Showing 129001 words to 132000 words out of 227321 words

Chapter 44 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1512

Na dai sanar da Baba kuma ya zo ya ga Baba an yi magana da shi, yanzu ya rage Baba ya bincika

 Okay, Allah ya tabbatar da alheri Noor, ina miki fatan jindadi da samun rayuwa mai kyau a duk inda zaki kasance

 Na gode

Na fada ina kallonsa shi kuma yaki yarda ya sake kallona a yanzu.

 Fada min abun da kace zamu tattauna!

 Nace za mu tattaunawa wani abu ne?

 Eh akan yarinyar ka

Yayi dariya mai sauti.

 Ni nawa labarin ba mai dadi ba ne...

Na yi hanzarin dakatar da shi domin bana son jin wani abu marar dadi daga gareshi, abun zai tsaya min a rai na yi ta tunani ina damuwa.

 Ba sai ka fada min ba

 Why? Baki son jin yadda na rasa yarinyar da nake so?

 Abun zai tsaya min a rai ne na yi ta tunawa ina jin babu dadi, bana son na ji wani abu marar dadi ya same ka, abun zai yi ta damuna ne yana hana ni sukuni da zarar na tuna, ban san miya ba ina damuwa da kai sosai Kareem

Ya kalleni yana murmushi mai laushi.

 Amman kin san idan kin yi aure zamu yanke alaka ne? Babu waya ko ziyara saboda ni ba muharraminki ba ne, ba ni kadai ba har ma duk wanda kika san ba Nabil ba ne, ki kula da aurenki kuma ki tsare hakokin Allah Besty, kin ga kin yi aure ba ki dade ba aka fara samun matsala, ki kula ki yi taka tsantsan da rayuwar aurenki

Na daga mishi kai hawaye na sauko min.

 Zan kiyaye Kareem, na gode

 Your Welcome, and maybe wannan ne zuwa na karshe da zan yi a gurinki, saboda kar ya zo ya tarar da ni na hada fitina a tsakaninku, kuma mahaifinku ba ba zai yarda an tsayar miki da wani ba ki kula wani

Na ji babu dadi a kalamansa sai dai hakan da zai yi shi ne daidai kuma shi ne gaskiya.

 Wish you all the besty

Ya bude motarsa ya shiga, zuciyata na ayyana min na fada masa Abdull mijin Safeena, sai kuma na fi karfinta na aje wannan sirrin a zuciyata ina kallonsa har ya tafi. Sannan ya shiga gida ina jin babu dadi a rai saboda bankwana da na yi da Kareem. Zuwan da Abdull yayi a wannan karon ya zo min da babbar waya da sabon liyi, na yi murna sosai domin bayan Hafiz wani be taba min kyautar waya ba, ya saka min line ya saka min numbersa da sunan da yake son na rika kiransa.

 Soul Yayi saving ya hannanta min wayar, na yi masa godiya sosai na shiga gida na nunawa Umma wayar na nunawa Hana Baba ma da ya dawo na karba na nuna masa, na dauki Number Ya Nabil ta sudan da ta nigeria sannan na dauki Number wasu yan'uwan Baba, na saka number Mama da na haddace na yi saving na kirata muka gaisa na fada mata Abdull ya kawo min wayar, ta taya ni murna sosai ta yi addu'ar Allah yasa alheri.

Da ya sake zuwa sai ya bude min WhatsApp wai saboda ya fi saukin chat, hakan kuma na kara min jindadi domin ta nan nake magana da Yaya Nabil ya turo mana hotuna da video sa, ni ma idan na dauka sai na aika masa, idan yayi status na kalla. Yawancin chat din da yake da ni yana gargadin idan na yi wannan auren na zauna ne. Na kuma yi masa alkawarin zan zauna domin na lura kamar Abdull ba shi da matsala, ko da yake ba a goshi ake likawa ba sai idan an zauna.

Zancen auren da zan yi, ya karade ko'ina cikin unguwarmu, wasu da gangan suke dukan cikina domin jin wanda zan aura. Mamaki be kashe su sai da Abdull ya zuba min lefe kamar budurwa, ya saka min kaya masu matukar tsada ni kaina na yi mamaki domin ban dauka arzikinsa ya kai can ba. Sadakin ma 100k Baba ya yanka masa sai gashi ya kawo 150k. A lokacin ne Baba ya fara saka min albarka yana fadin idan na yi auren nan bayan son ya ji wata matsala.

Sai dai iyayensa ne suka yi komai, domin shi baya garin ma a halin yanzu, ya koma Lagos gurin aikinsa, sai dai mu yi waya ko chatting idan hira ta yi dadi ya kan dauko zancen gidansu familynsa da abokai ya fada min. Ta haka ne nake jin cewar Safeena cousin dinsa ce, a gidansu take zama sai dai ba a gidan ta tashi ba, bayan gama SSCE ne ta dawo garin Kano daga Jigawa mahaifarta saboda admission da ta samu a BUK bayan kallama karatun kuma ta cigaba da zama a gidan, har Allah ya kulla alakar aure a tsakaninsa da ita.

Mahaifiyarsa ita ce mace ta biyu da Alhaji ya fara aure kamin ya auri wasu matan, ita ma bata gidan a yanzu tana can gidanta dabam tana zama tare da wasu iyalin a aurenta na biyu da ta yi. Hakan ya kara fito da maganar Mama cewar Alhaji kamar riga ya dauki mace, ko da yake Abdull be fada min cewar Babansa yayi aure aure ba, amman dai ya fada min mahaifiyarsa bata gidan kuma yaran da suke gidan uku ne kawai suke da uwa ana, na kuma gane karatun tass duk kuwa da kasancewar be fito min a fili ba.

Ina kyautata zaton sai bayan da ya biya sadaki an kawo lefe ne ya sanar da matarsa, wata kila kuma bata dauka da gaske ne ba har sai da ta ga haka. Sai gashi ta aiko min da zagi na cin mutunci da kaskanci a WhatsApp, har na yi kamar na rama sai kuma wata zuciyar ya hana ni. Kai tsaye na yi forwarding zagin gurin mijinta kuma na yi sa'a yana online.

 Subhanallahi waya miki wannan zagin haka?

Ban bashi amsa ba na tafi gurin chat din na yi screen shot din number ta da hotonta dake dp na tura masa.

 Safeena... Dan Allah ki yi hakuri zan dauki mataki, kin san mata idan za a kara aure sai an yi hakuri da su, ni kaina duk ta bi ta daga min hankali

Nan ma ban ce masa komai ba. Na kashe data na tashi na fara gyara dakinmu, ina tsaka da shara kira ya shigo wayata da bakuwar number. Na duba wayar da kyau ina mamakin waye mai number domin ban san na bawa wani number na ba, dan haka ban amsa kiran ba har sai da aka sake kira sannan na amsa ina sallama.

 Assalamu Alaikum

 Yar iska marar mutunci karuwa mai bibiyar mazan mutane, to kira na yi na miki gargadi, Wallahi Wallahi karki yarda ki ce zaki auri, domin zaki auri mutuwarki ne, akan mijina zan iya komai Wallahi, Idan ma burinki shigowa gidana to gidana kabari ne mai cike da azaba

Na sauke wayar daga kunnena na duba number sannan ya sake maida wayar kunena.

 Gidana zan zauna ba naki ba, kuma ni a Lagos zamu zauna da shi gurin da yake aiki ko be fada miki ba? Ke be isheki hankali ba yadda na bar ba banza ajiyarki na sauka daga WhatsApp din ba tare dana baki amsa ba? Hakan yana nufin ba a fada da mahaukaci

 Uwarki ce mahaukaciya, Noor baki san waye ni ba, na fi guba hadari kuma bana yafiya Wallahi, idan kuma na sakawa raina burin wani abu bana wasa sai na cin masa, tun wuri ki shafa kanki lafiya, wato za'a zo a ji dadi ko? An ga mai kudi? Daga auren uwarki ke kuma kin ga shiga gurin dan masu gida, kin manta karya miki hannuna da na yi ko? Wannan karon rayuwarki zan karya, wato baki samu shiga gurin Kareem ba shi ne kika dawo gurin mijina ko? Ke baki da aiki sai bibiyar mazan mutane, kin shigar min hanci da yawa Noor sai na fyato ki

 Ashe dai kin gane ni, Amman kika nuna baki san ni ba, a gidan da aka rika ki har kika auri dansu

 Okay wato shi dan dadi aure ko? Ya kwashe labarina na fada miki? To zan ci uwarku ne daga ke har shi

 Ashe dai baki da tarbiya, gaskiya akwai bukatar na shigo gidan ko dan gyara miki tarbiya, har yaushe zaki raina mijinki ki ce zaki ci uwarsa?

 Uwarki ce marar tarbiya jaka karuwa...

Na mike tsaye a fusace na ce.

 Safeena ina son ki saurare ni da kyau, kin san na san abun da mijinki be sani ba ko? Kina da aure kike nuna kishi da hauka akan wani? Ko kina tunanin na manta alakarki da Kareem? Ni Wallahi ban yi tunanin kina da aure ba ma, wai ashe kishinsa kike, to yanzu kuma kina kishin mijinki wace irin mace ce ke?

Ta yi shiru irin na wanda jikinta yayi sanyi.

 Me Kareem ya fada miki?

 Na fahimci komai Safeena, idan babu so miya kawo kishi? A yanzu kuma kina kishin mijinki har kina zagina akansa? Toh bari na fada miki wani abu, idan har ban auri Abdull ba ke kuma ba zaki taba cigaba da zama da shi ba Wallahi, sai na fadawa kowa abun da kika yi min saboda Kareem, kuma na fada musu har office dinsa kike zuwa, kin ga ni da ke duk muna ruwa kusa da kada, ko dai ya cinye mu duka ko kuma mu nutse a ruwan a ruwan mu mutu dukanmu

 Karya kike yar talakawa, babu wata alaka tsakanina da Kareem, ke kamarar yarinya ce da baki gama fahimtar komai akan rayuwar duniya ba, na fiki zama tantiyar yar iska, sai na koya miki darasi Noor

 Ni dince dai zan koya miki darasi kuma na gargade ki, karki sake daga ma mijina hankali, karki sake kirana ko aiko min da wani zagi ta WhatsApp, idan ba haka ba zan fadawa mijinki da iyayensa alakar dake tsakaninki da Kareem, daman ai kowa ya san tsohon saurayinki ne ko? Har gurin da kuke boya ku aikata alfaha da aurenki na sani, na san yadda kika yi yaki kamin ki samu kansa, na kuma san yadda abokinsa yayi fama raba tsakaninku, kuma abun takaicin idan mijinki ya sake ki Kareem ba zai taba iya aurenki ba, shiyasa ya janye jikinsa daga na ki, ke din kazantace a yanzu, to yanzu fada min tsakanin gasawa da suya wanne ya fi jin wuta?

Dip na ji ta katse wayar, sai na daka tsalle na dike, ashe dai ni ma mace zan iya yaki zan iya kwantarwa kaina yanci, a yanzu na samu baki ba irin wacan karon ba. Daman ance auren fari makaranta ce aiko na koyi darasi mai girma. Na nufi gurin da kayan kwalliyarmu suke na dauki madubi na duba bakina da fuskata. Ashe dai tsiwata tana nan, ni da kaina nake yi ma wata gargadi haka akan mijinta. Da mamaki na wuni a ranar da na tuna sai na ji raina yayo fari tass.



KAREEM POV

Da ciwon zuciya Kareem ya koma gida, abun da be saba ba ko a lokacin da ya rabu da Safeena be taba jin ciwon zuciya ba, ya ji babu dadi sosai kuma ya shiga damuwa amman be taba jin zuciyarsa na masa zafi da kuna irin wannan karon ba. Rasa Noor da yayi a yanzu na dago masa da damuwa ba suke zuciyarsa.

Yana shiga falon be ma kula yaransa da suka bar wasar da suke ba suka yi masa welcome, kansu kawai ya shafa ya haura sama ya kwanta ruf da ciki ya rufe ido. Yaran suka bishi suka shiga dakinsa domin ba su saba ganin mahaifinsu a haka ba, duk maganar da suke masa da tambayar da suke masa ko be da lafiya ne be iya amsa musu ba sai dai ya daga kai ko ya girgiza ba. Har suka gaji suka fito daga dakin suka shiga dakin mahaifiyarsu.

"Mamy Dady ya dawo yana yin damuwa kuma baya magana ya kwanta a haka

Areef ne mai maganar yana nuna yadda ya kwanta. Yusura dake shace kanta ta kallesu ta tabe baki.

 Wata kila kasa shi aka yi

Ta fadi hakan ne domin ta window ta hango yadda ya dade zaune a mota kamin ya shigo cikin gidan.

 Mamy kasha shi kamar yaya?

Tine ta tambaya, kamin Yusura ta bata amsa Areef ya ce.

 Mamy a tray aka kasa shi? Ko yaya?

Ta yi murmushi mai sauti ta saki gashin nata mai tsayi ta jasu a jikinta ta rumgume.

 Ku kadai ne nake gani na ji sanyi yanzu

 We love you Mamy

Cewar Tine Areef kuma ya cigaba da tambayar yadda aka kasa Dadynsa domin be fahimci zancen mahaifi????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
yarsa ba.
Tun daga ranar sai Kareem ya tattara komai ya aje gefe, ya karbi kaddararsa ta rasa Noor ya maida hankalinsa gurin aikinsa da yaransa, hakan kuma baya nufin ya manta da ita ya cireta a rayuwarsa, da zarar ya zauna baya komai ita ce take fado masa a rai kuma yawan tunata da yake yana saka shi damuwa sosai.

Ganin yake kamar nasa zanen kaddarar be zano masa da farinciki ba, domin ya rasa Safeena da farko a lokacin da yake jin ita ce farincikinsa aka musanya masa da Yusura a yanzu kuma da yake jin ya sake samun farinciki, sai gashi ya sake rasawa, ya kuma tabbatar rashi ne na har abada domin baya fatan ta Noor ta samu wata matsala a gidan aurenta balle har auren ya mutum.
Shi ma yana da ya mace ba zai yi mata fatan abun da ba zai so ya faru da yarsa ba.


*** *** ***

Hannu ya kai ya rage sautin dake tashi a motarsa sannan ya faka a inda ya saba fakawa ya bude motar ya fito ya rufe. Cikin natsuwa yake tafiya har ya shiga restaurant din ya amsa gaisuwarsu as usual sannan ya wuce office dinsa yana kokarin budewa ya ji kamshin turare a bayansa juyawa yayi ya duba. Safeena ce tsaye fuska babu annuri be ce mata komai ba ya sake juyawa ya bude kofar ya shiga sai ta take masa baya.
Sai da ta rufe kofar sannan ta dora jakarta akan teburinsa tana kallonsa kamar ba ita ba.

 Hausawa sun yi gaskiya da suka ce duk macen da ta rike namiji uba zata mutu marainiya

Kareem ya kalleta yana daga zaune fuska ba yabo ba fallasa.

 Ka fada min bayan ni ba zaka so wata ba, ban yi zaton bayan ni zaka iya kulla wata alaka makamanciyar tawa da wata ba, sai gashi ka ba ni mamaki

Be ce mata komai ba sai kallonta yake domin be fahimci da me ta zo ba wannan karon. Ganin hakan ya saka ta zaunawa, ba dan ta zo da niyar zaman ba.

 A baya ka yi min karya ka ce kai da Safeena ba ku zaman lafiya, sai gashi na je gidanmu na sameku cikin so da kauna, sannan kuma ka juya min baya ka kulla alaka da Noor, Kareem wai ba baka ji kunya ba? Yanzu na gama fahimtar gaskiyar da kake boyewa, na gama fahimtar yaudarata kake yi, tun asali ba wai kaki ka aure ni ba ne saboda Hajiyarka, kaki ka aure ni ne saboda zuciyarka tana son Yusura, lokacin da na ce zan kashe aurena mu yi aure kin amincewa ka yi, ashe saboda kana jin kamar yanzu na gama yi maka amfani ne ko? Bayan ka gama lalata min rayuwa

Ya kwanto jikin teburin dake tsakaninsa da ita yana kallonta.

 Kamin na aureki wata alaka makamanciyar wadda muka yi a baya ta taba hada ni dake? Na taba bukarta ki ba ni kanki? Ke kika kawo kanki bayan aurenki, babu yadda ban nuna miki hakan kuskure ba ne amman kika rufe ido har sai da muka aikata ya zame mana jiki, to yanzu kuma miye laifi idan na gane kuskuren hakan na tuba?

 Ba tuba ka yi ba, wata sabuwar ka samu, ni kuma ba zan taba manta cin amanar ka yi min ba, kuma ba zan yafe ba, dadin zama ne ya saka ka manta da komai ka fadawa Noor sirrina da kai? Har take min barazanar idan ban bari ta auri mijina ba, ni ma zan rasa aurena? Shikenan mu zuba zuwa ni da ita ga fili ga mai doki, daman ina da cikinta na bakinciki sai na haife shi...

Tana kaiwa nan ta mike tsaye ta fice daga office din. Kareem ya mike tsaye yana mamakin abun da ta fada cewar Noor ta yi, sai a yanzu ya gane mijin Safeena Noor zata aura, sunansa da ta fada masa Abdull da kuma inda yake aiki da kuma fada masa yana da aure. But abun da be fahimta me yasa Noor zata yi risking fadawa Safeena haka? Me yasa zata fara fallasa sirrinsa? He thought he save da ya fada mata damuwarsa, amman gashi a yanzu zata yi ma kanta da shi da kuma Safeena illa, why ya fada mata from first place?

Ya dafe kansa ya zauna yana jin tashin hankali yana tunkaro shi, ko kadan baya son abun da zai bata matsa suna ya bata sunan Yayansa da iyayensa, can kuma ya dago ya mike tsaye ya fice daga office din.




NOOR POV.

Washe garin ranar da muka yi fadan da Safeena, Mama ta aiko kanwarta Mama Jamila ta kawo min kayan kitchen daidai gwargwadon hali, ni ban yi tunanin zan samu ko kyale daga gareta ashe tana nan tana min tanadi ba wasu masu yawa ba be sosai ko masu tsada, sai dai za su wadace ni na yi duk abun da mace zata iya dafawa ko aikatawa da pot da plates jug da abubuwan bukata. Na jidadin haka wata kika Alhajin ne ya bata kudi ta siya min ko kuma kudin da take samu ne a gidan Allah masani, ko ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login