Showing 3001 words to 6000 words out of 227321 words

Chapter 2 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1510

motar da kida yake tashi a hankali. Zafeer ya dago ya kalleni yana mikewa tsaye.

 Aa....

Ni kuwa na yi karaf na tare numfashinsa na ce.

 Eh ni kanwarsa ce

Zafeer ya kalleni da sauri sai daga masa gira.

 Yaya zan aje abincin a can

Shi dai mamaki ya hana shi ce min komai har na juya na nufi gurin da yake zama na aje abincin, juyowar da zan yi sai ganinsa na yi a bayana.

 Me yasa kika ce haka Baby Noor

 To ka sani ko sonka take yi, baka ga mai kudi ba ce

 Idan tana so, me hakan zai kare ni da shi

 Sai ta rika baka kudi

 And...?

He asked still confuse.

 Sai ka aure ni..

Murmushi ne abun da ya biyo bayan mamakinsa sai ya girgiza kai ya juya ya koma gurin motar, ni ma na bi bayansa ina murmushi ina tsaye gefensa yayi mata facin ya gama, sai ta cire gilashin idonta ta miko masa 5k. Tana masa wani kallo kamar wata rikakkiyar karuwa.

 Gashi you can keep the change

A take na ji ana kirkira wani abu mai kamar wuta kamar garwashi a zuciyata.

 Na gode

Ya furta sannan ya juyo ya kalleni.

 And wannan matar da zan aura ce In Shaa Allah, so ba kanwata ba ce I'm her fiance an mana engage da ita shekara uku da suka wuce

 Wow Maa shaa Allah Allah ya sa alheri

Ta fada sannan ta rufe gilashin motarta ta yi mata key ta kama hanya. Na dube shi

 Me yasa ka fada haka? Gashi har ta baka kudi mai yawa ma tun yanzu

 Ta saba ai duk lokacin da ta zo kudi mai yawa take badawa, and ni bana jiran kudin wani na kusa kare karatu kuma ina wannan aikin waya san me zan zama nan gaba? Ban ga amfanin yin karya ba saboda na ci kudin wani, and be kamata na boyewa kowa a alakarmu ba i love you so much ban ga dalilin da zai saka na boye alakarmu a guron wani ba, you're my life Noor ke tawa ce har abada

Cikin tsakiyar idanuwana yake kallo yana kitsa min maganar da ta dade da zaunawa a zuciyata. Na yi murmushi wutar sonsa na kara huruwa a zuciyata.

 Mu tafi gida Zafeer

 Jira ni a nan zan bawa oga kudinsa sai mu tafi, i love you

Ya kashe min ido daya tare da yi min blow kiss. A gurin ya bar ni sai da ya bawa ogansa kudinsa ya dauko kayan aikinsa da cooler da na kawo masa abinci muka kamo hanyar gida muna tafe muna hira. Har muka shigo unguwar mu dabam tsakanin gidanmu da gidansu gida biyar ne a tsakani sai dai be shiga gidan na su ba duk da Kasancewar ya fi kusa har sai da ya rakani har kofar na mu gidan sai da na shiga sannan ya juya.






#KhadeejaCandy


https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx


Assalamu Alaikum...
Ina talata muku
KHADEEJA CANDY STORE >?p?=?L?
Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo.

''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


5??5?!?5??5?)?5?-?5??5?+? -2


Daga bakin zaure na tsaya ina leka ciki sai na hango Hana tana daka a turmi Mama kuma tana zaune gaban murhu tana aikin hura wuta. Yaya Nabil kuma yana daga gafe yana wanke wandonsa da talkami.

 Ina kika je?

Na kalli Yaya sai na jingina da kofar bana son amsa masa tambayar domin na san fada zai min ni kuma ban iya karya ba komai za ayi min sai na fadi gaskiya.

 Ba magana nake miki ba

Ya daka min tsawa, na dan matsa baya na saka hannu a baki ina cin akaifata.

 Yaya Mama fa ta cinye abincin da ka kawo kuma tace zata min duka shi ne na bar gidan na tafi gidansu Zee mamanta ta ba ni abinci bayan na ci ta zuba min wani a kula na kaiwa Zafeer

Yaya ya girgiza kai yana murmushi.

 Yanzu ke gidan ku ana kokuwar yadda za a cefane a girka masara amman kin samu abinci sai ki kaiwa saurayinki? Noor Allah ya shirya ki

Mama ta tabe baki

 Ai wannan yarinyar abu ne mai wahala ta yi jinkaina, duk abun da ta samu a duniyar nan sai dai ta kai ma saurayi babu ruwanta da ni

 Toh ni Mama me nake samu? Kullum fa babu ne a gidan, kuma ai kece kika ce dukana zaki yi shiyasa na kai masa

 Kya ji da shi dai, wuce ki daki kasan gadona ki dauki kudin adashe ki kai ma Assabe ki ce ga zubi na biyar nan

 Mama yanzu kina da kudin adashe kika hana ni na babur din da zan tafi bikinsu Salwa?

 Kudin adashen zan baki ki tafi biki? Wa nake ma dashen ba ku ba? Kudin kayan aure nake tara muku ai

Ina jin haka na san Mama ta sauko kenan dan haka na wuce cikin gidan na shiga dakinta na dauko kudin a gurin da ta saba ajewa na fito ina kallon Yaya Nabil da zai zubar da ruwan kumfa.

 Yaya na kawo kala Waya ka wanke min dan Allah?

Wata uwar harara ya watso min sai na yi saurin barin jikin kofar dakin na nufi hanyar waje.

 Kawo kala daya amman

Ban yi mamakin jin haka daga gareshi ba, daman Yaya Nabil mutum ne mai sauki kai a gareni. Na juyo cike da kuzari da jindadi na nufi dakinmu na dauko tufafina na sallah babba da mayafin sai kuma na tuna ba lallai ne Hana ta yarda ta min kwaliya ba dan haka na dauko abayata na mika masa ta.

 Gashi Yayana na gode

Na mika masa cike da ladabi.

 Kuma na fada miki ki daina zuwa gurin aikin Zafeer ko? Ba yau na sha miki magana amman baki ji

 Abinci kawai na kai mishi idan ba yace na kai mishi abinci ba ko kuma na zo na karbi abu Wallahi bana zuwa, Yaya ni ma fa ina da hankalina

Be sake ce min komai ba ya jefa abayar a ruwa ya fara wankewa ni kuma na nufi kofar fita ina yi ma Hana gwalo. Domin na san idan ita ce ba zata wanke min ba ko da kuwa zan yi hauka.

 Dan Allah can mai kayan aro

 Na ji dai na ji dai ba zan cire ba

Na fice abuna ina tafiya a natse, daman can bana kama da marasa tarbiya ko natsuwa zakewar da nake abu ma idan na san mutum ne ne nake yi, idan ban sake jiki a guri ba ko uffan bana cewa. Cikin natsuwa na isa gidansu Talatu mai adashe na bata kudin kuma na fada mata zubi na shida ne kamar yadda Mama tace ma fada, sannan na juyo na fito, a kokarina na takaitawa kaina wahala na biyo ta kwararo kwararo domin ya fi sauki sama da mike hanya sambal.

Wani abun da ban saka rai da tsammani ba ashe rabon ganin wani abun ne ya biyo da ni ta hanyar, Abbah na gani tsaye kofar gidansu Gambo mai furar yan gayu rike da yar ledarsa baka sai gyaran riga yake. Ban yo mamaki ba domin akwai zaurawa a gidan har biyu da kuma yan matan da ba a taba yi ma aure ba. Rage tafiya na yi saboda na samu damar ganin wadda Abbanmu yake so cikin ?a?an gidan, amman hakata bata cin ma ruwa ba, domin har na kawo kusa da Abbah yarinyar bata fito ba.

 Abbah ina wuni

Na gaishe shi, sai yayi saurin dauke kai kamar be gan ni ya hade rai.

 Abbah gidan dawo (Fura) za a siyo maka kawo na karbo maka

Na fada cikin ladabi sai dai hikimar ba dan na siyo masa ba ne kawai sai dan na dalilinsa na zuwa gurin.

 Me kike yi a nan?

Ya daka min tsawa dai da na zabura zuciyata ta buga kamar zata fado.

 Mama ce ta aike ni na siyo mata fura

Na fada ina kokarin kare kaina, rufe bakina ke da wuya sai ga Bilki ta fito daya daga cikin yan matan da suke gidan ta chaba ado kamar wanda zata je gurin biki. Ganina tsaye ina kallonta ya saka ta juya da sauri ta koma cikin gidan ba tare da ta fito ba.

 Zaki wuce ko sai na ci ubanki?

Kalamin da Abbah yayi ya dawo da dubana gurinsa sai na matsa baya da sauri na kama hanyar gida ina tafe ina waigensa shi kuma be fasa cika yana min dakuwa ba (Zagin hannu kun san hausar mu da ta ku ba daya ba=??) har sai da na karya kwana a nan na boya cikin wani kwararo ina lekonsa, wayarsa na ga ya ciro yana dannawa sai dai kamin ya kai wayar a kunne wani kamin yaro ya fito yayi magana da shi, sai na ga Abbah ya mika masa ledar hannunsa sannan ya juya ta hanyar da na biyo ya wuce.

 Wato Balki da Abbah na take soyayya kenan hmmm

Na fada a raina a zahiri kuma sai na juya na nufi hanyar gida, kamin na isa zuciyata ta cika har ta kusa fashewa tsabar takaici da baki ciki. Ban tsaya sallama ba haka na shiga gidan na zauna kusa da Mama dake tuka tuwon masara na jera mata abun da ya faru sai hakki nake saboda bacin rai.

 Wata kila dai fura zai siya

Yaya Nabil ya fada kamar wanda be yarda da maganar ta ba.

 Wallahi ba wata fura, ai ba leda aka kawo masa ba shi ya bada ledar aka shiga da ita gidan, kuma har ce masa na yi ya kawo kudi na karbo masa sai ma zagina da yayi

Ina maganar ina yamutsa fuska.

 Wallahi sai na mata mugun duka

Mama ta nuna ni da muciyar da take tuka tuwo da alamar dake nuna babu wasa maganarta.

 Wallahi ko yatsa na ji ance kin nunawa Balki sai na ci ubanki sai na miki dukan da zai daukeki lokaci kina jinya, kuma kin san halin Abbanku ko? Bara saboda Amaryarss ya karya miki hannu, idan baki cire idonki akan Balki ba sai zai iya kashe ki ma

 Amman abun da yake be dace ba, irin wannan ke janyo raini s unguwa, kuma ko aure zai yi me zai yi da Balki Fisabilillahi

Cewar Yaya Nabil cikin da bakinciki. Mama tace

 To ya zaku yi Mahaifinku ne sai Hakuri, idan ya tashi aikata abu kun san babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa, saboda haka bana son na ji bakin kowa a cikinku, musamman ma ke Noor ke ce marar jin magana, duk dukan da za'a miki ba ki ji

Na turo baki gaba, domin Allah kadai ya san irin rashin mutum da zan yi ma Balki idan ta yarda da auri ubanmu.

 Har da leda baka ya bata

Na sake fada ina tuna dukan da yayi ma Mama dazun saboda tace ya bada garin masara babu kudin cefane.

 Daman ke kin iya karawa miya gishi ai, idan baki fadi komai ba to ba ke ba ce

Na juya ba kalli Hana na watsa mata harara. Yaya Nabil ya shafa kansa damuws na bayyana a fuskarsa.

 Wani lokacin sai na ji kamar na tafi na bar garin nan Wallahi, abubuwan da Abbah yake sun yi yawa, muna neman abun da za mu ci amman shi ta aure yake, yaushe ya auro Baaba Maryam yanzu kuma ace har ya fara tunanin auro wata, watan ma karamar yarinya sa'ar yarsa

 Kuma dazun saboda kudin cefa ne ya doke ki Mama wai bata godewa komai ya kawo Allah kadai ya san meye a ledar nan da zai bawa Balki

Mama ta rufe tuwon tana fadar.

 Cigaba karki fasa, tun da kin zama yar iska gararariyar gidan nan, ke idan aka ce kar ayi abu sai kin yi, ki cigaba

Ina jin haka na yi shiru da bakina ban sake cewa komai ba, daga haka maganar ta mutu sai dai kowa da abun da yake sakawa a ransa. Ana hada hadar kiran sallah magariba Abbah ya shigo gidan a lokacin duka hannayenmu suna cikin tuwon masarar da Mama ta girka. Ni da Yaya muna ci a kwano daya daman idan yana gida hade mana abinci nake saboda na bawa Hana haushi.

 Wa'alaikumussalam

Mama ta amsa mu kuma muka masa sannu da zuwa, sama sama yake kallo kamar wanda yayi arba da abun kyama, more especially ma ni.

 A kawo abincin ko sai ka yi Sallah

Abbah yayi kamar be ji abun da Mama take fada ba ya nufi wani dutse da ya saba zama yayi alwala ya zauna, ina ganin haka na cire hannuna a abinci na nufi butarsa na dauka na zubo ruwa kamin na karasa gurin da yake zaune sai fada ya biyo baya.

 Wai kamar ni a cikin gidan za a wurgar min da buta a waje, aje ta babu ruwa har sai na taba, saboda an rai min wayo kuma duk laifinki ne Hajara

Ban yarda na karasa gurin da yake zaune ba, na aje butar daga nesa domin yanayinsa yana nuna alamar ransa a bace yake kuma zai iya kai min duka. A madadin ya dora laifin a gareni sai ya juya ya kalli Mama yana nuna ni da hannu.

 Kin gani ko? Raina nin da kike min yara sun dauka, gashi ta kawo ruwa ta aje nesa da ni wato na taso na dauka

Mama ta kalleni kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru, domin yanayin tsayin da na yi ya nuna alamar tsoron karasa nake kusa da shi. Ko da kuwa ban aikata komai ba Abbah zai iya min duka balle kuma na gan shi a gidansu Balki kuma ya san sai na fada.

 Ba zaki dauki ruwan ki bashi ba sai na ci ubanki

Yaya Nabil ya daka min tsawa kamar ba shi ba, wata kila laifin da Abbah ya dorawa Mama ne ya fusata shi. Na duka na dauki ruwa, ban kai ga mika ma Abbah ba ya juyo ya kalli Yaya Nabil.

 Tooooo ka ci ubanta, ni kake zagi ba ita ba, daman ai ni na san ba kaunata kake a gidan nan ba, to sai ka ta so gani zaune a nan ki cinye ni, zan baka mai da yaji, daman ai yanzu abun da yara suke yayi kenan su kashe iyayensu, sai a fara saka ka a gidan redio ana hira da kai ka ga ka ci riba...

 Subhanallahi kar Allah ya kaddara mana wannan ranar ko bana raye, kar Allah ya nuna mana wannan ranar, bana fatan hakan

Mama ta fada tana cire hannunta a kwanon tuwon da take ci.

 Kina fata kan ai duk tarbiyar da kika koya musu ita suke yi, daga matan har mazan ita dai wannan babu albarka a tare da ita tun da aka haife ta komai ya lalace, gashi nan kuma yanzu tana daukar tarbiyar da kike koya Musu

Ya karasa yana nuna ni haka yake yawan fada, wai tun da aka haife ni komai ya lalace masa har yau be zama kowa ba.

 Dukan abun da zai samu bawa daga Allah ne Malam ka daina maida laifin a gurin Noor, kuma ni bana koya musu tarbiyar da zai saka su raina ka Allah yana gani ai

Mama ta fada cikin yanayin dake nuna kukan na son fitowa a idanuwanta da bakinta. Sannan ta kalli Hana ta ce.

 Karbi ruwa ki ba shi wata kila tsoro take ji kar ka doketa kasan halin Noor Malam ba sai an fada maka ba

Kana ta kalli Nabil

 Tashi ka tafi gurin Sallah

Ya cire hannunsa a tuwon da tuni ya dakatar da cinsa ya mike tsaye ba tare da ya wanke hannun ba ya fice a haka kamar wanda baya son kara minti daya a gidan. Hana ta karbi ruwan hannuna ta karasa kusa da Abbah ta aje masa, sannan ta Abbah ya kalleni.

 Kuma bari na fada miki Noor, idan na ji yarinyar da fadi wani abu akanki sai na lahira ya fi ki jindadi, kin san sau uku ina neman aure kina lalatawa ko? Allah yasa ki aikata wani na ji

Na yi shiru ina tsaye a gurin kamar hoto har sai da Mama ta yi min alama da na bar gurin da kai. Sannan na kauce na koma na dauke kayan da muka ci abinci na kai gurin da muka saba ajewa, juyowar da zan yi sai hawaye ya sauko a ido. A cikin kalaman da Abbah yake yawan yi min babu mai bata min rai kamar cewar ni din ba alheri ba ce a tare da shi, kusan ya fi tsanata fiye da Hana da Ya Nabil. Hannuna na saka na share hawayena na nufi wata butar na dauka na zuba ruwa na nufi bandaki, ina fitsari ina hawaye, ban yarda na fito ba har sai da Abbah ya fice daga gidan, ba zan iya fadar cewar ni ce kadai ban san dadin mahaifi ba, kusan dukanmu haka muke tun da muka bude ido mun samu mahaifinmu mutum mai wuyar sha'ani da baya sakewa da iyalansa duka kuma babu kalar wanda be mana, musamman ma ni da na kasance marar jin magana. Abu ne mai wahala wani kalami mai dadi ya fito daga bakin mahaifinmu izuwa garemu, idan ma mun dada masa to zai bar abun a ransa ne ba zai yi magana ba, idan kuma muka bata masa a take zamu gani.
Mahaifina wani kalar mutum ne mai wuyar sha'ani mai wuyar mu'alama ga Iyalinsa, kuma mai son zuciya da zafin hannu abu kadan zai doke mu ko mahaifiyarmu a gaban idonmu. Rayuwar da muke yi a cikin gidan mu izuwa yanxu ya ci ace mun saba da ita amman ni na kasa sabawa da hakan, kullum ganin abun nake kamar sabo.

 Noor ba dai kuka kike ba?

Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login