Showing 174001 words to 177000 words out of 227321 words

Chapter 59 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1560

dafe da zuciyata, hawaye kam daman ai ranar yau ta su ce, idanuwan ma sun rufe ruf bana ganin komai sai duhu hayaniyar mutane kawai nake iya ji hankalin ma yana kokarin gushewa.

 Noor noor noor

Ta rumgume ni, wannan muryar da sanyin da na ji a yayinda ta rumgume ni na ji shi a dabam, dumin jikin na uwa ne data kawo wa yarta dauki a lokacin da ta fi bukatarta. Kuka take ni kuma hawaye nake gidan kuma ihu ake, mutuwa kadai ta kai haka, ba mai iya rarrashin wani. Wasu ruwa mai sanyi na ji an zuba min daga saman kai har jikina aka wanke min fuska da ruwan kankarar sannan aka cire min hijab dina Mama kankam tana kuka.

 Karki tafi bar ni ke kuma dan Allah

Na daga ido na kalli saitin da kanta yake a yanzu duhun ya yaye amman hawaye sun hana ni ganin fuskarta.

 Da gaske... Da gaske... Baba ya rasu Mama da gaske Hana ta rasu?

Rufe baki ta yi yana danne kukanta, a lokacin ne na kwala wani uban ihu na fashe da kuka na fara shurin kafafuwana ina buri kamar wata mai aljannuna.

 Ki yi hakuri Noor ki yi hakuri, kowa aka cewa yayi hakuri ya rasa ki yi hakuri Noor Allah yana son bayinsa masu hakuri

Babu irin kalmar da ba a fada min ba, babu irin rarrashin da ba ayi min ba, amman na kasa rike kaina har ji na yi ina ma ace da ni a cikin gobarar na mutu na huta. Babu irin bala'in da ban kira ba, babu kalar kukan da ban yi ba, da zuciya ta ayyana min sun tafi kenan sai na ji ba zan iya jurewa ba, musamman yar'uwata da take da kurciya da burika masu yawa a gabanta, wayar da muka yi ta karshe da Baba har yayi min fada ta fi tsaya min a rai, sai kuma Hana da na bari a gida cikin rashin na fito.

Ni sha kuka ni da Mama tun ina yi ina jin muryata na fita har ta daina fita. Hankalina be kara tashi ba sai na muka isa family house din su Baba muka tarar da gawar mutum uku ana yi mata sallah, Babana, kanwata da kuma matar ubana...
Mutuwa bata da kyau mutuwa bata da tausayi, bata da sabo, bata da dadi, na fara dandanarta ne tun a mutuwar mijina na farko. Amman bata min aci kamar yau ba.

Na yi kamar zan yi hauka, na ji kamar na bisu na ji kamar ace min komai ba gaske ba ne. Daga wajen da aka yi musu sallah aka wuce da su gidansu na gaskiya, ashe tun a jiya na yi bankwana da kanwata ban sani ba, na yi bankwana da ubana ban roki gafara ba, na san ya tafi da bakincikina da fushina a zuciyarsa. Gaisuwar ma idan aka yi min ciwo take min, Allah ya baki hakuri Allah ya jikansu da Rahama ki yi ta musu addu'a haka kowa yake fada, wasu na fadar na gode Allah bana cikin gidan ni ma da yanzu gawace, sai dai Allah yayi ba zan mutu a gobarar ba, babu rabon shan wahala shiyasa ban kwana a gidan ba.

Alhamdullahi nake ta maimaitawa a zuciyata, ba dan ina jindadi ni na rayu su sun mutu ba, sai dan ya wajaba na godewa Allah kuma na bukaci daukinsa a cikin tsanani da walwala a cikin kunci da bakinciki, a cikin farinciki ko kishiyarsa. Bana iya cin komai bana iya amsa gaisuwar kowa idan aka yi min, sai dai na bi kowa da ido. Masu fadar kyawawan hallayar Baba suna ta fada, masu fadar ta Hana ma suna ta fada. Babu zancen da ya dauki hankali kamar wanda Anty Larai take fadar Baba Kabiru yace a daki daya aka same su, kuma hannayensu a daure dukansu.

 Wannan abu yana da daure kai, Allah kadai ya san yadda wannan abun yake

 Ni ma abun ya ba ni mamaki matuka kam, wata kila gorar ce ta saka suka boya a daki daya, to amman kuma waya daure musu hannayen?

 Shi ne fa abun mamaki, Allah kadai ya san yadda wannan abun yake

Haka suke ta juya zancen, Wallahi ban san lokacin da na kwarara ihu ba na fashe da kuka mai karfi, domin na san ni na janyo komai, wata kila sai da aka kashe su sannan aka saka wutar saboda a batar da sawun, wata kila kuma dauresu aka yi aka bar su a gurin har wutar da cinye da su. Ga dukan alamu saka wuyar aka yi ba tashi tayi ba da kanta ba, domin na ji sun fada ko da aka yi abun babu wutar nepa a unguwar balle ace ita ce sanadi.

Na san iya juyawar da za'ayi a juyo ba zai wuce Abdull ba, shi ya aika a yi komai saboda asirin abun da ya aikata ya rufe, wata kila recording din da na yi ne ya daga masa hankali yana gudun tonuwar asirinsa. Daman Baba yana fadar cewar ni ba alheri ba ce a gareshi ashe ma ni zan zama sanadin mutuwarsa da ta kanwata, bayan na zama sanadin lalacewar rayuwarta. Baba yayi gaskiya babu alheri a tare da ni, wannan ya fi komai saka ni a kunci da damuwa.

A lokacin da Safeena ta zo mana gaisuwa tare da yan'uwan mijinta wadanda suka kasance step daughters ga Mama da Hajiyarsu wato abokiyar zaman Mama sai na ji kiyayyar mijinta ya kara fadada a kirjina, gashi na rasa wayar balle na kwatarwa kanwata yancinta ko da kuwa bata numfashi. Duk wani motsi da zan yi yana idon Safeena a yadda take kallona sai na lura kamar akwai magana a bakinta, daman ai ba zata rasa abun fada ba, domin tana cikin tashin hankalin barazanar da na yi mata.

 Sannu Noor Allah ya musu rahama, ya kyautata na mu zuwan

Ban amsa mata ba sai kanen mama ne suka amsa mata saboda bata da kunya har tambayar take wai ance ba a fita da komai ba

 Komai fa ba a fita da shi ba, ita dai Noor Allah be yi kwananta zai kare ba, shiyasa ta kwana gidanmu, ita bata kwana a can ba

 Allah sarki Allah ya bada hakuri

Daga haka bata sake cewa komai ba kuma bata fasa kallona har suka tafi. Da dare yayi Mama na shirin tafiya ta shiga daki sai na bi bayanta na fara fada mata abun da ke raina.

 Mama ganin nake kamar Abdull ne ya saka aka kashe su Baba kuma aka saka wutar saboda ace gobara ce

Mama ta yi shiru na dakiku kamin ta ce.

 Ni ma jikina ya ba ni haka, ashe mahaifinku ya ji zancen fyaden nan? Har ya saka maganar a kotun

 Shi na je na fada miki ban same ki ba, kuma Baba ya kira yayi min fada yace na dawo gida

 Na samu labarin bayan kin tafi, kuma na kira wayarki baki daga ba, daga baya kuma sai na ji wayar a kashe, ashe gida kika tafi

 Eh, saboda na ji raina ya bace ne sakamakin karbe wayar da Abdull yayi, na ji tsoron fadan da Baba zai yi min shiyasa ban koma gidan ba

Mama ta zauna gefen gadon dake dakin.

 Ta ya Abdull ya karbe wayar? Ina kika ganshi?

Ni ma na zauna sannan na labarta mata abun da ya faru tare da kudirina. Dauke ni ta yi da mari ta rufe ni da duka.

 Sakaryar yarinya shashasha, mahaukaciya, dabam da bata san ta tsaya ta yi tunani ba kamin ta aikata abu, ta ina zaki je ki yi recording din matarsa saboda kina mahaukaciya kuma ki yi nasa? Ke lauya ce da zaki yi amfani da wannan a matsayin shaida ko kuma yar daba ce ke da zaki riki hakan a matsayin garkuwa? Me yasa baki tunani kamin ki aikata abu? Mutumen da ya ci zarafin yar'uwarki ya keta haddinta shi zaki shiga motarsa har ki saurare shi? Har abada ba zaki gyaru ba Noor ke dai kam har abada ba zaki taba hankali ba, mahaukaciya sha sha sha...

Ta karasa fadan da kuka Mama Aisha na rike da hannayenta tana tare dukan da take min, a lokacin da na yi zurfi a cikin nawa kukan, na zube kasa na rarrafa na boya a bayan kofar dakin na takure guri daya, ina jin kaina cikin kuncin marar misaltuwa.
Mama ta yi gaskiya ni shashasha ce, kuma bana da tunani wannan ma gaskiya ne domin gashi na janyo mutuwar mahaifina da kanwata da Umma da bata ji ba ba ta gani ba.

Duk yadda aka so na fito daga bayan kofar sai na ji, domin na fi jin sanyi a gurin, a bayan kofar na kwana har safe kamar wata marar gata, hakan ya ba ni damar tausayawa kaina. Washe gari Sallah asuba ce kadai ta fitar da ni daga gurin, shi ma ina gamawa na dawo na zauna a gurin na takure ina jin tsanar kaina, meyasa na aikata haka? Me yasa ban yi tunani ba? Me yasa ma na roko Hana ta zo gurina from first plate? Wata kila da yanzu tana raye bata mutu ba. Ranar wuni na uku na zama kamar mahaukaciya ina ta tsoron mutane, gashi sai dorawa kaina laifi nake.

Bayan an yi musu addu'a ne mijin Mama ya saka aka kira ni, domin yace ni ce kadai be gani ba gurin gaisuwar, na fito ina rike da hannun Mama Aisha sai kallon mutane nake ina jin tsoro, gani nake kamar wani zai ce saboda ni Baba da Hana suka rasu. A wajen motarsa muka same shi yana zaune daga baya ya bude kofar motar yana jiran fitowata. Na risina a gurin jikina na bari gaba daya a tsorace nake.

 Noor

Na kalleshi da sauri ba tare da na amsa ba, daman kuma ba zan iya amsawar ba.

 Ya hakuri...

Na daga mishi kai hawaye shar kamar saukar ruwan sama.

 Ki yi hakuri kin ji, duk mai rai mamaci ne, kuma kowa baya wuce lokacinsa

Nan ma dai kai kawai na iya daga masa.

 Kuma na ji abun da ya faru, ma samu labarin a daren da Allah ya karbi rayuwar mahaifinki, domin na dawo gida sai na tararda sammaci daga gareshi, wai yana karata saboda ana ya keta haddin yarsa, ba zan boye miki ba na ji haushi sosai na yi mamaki kuma na yi bakinciki, ashe Allah yayi ba za a tsaya shari'ar ba, ba ni da tabbacin abun da yake zargin Abdullahi da shi...

Yayi shiru na dan dakiku sannan ya cigaba.

 Zan cika zan iya iya kokarina na gane gaskiya, idan har ta tabbatar Abdullahi ya aikata abun da ake zarginsa, to ina baki tabbacin zan hukunta shi, domin ya zalince ki ya zalinci yar'uwarki, zan zame miki uba Noor zaki same ni mai kaunarki kamar mahaifinki, sai dai ina son na fada miki ki aje sirrin nan a cikinki domin bayyanarsa zai rusa abubuwa da yawa ciki, hakan kuma ba yana nufin zan bar maganar ba zan yi abun da ya dace In shaa Allahu

 Shi ya kashe min Babana Abdull ne silar mutuwarsu, shi ya saka a kona gidan saboda na yi recording muryarsa yana fadar abun da ya aikata, kuma yayi hakan saboda kar kowa ya san abun da ya aikata

Ina maganar ina hakki sai ya kura min ido yana kallona kamar mai nazari.

 Ki shiga ciki, ki samu natsuwa

Na mike tsaye na nufi gurin da Mama Aisha take tsaye tana jirana, domin na fahimci ba da gaske yake ba daman ta ya zai hukunta dansa. I'm such a fool again. Na kama hannunta na rike muka shiga cikin gidan, wannan karon na samu zama akam tabarmar da aka shimfida ina kallon Mama dake rusar kuka, ni da ita duk mun fahimci Hana da Baba sun yi tafiyar da Baba dawowa.

 Na yafe ma yata duk abun da yake tsakanina da ita, Allah ka yafe mata, ka isar mata, mahaifinku ma na yafe masa duk wani abun da yayi min, Allah ya jikansa da rahama

Wani kukan be tashi ba sai da Yaya Nabil yayi mana saukar bazata, rirrike shi na yi ina karkarwa saboda kuka, shi ma kukan yake Mama haka, kusan sai da muka saka kowa kuka a gidan. Duk wanda zai ji mutuwar Hana be kai ni ba, domin muna tare da juna ni da ita a koda yaushe she's been with me for my life. A tare muka tafi da Mama a family house dinsu, duk yadda Anty Larai ta so a bar mata da ni Mama bata yarda ba. Domin yanzu mu biyu kawai muka rage mata, daga ni sai Yaya.

A dakin empty room din Yayanta muka tare har ita, ita da Yaya suka raya dare da hirar Hana da Baba ni kuma na raya shi da kuka da nadama. Washe gari na yi yaki sosai kamin na samu kai abu a cikina. Ina shan furar ina jin Yaya yana hirar Kareem ne ya siya masa masa ticket din jirgi saboda ya zo ya yi gaisuwa. Mama na ta saka masa albarka. Dakin yayi kamar zai kama a lokacin da Yaya ya samu labarin abun da ya faru, har fadar yake Wallahi da zai ga Abdull sai ya kashe shi sai dai shi ma a kai shi gidan yari.

 Haka Allah ya kaddara, ni yanzu ko sunan yaron bana son ji, shiyasa na ce ba zan koma gidan Ubansa ba, babu wanda ya fi mu ku yanzu

Duk hirar da suke bakina a rufe yake gum bana furta komai sai kallonsu nake idan hawaye suka zubo min sai na share. Da yamma Zafeer ya zo min gaisuwa ina cikin dakin ya shigo yayi ma Mama gaisuwa sannan ya dube ni ya ce.

 Noor ya hakuri?

Kallonsa kawai nake kai kace bana jin yaren da yake magana da ni.

 Ai ita bata uhm bata uhm uhm, tun da aka yi rasuwar nan bata iya amsa gaisuwar kowa

 Ki yi hakuri kowa yana da tabon mutuwa, kuma idan lokaci yayi ba a tsayawa Allah ya musu rahama ki yi ta musu addu'a kin ji?

Na daga mishi kai sai ya mike tsaye yana kallona cike da tausayi da damuwa ya fice, Yaya Nabil ya tashi ya bi bayansa, Yaya Nabil ya dawo mana da tsaraba mai yawa buhun shimkafa uku da cefa ne da kudi 100k daga Zafeer, Mama ta karba tana ta yaba masa da yana hallayensa...
Daidaikum mutane suna ta zuwa mana gaisuwa bayan an watse sadakan uku ciki har da manema auren Hana. Sai dai duk wannan ban ji daga Kareem ba har na tsawon kwana biyar, wata kila ya hakura da ni ne kamar yadda na fada masa, but no matter what ai mutuwa ta fi gaban wasa ya kamata yayi min gaisuwa ko fa yake na ji Yaya dake shirye shirye komawa a yau yana zancen Kareem ba shi da Lafiya har yana fadar Mama ta je ta duba shi.


Ranar da Ya Nabil zai bar garin mun kashe adashen kukan da muka zuba, ni da shi da Mama muka yi ta tunanin Hana musamman wacan bankwana da ta yi masa lokacin da zai tafi ashe na karshe ne ko gawarta ba zai sake gani ba. Haka ma Baba ashe ba zai ga karshen karatun dansa ba, kudin da yake kwadayi ashe ba zai ga dansa ya fara rikawa ba.

 Amman wai Mama haka za a bar maganar nan shikenan ya tafi a Free?

Ya tambayi abun da yayi fi masa ciwo a yanzu fiye da komai. Ni kaina ba ni da wata damuwa a yanzu kamar Abdull.

 To ya za'ayi, babu wata shaida ai, kuma ita wanda za ayi domin ita bata duniyar, wutar ma sai dai mu ce zargi muke domin ba mu da tabbacin komai

Yaya yayi kwafa ya girgiza kai ya cije baki. Kwana biyu da tafiyarsa Mama ta tafi asibiti duba Kareem, bayan ta dawo take ta bada labarin yadda ya rame ciwon ya taba shi sosai. Ni dai ban ce komai ba, domin damuwata yanzu ta ishe ni riga da wando bana bukatar damuwa ko tunanin kowa a yanzu. The following day kanensa Aaryam ya zo family house dinmu, ban san wanda ya kwakwanta masa ba domin be san gurin ba. Sai da yayi min gaisuwa sannan ya isar min da gaisuwar Kareem kuma ya fada min ba shi da lafiya sosai jibi za a fitar da shi waje domin yi masa aiki.

Ban san miyasa ba, na ji ina bukatar ganinsa duk kuwa da ina jin kamar be cancanci haka ba.

 A wane daki yake?

Na samu kaina da tambaya, wata kila na je duba shi domin ina gudun kar shi sai ya mutu na dawo nadamar rashin duba shi kamar yadda nake nadamar abubuwa da yawa a yanzu. Sai da Aaryam ya tafi sannan na koma cikin gidan na fadawa Mama ina son zan tafi na duba Kareem ance jikinsa da tsanani sosai.

 Karki ce ke kadai, ku tafi tare da Asma'u

 Toh

Na fita na nufi bangaren su Asma'u wacce ta kasance Cousin dita, sai dai ban same ta bangarensu mahaifinyarta ta fada min bata gidan ta fita, ban damuwa da na koma na nemi wani dan rakiyar ba na kama hanya ni kadai. Ba asibitin na nufa kai tsaye ba, zango na yada a unguwarmu ma shiga gidan da ya zama kofai, domin komai ya kone kurmus.

Bakin kofar dakinmu na zauna ina kallon cikin dakin, Hana kawai nake tunawa yadda muke rayuwa a ciki, da kuma ganina da ita na karshe na fita na barta tana rashin lafiya. Umman su Zainab ce ta shigo gidan ta fitar da ni tana ta ba ni hakuri har da addu'a take min tana tofa min a kai. A gidanta na zauna har sai da na samu sakewar zuciya sannan na fita daga unguwar na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login