Showing 177001 words to 180000 words out of 227321 words

Chapter 60 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1536

nufi asibitin da Kareem yake aiki kuma yake ciki.
KAREEM POV.

Yana ganinta sai ya ji kamar an zare masa ciwon dake kirjinsa, kusan daman ita ce energy sa a yanzu, da kuzari ya yunkura ya tashi daga kwance da yake yana kallonta, be tsammaci zuwanta ba ko da kuwa ace yana gangar mutuwa ne.

 Noor shigo mana

Ta kalli Kareem sannan ta kalli Hajiya Hassana dake tsaye tana kankare masa kwai, ta maida kanta kasa ba tare da ta shigo cikin ba kamar yadda ya bukata.

 Wannan Hajiyar mu ce, mahaifiyarmu karki ji komai shigo

Hajiya Hassana ta juya ta kalleta ganin ta tsane kanta gurin kofar kamar mai tsoron mutane.

 Shigo yarinya ni fita zan yi yanzu nan

Ta aje kwan da bata gama barewa ba ta nufi kofa, sai a lokacin Noor ta kauce daga jikin kofar kuma ta gaisheta.

 Lafiya Kalau, sannu

Hajiya Hassana ta fice daga dakin ta ja musu kofa duk kuwa da bata san wacece ba a gunsa. Noor ta tsaya a jikin kofar yatsun hannunta sarke da juna, fatar idonta da fuskarta kawai ya kalla ya fahimci irin kukan da ta sha, ta rame kamar ba ita ba ta zama so innocent.
Ji yayi kamar ace yana da iko da damar da zai sakata a kirjinsa ya rarrasheta da kalamai masu dadi, ina ma ace idan yayi mata alkawarin farinciki zata yarda da shi, ta ina zai fara rarrashin rabin rayuwarsa macen da ta hana shi ganin kyaun sauran matan duniya.

 Shigo ki zauna ko na taso ne Noor?

Ta dago ta kalleshi da raunannin idanuwanta a take ya ji kamar ba shi da wani gata a duniya sama da ita.

 Daman na zo dubaka ne

Tana maganar tana hawaye

 Baki son mu tattauna akan rayuwa? Wata kila idan aka tafi da ni aikin nan ba zaki sake ganina ba, shigo ki zauna Noor

T?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
a fara takowa ta isa gurin kujerar dake facing din gadonsa ta zauna.

 Ya kike?

Ta share hawayenta.

 Lafiya kalau

 No ya kike?

Ta dago ta kalleshi sai kawai ta fashe da kuka, rumtse ido yayi yana yawo da kansa a lokacin da sautin kukanta ke sauka kunnuwansa, be taba jin tausayinta a irin wannan karon ba, be taba kewa da kaunarta irin na yau ba, kamar ana cire kunnuwansa da zuciyarsa haka yake jin kukanta na kona masa rai.

 Na ji fiye da yadda ka ji a lokacin da ka rasa mahaifiyarka Kareem, na rasa miji na rasa uba na rasa kanwata saboda sakarcina da sha sha shanci

Ya bude idon ya kalleta

 Babu laifinki a mutuwar kowa cikinsu

 Akwai ni na aikata abun da ya zama silar mutuwarsu

 Me ya faru Noor dita fada min me kika yi

Ya cika da mamaki a lokacin da ta fada masa abun da ta aikata tana kuka.

 Me yasa haka Noor?

 Because i was so stupid, ni sakarya ce ai daman bana tunani irin na mutane, bana ganin dacewa da rashin dacewar komai sai bayan na aikata, bana da tunani irin na mutane ni mahaukaciya ce kawai mai tarin shashanci

Ya kara jin tausayinta ya rufe shi, zaunawa yayi da kyau yana kallonta, kaunarta ma figarsa.

 Kina da hankali da tunani irin na mutane Noor, zuciyarki da kwakwalwarki masu kyau ne, ke kawai mafita kike nema kokarin kare kanki da iyalanki kike, irinki kadan ne a duniyar nan, idan har abun da kike zargi ya tabbata to akasi ne aka samu a lokacin da kike kokarin neman mafita

Ya sauke numfashi a hankali yana kallon yadda hawaye sauko mata ta daga kanta tana kallonsa irin kallon nan mai cike da tsoro da fargaba.

 Rayuwa bata da sauki Kareem, abubuwa da yawa basa nufin samuwa, burika da yawa basa cika, kaddara ta zama babi babi, idan wata ta rufe kofa sai wata sabuwar ta bude, farinciki ya zame min kamar lu'u lu'u mai wuyar samu

Ta yi murmushi mai kone zuciya.

 Me yasa duk nake fada maka wannan? Kai ma kana cikin mutane da suka jefa ni a matsala, wata kila da Safeena bata samu labarin cire cikin ba, da duk haka be faru ba, da bata zuga Baba ya kai maganar kotu ba, da yanzu Hana tana raye

 Ban fada mata komai ba Noor, Safeena shu'umar mace ce da zan iya kira da mummunar kaddara, Wallahi ban fada mata komai ba, idan har zan fadi sirrin wani, to sirrin wani zan fada ba na ki ba Noor, ta hanyar Nurse din da ta yi mata wanki ciki ta samu labari, a ranar da kika ji muryarta a wayata na je na same ta mun yi magana kuma ta fada min yadda ta tsara komai, amman baki saurare ni ba Noor shiyasa baki fahimce ni ba, bana da wata alaka da Safeena, zuwan da na yi ma domin ke ne

Ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya.

 Na yi nufin baki farinciki Noor, na yi nufin maye miki gurbin abubuwa da yawa da kika rasa you're my only hope, ke ce cutata kuma ke ce magani, amman ba zan samu damar haka ba, domin na yi making mistake da zai yi ta hurting dina for the rest of my life, shiyasa duk abun da Allah yace kar a aikata a cikin hanin akwai alheri da nasara

Ya lumshe ido.

 Ko yaushe zan huta ni? Ko yaushe zan samu salama na samu kwanciyar hankali? Yaushe damuwa zata bar ni? Ina jin tsoron duniyar nan mai fadi Kareem

Ya kalleta idanuwansa cike da kaunarta.

 Nan gaba kadan Noor idan kin kwantar da hankali kin fahimce ni, kuma idan Allah ya ba ni aron domin ina tsakanin mutuwa da rayuwa ne a yanzu

Me yake damunka Kareem?

Ta tambaya tana share hawayenta.

 Tun a lokacin da na yi hadarin a baya, kirjina ya bugu amman ban dauka zai zo da matsala ba, shiyasa ban zafafa a gurin bincikar gurin ba, sai kawai na cigaba da harkokina, na kan ji yana min ciwo wani lokacin amman ba kamar yanzu ba, idan zan tashi sai na yi daker, ranar da muka yi waya dake na karshe a ranar na fadi, aka kawo ni asibitin nan ban san an zo ba, zuciyata ta yi kasa ta bar muhallinta dole sai an yi min aiki, aiki ne mai matukar hatsari wata kila na rayu wata kila kuma ba zan rayu ba

Ta sauko daga kan kujerar ta zube kasan guiwoyinta ta kama gadon ta rike tana kallon fuskarsa, duk yadda take tausayin kanta take cikin damuwa sai ta ji kamar ta Kareem ta dara tata. Shi ma kallonta yake yana jin tausayinta fiye da kullum ta shiga taskon rayuwa ta fuskanci kalubale tun tana karama har yanzu, a zuciyarsa yake ayyana yadda take ji a nata zuciyar, a yanzu bata da kowa sai Mamanta sai Nabil su kuma ba za su iya samar mata gatan da yake jin zai iya samar mata ba.

 Zaka rayu Kareem, zaka rayu ko dan ni da yaranka we need you

Ta kwantar da kanta saman gadon hawaye na sauko mata, Kareem ya kai hannu kamar ya shafa fuskarta sai kuma ita din ba halalinsa ba ce a yanzu. Jimke hannun yayi ya kwanto da kansa saman fuskarta tazara kadan ya bari a tsakanin fuskarsa da nata, lumshe ido yayi yana maida numfashi a hankali kamar yadda take yi, hawayenta na sauka a jikin gadon na idonsa kuma suna sauka a fuskarta.

Dif dif dif ta ji wasu ruwa masu dumi suna jika gefen fuskarta, har suka gangaro suka hade da nata hawayen suka sauka a kan gadon. Bude ido ta yi ta dago kadan ta kalleshi sai ga ta fuskarsa so cool very calm and innocent kamar ba daga idonsa hawayen suke fita ba.

 Kuka Kareem...

 Ina sonki Noor, ina son rayuwa da ke, ina kewar mahaifiyata ina son na rayu da Yayana, ina kewar abokina ina jin rashin abubuwa da yawa I'm hopeless now... Every one is lonely sometime

Ya furta ba tare da ya bude idon, kamin ya kai hannunsa ya share hawaye da be isa ya hana su zuba ba. Ba shi kadai ba kusan duk namiji da zai zubar da hawaye kuma ya bari a ga hawayensa tabbas yana cikin tsanani damuwa ko bukatar da abun da zuciyarsa take so. Ya bude idon ya kalleta yana maida numfashi a tare da ita zuciyarsa da nata suna bugawa at the same time something very deep inside their heart ya saka zuciyoyinsu nauyi.

 Idan wani ya sake nuna miki yatsa, Noor ki kaddara bana raye, idan wani ko wata ya saka ki zubar da hawaye i will show him the other side of me, as long as you're with me you're not alone and you will never be, you're not alone we're family. Ki fadawa Mama da duk wanda ya kamata ya sani, anjima Babana zai zo tare da Aaryam za ku tafi gurin DSS za'ayi yarjeje ni tsakanin ke fa Safeena da kuma ke da Abdull cewar idan wani abu ya same ki su ne

 Why?

 Duk wanda zai kona gidanku gaba daya, to rayuwarki yake nema ba ta iyayenki ba, an kashe su ko kuma an kone saboda tunanin ke ma kina ciki, kuma bana raba dayan biyu Abdull ko matarsa

 Na fi zargin Abdull saboda case din gaba daya akansa ne, kuma shi ya karbe min wayar ai

 Safeena ma zata iya, zuciyarta bata da kyau kuma ta san yadda nake sonki, a fada mata idan har zan sake yin aure a rayuwata to mace daya zan aura kuma ke ce Noor, idan har ban same ki ba, ba zan sake aure a rayuwata na hakura, idan ma na rayu hakan kuma ba zai hana na yi miki fatan auren wanda kike so ba kuma zai rike ki amana Noor ina son farincikinki a duk halin da zaki samu kanki i love you unconditionally, i never knew it could be so much, ina rokon Allah ya ba ni aron rayuwa i will spend every hour of every day keeping you safe, you're my favorite girl, na san wata rana zaki tuna da ni zaki so ni, sai dai babu tabbacin ina raye, but i will wait to capture your love, i will not give up

Ta baki yake furta kalaman amman ta ido yake zuba mata su, ta kasa dauke idonta akan nashi, zuciyarsa ba isarwa na ta zuciyar da sakonsa, sanyin jikin daga numfashinsa ya fito ya shiga nasa sai ya saukar mata da natsuwa da take jin da kamar ta rasa. Kalamansa sun yi nasara gaskiyarsa ta yi tasirin sanyaya zuciyarta a yanzu kwakwalwar ta bude zuciyarta ta karbi sakonsa.

 Zan aure ka Kareem!! Ka tafi jinyar zaka same ni a yadda kake son na kasance, zan aure ka kuma na maka alkawari zan rike an da ka haifa da Safeena i will save you, i will make your life complete 100%, dan Allah Kareem na roke ka cutar da ni please don't let me down...

Mafarki yake? Gaskiya ne? Ko dai suma yayi? Kuma tsananin kaunar Noor ta fara saka masa abubuwa ne? Ko dai yayi losing mind dinsa ne?
Zan aure ka Kareem!!
Zan aure ka Kareem!!
Zan aure ka Kareem!!

Haka yake ta jin sautin muryata mai dadin sauraro da taushi a kunnesa. Kallonta yake kamar be fahimci yarenta. Mikewa ta yi tsaye sakamakom shigowar da kanwarsa Khadija ta yi ba tare da sake furta masa komai ba ta fice daga dakin. Ya kasa motsi ya kasa numfashi ya kasa yarda idonsa na ne kawai suke kanta har ta fice, Khadija ta juyo ta kalli kofar da Noor ta rufe ta kalli Yayanta dake kallon kofar ta sake duban kofar ta dube shi har lokacin kofar yake kallo.

 Big Bro...

Ta tara masa hannunta tana motsa domin gani idan ya san abun da yake.
Sai ya lumshe ido ya koma ya kwanta a hankali numfashi ya dawo da karfi kamar zai fasa huhunsa zuciyarsa ta buga da karfi ya jimke hannunsa yana sauraren sauti daya na Noor Zan aure ka Kareem!! A yau kalaminta ya fi na kullum dadi, muryarta da fi ta kullum zaki.




NOOR POV.

Na aminta har a zuciyata na ji cewar zan iya auren Kareem a yanzu, i was afraid to lose him, a broken heart ce ta rage min yanzu, and i need someone who can fix it ba wanda zai saka broken heart dina into piece ba. And if Safeena zata min duk wannan saboda Kareem to akwai bukatar na aure shi saboda ta fahimci ni na ci gasan.

If Kareem zai bata lokaci kudinsa wajen ba ni kariya ko farinciki, to ya kamata na ba shi abun da yake so a gareni in har zan iya kuma ba tsabawa addini ba. I saw my future in his eyes.
Mun fara da kamar abota ne when we fell in love not knowing what it was. A yanzu dai yana fahimtata ina ji kamar zai iya rike ni. Ina tafe ina tunani kala kala har na iso gida, na ga bakuwar mota a kofar gidanmu ban kawo tunanin kowa ba, na shiga dakin Mama sai na samu mijinta a ciki tare da Yayanta suna magana. Waje na fito na zauna ina ji zazzabi zai rufe ni jikina yayi zafi ga ciwon kai da ya rufe idona, zuciyata na daukar abubuwan da suka fi karfinta.
Wani karamin cousin dina ya ce ana kirana a waje.

 Waye?

 Ban sani ba, da mota ya zo yana waje dai

 To je ka ce ina zuwa

Na fada masa ma my mind was telling me Aaryam ne ya zo daukata kamar yadda Kareem ya fada, wata kila kuma ya turo shi ne ya fada ma Mama da kansa, ko kuma ya zo daukar mu ne gashi kuma ban fadawa Mama ba domin na same ta da baki, haka dai nake ta sake sake, gudun barinsa a waje ya saka na fita domin sanar masa cewar ban riga na fadawa Mama ba ya dan jira su kare magana tukuna.

Zatona ya sha banban da abun da na gani, idanuwa suka yi arba da abun da zuciyata ta dade tana kauna, rashin tsammanin dawowarsa ya haddasa min faduwar gaba. Na taka na isa gurin da yake tsaye na rumgume hannayena kaina a kasa.

 Baby Noor

Sai da ya rufe ido na bude a lokacin da ya furta min sunan da yake kira na da shi a lokacin da muke abokan rayuwa. Ya matso kusa da ni, matsawowarsa ya masar d bugun zuciyata towards him.

 Ya kike ya hakuri ya gida ya Mama ya kowa?

 Kowa lafiya kalau

Na kasa daga ido na dube shi, kunya da nauyinsa sun baibaiye ni. Ya saka hannunaa daya a aljihu yana kallon unguwarmu.

 Kawai dai na zo na duba ki ne, ina fatar babu wata matsala

Na girgiza kai na amsa murya can kasa.

 Babu

Mun dauki tsawon lokaci a haka be sake magana ba ni ma ban sake cewa komai ba. Can kuma sai na ji ya kira sunana.

 Noor

 Na'am

Na amsa jikina na karkarwa.

 Daga ki kalleni mana, ko dai har yanzu tsanata kike?

Na girgiza kai alamar Aa sannan na dago a hankali na kalleshi, shi din dai Zafeer mutumen da Baba ya cilasta min juya masa baya a lokacin da yake tsananin kaunata, ashe har yanzu ina da kimar da zai biyo ni ya tambayi lafiyata, hawaye suka sauko min, shi ma kallona yake idanuwansa da rauni kamar yadda fuskarsa ma ta nuna.

 Na zo ne na dubaki, no matter what happen kina cikin raina ina tausayinki

 Na gode, na ba ni abun da ban cancanta ba

 Mu bar abaya ta wuce baby Noor abun da ya wuce ya wuce, mu fuskanci gaba

Na daga mishi kai sai ya sauke ajiyar zuciya.

 Zan tafi akwai abun da kike bukata?

 Aa bana bukatar komai

 Take care of your safe, sai na sake zagayowa

Na yi baya baya sai ya bude motarsa ya shiga ni kuma na juya na shiga cikin gidan. A zauren gidan na jingina na lumshe ido ina maida numfashi a hankali, na sani Zafeer ya zo duba ni saboda karfin zuciya irin nasa, ba dan yana nufin dawowa ba, domin ban cancanci haka ba. Kuma na yarda wata soyayyar bata nufin aure, wani auren kuma baya nufin zama. Na dade a gurin dafe da kirjina har sai da na ji na samu salama sannan na share hawayena domin yanzu kuka ya zama abinci na, na shiga cikin gidan, ban shiga bangaren da Mama take ba sai na zauna a dayan bangare da kanenta da yake da Amarya na shiga falonta na kwanta jikin kujera na rufe ido kamar mai bachi.


Ban san me suka tattauna ba, Mama ce dai ta shigo ta kawo min wayata da Abdull ya karba tare da sim din da komai a ciki amman babu recording din an goge shi har ma da wanda na yi ma Safeena. Kiran da na ga ya fi yawa a wayata har an hada da sako na mayar domin jin dalilin kiran da kuma sakon da aka turo min _ki kira ni_

Ina kira sai ya daga muka gaisa ya gabatar min da kansa.

 Sunana Alhaji Sule unguwa Uku

Har lokacin ban fahimci waye ba har sai da ya fada min shi ne wanda ya karbi number kwanan baya ina hanya.

 Na kira sai wani ya daga, yace kar na sake kira wai ke matar aure ce

Na dan yi murmushi na san Kareem zai aikata abun da ya fi wannan ma.

 Amman zuciyata bata aminta ba, domin matar aure ba zata yi irin shigar da kika yi ba, wata kila dai shi ma yana cikin masu neman auren ne kamar yadda ni ma zan shigo yanzu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login