Showing 180001 words to 183000 words out of 227321 words

Chapter 61 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1552

shiyasa ban yi kasa a guiwa ba na sake kira tana ringing ba a dagawa daga baya wani lokacin kuma sai na jita a kashe

 Eh wayar tana hannun Yayana ne

 Yayanki ko saurayinki? Ko dai karbe abarsa yayi saboda shi ya siya?

 Aa yanzu ta dawo hannuna ai

 Hakan yayi kyau, ya kamata na shigo mu gaisa ko ba haka ba? Mu fahimci juna kuma tattauna abun da ya kamata, ba mu san abun da Allah zai yi ba, ni dai na ga abun da ke min

Na cire wayar a kunne na kalli screen na sake mayarwa, ashe dai uban Aisha nan haka yake da son zuciya shiyasa ita ma take da son zuciyar ta hana ni zaman lafiya a gidan Hafiz. Idan ba son zuciyata ba ta ina zai kalli mace kamar ni yace wai na masa, yarsa Aisha ma yayata ce ta uku balle kuma ni.

 Ba yanzu ba gaskiya sai nan gaba

 Saboda me baki son na san gidanku ne? Ni fa da gaske nake babu alamar wasa

 Yanzu ba gida nake ba, yanzu ina family house din mahaifiyata ne saboda Babana ya rasu tare da kanwata

Ya tausaya min sosai yayi min gaisuwa sannan ya fada min zai zo yayi gaisuwa gurin Mama da ni. Na amsa masa da okay ne kawai dan babu yadda na iya, amman na kudiri aniyar idan ya zo zan fada masa gaskiya cewar ni ina da wanda zan aura wato Kareem... Minti goma da kare waya da shi airtime na 10k ya shigo wayata...



Alhamdullahi Allah ya maimaita mana. >?2?


? ? ***? ?? ***? ?? ***? ? ***? ? ***?? ***?? ***? ? ***

Sauka na yi daga kan kujerar na zauna kasa ina kallon Kareem dake shigowa bayan na Alhaji Sule unguwa uku ya sauka. Tun kamin na amsa wayar na samu kaina da murmushi.

 Hello

 My heart beat, my life, my happiness...

Ya fada murya can kasa kamar mai gudun wani ya ji.

-Uhm hmm-

 Kawai na kira ne na fada miki ina kaunarki

Na yi murmushi ina shafa fuskata.

 I love you so much, my Beb my one and only

 Hey... Ya isa haka

 Be isa ba, i love you i love you i love you i miss you i need you, Noor jin nake kamar ba ke ba ce a yau, gani nake kamar ranar yau mafarki ce, after this fever i will survive komai zai zama kalau

 Haha

Na yi dariya.

 Amsa min mana ki ce min ke ce Noor maybe zan yarda

 Ni ce Noor noor ta Kareem

Na fada ne da zolaya sai na ji ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru na wasu dakiku sannan ya ce.

 Noor da kin san yadda nake son ki a zuciyata wata kila da kin tsorata, ina masifar sonki Noor, irin son da ban taba mafarki ba

Na yi shiru kamar wadda ta rasa abun fada, ajiyar zuciya na ji ya sake saukewa.

 Ta ya wayarki ta dawo hannunki? Kawai na rike number ki ne ina kallo sai kuma na gwada kira ashe zai shiga

 Mama ta shigo ta kawo min, na dawo na tarar da mahaifin dare da Kawuna da Mama ban san me suke magana ba, kawai Mama ta shigo ta ba ni wayar

 Okay, zan aiko a karbe ta a canja miki wata, ina son zuciyata ta natsu kina cikin aminci Noor

 Okay

 I love you

Ya furta sannan ya kashe wayar, na mike tsaye na fice daga falon na shiga bangaren da Mama take, kamin na shiga dakinta Kareem ya sake kiran wayar.

 Hello

 Noor, na ce tun da kin amince da ni me zai hana a daura mana aure kamin na tafi?

Na yi baya baya na fasa shiga dakin Mama juyo ina rufe baki.

 Kareem yayi wuri ai, kwana biyu ya rage ka tafi fa, ni kuma ban fadawa kowa ba, babu wanda ya san da alakarmu

 Zan aiko neman aurenki ne, albashin idan suka zo sai su sanar cewar sun zo ba tare da izininki ba

 Aa ka bari sai ka dawo Kareem

 Noor what if ban dawo ba fa? Ina tsoron kar ki canja shawara kamin na dawo, ina tsoron rasaki Noor

 If we mean to be zaka samu sauki zaka dawo Kareem, kaddara ce ta hada mu ai ka fada

 Noor ina tsoron rasa ki

 Ta ya? Babu kowa a gabana yanzu sai kai Kareem

 Na gode da kika sanar min wannan, thank you anjima Aaryam zai zo ya dauke ki, ki sanar da Mama

 Okay

Sai da ya sake fada min yana kaunata sannan ya kashe wayar, ni kuma na juya na sake komawa bangaren na shiga dakin Mama, babu kalar tambayar da ban yi mata ba akan zuwan mahaifin Abdull da kuma yadda aka yi ya ba ni wayata amman Mama bata amsa min tambaya ko daya ba.

Daga karshe sai na sanar mata Kareem yace zai aiko kanensa ya dauke mu domin yin sharadi a gurin DSS.
Jimm Mama ta yi da alama hakan kamar be mata dadi ba, sai dai bata ce min komai ba, cewar na tafi ko kar na tafi, kuma bata amsa da cewar zata tafi tare da ni ko akasin haka ba.

 Mama baki ce komai ba

 Noor ki yi taka tsantsan da yaron nan, ba zan yanke alakarku kai tsaye ba, amman dai ki yi taka tsantsan da shi, izuwa yanzu ya kamata ace kin dauki darasin rayuwa, auren biyu kenan kika yi da kurciyarki da kananen shekarunki, duk yadda zai zubar da mutuncinki ko nawa to ki yi kokarin tsare shi, kin ga a yanzu hannuna kike mahaifinki baya raya dawainiyarki da tarbiyarki a kaina take, bana fatan ki aikata wani abun ko wani abun ya same ki da za a furt cewar ke yar mace ce

 In Shaa Allahu Mama zan kiyaye

Jikina yayi sanyi zuciyata na raya min akwai wani abu da Mama ta sani amman bata son fada min.

 Mama ko dai na fada masa ba zamu samu damar tafiya ba?

 Aa abun da yake bukatar a aikata abu ne mai kyau, ko da be kawo shawarar ba, ni zan kawo aikawatar da haka saboda tsaron lafiyarki domin gujewa gaba, za mu tafi

Na yi shiru na wani lokaci sannan na daga kai na kalleta.

 Mama ko wani abu kika ji akan Kareem ne? Domin mutumen kirki ne

 Ba a gane mutumen kirki a fuska ko a furuci, ba a fuska ake zanawa ba Noor, Abdull ma ba mu yi zaton zai aikata ba sai da muka gani

 Haka ne

Daga wannan ban sake furta komai ba. Da yamma Kareem ya aiko da mota kamar yadda ya fada aka dauke mu ni da Mama da Babban yayanta da kanen mahaifi da mama ta aika masa ya zo jar gida aka tafi tare da shi. Office din DSS aka kai mu kai tsaye, ko da muka isa mun tararda Safeena da mijinta a can a ranar na fara arba da mahaifin Kareem suna kama da Aaryam sosai fiye da Kareem wata kila Kareem din ya fi kama da Mamansu ne.

Ban ga alamar maraba a fuskar mahaifinsa ba, zuwansa sai yayi min kama da wanda aka tirsasa ya aikata abun da ba shi da ra'ayin akai, hakan kuma ya saka ni jin wani iri.

 To ni me ya shigar da ni cikin lamarinta? Ina ce Abdull ta aura ni miye nawa a ciki da za a zo nan da ni?

Aaryam ya dan tabe baki kadan irin na mai mamaki

 Ni ma na yi tunanin haka, but Kareem ya ce da ita za a zo

Abdull ya kalleshi.

 Wait Waye ya taramu a nan to? Ni fa d aka aika min da takardar gayyata cewa aka yi mahaifiyar Noor take nema

 An fada maka haka ne kawai, Yayana ne ya taraku a nan saboda a dauki matakin da ya dace

Abdull ya sake daga ido ya kalli Aaryam sannan ya sauke kansa ba tare da ya sake cewa komai. Har aka yi komai aka gama Mama ce take magana da yawuna, wani abun kuma Kawu ya saka baki ko Baba Kamilu. Motar da ta kawo mu ita ta dawo da mu gida. Bayan na shiga gidan Kareem ya kira wayata ya ce na fito waje Aaryam yana tsaye yana jirana. Ban bata lokaci ba na fito sai na same shi a gurin da na bar shi, sabuwar waya ya bude a gaban idona ya karbi ta hannu ya cire sim din ya saka min a sabuwar wayar sannan ya mika min ya tafi da tsohuwar.

Rayuwa ta cigaba da tafi min a yadda ubangiji ya tsara min ba a yadda ni na tsara ba, Alhaji Sule unguwa uku ya zo gidanmu yayi min gaisuwa kuma yayi ma Mama da yan gidan ya kawo mana alheri na abinci da kudi, wata matar Kawuna har tsokana ta take wai Noor mai kwashe kwashe, iyakaci murmushi bana cewa komai amman ni na san ba aurensa zan yi ba. Wannan ya saka ban yi kasa a guiwa ba zuwansa na biyu na fada masa cewar akwai wanda yake neman kuma nake saka ran aurensa nan kusa idan Allah ya amince.

 Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, ita mace allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka

 Haka ne

Na furta ina gyara mayafina.

 Dan haka karki yi saurin yanke hanzarina, ni ma zan gwada sa'ata kuma ko da ban aureki ba ni na ci riba domin na tsaya da ke kuma kin min tarba ta mutumci na jidadin haka

Na yi murmushi na sauke kaina kasa.

 Kuma kar haka ya saka ki ji nauyin tambayar wani abu a gurina ko bukatar wani abu, ni ina taimako ma ko a banza balle kuma akwai dalili, daga naira miliyan daya har miliyan dari zan iya kashe miki Khadija kashewa mace kudi ba asara ba ne, musamman macen da kake fatan ta zama Matarka kuma uwar yayanka

Mamaki ya kamani ashe dai su ma tsofi sun iya kalaman soyayya, bawan Allah nan sai kokarin daure ni yake da kalamansa. Sama sama muka yi hira sannan ya dauko leda motar ya aje min a gabana.

 Ban gama sanin komai akan sarauniyar ba, amman dai ina fatan abubuwan da na zabo za su burge ki

 Na gode, amman ba zai ka yi min dawainiya ba, bana bukatar komai a yanzu

 Sakamakon rashin bukatar da kike da shi ne ai, bukatar take nemanki ke dai ki bar ni na gina miki sabuwar rayuwa kawai

Na yi murmushi na sunkuya na dauki ledar.

 Na gode

 Toh sai mun yi waya, bye bye

Ya dago min hannu ni ma na daga masa. Ina shiga dakin na samu Mama bata ciki sai dariyar da na riko a waje ta subuce min, shi fa dattijon ya dage a bakin gaskiyarsa yaki yake yi ma soyayyarsa a gurin. Kayan tande tande ne da lashe lashe a ledar sai turaruka da bandir din 200 sabi. Na bude ice cream din na fara sha ina lumshe ido sanyi yana kai min har cikin zuciya.

Kiran Kareem ne ya shigo wayata sai da na daga na gane ashe video call ne. Na fara isar masa da murmushi sai dai shi tasa fuskar kamar yana cikin damuwa.

 Ya kike?

 Lafiya kalau, sad face?

 Me kike sha?

Na daga na nuna masa robar.

 Waya kawo?

Na yi shiru ina kallonsa i kNow if i lie zai gane domin ya san ba zan fita na siyawa kaina ice cream ba but me zan ce? Ban gama tunanin amsar da zan ba shi ba na ji ya ce.

 Wannan baban Aisha Alhaji Sule unguwa uku nan ba aurenki zai yi ba Noor, matansa hudu kuma yayansa duka manya ne, kuma yadda kike fresh and young me zaki yi d tsoho?

Na yi dariya.

 Ni ma na aurensa zan yi ba kuma na fada masa ina da wand nake so fa, shi ne kawai ya nace sai ya ce wai zai gwada sa'arsa

 Bana son na ji ya kara zuwa kofar gidanku nemanki, please ki fada masa kina da wanda zaki aura kuma baya son kina kula kowa

 Okay zan fada masa, amman ka sake fuskarka Kareem ka bata rai

Na fada a shagwabe kamar zan masa kuka.

 Any thing for my heart beat

Ya sake fuskar yayi murmushi tare da sumbantar screen din wayar ya shafa shi yana kallona. Mun sha hira sosai irin ta masoya haka muke a kullum baya gajiya da kira bana gajiya da amsawa kamar kar ya bar kasar nan wani irin shakuwa ya shiga tsakaninmu idan ya kir har bana son ya yanke kiran shi ma kamar zai dauke ni ya cinye haka yake min.

Daf da zamu yi sallama ya fada min gobe za a shiga da shi aiki, na ji hankalina ya tashi sosai domin ya damu da ciwo wata kila ya wuce yadda nake gani ko tsammanin ma.

 Na so na ganki Noor kika ki zuwa mu yi bankwana tun ranar ban sake sakaki ido ba and you know how much i love you

 A matsayina na wa zan tafi? Iyayenka ba su san alakarmu ba, ko da ma sun sani ai da kunya ace ina tafiya ganinka

 Sun sani mana, baki ga mahaifina ba? Kanena ma sun sani duk wanda ke gidanmu yanzu ya sani

 Yanzu dai Allah ya baka Lafiya ya dawo da kai lafiya kuma ya sa ayi aikin cikin nasara

 Ameen ki kula min da kanki please, bana son mazan nan dake kawo miki hari, kin ga ko Ustan din nan ya sake zuwa bayan ganin da na masa ya sauke ki a mota, Noor bana son kina kula kowa, ki rika daukarkanki kamar an daura mana aure

 I will

Ya sakar min ido sosai yana kallona.

 Aaryam zai zo ya kawo miki atm ko da zaki bukaci wani abu, bana son ki ji cewar kin rasa wani abu a lokacin da kike tare da ni

 Bana fa bukatar komai Kareem ba sai ya kawo min ba

 Ba ki bukata Alhaji Sule yake kawo miki leda kina karba?

Na zaro ido na juya na kalli gurin d ledar take baya ganinta amman ta ina ga ya ledar har yake fadar haka? Ko dai ya chanka ne kawai, amman fa dazun ya furta cewar Ustas din nan ya zo ta ina ya sani domin ban fada masa ba, amman na san Kareem da wayo wata kila yana son kure ni ne.

 Ni baya kawo min leda

 Hmmm na dai fada min kar na sake ganinsa a gurinki

 Gashin shi kake yi daman?

 Makaho ne ni? Ina nan amman duk wani motsinki idona yana kanki, idan kuma ke kika makantar da ni sai na ji

Na kyakkyale da dariya sosai har da tintsirawa. A lokacin da na dago sai na ga kallona yake da murmushinsa mai kyau.

 That's my girl, that's the real Noor i know i love you Babe

Na rufe idona ina jin kunya. Shigowar Mama ne ya saka na yi masa sallama na aje wayar.

 Wannan kuma minene?

 Wa.. Wannan ne Alhaji nan da yayi muku gaisuwa ya kawo min yau

Mama ta duka ta dauki kudin ta duba.

 Noor ina ta jan kunnenki, ki dai ba zaki taba hankali ba? Ga mugun kwadayi ki yi ta zubar da kanki mutunci a gurin maza? A tunanin tara maza wannan ya so gobe wani ya so shi ne soyayya?

 Aa

Na amsa a sanyaye sai ta nufi gurin ajiyarta ta aje kudin kayan zakin kam ko kallonsu bata yi ba ta sake ficewa.
Bayan sallah la'asar Alhaji Sule ya sake kiran wayata yana karyar da murya da marairaice gwanin shaushi.

 Uhm uhm ni baki kira ni kin ji ko na sauka Lafiya ba, ni na yi fushi zan yi kuka...

Na yatsina fuska ina jin kamar na buga masa robar ice cream din da ya kawo min dan haushi.

 Me yasa kake magana haka kamar yaro?

Yayi dariya.

 Soyayya ai bata san yaro ba bata san tsoho ba, soyyayya ce kawai domin na lura har yanzu akwai sauran kurciya a tare da ke Babe na

Wani amai na zo ya min da ya kirani da Babe.

 Wane irin Baby kuma dan Allah ka daina ni fa na san ba aurena zaka yi ba, kana yara kamar ni da wadanda suka girme ni ma to ta ina zaka aure ni, kuma matanka hudu fa haba

Shiru yayi na lokaci jin na harbo jirginsa, can kuma ya dan yi murmushi kadan.

 A ina wannan maganar ta fito Khadija?

 Kasan abun duniya baya boyuwa

 Haka ne, amman dole akwai wanda ya fada miki haka, ko kuma dai gidanku an yi bincike akaina ne?

 Aa ai maganar bata kai gurin iyaye ba balle su yi bincike, ina gida aka fada min yanzu ina son ka amsa min maganar haka ne ko ba haka ba?

 Ba gaskiya ba ne, matana uku ke nake fatan ki zama ta hudu

 Gaskiya ta gun da na ji ba zan za a maka karya ba, domin wanda ya fada min ya Sanka sosai

 Ko dai wani ne yake son shiga tsakaninmu? Fada min mana yan mata na waya fada miki wannan maganar? Wa yake min wannan sheri haka da tsakar rana?

 Aisha...

Na fada kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, kuma na yi hakan ne da nufin ya san ta majiya mai karfi na ji kuma ya san alakata da yarsa.

 Wace Aisha?

 Aisha yarka matar Magaryi Hafiz

 Ina kika san Aisha?

 Saboda mun auri miji daya ni da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login