Showing 192001 words to 195000 words out of 227321 words

Chapter 65 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1563

weekend din, na taya shi farinciki domin na ga farincikin ne a ransa, na yi ma kaina alkawari zan yi hakuri da duk halin da zan samu kaina, zan jure kuma zan yi masa biyayya na yi mata kamar yadda ya fada min a washe garin aurena idan har hakan ne zai dauwamar da ni a gidan aurena to zan aikata ko da kuwa ba zan samu farinciki ba.

 Akwai abun da za a shirya mata?

 Aa a gidansu aka aiko mata da abinci idan ta dawo

 Hakan yayi kyau, Allah ya dawo da ita lafiya

 Ameen

Ya sumbanci hannuna daga haka zancen ya sauya salo, sai dai hakar bata kai ga cin ma ruwa ba yayi saurin janye jikinsa ya tashi ya saka tufafin bachi ya kwanta, ni ma na saka nawa na kwanta. A weekend din da ya fada a weekend din ta dawo domin ya zo yayi min sallama ranar assabar ya fada min ta dawo zai kwana a gurinta. Na masa addu'a kuma na mika gaisuwa ta a gurinta, na raka shi har gurin mota ya shiga ya fice ya bar ni tsaye ina kallon gate din gidan. Idan har abun da nake ji a yanzu haka Aisha da Safeena suka ji lokacin da aka auro ni, gaskiya sun yi juriya domin na ji kamar na samu wuka na dabawa kaina da shi mu mutu gaba daya, kallon wanda kake kauna a tare da wata abu mai matukar ciwo da zafi.

Falo na shigo na zauna, ina ayyanawa kaina cewar ba zan yi kuka ba, ni ma ya kamata na zama mai juriya mana na zama kamar sauran mata. Na karafafa kaina guiwa kuma na yi nasara domin ban bari hawayen bakinciki sun sauka idona ba. Sai na cigaba da rayuwata irin yadda na saba kamar yana cikin gidan, sai a dare ne kawai tsoro ke kama ni shi ma idan na yi addu'a na kwanta sai na kwana cikin sallama. Ranar da yayi kwana biyu a can na girka taliya domin ina tsammanin dawowar a gurin, be fada mana ko kwana nawa zai yi ba amman a ka'ida kwana biyu ake yi ko daya ba kasafai ake uku ba balle kuma sati.

A ranar kuma na yi babban bako dan'uwana ya ziyarce ni, daman tun a tafiyan da na yi gida Mama ta fada min Ya Nabill ya fada mata a satin zai dawo. Last chat din da muka yi da shi ma yana tambayar me zai siyo min ne. Na yi murmushi na yi farinciki kamar zan cinye shi sai daka tsalle nake ina rumgume shi.

 Wai ke ba zaki girma ba? Miye haka?

 Yaya na jidadin ganinka ne

Mun sha hira yana ta ba ni labarin karatunsa da rayuwar mutanen Sudan abincinsu da tufafinsu ya kuma nuna min hotunan da suka dauka da yan karantarsu wani kuma da mutanen kasar.

 Na ji dadin tafiya kasar nan, shiyasa babu ni ba ni da kamar Oga Kareem a rayuwar nan, ina son mutumen nan ya tallafi rayuwata Allah ya saka masa da alheri

 Kareem yana da kirki sosai

Na fada kasa kasa.

 Wai ashe sonki yake Noor?

Na kalleshi.

 Ta ina ka sani?

 Ranar da aka daura aurenki da Zafeer na saka hotonki ina miki addu'a, sai ya min reply wai Nabil ka hana ni kanwarka ko? Na ce masa oga ai baka yi magana ba ne, Wallahi da ka fada ko bata sonka sai ta aureka, sai yace Uhmm Allah dai ya sa hakan shi ya fi alheri

 Ya ji sauki?

 Ya ji sauki sosai ya dawo da dadewa fa yana garin nan

Ban sake cewa komai ba na tashi na zubo masa taliyar da na dafa, ya ci sosai kuma ya yaba min har mamaki yake wai na yi girki yayi dadi, sai da yamma ya bar gidan na raka shi har gate ban dawo ba sai da na daina hangoshi domin a kafa yayi tafiya sai fa ya kai karshen layin sannu ya samu abun hawa kasancewar unguwar sabuwar unguwa ce ba kasafai kake ganin masu ababen hawa ba.

Zafeer be shigo ba sai da Magariba, ya shigo da far'asarsa kamar kullum na tarbe shi na yi masa sannu da zuwa ya amsa min sai na fara cire masa talkamin kafarsa.

 No ba sai kin cire ba, ko komawa zan yi, kawai na zo ne na duba ki na tafi

Na kalleshi da mamaki.

 Komawa kuma? Kwana nawa ka raba mana? Na yi zaton yau girkina ne

 Noor kin ga ita ba zata take a gari ba, kw kuma kullum a nan kike, shiyasa na yanke shawarar idan tana gari zan rika zama a gidanta sai ta tafi sai na dawo nan daman kwanakin da nake a nan sun fi wanda zan rika yi a can

 Ban taba jin hakan ba, wannan ba adalci ba ne Zafeer, raba kwana ake yi idan biyu ko uku ko sati ko kwana daya, abun da yayi min yayi mata ake yi ba abun da yayi maka ba, kuma tafiyar da take ai tana tafiya ne akan aikinta ba kai ka dauke mata kafa ba

 Na sani, amman ni hakan nake ganin zai fi

 Aa be fi ba kam, shi kenan za a ce idan tana gari ba zan samu mijina ba sai ta tafi? Ka zama mijin Hajiya kenan, wannan ai milkin mallaka ne, ta ina aka taba haka? Ba adalci ba ne gaskiya ni ba zan yarda fa hakan ba

 Ke kin san adalcin ne? Kin san shi kika zabi kudi kika bar ni? Ina ce a karkashina kike yanzu, kuma duk umarnin da na bada shi zaki bi, kuma ke da mai tunani ce yadda yarinyar nan ta zama silar gyaruwar rayuwata har kika gan ni kika aure ni ai ke da kanki zaki bada shawarar yafe mata kwananki har sai ta bar garin nan

Na mike tsaye a fusace na ce.

 Ni ban bi kudi na barka ba, kuma ban dawo gareka saboda kudi ba, idan har zan bi kudi to Kareem zan aura ba kai ba, domin ya fika arziki na ninka abun da kake ganin ka tara, kuma shi din arzikinsa ne ba na matarsa ko uban matarsa ba, kuma ban yarda ba ba zan yafe kwana na ba, dan bata fi ni gata ba

 Ta fi ki gata, ta fi ki ilmi ta fiki tarbiya domin bata taba daga min murya ba, bata taba sa'insa da ni ba, ban taba cewa A tace aa ba, kuma bata taba ambatar sunan wani namijin a gaban idona ba, ke kuma muradin kenan Kareem shiyasa kika bishi tun farko kika bar ni, yanzu kuma da kike ganin kamar zaki iya jindadi a gidan sai kika yarda kika aure ni, amman har kina da bakin da zaki ce ina takama da kudin wasu, ke ba kudin kika bi ba? Wane irin roko ne ban miki ba? Wace kalar soyayya ce ban nuna miki ba? Amman haka kika watsar da ita kika auri wanda kika ganin zaki huta a gidansa

Hawaye ya sauke min ina kallonsa.

 Wannan ba Zafeer din da na sani ba ne, ba ainahin masoyina ba ne, Zafeer din da yake jin ya fi kowa fahimtata, yake jin ya fi kowa kaunata ta, yake jin shi kadai zai iya zama da ni? Shi a yau yake fada min haka? Yake kyamata?

 Ada kenan kike da wannan kimar a idona Noor, amman daga baya na fahimci waye ke, kuma su waye iyayenki

 Ka sauya Zafeer...

Na fada cikin kuka sai ya mike tsaye yana daka min tsawa.

 Ke baki sauya ba? Rayuwarki dabi'unki jikinki komai ya sauya, i know who you're now

 Ka yi gaskiya jikina ya sauya amman zuciyata tana nan a yadda take, shiyasa ka kasa kusantata ji kake wani a jikina ya ragu?

 Wani abun be ragu ba? Yadda kike a da haka kike? Ba ni ne farkon ba ina kishin hakan

Na yi murmushi mai sauti kamin na fada wani irin ihu.

 Kasan da duk wannan me yasa ka aure ni?

Ya dauke ni mari sai na kawar da fuska gafe.

 Saboda ina sonki Noor, na yi tunanin zan jure bayan auren kuma sai na ji ina kyamar haka, na shirya yin rayuwa mai kyau da ke amman kika watsar da ni, tun a lokacin kimarki da ta iyayenta ta fita idona, daga baya kuma aka ba ni shawarar gwadaki, da na gwada kuma sai na fahimci gaskiya Safeena ta fada kudi kike bi, domin gashi kin amince da ni, saboda na raba ki da Kareem ya karfafa min guiwar aurenki, yanzu kuma burina ya cika fada min me kike saki? Daman ni na san ba za ki taba iya zaman aure da kowa ba, babu wanda zai iya da halinki sai ni, ni kuma kin riga kin zubar da kimarki a gurina, fada min saki kike so?


Na girgiza masa kai alamar aa, ya sake ni na tafi ina? Mutane su min shaidar abun da suka saba? ace TA KI ZAMAN AURE sai dandane take, na jefa Mama a cikin bakinciki? Hudubar da yan'uwan Baba da Mama suka min na watsar da ita na bi son zuciya? Wayarsa ta yi ringing ya ciro wayar ya amsa kiran da yanayin da ya fahimtar da ni Fanna ce.

 Hello Babe

 Eh amman gani nan dawowa na je gurin wani abokina ne

Ya yi murmushi sannan ya kashe wayar ya fice ba tare da yace da ni komai ba. Binsa na yi da kallo kamar wata tababbiya kamin na cira kafa na bishi har bakin kofa ina kallonsa ya shiga motarsa yayi mata key ya fice daga gidan. Da gaske tafiya yayi da gaske Zafeer ya sauya da gaske kyamata yake da gaske ya fifita wata akaina yanzu. Na sulale na zauna kasa a cikin kofar hawaye na bin kumatuna majina na fita daga hancina.

Ashe ma babu komai a cikin aure sai wahala da bakinciki, ashe ma babu komai a aure sai hakuri da ciwon zuciya, ashe duk masu nuna soyayya suke karya suke. Bana fata amman ko da Allah ya kaddara min fita a gidan Zafeer ni kam na gama aure ba zan sake auren kowa ba, domin na ga aure aure kuma ya gan ni, na dandana shi ya dandana ni na san me ake ji a ciki duk pretending ne. Idan har Zafeer zai iya juya min baya yayi min haka to waye ma ba zai iya ba?

Na dora hannaye biyu a fuskata, wai yau ni ce Zafeer ya mara, lallai kaddara ce tabam take ba ni da rabon dacewa a cikin aure, shiyasa a kowane aure mummunan abu yake bina, wannan ma idan ma har auren ya mutu jama'a za su zage ni za su kirga min aure, Mama ma ba zata min uzuri ba, gara kawai na hakura idan ma bakincikin zai yi ajalina na huta. Na gane ni kam ba a raba farinciki da ni ba, kuka na fara yi a gurin tun ina kuka da kuzari har karfi ya kare na fara amai a gurin kamar raina zai fita...





Tun da ya saka kafarsa ya fita be sake dawowa gidan ba, haka ya kara kwana uku bayan kwana biyu da yayi a gurinta. Tsoron saki da irin rayuwar da zan fuskarta bayan sakin ya haddasa min tashin hankali da tashin lafiya. Yaushe aka yi auren ma da za ace na fara samun matsala da mijina, koma minene ya kamata na jure na daure na rumgumi kaddarar aure uku ko yanka naman jikina ake ya kamata na hakuri na zauna.

Na gwada kiransa a waya amman idan na kira baya dagawa na aika masa sako na bada hakuri nan ma shiru, daga baya idan na kira sai na ji line busy da alama yayi blocking dina ne, hakan kuma ba karamar damuwa ya haifar min ba, kusan rabin rayuwar da na yi a gidan Hafiz ita nake fuskanta a yanzu, domin Zafeer yayi fushi da ni irin yadda Hafiz yayi, banbancinsa da Hafiz ya dawo min bayan kwana ki kadan amman shi sati muka dauka a haka babu aike babu waya babu zuwa dubana.

A duk lokacin da tuna Zafeer nake aure kuma yayi min haka, sai na ke ganin kamar waninsa ne aka kawo min aka dauke asalin Zafeer din da na sani. I spend hours ina kuka gaba daya na zama hopeless, tunanin ma sai na rasa ta ina zan fara, ya zaman kama zaren lamarin. Misalin karfe La'asar wani tunanin ya zo min, why not na shirya na tafi gidan uwargidansa matar da yake so a yanzu, na bashi hakuri, domin ban isa na fuskaci iyayensa da zancen ba kasancewar basa ganina da gashi.

Ban kuma isa na tafi gidanmu na daga hankalin Mama kuma na janyowa kaina fadanta da zaginta, na san laifina zata gani ba nasa ba. Tashi na yi na alwala na yi sallah La'asar sannan na dauki abaya na saka a saman atamfar dake jikina na bude zip din dake jiki ya sauka har kasa. Sannan na dauki jakata da wayata na fito rike da makullin gidan, a kofar falo na saka talkamina na rufe kofar falon na fita.

Karnunan dake tsakar gidan suna ganin fitowa na suka fara haushi, domin har yau har gobe zan saba da su ba, su ma ba su saba da ni ba, a duk lokacin da na fito sai sun yi haushi. Na fadawa mai gadin kar ya bar kowa ya shiga gidan domin zan fita, addu'a yayi tare da fatan dawowa lafiya. Na fita ina tafiya a hankali a hanya na rufe kaina ruf da babban mayafin abayata, tafiya sosai na yi kamin na samu Napep hakan ya saka ban tsaya tayawa ba na hau na fada masa unguwar da zai kai ni. Wani bangarena na zuciyata na fada min tafiyata zata iya kara laifi, dayar kuma tana karfafa min guiwar idan na tafi na ba shi hakuri wata kila zai dube ni ya yafe min.

A kofar gidan aka saukewa na sallami mai Napep na kwankwasa gate din, abun da Zafeer be fada min a lokacin da yake nuna min gida shi ne, sai an bincike waye zai shiga kamin a bar mutum ya shiga. Mutanen da suke gadin gidan sun fi kama da jami'an tsaro, sai dai kuma babu uniform a tare da su sai bakin wando da riga. Sai da dayan ya fara lekowa ta wata karamar huduwa dake jikin gate din sannan ya bude.

 Lafiya?

 Na zo gurin Zafeer ne ko yana ciki?

 Wacece ke?

Cikin tsoro da faduwar gaba na ce

 Noor ka fada masa Noor ce zai gane ni din matarsa ce

Mutumen mai kirar manyan duwatsu ya kalli daga sama har kasa sannan ya ce.

 Baya gidan ya fita

Na ji babu dadi tafiyata ta zama aikin banza kenan.

 Amman matarsa tana nan?

 Eh tana nan

 Dan Allah ka fada mata zan shigo na jira shi ya dawo?

 Ta san da zuwanki?

Toh ashe tana da matsayin ne har haka ko da yake ance mahaifinta babban mutum ne kuma ita ce babbar yarsa mai tafiyar da kasuwancinsa dole a bata tsoro da gata sosai har haka. Na fada a raina a zahiri kuma sai na ce

 Eh ka fada mata Noor ce matar Zafeer

 Okay ina zuwa

Ya koma ciki na wasu mintuna sannan ya bude ya fito ya miko min wayar hannunsa.

 Noor wace Noor

 Noor dai da kika sani, tsohuwar budurwar Zafeer kuma matarsa a yanzu

 Me kike nema?

 Ina son na yi magana da shi ne so badly kuma baya nan ina son na jira shi ne

 Ba shi wayar

Na mika masa, ban san me ta fada masa ba kawai na ga ya bude min kofar gate din yace na wuce. Shi yayi guiding din na har kofar falon, a ranar na raina duk wani kalar kawa da arziki da na taba gani a duniya, harabar gidan ta yi kamar a wata kasar turawa kake ciki ba nigeria ko Kano ba. Ba a wani cika falon da kwalliya ba amman an masa ido irin an burgewa da wayewa kana ganin kasan an kashe nairori ko dollars a kawata falon kadai.

Tun kamin ayi min izini na zauna kan sofa laushin kujerar ya wuce yadda nake tsammani.
Abu na biyu da idanuwa suka akai shi ne hoton Zafeer da Fanna na aure wani gurin tana sanye da wedding gown wani kuma pre-wedding picture ne.
Sun yi kyau ta ko'ina daman Zafeer a kyau ba baya ba, ita ma kuma kyakkyawa ce mai jiki ba kamar ni ba.

 Noor Noor Noor haka sunan yake ko?

Na juya na kalli stairs din da take saukowa wando da riga ne a jikinta irin ready-made din nan masu kyau na waje. Ban amsa ba domin na ji a kiran sunan kamar da rainin hankali. Ta zauna nesa da ni tana kallona kamar bata gane ni ba.

 Ban fa waye ki ba can you introduce yourself

Is like kamar tana son ta wulakanci a gidanta taya zata ce bata gane ni ba bayan gabatar da kaina da na yi a kofar gidanta.

 Karki damu ba gurinki na zo ba, ba dole sai kin gane ni ne

Ta yi murmushin shakiyanci.

 Yarinya a falona kike zaune, ki iya kalaminki

 Karki sake kirana da yarinya ni da ke matsayi daya muke

 Karya kike Wallahi har abada ba zaki taka matsayin da na taka ba, ko auren Zafeer kawai da ni ke kin san na ci ki da yaki, kwadayayyiya mai gudun dangi, butulu marar kunya, ashe har kina iya daga kafa ki tako a gidan da Zafeer yake rayuwa da iyalinsa? Bayan kin gushe shi saboda kina ganin ba shi da arziki, to wai me ya dawo da ke yanzu? Har kike ikirarin matarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login