Showing 144001 words to 147000 words out of 227321 words

Chapter 49 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1538

sun san baka da shi, wasu kuma suna bakincikin abun da zaka samu ma

Cewar Baba Garba.

 Haka ne, ni farko ma na dauka shi zai ce yana son Noor ne, kuma na ga kamar ba haka ba ne, ai ba dan kar ta ba ni kunya irin na wacan karon ba, Wallahi da sai na aura masa ita saboda kunyar abun da yake min, ya rike amanar abota

Jin hakan a gurin Baba ya saka na ji Kareem ya kara kima a idona, tabbas shi din mutumen kirki mai son taimako, babu ruwansa da duba matsayi ko girma. Haka dai na yi ta jin suna ta hirarsu ta yan'uwa yana fadin mutanen da suka taimaka masa a yanzu da kuma aurena na farko. A lokacin da suka dauko zancen abubuwan da zai kai na ji Baba Garba yana tambayar Baba.

 Toh yanzu kai Magaji ka siyo mata kayan dakin ne?

 Ni babu abun da na siya kuma babu abun da zan siya, ai ya fada mana da zarar an daura aure za su wuce can Lagos din da ita, to taya za a tsaya wani siyen kaya nan tun da nan za su zauna ba? Dubu hansin zan bashi a cikin kudin sadakinta idan sun je can ya siya mata abun da ya kamata

Anty Larai ta ce

 Aa gaskiya be dace ka yi haka ba, ai ana son ka siyama yarka girm????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a, ko dai ba mai tsada ba kowa ya san karfi ba daya ba, sai ka mata na iya karfinka saboda Allah magaji

 To wai me za'a siya ma? Uwarta ta aiko mata da kaya, kuma ba a nan za su zauna ba, ai kayan sun isheta komai

 Kayan da ta aiko mata kayan kitchen ne, kai kuma naka kayan daki ne da dan wani abu da za aka bawa ango

 Aa aa aa karya haram ba zan iya kashe kaina ba, yarinya suka ce suna so ita za a ba su, ita da Allah yayi jininta jinin masu kudi me zai kai ni wahalar da kai na siye wasu kayan daki? Hafizu ma Allah ya masa rahama da kansa yace ba zai na yi komai ba ya dauke min komai

 Toh shi wannan ai be ce ba, gaskiy...

Bata karasa ba Baba ta tari numfashinta.

 Ni fa dan abun da na samu, gyaran gidana zan yi na kuna kallon yadda gidan nan gaba daya ya canja babu wani taimako da na samu, sauran kuma sai na bude shago na zuba kayan masarufi

Jin cewar Baba ba zai yi min furniture ba ya disashe farinciki dake zuciyata, wata kila shi din ba kamar Hafiz ba ne da zai ce ya yafe komai, hakan kuma wani abun gori ne a gurina da danginsa da ma kishiyata. A ranar aka yi min kunshi mai kyau mai ja sosai, da dare kuma Hana da kawata Zainab suka raka ni na tafi gurin gyaran gashi domin ni ba mace ce ma'abociyar son kitso ba. A nan na samu damar fada musu damuwata, Hana ta nuna damuwata da jin cewar Baba ba zai siya min komai ba har ma take cewa.

 Yanzu da ace Mama bata aiko da wannan ba haka za'a kai ki ko spoon din aiki ba ki da shi?

Na sake jin babu dadi domin Baba baya kyautata min a rayuwa, wasu hakokan da ya kamata uba ya saukewa yarsa shi baya sauke min su.

 Noor kar hakan ya daga miki hankali, Baba ya fadi gaskiya idan ba nan za su zauna ba, babu amfanin siyen kaya, daukar kaya daga Kano zuwa Lagos wani aiki ne babba, kuma kin ga yace ba a nan za su tare ba

Zainab ta shiga kwantar min da hankali, na dube ta na ce.

 Amman wasu ko ba a garin za su zauna ba, ana yi komai Zainab a garin da miji yake, saboda can aiki yake yi ai, wata rana zai iya dawowa mahaifarsa

 Ki gode Allah Noor, idan mijinki mai sonki ne duk ba zai ga wannan ba, kuma zai rike ki amana, idan ma Baba bai miki ba ke zaki iya yi ma kanki ko kuma shi mijinki yayi miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki Noor

Duk yadda zata karfafa min guiwa sai da ta yi har ta yi nasarar kwantar min da hankali na dan sake raina. A napep muke ta labarin Zafeer da sabon auren da aka ce yayi a gurinta nake jin labarin irin hidimar da aka yi na bikin auren domin Zainab tana abota da kanwar Zafeer sosai, shi ma kuma yana good time da ita ko a lokacin da muka samu matsala ita yake aikowa gurina.

 Amman kin ga yana dariya?

Na tambaya ina jin bakinciki marar misaltuwa kamar ba ni na fara guje masa.

 To zai ki dariya ne Noor? Ai dole yayi farinciki ko yaya ne, wata kila ma yanzu ya manta da soyayyarki, domin yar masu kudi ya aura ance mahaifinsa ma shi zai sama masa aiki, daman ita yarinyar tana aikinta, ance ta girme shi da shekara uku

 Allah ya saka masa tun ba ayi nisa ba, ya samu wadda ta fi ni komai

Na fada hawaye na sauko min, Zainab ta dube ni.

 Noor har yanzu kina son Zafeer wai?

 Unconditionally, har abada zuciyata ba zata daina son Zafeer ba, ba zan taba son kowa kamar yadda na so shi ba

Shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa Uffan daga ni har su. Har muka isa gida hawaye nake, haka na shiga gida rai babu dadi zuciya na kuna, kiran da Abdull yayi ta min ma kasa dagwa na yi saboda damuwar data haifar min da ciwon kai.
Washe gari ya Friday gidanmu ya cika da makota da yan'uwa na kusa da nesa maza da mata, kusan wannan bikin ma kamar ya fi wacan yawan jama'a.

Bayan saukowa daga Massallaci na fita waje na yi alwala na shigo dakinmu kenan wayata ta yi kara, dubarwa da zan yi sai na yi arba da number Abdull, a take na amsa kiran na kara wayar a kunnena.

 Hello...

 Congratulations an daura aurenmu, Alhamdullahi

Gabana ya fadi har sai da kaina ya sara, kai kace ban tsammaci zuwan wannan ranar ba.

 Allah ya ba mu zama lafiya

 Ameen

Ya amsa sannan ya kashe wayar, shi ne mutum na farko da ya fara min albishir, kamin gidan mu ya dauki guda har Hana ta shigo dakin tana rangwada guda tana farinciki, sabanin wacan auren na farko da bata yi farinciki ba. Madadin na yi murna sai na fashe da kuka na zube a gurin an rufe idona ina ta rutsar kuka kamar wanda aka sake yi ma auren dole.

Haka na wuni ban iya cin komai ba, sai da Anty Larai ta siyo fura ta dama min ta saka kankara sannan na iya sha shi ma ba da yawa ba, yan'uwan Abdull sun leko mana wuni, daga bangaren mahaifiyarsa da kuma na mahaifina. Angon kuma be duro gidan ba sai isalin karfe takwas na dare. A lokacin da na kira a waya ya sanar min yana waje, sai na jin kunyar fita a dole na yi masa karyar Gwaggonta tace ba zan fito ba.

Ban san da wa yayi magana ba, sai ga Baba ya shigo yana fadin na tashi na leka waje mijina ya zo tare da abokinsa yana son magana da ni. Jin cewar yana tare da wani ya karfafa min guiwa kuma ya rage min kunyar da nake ji ta mutane. Hana ta dauko turare ta kara fesa min, Anty Larai kuma ta saka na cire lace din dake jikina na saka farar lafaya sannan na fita gashin kaina na yawo domin ban saka ribbon ba.

Nesa da gidanmu ya faka ta inda mutane ba za su ganshi ba, ni ma ba dan na kira shi a waya ba ba zan iya gane shi ba. Kamar ana daure min kafafuwa haka na karasa gurin motar sai ya sauke gilashin ya kunna hasken wayarsa ya haska fuskata.

 Amarya ba kya laifi, kyakkyawar amarya mai tsaye siririya duk ni kadai

Kunya ta saka ni sauke kai kasa ina murmushi.

 Shigo motar mana, kar na gajiyar da matata

 zan iya tsayuwa a nan

Bude motar yayi ya fito ina kallonsa ya kama hannuna ya zagaya da ni ta baya ya saka ni a back seat sannan shi ma ya shiga. Rabon nake ko zan ga abokinsa amman ban ga kowa ba.

 Ka ce kana tare da abokinka...

 Na fadi haka ne saboda na rage miki kunyar dake kanki

Ya yana maganar kallon bakina zuwa kirjina.

 Ko ban kyauta ba?

Kamin na amsa na ji na kara matsowa kusa da ni sosai har ina jin numfashinsa, ta dama da ni ya lakamo hannunsa yana lasa cikina a hankali.

 Ya gajiyar biki?

 Alhamdullahi

Ina kokarin cire hannunsa sai ya juyo da fuskata zai sumbance ni, na dauke kai na dauke numfashi ina jin wani iri. Murmushi yayi ya saka dayan hannunsa ya juyo da kaina.

 Da alama dai kunyar nan zata cutar da ni

Ya sumbanci goshina ya shinshina hancina kamar mai kokarin tantance wani abu. Rufe ido na yi jikina ya hau bari ina jin wani bakon al'amari. Hakan kuma be hana shi kai bakinsa cikin nawa, sai da na ji yana kokarin wuce gona da iri tukuna an matsa baya na rike hannunsa.

 Abdull za a iya ganinmu fa

 Babu wanda zai gani bakin gilashi ne

Ya sake kai hannunsa a jikina sai na tare.

 Baba zai ga na dade

 Me yasa kike ta guje min ne Noor? Kin san how long nake ta jiran wannan ranar? Ni fa yanxu halalinki ne

 Na sani amman ban tare ba, kuma na fito gida ne da sunan zaka yi magana da ni

 An riga an daura ko da sadakin da na biya kin zama mallakina balle kuma an daura, sadaki shi ne aure ai wasu da zarar an biya sadaki ma suke sakewa juna balle mu da har an daura mana aure

 Auren dai shi ne gaskiya, amman biyan sadaki ba aure ba ne, tun da har ana daura mana ai ya kamata mu yi hakuri har zuwa lokacin da za mu tare babu dadewa

 Allah yasa zan iya jira, sai monday zamu bar garin nan Noor, kuma ba wani abu zan aikata da ke ba a yanzu, it's just a kiss, ina kokarin wayar da ke kamin mu tare domin na lura kamar baki gama fahimtar rayuwa ba

Na yi murmushi karfin ina mamakin yadda yake da rawar jiki haka, kuma ina yaba kokarin Hafiz na jurewa da yayi ashe shi din jarumi ne sosai. Na matsa ta gefen da kofar take na bude na fita.

 Sai da safe

 Sai da safe my shy Bride, an hana ni kiss ko? Zan rama

Murmushi na kawai abun da na yi na fara takawa ina tafiya har na isa cikin gidanmu. A dare wata kanwar Mama ta cika min ciki da wasu kayan mata har sai da kaina ya fara ciwo. Haka na kwashe kwana biyu ana ba ni abubuwan nan da bana bukata, ban kuma isa na ce aa sai a rufe ni fada.

A cikin kwanakin da na yi a gida bayan daura auren, babu ranar da Abdull baya zuwa da dare a kowa dare kuma sai yayi kokarin taba ni har ya wuce gona da iri. Baba yayi min nasiha da kuma jan kunne, ranar Lahadi Mama ta aiko da mota aka dauki zuwa gidanta ta yi nata nasihar, acan na kwana sai washe gari na dawo. Na dawo gidan na tarar Hana ta gyara min kayana ta kintsa komai, a take na fara jin kewar gidanmu duk kuwa da kasancewar ba wani dadin zaman gidan nake ji na.

Ranar Monday da misalin karfe 2pm Abdull ya iso gidanmu tare da wani abokinsa da kanensa mata biyu da sunan za su dauke ni. Sai Baba ya tsayar da shi jege suka tattauna, ban san me suka tattauna a kai ba, bayan sun gama na fito ina sanye da green abaya da mayafinta sai mask da na saka na rufe fuskata. Handbag dina tana hannuna tare da wayata da karamin akwaitin da yace da shi kadai zamu tafi a yanzu saboda jirgi zamu shiga.

Yace daga baya zai aiko da mota a dauki saura kayan nawa da kuma yan'uwana domin su ga gurin da muke rayuwa. Da ace ina da iko da tun a yanzu zan tafi da Hana domin ta rage min kewar gida da kuma bakuntar gurin da ban sani ba. Na yi kuka sosai ina jin kamar wata kasar zan tafi ba iya Lagos ba. Har gurin mota Baba ya rako mu tare da Hana da Umma, na shiga gidan baya tare da kanensa shi kuma yayi ma Baba sallama ya shiga front seat kanensa kuma yaja motar sai airport....


Ban taba ganin airport a fili ba sai a ranar da muka isa gurin, ashe babban guri ne mai hada hadar jama'a mun zauna a wani guri jiran jirgin bayan an gama yi mana check-in. Id card din dake hannuna nake ta kallo, sai dai zuciyar da tunanin yana can wani guri. Hannun Abdull na ji cikin nawa yana kokarin saka yatsunsa cikin nawa.

 Amarya are you Okay

Na kalleshi sai na ji hannunsa a fuskata yana share min hawayen da ban san taya suka zubo ba.

 Har kin fara missing din gida ne?

Ban yi magana ba na kalli kanensa dake can gefe zaune suna ta hirarsu, jira suke har sai jirginmu ya tashi sannan su koma gida.

 Ka yi min wani alkawari

 Cewar ba zaka taba cutar da ni ba

 Me yasa kika fadi haka Noor

 Ba komai ni dai ka yi min alkwarin rike ni amana, ina fatan wannan auren da muka yi mutuwa ce kadai zata raba

 In Shaa Allahu, na miki alkawari ba zan taba cutar da ke ba Noor

Ya ba ni tabbacin da nake bukata sannan ya amsa kiran dake shigowa wayarsa ban san da wa yake magana amman na ji yana fada masa lokacin da zamu sauka. Ni kuma na juyar da kaina ina kallon wani gafen.
Kalamansa sun saka na ji hankalina ya kwanta, na samu natsuwar da na rasa.

Na sani mutum ba zai taba samun abun da yake so dari kan dari ba, shiyasa na yarda da wannan kaddarar kuma na shiryawa wannan zaman aure da dadi babu dadi zan zauna, ko da Abdul zai rika yanka naman jikina ya siyarwa ne. Zan jure ko wace kalar azaba da ukuba ko da kuwa ita ce zata yi silar ajalina...

An samu delaying gurin tashin jirgin, karfe biyu da mintuna goma sha biyar ya kamata mu tashi amman ba mu tashi ba sai misalin Karfe uku daidai muka tashi daga filin jirkin saman Aminu Kano, bayan mun yi bankwana da yan'uwan Abdull, har na ji ina ma ace ni ma nawa yan'uwan sun rakoni kamar yadda na shi suka yi. Abdull ne ya saka min belt ya sakawa kasa ya rike hannuna ganin yadda nake jin tsoro sosai lokacin da na yi arba da jirgin for the first time.

Sai da muka yi nisa da kasa sosai jirgin ya fara tafiya sannan ya cire min belt din shi ma y








https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0



Washe Gari na tashi da wuri saboda zan tafi asibiti, dan haka na gyara da wuri na fito falo, ina jin motsin Hana na nufi kitchen din na dan rikawa mata aiki.
Ina tsaka da kashe socket ta yi min wata magana da ta saka na kalleta.

 Noor ina son na tafi gida

 Me yasa Baba ya sake magana ne?

 Aa kawai dai ina son gida yanzu, na fi jindadin zama gida sama da nan

Na juyo da kyau na fuskance.

 Hana wani abu na yi miki ba daidai ba ko Abdull yayi miki?

 Aa ba ko daya, kawai dai na fi sha'awar tafiya gida ne

Na dan jimm ina mamakin dalilinta na fadar haka a yanzu, daman na lura yanayinta gaba daya ya canja.

 Hana mafarki kika yi marar kyau ko me?

 Ba komai ni dai kawai ina son na tafi gida

 To kije ki dawo ko kuma ki koma gidan gaba daya?

 Gaba daya dai nake son na koma

 Karatunkin fa?

 Zan hakura na san idan naje can Mama zata iya sakani idan Baba ya yarda

Na matsa kusa da ita domin babu ta yadda lafiya zata saka ya yanke karatunta ta koma gida haka nan kawai sai da dalili.

 Hana na san muma yawan samun tsabani da ke a gida, amman nan gidan aurena ne, idan kina ganin akwai abun da nake miki da baya miki dadi zaki iya fada min sai na gyara, idan kuma aiki ne kike ganin na sakar miki ragamarsa zan rika yin rabi, amman dan Allah ki zauna ina jindadin zamanki ina son yar'uwa a kusa da ni, ba ni da kowa nan zamanki a gidan nan yana rage min kewa

 Babu wani tsabani da zamu samu har ya saka na ji bana bukarki a kusa da ni, mu na samu tsabani a gida a nan ma zamu iya samu, saboda zama tare dole wata rana zaka ji an maka ba daidai ba, amman Noor ni ba zan iya cin amanarki ba

Ta rumgume ni tana kuka, jikina yayi sanyi sosai kalaminta na karshe ya saka min shakku a zuciya.

 Akwai abun da yake faruwa tsakaninki da Abdull ne?

Ta dago da sauri.

 Aa Wallahi Babu, dan Allah karki zarge shi ki lalata aurenki, Wallahi Wallahi na rantse miki da Allah babu wani abu tsakanina da Abdull

Hankali ya dan kwanta da ta yi min rantsuwa cewar ba tsakaninta da Abdull ba ne.

 To ya kawo zancen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login