Showing 165001 words to 168000 words out of 227321 words

Chapter 56 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1569

number zan kira ki anjima, na gode da kika shiga motata

Na bude na fita ba tare da na ce masa komai ba. Shi kuma yayi reverse ya juya, na ciro wayar a jakata na yi saving number, ashe Kareem ya ga fitowa motar domin motarsa tana fake a gefen gidan makotanmu ne, ban lura ba sai da na karasa, gaba daya sai farinciki ya baibaye ni, ganinsa da na yi.

 Laa Kareem baka fada min zaka zo?

 Laa Kareem baka fada min zaka zo?

Ya kwaikwaye ni da wata murya kamar ba shi ba yana mocking dina fuska a hade.

 Ba ki da aiki sai raba Number, ki so wannan ki so wannan, ke baki ma san abun da kike so ba, baki san mai son ki ba, ke baki ma gajiya da halin maza ne?

 Haka zan yi ta yi har na dace Kareem

Na fada a shagwabe murya kamar zan yi kuka.

 Ba ni wayata

Yana fada be jira na ba shi ya fisge wayarsa dake hannuna ya bude motarsa ya shiga.

 To ai line na yana ciki ka ba ni layina

Banza yayi min ya ja motarsa baya ya bar ni tsaye na fara dora hannu a fuska zan yi kuka, ganin hakan ya saka tsaya da motar be tafi ba kuma be yi gaba zuwa inda yake dazun ba, ya dade a ciki sannan ya fito motar ya tako da kafa ya zo ya mika min wayar.

 Kalli wani mayafi da kika saka kika fita, haba Noor, kin saka duk raina ya bace Wallahi, idan kika sake shiga motar wani ko kika saka mayafi irin wannan kika fita, ban yafe miki ba, kuma mun bata ba zan sake kula ki ba

Na karbi wayar ina kara bata fuska alamar zan yi masa kuka, i feel so childish when ever I'm near him, da wani ne ya fada min haka ba zan damu ba amman shi na ji babu dadi, kuma abu kadan idan yayi min sai na masa kuka nake jindadi. Motarsa ya koma rai a hade ya bar ni a gurin, sai da ya wuce na duba sai na ga babu liyi a wayar, ashe sim din ne ya cire a motar ya kawo min wayar kawai. Kamar na kwala ihu haka na ji a wane dalili zai karbe min layi ya tafi da shi.

Hayaniyar da na ji a zaure ne ya saka ni karasawa cikin gidan da sauri, Hana na zube a kasa tana rusar kuka Baba kuma yana ta zazzaga masifa.

 Shiyasa aka boye min, saboda tana auren ubansa, wato kar aka taba mutumcin aurenta ko? Bayan ni kuma ya taba mutuncin aurena

 Me ya faru Hana?

Hana nake tambaya sai Baba ya amsa min.

 Munafukar yarinya, daman ai uwarki ta koya miki kiyayya da ni, shiyasa ni baki son farinciki ba ruwanki da damuwa da uwarki kawai kika damu, ashe abun da ya kashe miki aure kenan amman kika boye

 Baba me kake fada?

 Ashe mijinki mutumen banza ne, fyade yayi ma Hana shiyasa kuka rabu, kuma aka boye min? Magana mai girma haka? To ba zan bar wannan ba, Wallahi sai na ja hakkin yata ba zan bari a tafi a banza ba, sai na yi karar ubansa

Na saki wayar hannuna da jakata da mayafin duka suka zube a kasa.

 Baba a ina ka ji wannan? Ba gaskiya ba ne sheri ne...

 Sheri? Ai abun duniya baya boya ina zamana wata mata ta zo ta fada min

Na dafe kaina.

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Baba ba gaskiya ba ne, kawai na gaji da zama da shi ne muka rabu

 Kika sake magana sai na tsine miki albarka ma, har matar da ta cirewa Hana ciki na ganta da idona na yi magana da ita, kuma ba zan bar maganar nan ba

Hana ta girgiza min kai tana kuka ni ma kukan na fara Umma kuma ta saka salati yana tabi da rike baki...





Pay 500 to
2451879008
Zenith Bank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.

Da zullumi da tunani kala kala na kwana a raina kamin safiya ta waye har na matsu, haske na fara fitowa na safa hijab dina na sa ci kafa na fice daga gidan ba tare da kowa ya sani ba.
Na isa titi ina kama jiki domin hadari ya hadu a garin iska mai sanyi na kadawa sosai, na wahala sosai kamin na samu napep din da ta dauke ni, tun a cikin Napep din na ba shi kudinsa.

Ina sauka na kwankwasa kofar gate din gidan Kareem, babu jimawa mai gadin ya bude, na yi zaton zai kauce ya ba ni hanya na shiga ne sai ya tare ni, ya hana ni shiga. Wai ya masa warning cewar idan ya bar wata ta shiga a bakin aikinsa.

 Abu ne mai muhimmanci, dan Allah ka shiga ka fada masa Noor ce

 Ko fa haske ce yace kar na sake bari mace ta shiga, ba zan yarda na rasa aikina saboda ke ba

 Fada masa kawai zaka yi, ba shiga zan yi ciki ba

Kusan ni zan iya cewa ban taba haduwa da mutum mai tsananin kafiya da kin yin alfarma ba irin mai gadin Kareem, babu irin magiyar da ban masa ba amman sam yaki bari na shiga kuma ya ki tafiya ya fadawa Kareem din ina waje. Na bata awa 2 a gurin domin na iso ne karfe 7 na safe kareem kuma be fito gidan ba sai tara da wani abu. Ana bude gate din na auna da gudu cikin gidan, mai gadin ya biyo ni yana fadin na fita ban kula shi ba na nufi Kareem.
Fitowa mota yayi ya daga mai gadin hannu alamar ya kyale ni, sannan ya rufe motar yana kallona.

 Sim kika zo karba?

 Me yasa ka ce mai gadinka kar ya bar ni na shigo? Ko ka gaji da ni ba zan daina kawo maka bukata na ba mun riga mun zama Family

 Ba ke na ce kar ya bari ki shigo ba, amman ko ba a fada ba ke ma kin san be dace ba, ba mutuncinki ba ne, zaki iya kirana na zo na same ki mu yi magana idan kina da bukata

 Da me zan kira? Ba ni da number ka, kuma ka karbe sim din, mai gadinka ya aje ni a waje har na awa biyu na wahala sosai

 Kin yi samari ba zaki iya zama ba sai kin yi waya da su ko? Tun jiya da dare suke kirana har yau da safe, har da wani mijin kawarki wai ya kira ya ji kin isa Lafiya, me yasa zaki yi ta raba numbobinki ga maza Noor?

Da fada yake min maganar ransa a bace har fuskarsa ta nuna.

 Mijin kawata ba ni na bashi number na ba, ban san ina ya samu ba, kuma ni ban taba waya da shi ba, tun zuwan da na yi ma na yi muka gaisa ya tafi ban sake magana da shi ba

 Su kuma mazan biyu da suka kira fa? Sannan wani ya sauke ki mota a gaban idona ai waye shi

Na turo baki gaba ina wasa da yatsuna.

 Shi.. Shi..shi... Ai rage min hanya yayi sai kuma ya karbi number na, ka ganshi yana da kyau ko?

Na wara masa ido ina murmushi sai ya kara hade rai.

 Ni ba ni da kyau ne da wani zai burgeki? Me yasa ni baki taba ganin kyauna ba? Noor ki tsayar da hankalinki ki fahimci rayuwa please

 Are you jealous?

 Yes...

Ya amsa min kai tsaye yana kallon cikin idona kamin ya dauke idonsa ya lumshe ido, sasauta fushinsa yayi sannan ya kalleni.

 Shi kuma Baban Aisha fa miye hadinki da shi?

 Baban Aisha? Wace Aisha?

 Matar Hafiz

Baki sake nake kallonsa da mamaki.

 Ya fadi cewar ya san ni ne?

 Duk wanda ya kira yana introducing kansa, sannan yace da ke yake son magana, kuma na saka Sim dinki a wayata truecaller yana nuna sunan kowa

 Amman ba ni da number Babanta ni ban ma taba ganin mahaifinta ba, sai idan wani abun kuma ta hada min har mahaifinta zai kira ya min magana to ma ina ya samu number na?

Ina karashe maganar wani tunanin ya fado min, wata kila tsohon da na fara haduwa da shi har ya ba ni kudin Napep mahaifinta ne.

 Na tuna jiya na hadu da wani tsoho mahaifinta ne kenan?

 Ban sani ba, tare muka tafi? Taya zaki tambaye ni

Ya amsa min kamar da fada, gaba daya na lura daga jiya zuwa yau kamar dai haushina yake ji ko kuma baya son mu yi zaman lafiya. Ya bude motarsa zai shiga.

 Ni fa ba sim din na zo karba ba, wata matsala ce ta faru jiya bayan ka wuce shiyasa na zo nan, babu wanda ya san na fito ma

Ya kalli ruwan da suka fara dauka ya kalleni.

 Shigo ciki

Ya rufe motar ya koma cikin gidan ni kuma na bi bayansa muka shiga falon, ac ya fara kashewa sannan ya zauna a hannu kujera ya duba agogon hannunsa sannnan ya kalleni kallona.

 Zauna fada min minene?

 Baba ne, wai zai yi karar mahaifin Abdull saboda abun da ya faru da Hana

Mikewa yayi tsaye yana mamaki.

 Ta ina ya ji wannan maganar?

 Ban sani ba, amman yace wata mace ce ta fada masa kuma har matar da ta zubar mata da cikin ya gani da idonsa, kuma idan maganar nan ta fita, rayuwarta zata lalace ni ma ba zan sake samun wanda zai aure ni ba

Ya kalleni with so much effection.

 Duk yadda zaki zama Noor akwai wani yana nan yana jiranki, idan duniya da mutanen cikinta suka juya miki ba, shi yana nan tare da ke, babu wani abu da zaki aikata ko waninki ya aikata da zai saka shi gudunki, idan kika ga ba ki da kowa a duniyar nan hakan yana nufin ba shi a raye

 Waye?

A madadin ya amsa min sai ya sauke kai ya jefo min wata tambayar.

 Kin fadawa Safeena abun da ya faru da Hana ne?

 Ban fada mata ba, ni ban ma yi magana da ita bayan faruwar hakan ba, sai dai idan shi ya fada mata, ko kuma kai!

Ya girgiza min kai

 No ba ni da wata alaka da Safeena yanzu, babu yadda za'ayi wata maganar ta shiga tsakanina da ita, balle wannan sirrinku ne, ba zan iya cutar da ke ko wani na ki ba Noor

 Me yasa ka ambaci sunanta? Kana ganin zata iya wani abu?

 Saboda zata iya yin haka, zata iya tona wannan asirin ta hada wannan makircin saboda bakinciki rasa ni, saboda na fada mata ba zan sake dubanta ba, na san na yi kuskure a baya, amman yanzu na gyara komai ya wuce, ta fada min aurenta yana gad da lalacewa saboda kin fadawa mijinta cewar danta data haifa ba na shi ba ne, kuma ya dauki yaran yaje gwada jininsu, ta fada min idan aurenta ya mutu ba zata kyale ki ba, kuma dole sai na aureta ni kuma ba zan taba aurenta ba

 Me yasa ba zaka aureta ba? Ya zaku yi da dan kenan?

 Me zan yi da ita? Ko ba ita ba ba zan sake yin aure ba a rayuwata

 Saboda me?

 Ba zan auri macen da bana so ko bata so na ba, mace daya nake so a duniyar nan, idan har ba zan same ta ba, to zan hakura da aure ne har abada

 Wacece? Hafsat

 Noor... Noor ce...

Ya amsa min tare da sautin fitar iska, fuskarsa kuma cike da rauni. Na mike tsaye ina kallonsa, sai ya tako ya matso kusa da ni, ya zuba min kalaman da na gagara mantawa.

 Babu wata Hafsat Noor ke ce, i love you so much, tun a farkon haduwata da ke na ka mu da sonki Noor, amman a lokacin baki ganin kowa a gabanki sai Zafeer, bana son na lalata alakarku saboda bana son ki samu rauni a zuciyarki, ni ne dalilin da ya saka Hafiz ya aureki, saboda ya fahimci ina sonki, amman ina tsoron na yi rayuwar aure da babu dadi a tsakanina dake, a kokarinsa na gyara tsakanin ginin da ya rusa na Zafeer da ke, mahaifinki ya Kyautar masa da ke

Kallon juna muke daga ni har shi falon yayi tsif kamar babu kowa a ciki.

 Kamin ya rasu ya fada min na samawa zuciyata abun da take so, kuma ke zuciyata take so Noor, yarinyar da na baki labarin wani ya riga ni ke ce Noor, ke ce karshen bukatuna, ina son ki Noor

Na sauke idona kasa hawaye suka sauko min.

 Ina jin zan iya kyautata miki Noor, na baki rayuwa mai kyau, gatan da kika rasa, zan sama miki, burina kullum na ganki a farinciki, but i know I'm not perfect, ban cancance ki ba, you deserve someone better da me, akwai wata kofa da ba zata bude ba a tsakanina da ke, na bata rayuwata na sani, kin fada min ba zaki iya zama da mazinaci ba, ko da ya tuba, kina da gaskiya Noor na girmama ra'ayinki

Hannu ya saka ya cire hawayen da ya taru a idonsa.

 Ina son murmushinki, ina son dariyarki, ina damuwa idan kin damu, ina jin farinciki da farincikinki, idan na tunaki ina jin nishadi, ina son rautarki i love every about you Noor but I'm weak, ban cancance ki ba, ni ba mutumen kirki ba ne, taya nagartacciyar yarinya irinki zata auri namiji kamar ni wanda ya aje a ba tare da aure ba? Kuma da matar wani matar sunna?

Yayi murmushi

 I'm so lonely, ina fatar kalamaina ba za su bata miki rai ba, i hope ba zaki yanke alaka da ni ba, ganinki ma yana saka ni jindadi, ina son na roki abu daya

He take one step forward i take one step backward.

 Kawai ki bar ni na rayu da kaunarki, if you ever need someone you know I'm here, daga yanzu har zuwa karshen rayuwa, ina fatan duk wanda zaki aura nan gaba, zai rike ki amana ya baki kulawa irin wacce na so baki, ban miki fatan rashin dacewa duk da yake kaddara tana rabaki da su, tana kara kusancinmu, amman bayan nufin zan aure ki Noor, amman ina sonki Noor na mutu a kaunarki, i was waiting for so long ma fada miki yadda nake ji akanki, ba ni da sauran farinciki a yanzu sai ke sai yarana

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro sim din ya miko min, na daga kai ina kallonsa.

 Ba ni da wata dama na hana kowa rabarki, ina jin kishi saboda ina sonki, amman ba ni da wata hujja ta alakantuwa da ke, amman ko na mutu noor ina son ki sani KAREEM YANA KAUNARKI i wanna tell what i feel in million meaning...

Juyowa na yi ya nufo kofar fita daga falon da nake jin yayi min kada a yau duk kuwa da irin girmansa.

 Ruwa ake Noor ki bari a dauke ruwan

Ban juyo ba balle na amsa shi haka na fita cikin ruwan ina hawaye da ban san na miye ba, me yasa bake kuka? Me yasa Kareem ya fada min haka yanzu? Da gaske so na yake ko dai yana son yayi min irin na Safeena ne? Kalamansa sun yi min nauyi sun mantar da ni dalilina na tafiya gidan.
Ashe Zainab ta fadi gaskiya Hana ma ta fada cewar Kareem yana so na.

Tafiya kawai nake irin na wanda ya rasa gurin zuwa, ruwan saman da ake kama da bakin kwarya yana dukana, da na fara gajiya da tafiyar sai na samu wani guri a gafen wani babban gida dake unguwar na tsaya, ina matukar tsoron ruwa da tsawa ko walkiya amman a ranar gaba daya tsoron komai ya fice min a kai. Motar Kareem nake facing dake fake a daidai inda nake tsaye, abun da ban sani ba ina tafiya yana bina a baya har na samu gurin tsayuwa.

Front seat ya bude yana kallona, takawa na yi cikin ruwan na nufi motar na shiga na zauna, a bude na bar kofar har sai ya kwanto ya miko hannunsa ya rufe gambun motar. Wani yanayi nake ji na dabam shi ba tsoro ba, ba jindadi ko akasinsa ba, a yanzu na kasa sakewa da shi, kamar bako haka nake jinsa. A tsawon awannin da muka yi a motar ko kadan ban yarda na kalli hafen da yake zaune. Amman shi nasa idon suna kaina har aka dauke ruwan. Sannan ya tashi motar yana tuki yana kallona har muka isa.

A gaban gidanmu ya faka sai a lokacin na juyo kadan na kalleshi idanuwana suka sauka cikin nasa.

 I'm sorry i hurt your feelings, wata kila kin fi son abota da ni, wata kin fi sakewa idan ba soyayya ba ce, bana nufin bata ranki Noor kawai dai na fada miki ne saboda na samu sassaucin abun da yake zuciyata, dan Allah kar hakan ya saka ki canja min ina jindadin kasantuwata da ke

Na juya na bude motar na fita, shi ma sai ya bude ya fito.

 Ki sanar da Baba ina waje

Ban juyo ba kuma ban amsa bana shiga ciki, a zaurenmu na tsaya na rumgume kaina ina wani irin kuka mai karfi amman bana iya barin sautin ya fita, da za a tambaye dalilin kukan ni kaina ban sani ba, zuciyata ta yi min nauyi da bata taba min ba kamar ba zan iya daukarta a kirjina ba haka nake ji. Gefen hijabina na saka na share hawayena sannan na shiga cikin gidan da idanuwa da suka yi ja.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login