Showing 153001 words to 156000 words out of 227321 words

Chapter 52 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1514

dauke ni ba, bayan ruwa bana shan komai ba, shi kuma tun da ya fita be dawo ba, har garin Allah ya waye.

Cikin kuka da bakinciki na yi sallah Asuba, na roki Allah ya sanyaya min zuciyata ya sanya min saka min kana'a domin har lokacin ban ji zan iya yi ma yar'uwata wata bakar addu'a ba, har gobe ita din jini na ce idan wani abun ya faru da ita kamar ya faru da ni ne. Ni dai na san na barta da Allah shi ya san abun da ya dace da ita kuma shi ya san sakamakon da zai yi min akanta.

Misalin shida da rabi na fara hada kayana cikin akwaiti sai da na yi nisa da hadawa sai kuma, sai kuma na ji bana bukatar kala ko daya domin Abdull ne ya siya, a yanzu kuma bana sha'awar duk wani abu mai alaka da shi. Cikinsa ma da yake jikina da ace zan iya da cire shi zan yi na aje masa a gidansa na yi tafiyata. Jaka kawai na nufa na dauka na hada yan kudadena na dauki wayata ita ma dan ta zame min dole a yanzu.

Hijabi na saka sannan na dauki takardar sakin da ban iya karantawa ba na saka a jaka na nufi kofar dakin na bude, sai na yi arba da doguwar takardar aje a kofar daki. Na duka na saka hannu na dauka a tunani Abdull ne ya aje min amman da na fara karantawa sai na tararda sabanin haka..

_Yar uwata noor, ban ci amanarki, ba zan taba iya cin amanarki ba, ba ki saurare ni ba, bakinciki be bari kin tuna da halina ba! Yadda kika dauki abun ba haka yake ba, Wallahi mijinki ya nuna min fin karfi ne, ya fara tallata min bukatarsa tun a lokacin da na bukaci tafiya gida kika hanani ne. A lokacin bana son fada miki ne saboda kar na zama silar lalacewar aurenki..._

Na hade yawu na nufi kujera na zauna.

_Da ya fahimci ba zan aminta ba, sai ya shirya min tarko, ranar Monday da muka fita da sunan zai sauke ni a hanya, sai ya biya da ni a wata tsohuwar ma'aikatarsu, yace min zai tafi ya duba wani abun ne, ban yi tunanin zai nuna min karfi ba ne, shiyasa ta yace na shiga wani office na dan jira shi, na jira har na gaji da zama be dawo ba da na fito sai na lura gurin babu mutane sosai, na tsorata da farko na dauka siyar da ni zai yi, ashe kudirinsa dabam ne. Na koma ciki na zauna jiransa har ya dawo, sai ya fara lallaba ni yana min kamfe da abubuwan da yake min na kyautatawa ashe ba dan Allah yayi min ba, da na nuna masa ba haka ya fara kokawa da ni, Wallahi na yi ina yadda zan iya na kare kaina Noor amman hakan be samu ba sai da ya biya bukatarsa, a ranar ban samu tafiya makaranta ba a gurin na wuni, sai da ya dawo aiki ya biyo ya dauke ni aje ni nesa da gidan na tako na iso da kafa sannan ya shigo_

Hawayena sun zuba jikin takardar na juya dayan shafin ina karantawa.

_Daga ranar ne ciki ya shige ni, tun daga lokacin yake bibiyata yana ba ni hakuri kuma yana lallaba ni ko zan amince amman ban amince masa ba, ba zan iya fada miki ba ne, saboda kar na zama silar lalacewar aurenki da na Mama na rumgumi a abun a matsayin kaddara. Shi da kansa ya ba ni abun auna ciki ya ce na auna idan babu ciki saboda kar mu ya bayyana mu ji kunya, kuma da na auna sai na samu akwai ciki amman ban san ko wata nawa ba ne, da na fada masa sai yace za a zubar amman sai na amince masa ya ci gaba da mu'alama da ni, da hakan ya ribance ni na amince saboda ina son a cire cikin kar ki gane, domin ya fada min ya san duk yadda zai yi ya wanke kansa ni ya bar ni a ruwa idan ban aminta ba, kuma gaskiya ya fada ni mace ce bayyanar cikin zai rusa rayuwata, shi kuma namiji ne, wanda ya riga ya gina rayuwarsa kaddarata bata isa ruguza komai ba_

Ya share hawayena ina kuka.

_Ki yi tunani mana Noor yadda dangi da iyaye suke murna da dan halak, haka suke bakinciki da na haram, na san Baba kashe ni zai yi idan ya sani, buri na yadda za a zubar da ciki ne ba tare da kowa ya ji ba. Kullum maganar da nake masa kenan kuma saboda haka nake amincewa da shi, shi kuma yana ga jan lokaci saboda biyan bukatarsa. Amman ni ba zan iya cin amanarki ba Noor zuciyata ba haka take ba, ba a mana wannan tarbiyarba, tsorona na lalacewar aurenki ne da na Mama, ba ki tsaya kin saurare ni ba, ban san ya zan miki bayani ba_

Na mike tsaye da sauri a lokacin da nake karanta sakonta na karshe.

_A lokacin da zaki samu sakon nan ki karanta bana gidanki, na bar gidanki Noor, kuma ba gida zan tafi ba, ba zan kaiwa Mama abun kunya ba, ba zan tafi da cikin shege gidan Baba ba, na san zaki fada musu dukan abun da ya faru a lokacin da zaki koma gida ko kuma aka neme ni aka rasa. Dan Allah ki fada musu gaskiya Wallahi ba da son na aikata ba, kaddara ce ta riga fata, zan tafi inda ban san kowa ba kuma kowa be san ni ba, na bar ku Noor ku yafe ni, musamman ke...!_

Na jefar da takardar na nufi dakinta da sauri ina kiranta.

 Hana Hana Hana...

Na tura sai na samu dakin babu kowa, na fada bandaki nan ma bata nan, na fito da gudu na nufo gate ina tambayar mai gadi ko ya ga fitarta.

 Hana ai tun jiya da dare ta fita, misalin sha daya na dare

Na fashe da kuka na bude gate din na fita da gudu kamar ance zan ganta. Na yi dama na kalli karshen Titi da babu mutane na juyo na yi hagu nan ma babu alamar sawunta. A gurin na zube na kwarara wani irin ihu da dukan karfina ina kuka har sai da abun da ke cikina na motsa....



Duk wanda ta karanta min littafi bata biya ba na barta da ALLAH. duk wanda ta yi min sharing paid pages na barta da ALLAH.


It's 500
Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660

 Lafiya Hajiya Lafiya?

Ban kula mai gadin ba na dago da guduna na dawo cikin gidan na nufi jakata na bude na kira number wayarta. Na yi sa'a ta shiga kamin ta amsa har wani jiri nake ganin tsabar bugun da zuciyata yake yi. Ringing tayi ta katse bata daga ba, ina sake kira sai na ji wayar a kashe. Faduwa na yi zaune kan kujerar, ban san abun da zan yi ba, ban san ta ina zan fara nemanta ba. Ban san kowa cikin kawayenta ba. Hana bata da kawaye a garin nan sai yan makaranta kuma ban san waye zan fara bincika ba, ni ban ma san ina makarantarsu yake ba.

Takardar na dauka na saka a jakata na koma dakin na dauko babban akwatina na zuba iya kayan da nake iya gani na rufe na janyo akwati na fito ina kuka. Bana son na kira Mama na fada mata domin bana son su san abun da yake faruwa da Hana, musamman Baba da ba fahimta zai yi ba. Idan kuma na koma me zan fada musu? Miye silar mutuwar aurena? Kuma ina zan ce na bar Hana. Ban amsa tambaya ko daya da mai gadin date din yake min ba. Na mike hanya na fara tafiya ina hawaye har na isa babban titi na tari okada na fada masa tashar da zan hau motar Kano zai kai ni.

Ya charje ni dubu biyu daga unguwar da nake zuwa unguwar da ya kai na hau mota. Na taki sa'a na isar tashar a lokacin da ake neman mutum daya motar Kano ta tashi na mika duka kudin da nake da su na shiga motar na zauna bayan sun karbi information dina. Tafiyar ta min nisa sosai wata kila saboda mota na hau, domin ban tana zuwa ko dawowa a mota ba sai wannan karon, wata kila kuma saboda abubuwan da suka saka ni gaba ne. Dan carjin da ya rage min na siye ruwa da shi su nayi ta sha, har muka isa Kano.

Karfe shida muka sauka garin Kano, domin Tafiyar awa tara ne daga Kano to Lagos a babbar mota. Na fito motar aka cire min akwatina na karba na fara ja zuwa gate din tashar. Napep na shiga na fada masa kasuwar da zai ni, wato kasuwar yan waya.

 Dan Allah ka dan jira ni sako kawai zai karbo

 Okay amman Karki dade

 Ba zan dade ba

Na bar akwatina a ciki na shiga cikin kasuwar a lokacin da wasu suke ta hada hadar tashi saboda yamma ta yi. Wani shagon na nufa na nuna masa wayar hannuna.

 Malam kuna siyen irin wannan wayar?

Ya kalleni irin duban nan na rashin yarda. Sannan ya karbi wayar ya duba waje da ciki.

 Wayar waye?

 Tawa ce siyarwa zan yi

 Saboda me zaki siyar?

 Ina cikin matsalane ina bukatar kudi

 Ina receipt da kwalin wayar

 Suna gida

 To kije ki dauko waya a hannuna haka ai ta sata ce

 Wallahi tawa ce, ka duba ciki akwai hotuna na a ciki, kawai ina cikin matsala ne ina bukatar kudi

Na fada hawaye na jika fuskata. Dayan dake gefensa ya taso ya karbi wayar ya duba.

 Nawa zaki siyar

 Ni ban san kudinta ba ku siya kawai

 Iphone 14pro max mu baki 305k kin ga ta dan ji jiki

Na zaro ido ashe babbar waya nake riko ban sani ba. A zatona wayar ba zata wuce 50k ba idan ma ta yi tsada.

 Ka dai kara, dan Allah matsala ce ta saka zan siyar Wallahi

Sai ya miko min wayar.

 Ba zan iya siyenta fiye da haka ba, siyen waya haka ma ai it's risk kawai dan na ga kina cikin damuwa ne zan siya, kin ga ma yanzu tashi zamu yi

 To kawo kudi

Ya cire min layina ya miko min sannan ya kirgo kudin ya miko min ba tare da na kirga ba na karba ina masa godiya. Na fito da sauri na samu mai napep din nan a inda na bar shi ina shiga ciki ya rufe ni da fada wai na bar shi yana ta jira.

 Yi hakuri

 Ina zan kaiki?

 Hotel

Na fada kai tsaye domin kudirin da ya saka na siyar da wayar kenan domin babu sauran kudi a hannuna.

 Wace hotel

 Ko wace ma wacce dai mutane ba su cika yawan cikawa ba

Ya fara lissafa min sunayen hotel yana tambayar wacce za zai kai ni. Zuciyata kuma taya raya me kamata na tafi can ba, gida ya kamata na tafi, amman idan na tafi gida me zan fada.

 Kai ni ko wace ma

 Okay

Na share hawaye ina jin bakinciki a zuciyata, yau ga ni a garin Kano amman ba damar tafiya gidanmu. Ina yar'uwata take a wane hali take yanzu? Me ye makomar cikin dake jikinta? Me yasa ban saurareta ba wata kila da bata gudu ba. Ya sauke ni a gaban wata katafariyar hotel mai girma da haske ko'ina.

 Mu shiga ciki ko na sauke ki a nan?

 Nan ma ya isa

Na fito na dauko akwaiti na bude jakata na dauko 3k cikin kudin wayar na mika masa, sai ya karba yana min godiya. Na juya na hotel din sai kuma na ji bana ra'ayin shiga ciki. Dan haka na tari wata Napep din na shiga domin aiwatar da kudirina.
A kofar gidan Kareem mai napep din ya sauke ni, na sallame shi na nufi flowers din da suke gefen gidan na daga akwaitina na jefa a ciki sannan na nufi gate din. Na kwankwasa na san by that time yana gida ko hanyar gida, domin muna hanya aka yi sallah Magariba.
Mai gadin ya bude ya leko.

 Mai gidan yana nan?

Ina magana numfashi daker domin karfina ya gama karewa ga bakina ya bushe, har lokacin kuma ban ji ina sha'awar komai ba duk da kasancewar ina jin yunwa.

 Eh yana nan

 Dan Allah ka ce mishi yana da bako a waje dan Allah ya fito abu ne mai muhimmanci

 Wa zan ce masa?

 Kawai ka fadi haka dai

 Tohm

Ya juya ya koma ya rufe gate din. Ni kuma na kai hannuna na dafa ginin ina jin zuciyata kamar zata fashe. Tun a lagos na kudurtawa zuciyata zuwa na fada masa damuwa ba, da na yi nufin na fara sauka hotel ne washe gari na je na same shi a restaurant ko asibitinsa na fada masa, amman burin ceton yar'uwata ya saka na ji kamar idan ta kai gobe zan iya rasa rayuwarta. Na kwashe minti talatin tsaye a gurin sannan ya sake bude gate din.

 Yace a shigo da bakon

Na cira kafa na shiga cikin gidan na fara takawa sai na hango shi tsaye a entrance yana kallona har na karaso. Ya kalli daga kasa har zuwa sama.

 Noor

Na kalleshi ba tare da na amsa ba.

 Minene kuma wannan karon?

 Kareem na san ina damunka ina shiga rayuwarka da yawa, amman dan Allah karka ce min aa na maka alkawari daga wannan ba za sake ba, dan Allah ka taimaka min dan girman Allah

Na kai kasa ina rokonsa sai kallona yake ya kasa cewa komai. Na nufo shi ne saboda ina jin yana karfi na dukiya wata kila har da hanyar da zai taimaka min.

 Shigo ciki

Ya juya.

 Matarka za....

 Bata nan

Na mike tsaye na bi bayansa na shiga cikin falon sai na zauna a kujera shi ma ya zauna nesa da ni yana kallona.

 Me ya faru?

Na bude jakata na dauko takardar sakin zan tashi na kai masa sai ya taso ya karba ya zauna a dayar kujerar dake kusa da tawa. Yana gama karanta takardar ya kalleni

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Saki Noor mi ya faru?

Na ciro dayar takardar da Hana ta aje min na mika masa ina hawaye. Ya karba ya fara karantawa mikewa yayi tsaye ya girgiza kai ya runtse ido, can kuma ya bude idon ya kalleni.

 Da gaske?

Na daga mishi kai har sau uku, ya koma ya zauna na dafe kansa.

 Ko da yaushe idan ina cikin damuwa, na kan zo gareka saboda ina samun mafita kuma kana taimaka min, dan Allah ka taimaka min ta dawo, bana son Mama ta sani ko Baba domin idan Baba ya ji zai Fadawa Umma ita kuma zata yada a cikin unguwa, Mama kuma idan ta ji wata kila ba zata iya hakuri zata janyo mutuwar aurenta, bana son daya daga ciki ya faru?

 Na ji zan taimaka miki amman dole ne iyayenki su sani Noor, me zaki fada musu a mutuwar aurenki? Kuma yanzu kamin a gano yar'uwarki me zaki fada? And idan ma an ganta amman ba a cikin hali mai kyau ba dole za su ji ba zaki iya boye wannan ba, yanzu idan kin tafi gida me zaki fada?

 Ba gida zan tafi ba Hotel zan zauna, har sai an gane Hana sai mu tafi gida tare, na Fadawa Baba kawai mun yi fada ne ya sake ni

 Noor yanzu kurciyata tana damunki, matsala irin wannan iyaye kadai suke iya tsayawa mutum, dole ne ki fada musu gaskiya, gidan ba zaki iya Fadawa Baba ba, to ki fadawa Mahaifiyarki, kaddara ce babu wanda ya wuce kaddara

 Kaddarar ita ce kullum a biye da ni, aure na biyu kenan ina yi babu dadi, gashi yanzu har na janyo Hana ta gudu ta shiga duniya

Na fada ina kuka. Mikewa yayi tsaye ya haura sama ya bar ni a falon ina ta kuka ni kadai gaba daya ma duniyar ta isheni. Be dade ba ya sauko da waya a kunnensa.

 Yeah let me ask her

Ya kalleni.

 Ina kika saka ran zata tafi?

 Ni da ita ba mu san kowa a Lagos ba, ban san inda zata tafi ba, bata da kawaye sai yan karantarsu ban san gurin waye zata tafi ba

 Wai bata san kowa a lagos ba

Can kuma na ji ya amsa da

 Okay Thank you

Ya zauna sannan ya amsa kiran da ya shigo.

 Aaryam na kira baka daga ba

Ya kalli agogo.

 Okay, daman wani taimako nake so dan Allah, wata yarinya ce ta gudu a Lagos nale son a nemo ta, na san kana da friends yan Lagos sosai maybe you can help

Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya turo kofar, bana jin komai da yake fada har sai da ya gama wayar ya dawo ya zauna.

 Ina wayarki dole sai an tura hotonta

 Na siyar na siyar da ita yanzu, suka ba ni 305

 Wayar?

 Eh

 Saboda me?

 Ba ni da kudi ne, kudin sun kare a hawan mota, shi ne na siyar da wayar saboda na yi amfani da kudin, irin wayarka ne

Ya kalli wayar ya kalleni.

 15 pro max suka baki 305k?

 Aa taka ta tsufe tawa da shekara daya, tawa 14pro max ce

Na ciro kudin na zube duka a gurin.

 Wane barayo ya siye wayar?

 Ba barawo ba ne shago ne

 Saboda kawai sun ga baki san kan waya ba sai su siye a 305k? Dole sai an nemo hotonta da Yanzu ina layinki yake? Dole sai an nemo hotonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login