Showing 78001 words to 81000 words out of 227321 words

Chapter 27 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1528

nuna mata fin karfi da ido na ganin ido? Kowa ya san halin da kuke ciki? Mai gadi ne fa ya fada min ihun da yake ji a nan yayi yawa naje na duba? Yanzu wannan ba abun kunya ba ne? Kuma duk zaman da ka yi be wadatar ba sai ka shiga hakkina? Yau fa zaka bar nan, daga yin auren kuma sai ka fara abu kamar karamin yaro ko wanda ya fita hayyacinsa? Me kake haka Barristers kanka farau auren budurwa?

Ta fashe da kuka ta fice daga dakin, sai ya juyo ya watso min wani mugun kallo.

 Kin ga abun da kika ja ko?

Na sauke kaina kasa.

 Ke wai wace irin yarinya ce? Wawuya kawai sakarya, marar hankali marar tarbiya

Uffan ban ce masa ba, ba dan kuma bana jin zafin kalaman nasa ba, sai dan na san nice marar gaskiya a nan, be kamata na yi ihu ba amman kuma kiyayyarsa da tsoron da matarsa ta ba ni ba zai bari na zame masa yadda yake so ba. A fusace ya fice daga dakin, ni kuma na kwanta a gurin ban tashi ba sai da aka yi kiran sallah Magariba bayan na yi sallah na fito daga dakin na sai na samu plate din abincin da ya zuba a dazun aje a gurin, kadan na ci na ji gishiri kamar zai yanka halshena da sauri na zubar kasa na kasa hadewa na nufi kitchen da sauri ina taba kofar na ji ta a rufe da makulli a dole na dawo dakina na shiga bandaki na wanke bakina ina mamakin yadda gishiri yayi yawa haka domin na dandana abinci a lokacin da na gama girkin ban ji gishiri haka ba. Dawowa na yi na zauna a dakina domin zuciyata bata raya min cewar Aisha zata iya kara min gishiri a abinci ba balle na zarge ta, da ma dai ace bama zaman lafiya ne, wata kila kuma jika yayi a yanzu shiyasa yayi yawa.

Bayan sallah Isha'i na sake fita na taba kofar kitchen din sai na same ta a rufe da alama da Hafiz ya rufe kitchen yayi tafiyarsa ya bar ni da yunwar cikina. Ni nake kamar zan iya jurewa na dan lokaci ne zai hakura ya dawo min da keys din ko kuma ya shigo ya bude min idan ya gaji. Saboda haka na sh???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?iga dakina na kwanta cikin tsoro domin wannan ne karo na biyu da na kwanta ni kadai a bangaren bayan kwanan da na yi na daren farko a gidan. Washe Gari na farka da tunanin yadda za'ayi ni ma kanwata Hana ta zo ta rika taya ni bachi idan baya bangarena saboda na rage kadaici kamar yadda ita ma kanwarta Ni'ima take tayata kwana, na yi ta jiran tsammanin ko ko Hafiz zai leko bangare ya duba lafiya kamar yadda yake duba lafiyar Aisha kullum amman shiru ko da yake ni idan yana nawa bangaren yaransa ne suke tashinmu daga bachin safe da muke komawa, yau kuma yana bangaresu wata kila shiyasa be leko nan ba, ko kuma dai fushi yake ne har yanzu be sauko ba? Domin jiyan nan na bata masa rai sosai, to me ya kamata na yi na bashi hakuri? Ko kuma na share shi idan ya gaji ya zo? Ni kadai nake ta sake sake na na rasa makama. Shiru shiru be shigo ba matarsa ma bata leko ni har azahar gashi yunwa sai cini take daman na kwana da ita. Sai kusan uku na rana sannan ya fita ina ganin haka na jikina ya mutu kuma na gane kuskuren abun da na aikata. Falon na dawo na zauna ina jin wata azzababiyar yunwa gashi babu kudi hannuna balle na siya wani abu kuma kitchen da rufe balle na saffara wani abu. A wani taimako na Allah sai ga matarsa ta shigo da sauri bangarena da far'ata kamar kullum ni kuma na dube irin duba na yar'uwa.

 Kanwata ya kike?

 Lafiya kalau

Ta yi fuskar tausayi.

 Wallahi ina can amman zuciyata na tare da ke ina tausayinki sosai, na san kin sha yunwa yau ko?

Na daga mata kai.

 Ya ji haushina jiya ko? Ina son na bashi hakuri amman ban san ya zan yi ba, na ga har ya rufe kitchen din ya tafi da key din haka na kwana da yunwa

 Allah sarki, gashi ya rantse kar na baki abincin da na dafa, saboda na fada masa da ke zan dafa

Na ji babu dadi kamar na yi kuka kuma dai na daure kar na zubar da hawaye a gabanta.

 Aisha ki ce yayi hakuri

 Zan fada masa amman ke karki yi saurin ba shi hakuri ki zubar da ajinki, yanzu kin san yadda zamu yi ga kudi 5k ki tafi ki siyo abinci a waje ki dawo ki ci

Na zaro ido da sauri gabana na faduwa.

 Aa ba zan iya ba, jiya fa a gabanki na ce zan fita kin ga yadda yake fada shi ne sanadin ma duk wannan abun balle kuma ace na fita be sani ba

 To zaunawa zaki yi yunwa ta kashe ki Noor? Ya tafi da keys din kuma ya rantse kar na baki abincinsa kuma ya fita ya fada min sai bayan Isha'i zai dawo saboda gurin Hajiyarsa zai tafi na bashi abinci ya tafi mata da shi

Na kalli kudin sannan na girgiza mata kai.

 Ba zan iya ba, be kamata na fita be sani ba balle kuma ace siyen abinci zai yi fada idan ya ji

 Taya zai ji? Ba zan fada masa ba

Na girgiza kai na lake kafada.

 Ni dai ba zan je ba

 Shikenan ni daman saboda ina tausayinki ne, bari na aje kudin

 Sai idan ba a bawa mai gadi ya siyo min

 Maigadin kuma? Ai ba zai yiyu ki aike shi ba, ba zai ma tafi ba saboda gadi yake yi kuma zai iya fadawa Barrister

 Ni dai ba zan iya tafiya ba, sai dai ko ke idan zaki siyo min

 Ni kuma? Da ciki dako dako na tafi siyo miki abinci.? Ina laifina na tausaya miki Allah ya baki hakuri

Ta mayarda kudinta ya fice daga falon, ni kuma na koma na kwanta ina jin yunwar na min yawo a cikin, haka na kwana da wahala da kuka da bakinciki wata zuciyar na cewa na tafi na karbi kudin na siyo abinci domin ba ni da wata mafita bayan wannan, wata zuciyar kuma na fada min na tafi kawai na bashi hakuri kuma na fada masa ina jin yunwa ya ba ni key na dafa abinci domin alama ta nuna ba zai shigo bangaren nawa ba ya duba ni tun da gashi har dare yayi be shigo ba kuma ya dawo. Na tashi ina jin jiri na fita daga bangaren nawa ina sanye da atamfa riga da zane na shiga bangaren Aisha na samu yaranta suna ta wasa a falon ita kuma tana bare gia. Da far'a ta tarbe ni ta dakawa yaranta tsawa wai su gaishe ni haka suka gaishe ni jikinsu na rawa na amsa ina zaunawa, kana ganina ka san yunwa ta ci ni har ta gaji.

 Lafiya Amarya?

 Hafiz yana nan?

Yaransa duk suka kalleni jin na fadi sunan mahaifinsu kai tsaye.

 Eh yana nan? A kira Miki shi?

 Eh ina son na yi magana da shi

 Toh

Ta aje plate din giar ta tashi ta shiga dakinta, bata wani jima ba ta fito ta ce min.

 Yace ki jira shi zai yi wanka

 Tohm

Na amsa idanuwana kamar za su yi magana tsabar yunwa dake matsa min lamba. Haka suka bar ni a gurin tun ina jiran fitowarsa har na fara bachi....
Ko da na farka babu kowa a falon sai ni kadai, tashi na yi na kamar zan fadi na fice daga falon na dawo bangarena ina kuka. Indai har horo ne Hafiz ne Wallahi na horu daga jiya zuwa yau kawai...




**** **** ****

Yusura na kokarin aje remote din hannunta akan Center table ta dago tana amsa sallamar da Safeena take yi.

 Wa'alaikusalam

 Sannu da gida

 Yauwa sannu dai

Safeena ta maida kofar falon ta rufe ta shigo cikin falon ba tare da an yi mata izini ba ta zauna a kujera.

 Kin gane ni kuwa?

Yusura ta yi murmushi yake.

 Ta ina fuskarki zata bace min? Safeena Right

Safeena ta yi murmushi.

 Haka ne, na ga kamar ba jiya ba ne abun, ya gida ya karin hakuri? Na zo gaisuwar Momy ne

 Gaisuwa...? Ko dai murna?

Cewar Yusura babu alamar wasa a maganarta.

 Ah haba Subhanallahi ana murnar mutuwa ne? Hana dai Yusura sai kace wata kafura

 Na ga abubuwa sun yi ta faruwa ba ki taba zuwa ba, kamar haihuwata sau biyu ina haihuwa da Kareem amman baki zo mana barka ba, sai yanzu?

 Ban ji ba ne, amman ita mutuwa kin san ba a sanarwarta ni fa gaisuwa kawai na zo, ba fada ba ina tunanin yanzu duk mun girma mun zama manya har da yara

Yusura ta yi murmushi.

 Haka ne, baya gida amman ki jira shi ba jimawa zai shigo sai ku gaisa

Ta mike tsaye ta haye dama Safeena ta bita da harara tana jin wani masifaffin kishi na cinta. Yusura na shiga dakinta ta fara safa da marwa tana cizon bakinta gaba daya ta ma rasa gane hikimar zuwan Safeena gidan, ko bata rantse ba ta san Safeena ta yi farinciki da mutuwar Momy domin tana cikin manyan makiyanta da suka hana Kareem aurenta. Kasa zama ta yi har sai da ta hango tsayawar motar Kareem a gurin da ya saba tsayuwa sannan ta nufi kofar dakin ta fita, ta san be kamata ta nuna kishi ba domin ba son Kareem take ba, but abun da Safeena ta yi a yanzu kamar cin fuska ne da mutuncinta, kuma idan har Momy zata tsani Safeena ita kuwa bata san dalilinta na kaunarta ba, zuwanta kuma ya nuna ta jidadin mutuwar Momy if not ai tana da number wayarsa sai ta kira shi ta yi masa gaisuwa ko kuma ta same shi a wani gurin.



KAREEM POV.

A lokacin da ya faka motarsa ya lura da wata bakuwar mota fake a kusa da Entrance din shiga falonsu. Be raba dayan biyu ba ko dai yar'uwarsa ko kuma yan'uwan Yusura ta bangaren uba ne suka zo gaisuwa ko ziyara, ba tare da fargabar komai ba ya shiga falon. Yana rufe kofar Falon Yusura na saukowa ta karaso gurinsa ta karbi Keys din hannunsa da ledar hannunsa tana murmushi kamar ba ita ba, sai kuma ta sumbanci bakinsa.

 Sannu da zuwa...

Safeena na kallonsu ta ji kamar ta kama da wuta, Kareem kam be lura da Safeena sai kallon matarsa yake yana mamakin inda wannan ya samo asali.

 Ga Safeena ta zo gaisuwa

Ya juya ya kalli saitin da Safeena take zaune tana ci da wuta. Ya tako ya karaso gurin da take zaune da mamaki a fuskarsa.

 Safeena? Me kika zo yi nan?

 Gaisuwa...

Ta amsa daker numfashinta na gargada. Ya kalli Yusura sannan ya sake kallon Safeena

 Ashe Momy lokaci yayi

 Haka Allah ya so

 Allah ya mata rahama, ya bada hakuri zan tafi

Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fara tafiya kamar wadda ta rikice.

 Ka rakata mata, amman karka dade ka ji Babyna... Bari na hada maka ruwan wanka

Kareem ya kalleta sai ta sakar masa murmushi tana masa alama da ya amsa da gira.

 Okay...

Ya amsa With so many questions da yake bukatar amsarsu. Sannan ya juya ya bi bayan Safeena da ke tsaye jikin kofar tana jin komai. Rufe kofar falon yayi suka sauka kasa.

 Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki sake tako kafarki a gidana, ba zan daukar miki wannan ba

 Me yasa ka yi min karya? Kace kai da Yusura baku zaman lafiya, kalli yadda ta tarbeka a gaban idona? Da far'a da soyayya, shiyasa gaba daya ka canja min, tun kamin Momy ta rasu daker na samu kanka yanzu kuma baka amsa kirana baka mayar min da amsar sakona

 Safeena ina cikin jimami na rashin Momy a yanzu, bana bukatar wata maganar, abu na biyu kuma ki natsu ki fara tunanin yayanki da mijinki ki cire ni a rayuwarki... Na gane baki da hankali shiyasa har kika tunanin kashe aurenki ki bar yaranki ki dawo gareni, yanzu kuma abun ya wuce da har kin kai ki tako kafarki a gida? Ba zan daukar miki wannan ba, ban hada iyalina da kowa ba

 Idan na ce zan aikata wani abu akanka Kareem baka ganewa, baka amsa kirana kana ta kokarin kauce min a lokacin da nake da tsananin bukatar saka ka farinciki, da kana kula ni da ban zo gidan nan ba, na riga na sabu da kai, na cutu da soyayyarka ba zan oya warkewa ba amman a haka a mahaukaciya kake kallona?

 Taya mahaifiyata zata hane ni da abu na aikata? Taya tana raye zata hana ni aurenki yanzu kuma bayan ta mutu kike tunanin zan iya cigaba da wani mu'amala da ke? Safeena wake-up ki cireni a rayuwarki and i mean it....

Ya bar ta tsaye a gurin ya rufe kofar falon ya shige ciki.

 Aurenta ya mutu ne?

Ita ce tambayar da Yusura ta fara yi masa a lokacin da ya shigo falon. Be tunanin ta yi labe ta saurari abun da suke tattaunawa sai idan zuwanta a gidan ne ya bata mamaki.

 Me ye ma'anar abun da kika yi?

Ta mike tsaye tana kallonsa.

 Irin abun da muka saba yi ne, a duk lokacin da baki suka zo, nuna cewar muna cikin soyayya da kaunar juna. Aurenta ya mutu ne ko kuma kashewa zata yi ta aureka saboda macen da ta yi mata karan tsaye ta bar mata duniyar?

 Miye matsalarki da hakan?

 Kana tunanin zan so abun da Momy ta ki? Har abada...! Ka fada mata kar ta sake zuwa gidan nan ba saboda ni ba saboda yaranka

Ta aje masa keys dinsa da ledar dake hannunta a kujera ta nufi stairs, binta yayi da kallo har ta haye sannan ya zauna yana kai hannunsa ya taba hancinsa.

 Kai Mata kuna da wuyar sha'ani

Ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dauki ledarsa da keys din ya haura sama ya shiga dakinsa...



#KhadeejaCandy



PAID PAGE 5??


?KhadeejaCandy
??Copyright
2024

Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba.
To be part of the journey pay 500 to 2451879008
ZenithBank
Hadiza Abubakar

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660....


You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy
https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153


_______" " " _______


Tsananin yunwar da nake ji bata bar ni na yi bachi ba, haka na zauna a falon ina kuka jikina na rawa ga kuma tsoro da ya baibaye ni. Misalin shabiyu na dare na ji an murda kofar dakin an shigo, na zabura na tashi da sauri ina kallon kofar sai na yi arba da Hafiz sanye da kayan bachi fuska ba yabo ba fallasa ya shigo.

 Baki yi bachi ba?

Madadin na amsa sai na duka a kasa ina kuka.

 Ka yo hakuri dan Allah, na daina ba zan sake ba, karka min horo da yunwa ina wahala sosai kuma ina jin tsoro

Be ce min komai ba ya nufi kitchen din ya bude, ni kuma na zauna a gurin ji nake ko kallonsa ba zan iya sake yi ba idan be min izini ba, domin na lura babu imani a tare da shi. Shayi ya hada min ya kawo min, sannan ya sake komawa ciki ina jin kamshi yana tashi, ni dai ban yi komai ba ina zaune a gurin da ya bar ni har sai da ya gama abun da yake ya fito da plate din indomie ya aje min.

 Taso ki ci

Na taso na dawo kusa da shi na zauna na fara cin indomie yana kallona har na gama ya kawo min ruwa na sha.

 Na gode

 Zaki iya kwana ke kadai?

Na girgiza kai.

 Ina jin tsoro

 Zan kawo Ikram da Yayarta ta kwana tare da ke, amman Noor ki zama mai tsananin biyayya da gudun bacin rai please, ina da tsananin fushi da fada, amman idan ka iya zama da ni, ba wahala mun saba, kamar yadda yayarki take yi yanzu

Na daga mishi kai. Sai ya kai hannunsa ya shafa fuska yana murmushi.

 Ki yi hakuri, be kamata na yi haka ba, amman na yi ne saboda ki gane kuskuren abun da kika aikata

Ya sumbanci kumatuna sannan ya mike tsaye.

 Muje ki saka kayan bachinki

 Nan zaka kwana?

Na tambaya ina kallonsa.

 Aa yau ai ba girkin ba ba ne dakin Yayarki zan kwana sai nan da kwana biyu zan dawo

Gaba ya saka ni na har cikin dakin na dauko kayan bachina yana kallona na canja arzikina daya ina da zanen dake daure tare da tare da shi na samu na yi dabara har na canja na saka riga da wando na bachi. Cak na ji an dauke ni daman ba wani jiki da ni ba kuma ya fi ni girma nesa ba kusa ba, saman gadon ya aje ni kwance ya kwanta da jikinsa ban gama fahimta ba na ji bakinsa cikin nawa. Na daure ne kawai saboda babu yadda zan yi ba dan ina so ba, ya dauki dakiku a haka sannan ya cire bakinsa ya daga ni ya sauka daga kan gadon.

 Ko ke fa amman da ba ni da ikon taba ki sai ihu, kamar budurwar kauye

Na yi shiru ina kallonsa zuciyata na bugawa da karfi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login