Showing 171001 words to 174000 words out of 227321 words

Chapter 58 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1525

zan sake samun shi gida mu yi magana karki daga hankalinki

 Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...

Safeena ta fada da karfi, Kareem yayi hanzarin kashe wayar, fuska a hade ya jefawa Safeena mugun kallo da idanuwansa da suka gama canjawa. Wani marin ya sake kai wata, ya saka kafarsa ya kwashe nata kafafuwan sai da ta fadi kasa, ya daga kafarsa ya daki bayanta sai da ya amsa, sannan ya cire belt din jikinsa ya fara zuba mata ba ji ba gani...
Duka yayi mata sosai kamar wani ubanta sannan ya fice ya barta a gurin tana ihu tana kuka. Motarsa ya shiga ya kama hanyar tafiya ganin yarsa domin ya san a yanzu su kadai suke rage masa, aikin ma baya jin zai iya tafiya a yau tun tashinsa baya jin lafiya balle kuma yanzu da abubuwa suke juye masa. Sai da ya shiga unguwa ya ji ba zai iya karasa family house dinsu ba, nesa da gidan ya faka mota ya kwantar da kujerarsa ya jinke hannunsa ya rufe ido yana nadamar dukan da yayi ma Safeena, domin be tana kai hannunsa yayi ma mace duka irin wanda yayi mata a yau.

Yana cikin motar ya aka kira sallah azahar sannan yaja motar daker yana jin kansa na ciwo kamar zai tsage gida biyu ya isa masallacin unguwar yayi sallah ya sake komawa motarsa, sannan ya karasa gidansu. A harabar gidan ya faka motar ya kashe yana kallon flowers din da suke gabansa amman zuciyarsa tana can wata duniyar. Wayarsa ya ciro ya duba number Noor ya sauke ajiya zuciya ya kai sau takwas sannan ya danna na aika mata kira cikin tsoro jikinsa har rawa yake.

Shiru yayi bayan ta daga kiran, sai kuma ya rasa me zai fada mata, ya zai fara mata bayanin komai ya zai wanke kansa, ta ina zai fara fahimtar da ita, be ma yi tsammanin zata amsa kiran ba.

 Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!

 Noor

Zai yi magana ta yanke kiran, runtse ido yayi sosai, ne bude ba sai da ya ji an bude gate din gidan, direban dake dauko yaransa daga makaranta ne ya dauko su ya faka a inda ya saba faka motar. A yake Kareem ya nemo kwarin guiwa da juriya ya sakawa zuciyarsa ya bude motar ya fito cikin karfi hali yake takawa yana murmushi ya nufi yaransa da suka nufo shi suna.

 Oyoyo Dady Dady Dady

Kamin ya karasa gurinsu su ma su karaso gurinsa ya yanke jiki ya fadi kasa ribbbb.

 Dady.....!

Tine ta saka ihu ta saki bag dinta da lunch box din dake hannunta ta kama mahaifinta tana kiran.

 Momy Hajiya... Anty Khadija... Yaya Aaryam... Dady na ya fadi... Dady...





NOOR POV.

Sai da na zabura a lokacin da yayi hanzarin yanke wayar, kenan yana tare da Safeena har yanzu? Kuma yake fadar yana so na? Yake fadar ya tuba? Yake fadar yayi nadama? Me ya kai shi gurinta? Me yasa ma zai amsa wayata a gabanta.

 Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...

Maganar Safeena ta sake nanata kanta a kunnena, zai iya zama gaskiya shiyasa dazun ya daure ni da kalamansa, namiji zai iya aikata komai domin ya samu biyan bukatar kansa. Na mike tsaye zuciyata na raya min Safeena ce matar da Baba yace ta same shi da maganar, ita kuma ta ji ne ta gurin Kareem.
Ya fada mata sirrina kamar yadda ya fada min nata, me yasa yake haka? So yake ta jefa ni a matsala ta yadda zan rasa kowa sai shi kadai shiyasa yake taimako na a ko da yaushe? So yake na rasa kowa na zama tare da shi shi kadai, shi kuma sai ya juya ni a yadda yake so? Yanzu na gane dalilin duka taimakonsa na gane manufarsa, na gane buri da bukatunsa.

Sai bayan Sallah azahar sannan kiran Kareem ya shigo wayata, na sani daman zai kira ko ya zo domin kare kansa, kuma na shiryawa duk wata karyarsa sai na ga iya gudun ruwansa. Na amsa kira sai yayi shiru ba tare da ya ce komai ba.

 Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!

Na fada masa kai tsaye hawaye na zubo min zuciyata na zafi because this is the most hardest words i had ever said to someone, who's there for me in every Situations, rabuwa ce irin wanda rai be so ba amman dole na yi.

 Noor...

Zai yi magana na yanke kiran ba tare da na tsaya na saurari abun da zai fada ba. Na dafe zuciyata ina kuka he's?someone?who's ?always?been?a?good?friend?to me, but the fact that i know yana da manufa na yin haka ya yanke duk wani hanzari, ya ture duk wani uzuri nasa, ba zan iya yarda na lalata rayuwa saboda namiji ba.
Karfin hali na yi na fita na siyowa Hana maganin zazzabi domin jikinta yayi zafi sosai fever ya rufe ta.

Ana gama sallah la'asar ban tsaya cin abincin rana da Umma ta sauke ba na yi mata karya cewar Zainab ta kira waya na kaiwa mahaifiyarta su yi magana saboda wayar mahaifiyarta ta lalace.

 Ki dawo da wuri, domin Babanki tun da ya fita be dawo ba har yanzu kin san kuwa yana hanya a yanzu, idan ya dawo be same ki ba, ke ce a ruwa

 Ba zan dade ba In Shaa Allahu

Na saka talkamina ina kara sirranta jakata dake boye a hijab dina na fice daga gidan, kai tsaye titi na nufa daman manufar ta samu dalilin fitar ne. Ina kokarin taron Napep na muka yi ido hudu da Zafeer zai karya kwanar gidanmu da wata kafirar mota mai kyau da kyalli. Wuce ni yayi ya shiga kwanar ni kuma na shiga Napep din na fada masa inda zai kai ni, yana tafe ina mamakin mi ya kawo Zafeer a nan ya domin tuni ya dauke iyayensa daga unguwar saboda likkafa ta yi gaba a wata unguwa mai kyau suke zaune a yanzu.

A kofar gidan Abdull kuma gidan Safeena mai napep din ya sauke ni na bashi kudinsa na shiga gidan bayan mun gaisa da mai gadin, har yake fada min bata dade da shigowa gidan ba. Da manifa biyu na zo gidan an roketa alfarma ta saka mahaifina ya janye ko kuma na yi mata ta karfi.
A bakin kofar falon na tsaya na bude jakata na dauko wayata na sakata a airplane mode sannan na kunna recording na shiga falon ina sallama, wayar na rike a hannuna.

 Wa'alaikumussalam, bakar macijiya me kuma ya kawo ki?

Ta amsa min tana tsaye rike da maganin da ban san na miye ba a hannunta, fuskarta ta kumbura daga bakin inda yake ina kallo a jikin, fuskarta da kafadarta zuwa kafafuwanta da hannunta sun yi ja, alamar an mata duka.

 Magana na zo mu yi dan Allah ki saurare ni Safeena

 Ina jinki

Na matsa kusa da ita na fara mata magiya da raunaniyar murya.

 Idan kina tunanin wani abu ne a tsakanina da Kareem, Wallahi babu dan Allah dan girman Allah ki yi hakuri da abun da na yi miki, ina rokonki alfarma ki saka Baba ya janye shari'ar nan

 Ashe kin san kin cutar da ni, wato yanzu kina son mu sasanta dan kar auren uwarki ya mutu kuma asirin kawarki ya tonu ku kunyata ko? Amman ke kika son kunyata ni, ki bara ni da abun da nake so, kin yi iya yadda kika iya har sai da kika fitar da ni a zuciyar Kareem, hakan be miki ba sai da kika auri mijina, hankalinki be kwanta ba sai da kika fada masa cewar dan da na haifa ba jininsa ba ne

 Cikin fushi na fada masa hakan, kuma ba dan ya sake ko ya juya miki baya ba, kawai na fada ne saboda a lokacin raina yana bace ne, na bakinciki abun da yayi ma kanwata

 Ai kin ci riba idan bibiyar mazan mutane yana da kyau kin gani ai, kin gaji kwadayi gurin ubanki, gaba daya kin firgita min tunani, kin saka Kareem ya tsane ni mijina ya tsane ni, mijina yana garin nan amman ya ki ya zo gidana, yau kuma Kareem yayi min abun da be taba ba, kin saka masa wani banzan hali da ba na shi ba, na tsane ki Noor

Na risina kasa ina rokonta.

 Dan Allah ki taimaka min Safeena, Wallahi ba zan fadawa kowa cewar kin haihu a waje ba, dan Allah ki fadawa Baba karya kike ya janye shari'ar nan

 Fadi na nawa kuma, ai kin gama fada tun da kika fadawa mai gayya mai aiki, kin fadawa Abdull ya sani to miya rage? Wato Kareem fada miki ni na fadawa mahaifinki haka ko? To be yi karya ba ni na fada, ni kuma shi ya fada min, ki daina biye masa kina yaudarar kanki ni dai na riga na harbo jirginsa, kuma babu abun da za a fasa idan kina son ubanki ya fasa shari'a to ki fadawa Kareem ya aure ni, ya kyale ki shikenan nake bukata sai ki samu salama idan ba haka ba kin fara ganin matsala kenan a rayuwarki tafi ki bar min gidana

Ta fara turani, sai na tashi na share hawaye na fice daga falon, ban yi nisa da gidan ba na shiga contact list din na whatsapp na tura mata recording din da na yi saving sannan na buga mata warning.

 Ko dai ki fadawa Baba karya kike ki karyata kanki, ko kuma na tura audio nan a gurin surukarki da mahaifin mijinki da kanensa kuma da gaske nake na baki daga yau zuwa gobe

Ina fitowa na cire airplane mode din na kunna data da domin sakon ya samu isa, sannan na tari Napep na shiga, gidan Mama na nufa domin labarta mata halin da ake ciki na tabbatar bata san wainar da ake soyawa ba, idan har ta sani zata kira ta fada min ko ta tambayi wani abu, wata kila ita ma idan ta saka baki Baba zai aminta ya sauko. Sai dai na yi rashin sa'a ban same ta a gidan ba, sai mai aikinta na samu tana kallo a falo.

Ruwa kawai na sha na kira wayar Mama, ta amsa ni ta fada min bata gidan tana gurin gaisuwa wata kanwar mijinta mahaifin Abdull ce ta rasu.

 Mama idan kin dawo ki kira ni akwai maganar da zamu

 Ki jira na dawo, lafiya na ji yanayinki haka?

 Mama bari sai kin dawo

Kiran Mama na yankewa, sai ga kiran Baba ya shigo wayata ina dauka ya fara zagina yana tambayar ina na tafi.

 Ina gidan Mama

 Maza maza ki dawo gida yanzu nan

Na mike tsaye babu shiri na yi ma mai aikin sallama na fice. Tare muka fito gidan da Abdull yana cikin motarsa ni kuma ina tafiya a kafa, ban yi mamakin ganinsa ba domin gidan ubansa ne, kuma Safeena ta fada cewar yana gari. Sai dai abun da ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni a lokaci daya tsayar da ni da yayi yana son magana da ni, ashe karfin halin maza har ya kai haka.

 Magana ce kawai zamu yi Noor dan Allah ki shigo

Na yi kamar ban san da wanzuwarsa a duniya ba domin babu wanda na tsana irinsa kallonsa ma idan na yi bakinciki nake ji.

 Zamu yi magana ne akan karar da mahaifinki ya shigar, ina nan ya kawo sammaci, magana ce da zata sama mana masalaha gaba dayanmu

Na tsaya wata idea na zo min, sai na saka wayata a recording kamar yadda na yi dazun idan na samu yadda nake so, zan iya mixing abubuwa su tafi yadda nake so. A gurin da na tsaya ya faka motar ya bude min front seat.

 I know you hate me but please ki shigo mu yi magana magana ce ta sirri

Na kalli gurin sannan na shiga na zauna.

 Na ga shigowarki, na so na miki magana amman na san ba zaki saurare ni a lokacin ba, shiyasa na jira har kika fito

 Ka ce zamu yi magana akan abun da ya shafi Shari'a ne ba wani abu ba, idan baka ka abun fada zan fita

Na fada a tsawace jikina har bari yake ji nake kamar ace akwai wuka kusa da ni na caka masa.

 Akan shari'ar da mahaifin ya shigar ne, baki tunanin hakan zai iya shafar ki ya shafi kanwarki? Ni fa ban aikata komai ba? Wane tabbaci kike da shi cewar ni na yi mata fyade?

Na dube shi.

 Baka aikata ba karya ake maka?

Sai yayi saurin dauke idonsa.

 Na ji na aikata, amman ai kaddara ce da bata wuce kowa ba, kuma ke kin san ba zan amsa wannan a kotu ba, kuma baku da wata shaida, na san ubanki ya shirya haka ne saboda kwadayi irin nasa, zan bashi kudi enough, ya janye karar nan karya bata min suna ni da mahaifina, abun da zai biyo baya ba zai muku dadi ba

Kalaman da suke fitowa bakinsa sun karfafa min guiwar aje wayata a cinyata fa yadda sautin zai samu daukuwa da kyau.

 Sannu namiji wato har kana da baki da karfin halin da zaka min bazarana kuma ka cilasta ni ko mahaifina, bayan duk abun da ka yi? Ka keta haddin kanwata har ka yi mata ciki sannan ka kalli kwayar idona ka yi min barazana Abdull...!

 Baku da wata hujja akan hakan, kuma fitar wannan zancen zai zubar mata da mutunci ne kawai, dan haka ki natsu ki tattauna da mahaifinki mu taru mu rufawa juna asiri, idan wani abu yake so zan ba shi

Kiran mahaifina da kwadayayyen da suke ya fi komai kona min rai sai dai babu yadda zan yi domin Baba ne ya budewa kowa kofa. Sam na manta da ban saka wayata a airplane mode ba, sai da kira ya shigo wayar. Wayar ta kawo haske kiran yayi appearing saman screen recording din kuma daga tsayaki daman wayar ba a key take ba, tun da Kareem ya ba ni ita ban saka mata password ba. Na yi hanzarin daukar wayar amman hakan be hana shi gani ba, daga Safeena da take kira har zuwa Recording din da nake.

 Recording kike? Ina kika dosa Noor

Na bude motar na fita da sauri sai ya bude ya zagayo kamin na yi wani yunkuri ya kamani da kokawa ya murde min hannu ya karbe wayar.

 Ka ba ni wayata Abdull

Be kula ni ya rufe gefen da nake tsaye ya zagaya zai shiga motarsa na bishi ina fadin ya ba ni wayar.

 Ka goge recording din ka ba ni wayata

Be kula ni ba ya rufe motar yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin bakinciki da nadama. Why I'm such a fool and idiot me yasa ma na yarda na yi magana da shi, no wait me yasa ban saka wayar a airplane mode ba kamar yadda na yi dazun.
Da kafa na taka na isa Family house din su Mama, a gidan na kwana gaba daya na rasa ya zan yi kuma na san idan na koma gida Baba zai rufe ni da fada ne wata kila har da duka. Abun da ban sani ba, ashe bachin da na yi a gidansu Mama na tsira ne, bachin na chanji ne daga wata kaddarar zuwa wata, ashe na bude wani sabon babin ne na kaddara, domin na wayi gari da mummunan labari...
 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un...

Haka kowa ke fada sai kallona suke na rasa wanda zai amsa min tambayar da nake, sai rufe rufe suke min.

 Hana ce ta rasu na san jiya na barta bata da lafiya

 Ke Noor shiga daki ki zauna

 Ba zan iya ba Kawu, gida ya rikice haka kowa yana uhu amman na kasa fada min komai, ni dai ina son na tafi gidan na ji

Na mike tsaye na fara takawa domin a bakin gaskiyata gidan zan tafi na ga abun da yake faruwa. Sai wata matar Yayan Mama ta rikoni.

 Dawo Noor zuwanki ba shi da amfani

 Ku fada mata gaskiya mana dole ai zata ji ba a boye mutuwa

Na juyo na kalli kanwar mahaifiyata wato Mama Aisha dake maganar.

 Wa na rasa? Mama ko Baba ko Hana ko duka?

Wani irin numfashi ya fara zuwa min da karfi yana shiga haka ma idan zai fita sai ya fisga da karfi.

 Gobara ta tashi jiya, gidan ya kone gaba daya babu abun da ya fita

Na rufe ido da sauri ina jin kamar mafarki nake.

 Sai hakuri Noor sai hakuri

Haka na ji kowa na fada, sai kuma na jini a jikin mutane ashe faduwa na yi ban sani ba.

 Ki yi hakuri Noor haka Allah ya so

Bana gana mai magana sai kallon gurin da sautin yake fitowa nake amman bana iya ganin komai sai duhu.

 Baba ya rasu kenan? Hana ma? Biyu na rasa ko daya?

 Biyu kika rasa Noor kin rasa uba kin rasa yar'uwa, sai hakuri

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Allah ka wakwantar min da hankalina Allah ka ba ni natsuwa Allah ka kara min karfin imani, ka ba ni ikon jure wannan jarabarwar

Shi ne abun da nake ta fada ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login