nake ina jin bana da makiyi a duniyar kamar Kareem, sai kuma mahaifina da nake jin na tsane shi a yanzu. Na dago daga jikin Mama na kalli Ya Nabil

 Yaya dan Allah ko zaka kira min Kareem a wayarka na yi magana da shi please? Dan Allah?

 Me zaki ce masa?

 Magana kawai zan yi da shi dan Allah Yaya, kar yaje yayi ma Zafeer wani abu dan Allah Yaya

Rokonsa nake da muryar kuka hawaye na min zuba, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kama number sai da ya kira sannan ya mika min. Ni kuma na karba na mike tsaye na shiga dakinmu.

 Assalamu Alaikum

Ban amsa sallamar ba na yi shiru kamar wadda ta rasa abun cewa. Hakan sai ya fahimtar da shi ni ce a waya ba Yayana ba.

 Noor me ya faru...?

 Komai ma ya faru Kareem, na yi dana sanin saninka a rayuwata, sanadinka Baba ya raba ni da Zafeer ni shi kadai nake so ba zan taba son kowa ba, saboda me zaka kama shi?

 Ba a fada miki abun da yayi ba? Planning ma fa nake na yadda zan taimaka masa ya aureki, tun jiya da na fahimci abun da Babanki yake kokarin aikatawa, amman sai gashi yau a restaurant a gaban jama'a yana ci min mutunci yana kira da sunaye kala kala, shiyasa ai na rufe shi sai yayi hankali tukuna

 Kana takama da kudi ne kawai Kareem, shiyasa ka siye Babana kuma yanzu ka kulle saurayina, to ni ba zan siyu ba, ba zan taba sonka ba, kuma na tsane ka da na san bakincikin da zaka haifar min kenan ba zan yarda ko magana ta shiga tsakanina da kai ba...Ka sake shi Wallahi saboda ka ga shi ba shi da kudi ka yi masa haka...

Ban gama fadar Abun da nake son fada ba Yaya ya fisge wayar ya kashe.

 Shi ke nan na rasa aikina...






KAREEM POV.

Sai da kiran ya katse sannan ya kalli Hafiz dake zaune a gabansa.

 Ka ji da kunnenka ko? Shiyasa na saka hands-free ai saboda ka ji

Hafiz ya dauke idonsa daga wayar ta Kareem dake aje a kan teburin ya kalli Kareem.

 Kurciya ce fa kawai take damun yarinyar nan, ai kai baka fito ka fada mata cewar kana sonta ba ko? In ba shi ba miye na wani kiranka ta fada maka magana haka? Wallahi bata da wayo

 Ko ma dai minene yanzu ta fadi mind dinta, tun farko na fada maka yaron nan take so, ko na rasa matar aure a duniya ba zan taba auren matar da bata so na ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin masoya ba, so ka sake tunani Hafiz ka je ka gyara lamarin yarinyar da saurayinta kuma ka nunawa mahaifinta gaskiya, karka cutar da ita ka cutar da saurayinta

 Amman baka ga abun da ya zo mana ba dazun nan

 Abun da yayi be kyauta ba, abu ne da kowa ya sani, shiyasa har na saka aka kama shi, kuma yanzu za a sake shi, amman kokarin ganin ka shiga tsakaninsa da Noor daukar alhaki ne, indai saboda ni kake yi ka daina ni dai ba zan auri yarinyar nan

 Ni fa alheri kawai nake kokarin kullawa, kuma ni ban cewa mahaifinta ya rabata da saurayinta ba, kuma ban cewa saurayinta ko ita su rabu da juna ba, ni dai ina kokarin sama maka mafita ne Allah ya san manufata shiyasa nake ganin zaka iya koya mata sonka cikin kankanen lokaci, amman zan gyara komai kuma na maka alkawari daga yau ba zan sake rokon ka auri Noor ba, kuma zan je na samu mahaifinta zan gyara duk inda kake tunanin na lalata, daga nan har zuwa nadewar duniya Kareem ka cigaba da zama a haka ba zan sake maka magana ba

 Hakan ya fi ba, na san yadda kiyayya take ba zan yarda na sake aikata kuskure a karo na biyu ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin soyayyar kowa ba, yadda rayuwar Noor take ba zan yi mata sha'awar ta zauna da wadda bata so ba

Ya dauki wayarsa ya mike tsaye ya fice a office din a fusace. Hafiz ya bishi da kallo yana murmushin takaici.

 Ba laifinka ba ne laifina ne, kuma zaka gane ka yi da an halak...

Ya fada sannan ya cize bakinsa ya hade rai.

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??



*Chapter 14*


 Kasan halinta ai da shirme da ma dai baka bata wayar ba

Mama ta fada sai ya juya ya kalleta.

 Na dauka magana zata yi masa ta hankali amman meye na fada masa magana haka gatsai, babban mutum ne fa Mama kawai yana da saukin kai ne shiyasa Noor ta same a ruwan sanyi

 Yanzu aikin gama ai ya gama, sai a tari gaba, ka je ka bashi hakuri kace baka sani ba ta dauki wayarka ta kira shi

 Haka zan yi

Ya juya ya fita Mama ta bi bayansa ni kuma na zauna ina ta aikin kuka. Yadda na kwana banci ba haka na wuni haka wani daren ya sake tararda ni na kasa cin komai sai ruwa kawai nake iya sha...
A daren ma sai na kasa bachi saboda tunanin Zafeer ko ya dawo ko kuma yana can, a wane hali yake a can? Wace kalar azaba suke gana masa? Me zai saka ma su kama shi? Na ji yayi abun da be dace ba amman ai taba shi aka yi domin be taba zuwa haka nan kawai ya ci mutuncin Kareem ko ya masa wani abun ba sai yanzu.

Mama ce ta shigo har cikin damunmu a lokacin da Hana take shirin makarantar Islamiya kasancewar yau assabar ba kamar sauran ranakun da take zuwa makarantar boko ba. Ta zauna kusa da ni ta aje min kunun.

 Noor daure ki sha idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zata wahalar da ke, kuma ita kaddara ba a kauce mata komai wayon mutum, idan Allah ya kaddara Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isaya hana, idan kuma Allah yayi shi ne mijin ba ko an taru an hadu za a daura muku aure ba zai dauru ba, kalli yadda kika rame cikin kwana daya da rabi, kin koma kamar ba ke ba, ki yi hakuri kinji ?ata

Ta kwanto da ni jikinta sai na ji sanyi a raina na lallabar da ta yi min da kuma kokarin kwantar min da hankali. Na bude bakin a hankali ta fara ba ni kunun ina sha har na sha rabin kofin sannan na ji na koshi.

 Na koshi Mama

Hana ta kalli kunun ta kalleni.

 Lallai na yarda kina son Zafeer kalli yadda kika natsu kika koma kamar ba ke ba, kuma yadda kike fushi ko kuka baki rabuwa da abinci amman yau dubi yadda kika ki cin abinci

Na kalleta kawai na dauke kai domin ni kadai na san yadda nake ji a raina ni kadai na san halin rayuwar da bake ciki

 Ni ma dai na yi mamakin yadda noor ta natsu kamar ba ita ba

Mama ta fada kamin ta yunkura ta tashi tsaye ta dauke kunun ta fice daga dakin. Hana kuma ta gama shirinta ta kama hanyar makaranta, aka bar ni a dakin ni kadai ina jin jikina babu karfi tunani ne ko kuma dai yunwar da bana ji ce take karya garkuwar jikina. Ina daga kwance na ji sallamar kawata Zainab, na tabbatar a lokacin Mama bachi take domin ban ji ta amsa mata ba, wata kila kuma tana bandakin ne ko kuma ta fita ba tare da na sani ba. Cikin dakinmu ta shigo ganinta ya saka na tashi zaune domin na san ba zan rasa labarin Zafeer a bakinta ba.

 Noor amman dai baki da lafiya ko?

Na daga mata kai.

 Me yake damunki?

 Ni ma ban sani ba

Ta yi shiru tana kallona kamin ta kawar da kai ta ce.

 Wata magana na ji ana ta yi Noor, ko da yake dai ba zan boye miki komai ba gaskiya Zafeer ma ya fada min kuma ya aiko ni gurinki na kawo miki wannan takardar, amman ina son na san me ya hada ku Noor?

 Ba abin da ya hada mu, me kika ji?

 Baki ji an kama Zafeer ba? Jiya misalin sha daya na dare ya dawo gida, kuma kamin a kama shi ina ta jin magana sama sama cewar ke da mahaifinki kun bi kudi wai ana son a aura miki wani ba Zafeer ba, ance har da gida ya siyawa Babanki kuma yana kawo muku kayan dadi a gida

Mamankin jin cewar ya siyawa Babana gida ba abu ne na mamaki ba, wata kila Baba ne ya fada wata kila kuma abokansa. Amman zancen yana kawo mana kayan dadi wani zance ne da ban san da zamansa ba. Kuma ban san wata rana da Kareem ya kawo mana kayan dadi haka nan siddan ba, har sai idan ni na shigo da su, jin cewar mahaifina da ni kaina mun karkarta ga mai arziki wani abu ne da ya fi ko wane yi min daci, domin idan har abun da Baba yake kudiri ya tabbata mutane za su yi mana kallon maciya amana ne. Musamma ni babu ta inda zan iya wanke kaina. Ta damka min takardar dake hannunta.


 Gashi Zafeer yace na kawo miki, kuma Noor da gaske ne Babanki yace kar Zafeer ya sake zuwa kofar gidanku?

Hawaye na amsar tambayarta domin su suka fara fita madadin kalma a bakina.

 Ina ganin kamar da akwai matsala a kasa Noor baki son fada ne kawai, ko dai dole ake son yi miki?

Nan ma bance mata komai ba, zata sake yin wata maganar ta ji muryar Mama da ta fito daga bandaki.

 Zainab ce

Sai ta tashi da sauri ta fita daga dakin tana gaisawa da Mama. Ban bude takardar ba sai da ta fice gaba daya daga cikin gidan, ina warwarewa gabana yana faduwa kamar ance zan karanta sakon mutuwarsa ne a ciki.

 Noor... Me yake faruwa? Nace ki zo ki same ina son magana da ke kin ki, na hadu dake na miki magana kin ki ki amsa ni, an kama ni jiya na yi tunanin zaki zo ko da gidanmu ne ki tambaya ko ki kira wayata, amman na tambaya baki yi ko daya ba, why? Da farko na dauka ko Baba ne kawai aka yi nasarar sauya masa ra'ayi kaina, amman jikina yayi sanyi a lokacin da na ji baki neme ni ba, ko dai ke ma ya sauya miki ra'ayi akaina ne Noor? Shekara uku da muka yi a tare kike son batawa saboda kudi? Kina son ki manta da ni ki rayuwa da wani saboda kudi? Haba Noor kin san fa ina sonki, jiya da na dawo gida ke na fara tambayar kin zo, Inna ta yi kamar zata kashe ni saboda haushi, amman hakan be hana ni rubuto miki wannan wasikar ba a yau kuma zan sake rokokin ki a karo na karshe... Ina son ki fito mu hadu a bayan islamiyarku, zan jira ki a gurin daga yanzu har zuwa azahar, ina son mu yi magana ne Noor bana nufin cutar dake, kuma hakan zai karyata abun da zuciyata take hararon game dake, na san ke karamar yarinya ce kuma kina son rayuwar jindadi, amman hakan be isa ya saka ki yi watsi da ni ba ki kama wani da baki da tabbacin ko zai iya rike ki... Noor in har baki fito ba to ni ma zan hakura dake har abada kuma hakan yana nufin ya sauya miki ra'ayi akaina kenan!

Ina karatun hawayena na jika takardar, Zafeer ya zo min da wani abu mai nauyi da ba zan aikatawa a yanzu ba, domin ba zan tsallake maganar mahaifina kuma na yi silar mutuwar auren mahaifiyata a yanzu ba. Ina sonsa amman Baba ya shata liyi a tsakaninmu. A nan wata zuciyar ke ce min na fita naje na dawo ai Baba baya gidan kuma be san an yi ba, wata kuma na ce min na lallaba Mama na ce ta roki Baba naje an ga Zafeer ko da na iya yau ne kawai. A cikin duka shawarwarin ban dauki ko daya ba, A kowane sakon da minti idan na tuna Zafeer yana can yana jirana sai na ji hankalina ya tashi, a haka na wuni a dakin ina kuka har na ji kiran sallah Azahar.
Shinkafa da miya na daga cikin favorite food dina amman ranar sai na kasa cin wadda Mama ta girka. Da dare ina jin lokacin da take labartawa Mama cewar tun ranar ban sake cin komai ba har yanzu, a madadin Baba ya ji tausayina sai ya rufe ta fada wai ita take goya min baya nake wannan iskanci. Tashi na yi zan fita sai Hana ta fara kokarin hana ni.

 Noor karki fita

 Magana kawai zan yi da Baba

Na amsa ta sannan na fita na isa har gurin da Baba yake na risina kasa ina kuka.

 Baba dan Allah dan Allah Baba ka yi hakuri karka aura min wani idan ba Zafeer ba, Wallahi Zafeer nake so Baba shi kadai nake so, idan na auri wani ba shi ba mutuwa zan yi Wallahi

Ya haska ni da fitilarsa mai haske...

 Eyyyyyyeeee lallai duniya ta miki dadi, tabbas kin samu yadda kike so Noor, yanzu har abun ya kai ki dubi idona ki fada min ga wadda kike so ki aura? Duka nawa kike? Ke har wata soyayya kika sani ma? Dan uwarki can da da ake aure wata soyayya aka sani amman yanzu saboda zamani ya lalace duniya ta bude muku ido kuma uwarki ta saka kin raina ni shiyasa kika zo kika zame ni kina fadar zaki mutu idan ba Zafeer ba?

Ya juya gurin Mama ya rufe da fada tana amsa masa sai ya rufe ta da duka ni kuma na yi hanzari tashi cikin karfi hali da rashin karfin jiki na tare Mama sai ya hada ni da ita yayi mana duka kamar be san inda muka fito ba. Dukan Mama a gaban idonmu wani abu ne da yake saka mana tsanar mahaifinmu kullum kuma wani abu ne da Baba yake jin dadi aikatashi, wata kila yana tunanin hakan zai saka mu kara tsoronsa ne abun da be sani ba hakan yana saka sanar kiyayyarsa a zuciyarmu ne kawai kuma ya kan saka mu yi masa kallon wani azzalumin mutun tsabanin Uba da kowa wane yaya suke yi ma iyayensu.

 Dacan ina cewa Haihuwar Noor ce ta kawo min kariyar arziki, ashe ke ma baki so na da arziki duba abun da yaron nan yayi mana daga zuwansa, kuma inda zata huta ne ba gidan wahala ba amman kin bi rana da safiya idan na fita kina hore mata kunne kar ta saurare shi idan ya zo ko? To ni zan kira shi zan bashi ita sadaka na ga uban da zai hana auren idan akwai wadda ya haifa min Noor din, gaba daya baki iya ba su tarbiya ta kwarai saboda baki san zafin haihuwa ba

Haka Mama ta mike tsaye tana kuka tana fadin.

 Malam idan har ka aikata hakan ni kuwa zamana a gidanka ya kare, ba ta yadda zan zauna ka wulakanta ni kuma ka aurar da yata a inda za a wulakanta, babu yadda za'ayi wadda ka aura mata ya ga dararja ko taka, babu ta inda zata yi kima a gurinsa, mutumen da be bude baki yace yana sonta ba saboda ya siya maka gida zaka ce ka dauki Noor ka bashi sadaka bayan kuma yarinyar nan ba shi take so? Wannan abun kunyar har ina?

Baba ya dan matsa baya ya ce.

 Ni kike fadawa Haka Hajara?

 Na fada maka Malam Naziru, ka yanka ni yau ka ci, na gaji da kai na gaji da halinka...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login