Showing 75001 words to 78000 words out of 227321 words

Chapter 26 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1513

riga ta zubar da kamarta a idona

Hafiz ya kalleshi

 Amman kana son jikinta?

 Wannan jikinta ne ita ta bani a kyauta, da farko ina tausayin yarinyar nan amman yau ta ba ni mamaki, ba Allah a zuciyar Safeena

Hafiz yayi wata yar siririyar dariya.

 I'm glad ka fara ganewa next time sai ka kiyayeta

Daga haka ba Kareem be sake cewa komai ba har suka isa Asibiti. Ya san gurin da ake yawan aje ta sai dai ba shi da tabbacin dakin da aka aje ta har sai da ya bincika. Waje ya tarar da Aryam da Khadija da Abokiyar Zamanta wacce ta kasance tamkar yar'uwa a gareta, Yusura kuma tana tsaye jikin kofar saboda an hana kowa shiga dakin, idonta har ya kumbura kuma still hawaye take kana kallonta ka san a firgice take irin firgita nan na mai tsoron mummunan labari.
Kareem ya rage tafiyar da yake yana kallon yanayinsu gabansa yana dukan uku uku, Hafiz ya karasa gurin Aryam.

 Wani abun ne ya faru?

 Aa jikin ne dai yayi tsananin, sosai ko da muka kawo ta nan bata san inda take ba

Sai a lokacin Kareem ya samu kuzarin karasowa gurin ya tambaya dalilin tashin ciwon.

 Fitarka babu jimawa ta ce tana jin jiri jikin ya kara zafi sosai, 2 hours later ta fara Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un in less than 5 minutes ta rikice mana, amman yanzu likitocin sun saka mata oxygen sun mata allura amman dai sun hana mu shiga mu dubata

Kareem na jin haka ya nufi dakin da Momy take ya tura ya shiga. Hankalinsa ya tashi sosai fiye da yadda ya saba ganinta a halin ciwon, ba wannan ne karon farko da aka saka mata oxygen ba kuma ba wannan ne karon farko da take shiga matsananin hali irin wannan ba. Amman wannan ne karon farko da ya kasa ganin bakin idonta sai zallar farin kawai, jikinta yayi fari ba irin farin fata nutural ba, irin farin nan mai ban tsoro, and kokarin da likiton suke na gano jijiyarda za a saka mata drip ya gagara.
Juyowa yayi ya fito jiki a mace kamar ba likita ba, ya saba ganin irin wannan amman ya kasa dauka na mahaifiyarsa ya kasa jure kallon yadda ake ta neman jijiyar.

 Da Sauki?

Yusura ta tambaya hawaye na sauko mata. Kallonta kawai yayi ya dauke kai be ce mata komai ba.

 Ka fada min mana Kareem

Wannan karon jikinta har rawa yake kamar zata fadi. Kareem ya karasa kusa da matarsa ya rikata sai ta kwanto jikinsa tana numfashi da karfi, ji take ba zata iya daukar rashin macen da ta zame mata uwa da uba a lokaci daya, even though tana ganin kamar mutuwar Momy mafita a gareta but da abun ya zo mata a gaske yau din sai ta ji shi a dabam.

 Da sauki, likitocin suna bata taimako da ya dace

Ta sassauta numfashi yana sauke ajiyar zuciya. Mayar da numfashi da zata yi sai ta maida tare da wani kamshin turaren da tabbatar ba na shi ba ne, ko da bata shiga jikinsa kullum ta san kalar kamshin da mijinta yake yi, domin turarensa irin mai sanar da isowarsa ne tun kam ya karaso a guri idan kuma ya bar guri zai bar kamshin ne for the whole day, and the most curious thing is turaren ya fi yi mata kama da na mata. In a curious manner ta dago daga jikinsa ta kalli fuskarsa sai ta tarar ita yake kallo. In a low voice ya ce.

 Why are you faked it?

 Why do you hug me then?

Ya dauke hannayensa daga jikinta ya kauce daga inda take tsaye ya nufi gurin da Hafiz yake ya zauna.

 Na dauka ciki zaka koma ko zaka iya bata wani taimako?

 Ba zan iya ba Hafiz I'm scared

 Scared...?

Hafiz ya maimaita cike da fahimtar inda Kareem ya nufa. Hafiz ya daga hannunsa ya dafa abokinsa.

 Zata samu sauki da yardar Allah

Kareem ya daga kai cike da karfin hali. Kusan gaba daya dayansu a asibitin suka kwana daga Aryam har Khadija da Yusura da Hafiz da ya kasa tafiya ya bar abokinsa a halin da ya fi bukatarsa. Har garin Allah ya waye babu wanda ya samu shiga dakin sai Kareem shi ma dan yana likita ne. Shi ya kwana da ita bayan an yi nasarar samun jijiyar hannunta an saka mata drip.
Sai bayan da suka yi sallah asuba suka ka jikinta d sauki sannan Hafix na koma gida Aryam ya tafi Yusura ma aka aka bar Hajiya da Kareem a gurinta da kuma autarta Khadija.

Dalilin ciwon Momy ya hana Kareem halarta daurin auren abokinsa da aka gabatar a washe garin Ranar ta assabar, be je daukar amarya ba ba da shi aka kai ango ba. Daman kuma be jin zai iya yin haka ba ko da babu dalilin ciwon Momy. Around 5pm Kareem na zaune kusa da Momy yana bata ruwan zamzam a baki a hankali Aryam Khadija ta mike tsaye ta dauki kulolin abincin da aka kawo da safe ta fara sakawa a basket.

 Gida zaki tafi Khadija?

Hajiya ta tambaya tana rike da karbinta, Hajj Farisa ma dake zaune kusa da Hajiyar ta kalleta.

 Eh kayan abincin zan tafi da su

Kareem ya mike tsaye ya cire Lapcoat dinsa ya mika mata.

 Wuce da ita gida, ki dauko wata

 Daman ba a nan kuke bari kayan ba?

Hajj Farisa ta tambaya.

 Ana bari amman na fi sha'awar na tafi da tawa gida, akwai ta office tana cikin office ai

Ya amsa cikin yanayi na rashin son magana. Momy ta juya ta kalli aurarta wadda ta kasance budurwa yar 200L a jami'a kamar zata yi magana amman babu hali domin tun da ta farka bata cewa kowa komai ba, an karya halshen bakin idon ya bata ya bar fari, jikin yayi sanyi ya saki da idanuwa kawai take iya bin mutane da kallo, tun daga yan'uwanta dake ta shigowa da safe har zuwa yanzu idan an mata sannu bata amsawa sai dai ta daga kai, kuma komai aka saka mata bata iya hadewa dawo mata yake.

 Kai ba zaka tafi gida ka huta ba Kareem tun jiya kake a nan fa

Hajiya ta fada cike da tausayinsa domin shi ne mai damuwa sosai fiye da yan'uwansa. Hajj Farisa ta sauke ajiyar ta ce.

 Ya kamata kam ka tafi ka huta Kareem

 Hajiya ku bar ni nan, hankalina zai fi kwanciya idan ina kusa da ita fiye da gidan, idan ma na koma ba wani abu zan yi ba

Momy ta kalleshi ta yi murmushi, shi ma murmushin ya mayar mata sai ta kai hannu ta taba fuskarsa.

 Allah ya maka albarka... Ya hada kanku

Ta fada cikin wani irin furuci mai daga hankali da tsoratarwa, domin maganar nata be fita sosai. Hajj Farisa da Hajiya suka taso da sauri suna kallonta. Momy ta juyar da kanta ta kalli abokiyar zamanta wadda ta zame mata kamar yar'uwa.

 Ga amana nan mai nauyi na baki, na san kin riga a ido balle kuma bayan idon zaki kyautata, Musamman Khadija yarinya ce karama bata gama mallakar hankalin kanta ba

Khadija ta saki kayan dake hannunta ta fashe da kuka.

 Haba Yaya ki daina wannan Maganar dan Allah zaki tashi da yardar Allah zaki yi ma yarki aure da kanki har jikokinki za ki gani

Hajiya Hassana ta fada tana kuka. Hajj Farisa ma ta saka kuka. Kareem ya aje ruwan zamzam din dake hannunsa ya rike hannunta.

 Momy akwai mai binki bashi ko kike bi?

Ta kalleshi na tsawon dakiku sannan ta ce.

 Eh Akwai Murja mai mana wanki, akwai kudinta na wata biyu a hannuna, kuma na arawa Hajiya Kudirat kudi Hassana ta san komai a gabanta aka yi

Kareem ya daga kai cike da gamsuwa zuciya kuma cike da nauyi.

 Bayan wannan ba wani abu?

 Akwai filina na gado da gada gurin mahaifina, na bawa Yusura kyautar filin nan na fadawa mahaifinka kuma na rubuta Hassana kuma ta sani

 Bayan shi babu wani abu? Ko kasuwanci tsakaninki da wani ko wata?

Ta girgiza masa kai. Sai ya hade yawu mai daci ya danne zuciyarsa ya ce.

 Momy ki yafe duk abun da na yi miki

 Kareem Allah ya maka albarka, ya baka yaran da za su maka biyayya fiye da yadda ka yi min, na hana ka auren wadda kake so kuma ka ha nu... 

Ta tsaya ta kalli Khadija dake kuka.

 Ka auri wadda nake so, ban taba jin wani abu marar dadi a tsakaninku ba, hakan na saka na jidadi na ranta min rai

Ta juyo ta kalleshi idomsa na cika da hawaye.

 Ko da zaka kara aure a gaba, karka wulakanta Yusura, Allah ya baka mai kaunarka macen kirki wadda ta dace da kai kuma wadda kake so, Allah ya muku albarka gaba dayanku, na yafe muku dukanku, Allah ya hada kanku mahaifinku ma idan akwai wani abu a tsakaninmu na yafe masa, Na yafewa Hassana na yafewa kowa ma... Ina fatar Allah ya yafe min

Bata sake cewa komai ba sai hawaye ya sauko mata. Khadija ta fada jikinta tana kuka.

 Mama dan Allah ki daina wannan maganar zaki tashi da yardar Allah, karki tafi ki bar ni ina da bukatarki

Kareem ya daga ta daga jikin Momy ya rike hannunta ya fice da ita daga cikin dakin. Sai da ya rufe kofar dakin sannan ya fara yi mata magana cikin natsuwa.

 Khadija, kukanki nan zai daga hankalin Momy sosai, kuma shi marar lafiya natsuwa da kwanciyar hankali yake so

 Ya Kareem baka ji abun da take fada ba?

Yayi kokarin hana hawayen idonsa fita.

 Marar yana zama kamar tsoho ko yaro ne, wasu komai sai an musu, wasu kuma suka samu gushewar tunani na dan lokaci, amman ni ban ga wata alama na mutuwa a jikin Momy ba, tambayar da kika ji ina mata ina yi ne saboda na ji idan tana a cikin hayyacinta

 Da gaske Yaya?

 Likita ne ni na san irin abubuwan nan, kuma na sha haduwa da cases irin wannan

Kalamansa sun karfafa mata guiwa har ta share hawayenta.

 Yanzu daga nan ki wuce gida ba zai kin koma dakin ba

 Tohm

Ta yi yadda ya bukata bata koma dakin ba ta kama hanya. Rakata yayi har sai da ta shiga adaidaita sannan ya dawo cikin asibitin, Office dinsa ya shiga ya jingina kansa a one of the visitors chair ya rufe ido. Can kuma ya kira mahaifinsa ya sannan ya nufi kujerar ya zauna....






NOOR POV.

Sai da aka fara shiga da ni bangaren uwargidan aka yi mana huduba, yan'uwan mahaifina suka jadda mata amanar da suka bata, ta ba ni atamfa Julius Holland exclusive da turare, suka karba min suna godiya sannan aka shiga daki bangarene sai kamshin turare yake irin na amare. Can tsakar gadona aka zaunar da ni kaina a lullube har lokacin hawaye nake.
Gwaggwanina suka sake yi min huduwa tare da kashe na kar su ji wani abu kar su gani na san waye mahaifina.
Bayan sun tafi aka bar ni daga ni sai kawaye na, Zainab ce zaune a kusa da ni ta kama hannuna ta rike sai magana take ba ni tana kwantar min da hankali.

 Dan Allah Noor ki bawa mara da kunya, kin ga yanzu ido yana kanki, idan baki zauna ba za a ce amanar Zafeer ce, kuma kin ga Baba ba zai miki da kyau ba, haka kuma hankalin Mama zai tashi, mutanen unguwa ma idonsu duk kanki yake dan Allah karki aikata abun da zai raba ku Noor mutumen ya nuna miki kauna kalli irin hidimar da yayi miki yayi ma mahaifinki kuma duba irin gidan da ya kawo ki

 In Shaa Allahu ba za aji wata matsala daga gareni ba, zan bawa mutane mamaki

 Allah ya ba ku zaman lafiya

Na kasa amsawa da Ameen kuma na kasa daina kukan da nake wadda ya zame min al'ada. Mun kwashe awa daya a dakin sannan aka shigo da ango, wani abun da ya ba ni mamaki shi ne, ban ga Kareem a tare da shi ba babban abokinsa, a madadin haka uwargidansa ce ta yi masa rakiya ta chaba ido na irin wanda na ga a dazun da muka shiga bangarenta ba. Kaina ya daure sosai me yasa Kareem be zo ba? Na tsammaci ganinsa har a gurin dauka balle kuma zuwa raka ango. Ta dayan bangaren kuma ina mamakin kalar zuciyar da take a kirjin matar Hafiz daman aka samu mata irinta masu yi ma miji komai babu nuna kishi ko kadan, har ma su raka ango dakin amaryarsa.

Abokansa sai saka mata albarka suke suna yaba halinta, ni kuma suka ja min kunne akan na rike ta tamkar Yayata ita ma zata rike ni a matsayin kanwa. Anyi siyen baki cikin mutunci da karamci, suka bada kudi da kyautar da kawaye na ba su yi tsammani ba, abokansa suka maida kawayena gida, aka bar mu daga ni sai Hafiz sai kuma matarsa da har yanzu ban san sunanta ba bayan Madam da yake kiranta da shi. Hada mu yayi yayi mana nasiha da jan hankali akan yadda zamu mu'amalanci junanmu da kuma dora shi a hanya idan ya kauce. Ni dai har lokacin ban iya hada ido da daya daga cikinsu ita har shi. Sai dai zan iya shaidar muryarta dake fita tana jaddada akidarta ta yin adalci da rike tamkar yar'uwa.

 Ni yar'uwa aka kawo min ba kishiya ba, yarinya ce karama idan ma ban rike ta amana ba ai Allah sai ya tambaye ni, kuma duk abun da zai kwantar maka da hankali kai ka sani ina son shi ko da ba zai min dadi ba, idan na ga ta yi ba daidai ba zan gyara mata ni ma idan na yi kuskure ko mantuwa sai ki tunatar da ni saboda na ankara, kuma karki biye zugar kawaye zai lalata miki zaman aurenki ne, ni ma kuma zan yi kokarin ganin ban yi haka ba. Allah ya baka ikon yi mana adalci...

Ta fashe da kuka ta tashi ta fice daga dakin da saurinta tana kuka sosai. Hannayensa na ji a jikin mayafina yana kokarin daga mayafin nawa har yayi nasarar yin haka ya kalli fuskata yana murmushi.

 Amarya ayi min uzuri a gafarce ni zan tafi na lallaba yayarki, na dawo yanzu nan kin san zuciya bata da kashi...

Na daga mishi kai sai ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje a gurin ya fice daga dakin, fitar da be dawo ba kenan har garin Allah ya waye....





__________________

Alhamdullahi a nan na kawo karshen free pages na TA KI ZAMAN AURE labari mai cike da darasi da kalubale da kuma soyayya da kunci. Me ke hana ta zaman auren ne? Hakkin Zafeer ne ko rashin dace, ko halinta ne ko kuma bakin iyayene ko dai duka hudun ne? Kun san dai ban saba ba ku kunya ba ina kokarin ganin na isar da sakon ta inda ya dace kuma ta yadda kuke so. Wannan ma dabam yake da sauran wata kila ma ya fi sauran, zabi yana gareku sai kun karanta za ku yi judging.

Mai son cigaba zai biya 500 to


Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

Or

6484787074
Khadeeja Candy
Moneypoint

And send the evidence of payment to 08036126660 za mu fara Paid Pages on Monday In shaa Allah. And za ku iya samunsa a AREWABOOKS @KhadeejaCandy karku manta ku yi following dina domin samun notifications da zarar na Update.


See you>?p? ' #KhadeejaCandy
08036126660

PAID PAGE 4??


?KhadeejaCandy
??Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______" " " _______


Zaunawa yayi bakin gadon yana kallona.

 Noor dan Allah ki kwantar da hankalinki, abun nan be kai yadda kike tunani ba, kuma ke ba fa jaririya ba ce da za ace idan zan matsa kusa da ki ri rika ihu kina daga hankalinki kamar yar shekara shida, haba Noor tun yaushe muke abu daya gashi har yau nake shirin barin dakinki? Hmmm i promise you i won't hurt you

Ya miko hannunsa gaba daya sai na ji hankalina ya kara tashi, ko da ace ina son shi yadda Aisha ta fada min halinshi yake da yadda zafin abun yake dole na tsorata balle kuma bana son shi.

 Zo mana Noor...

Na matsa can nesa ganin ya mike tsaye, ina ganin ya doso inda nake ya rikona na fara masa ihu iyakar karfina irin da na tsira yi masa a duk lokacin da ya nuna zai yi forcing kansa a gareni, sai dai a duk lokacin da na fara ihun yana saurin saki na ya kyale ni ba kamar wannan karon ba, da ya rike sai ya rikide min kamar ba shi ba ya sakar min karfinsa na kasa motsa hannuna ma ihun kawai nake iya yi, kamin mu ji ana dukan kofa da karfi kamar za a ballata, can kuma aka dawo gurin windows din ana bugawa da karfi. Sakina yayi dan dole ba dan ya samu abun da yake so ba, ya sauka daga kan gadon ya dauki rigarsa ya saka ya bude kofar dakin ya fita, ni kuma na tashi zaune na gyara rigata na ina jan numfashi da karfi. Aisha ce ta shigo dakin da gudunta

 Noor Lafiya?

Na rumgume jikina ina hawaye sai ta juya ta kalleshi.

 Barristers miye haka? Da yamma haka? Wane irin rashin hakuri ne? Sati daya da aka yi a bangarenta be wadatar da kai ba sai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login