Showing 60001 words to 63000 words out of 227321 words

Chapter 21 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1523

bawa mutum shawara akan lafiyarsa da irin abincin da ya kamata ace ya ci ko?

 Eh mana abun ai kamar da gayya kuke yi, ni ba wanda zai hana ni cin kayan dadi wani wai ina da suga

Ta sauke daukar wani naman ta kai bakinta, sai Kareem ya mika hannu kamar zai sake dauka ya ci ya fisge plate din ya mike tsaye ya koma nesa da ita ya zauna ya cigaba da cin naman da spoon din dake kai. Kallon mamaki take masa kamin ta hade rai daman ya saba yi mata haka idan ya tarar tana cin wani abun da yake da illa ga lafiyarta.

 Kareem rainin nan fa ya fara yawa! Dawo min da plate dina

 Momy ba zan yarda cuta ta yi miki yawa ba, yanzu idan kika fara ciwo waye a wahala? Mu ne a tashin hankali mahaifina da kashe kudi

 Okay... Wato tashin hankalin da kashe kudin kake mahaifinka kake ji ba ciwon da nake ji ba ko?

Ya saka dariya yana auna naman a bakinsa daman be karya ba ya fito.

 Toh Momy ban da neman rigima Fisabillilahi miye na saka kayan dadi a gaba kina ci, kuma idan kika yi rashin lafiya a dora mana laifi?

 Amman kai naman kake ci yanzu ai? Ka bar ni na ci kamin na tafi na bar muku duniyar

 Ba zaki tafi ba, zaki zauna tare da mu har sai mun riga ki tafiya, me aka girka miki da safen nan First Love?

 Ban sani ba, can gidanka baka ci abinci ba ka fito?

 Wallahi ban ci ba

 Saboda me?

Ya kalleta kamar mai tunani.

 Saboda Me? Ra'ayi Momy sau nawa nake zuwa nan ina cin abinci

 Amman ba haka ake so ba kanen miji ya fi Miji kyau

 Toh ai Aryam be fi ni kyau ba balle Yusura ta fi sonsa da ni

Ya fada yayinda yake mikewa tsaye Momy ta girgiza kai tana murmushi.

 Allah ya shirye kai kam

Dinning din falon ya nufa ya hada tea ya dauko biredin da kanwarsa Khadija ta gasa ya dawo ya zauna.

 Ya shirye shirye?

Ya kalleta cikin rashin fahimta yana zauna bread din.

 Na Hafiz mana

 Oh yana nan muna yi

 Toh Allah ya taimaka, yanzu ya bude maka Kofa ko?

 Kofar me?

 Kofar aure mana, ai daman Abokai ne suke budewa aboki kofa, mahaifinka ma Abokinsa ne sila

Yayi murmushi

 Momy Tsoron kike yi ma yarki kishiya?

 Toh ya muka iya Allah yace ayi, ko bama so dole mu hakura ai, ni ma hakurin na yi da aka min ita gashi yanzu an zama daya, kuma Allah yasa dai macen kirki ce, dawowar nan ma da na yi Khadija bata son zama bangaren nan sai can

 Momy ba wani kwana kwana kawai Daddy na ya iya kwatanta adalci ne shiyasa

 Ba laifi ya rike amana gaskiya, kuma ita ma Husaina tana da hankali tana kokarin nuna masa idan ya kwance, shi ma kuma ya san duk yadda aka yi ba a kaiwa gun uwargida har abada, da ya rike wannan sai muka zauna lafiya. kai ma dai ba dan halin maza ba wanda ke da mace kamar Diyata ai wata ba zata burge shi ba, mace ga kyau ga kyau hali

Kareem ya aje cup din dake hannunsa yana tabe baki.

 Yusura dai ta samu sa'a bana sha'awar tara mata ne kawai, amman kyauta be taba burgeni ba balle ya hana ni ganin kyau wasu matan, kyau hali kuma ita zai amfana ba ni ba

Momy ta karkato tana kallonsa.

 Kyauta be taba burge ka ba? Amman tana da kyau ko?

Kamar mai nazari haka yayi sannan yayi murmushi ya amsawa Momy.

 Kin san ni kyau mace be cika daukar hankalina ba, na fi son na ga mace tana amsa sunanta na mace da rauni irin na mata da wasu abubuwa da suka shafi mata

 Karya kake yi Kareem kana son kyau, me yasa ka nacewa yarinyar nan marar tarbiya

Yayi murmushi domin ba wannan ne karon farko da mahaifiyarsa take kiran tsohuwar budurwarsa da marar tarbiya ba.

 Ba dan kyau ba ne, kawai dai ina sonta ne

Ya duba agogon hannunsa ya mike tsaye.

 Kar na yi latti bari na wuce gurin aiki

Ya fara takawa ya isa kofa yana kai hannunsa ya bude kofar Momy ta ce.

 Kareem...

Ya juyo ya kalleta

 Allah ya maka albarka

Yayi fuskar mamaki yana dan murmushin da ya zame masa ado.

 Na minene?

 Ina jindadin yadda kake zuwa kullum ka gaishe ni sannan ka tafi aiki, ka yaro ne mai tsananin biyayya da son farincikin iyaye, idan na ce kar ka aikata kana gudu kake kaucewa hanina idan kuma na ce ka aikata a take kake aikatawa ka banbanta da yaran zamanin nan kana da biyayya da gudun bacin ran iyaye fiye da yan'uwanka, wasu iyayen basa samun haka

Fasa bude kofar yayi ya dawo gurin mahaifiyarsa da kusan zai iya kiranta da kawarsa saboda yadda yake mu'amala da ita.

 Na gode Momy, Allah kara miki lafiya

Yayi mata side hug ita kuma ta amsa da Ameen sannan ya fice daga gidan... Daga gidan kai tsaye asibiti ya wuce gurin aikinsa, he spend 6 hours a gurin sai da yayi Sallah La'asar sannan ya koma gidansa kai tsaye ya wuce dakinsa yayi wanka ya canja wasu tufafin sannan ya fito ya sauko kasa ya fice daga falon ba tare da ya kalli kofar kitchen din da yake jin motsi ba. Restaurant dinsa ya wuce ya shiga office dinsa, da telephone yayi using ya fadi abun da yake bukata for lunch aka kawo masa. Daf da zai gama cin abincin Hafiz ya turo kofar Office din ya shigo.

Kareem na ganinsa ya aje abincin ya zari tissue ya goge bakinsa ya dauki ruwa ya sha, sannan ya kalli Abokinsa da murmushi a fuskarsa.

 Ango, da gaske dai auren yarinyar nan zaka yi

Hafiz ya zauna yana fadin.

 Idan har wani sai ce zai yi abu kuma ya fasa, to wani dabam ba Hafiz ba, ka fi kowa sanin idan na yi magana daya bana canjawa

 Amman me yasa ake ta boye min? Kai sadakinka ma a gurin wani na ji, dazun kuma Abbah ya kira yana tambayar ko lafiya baya ganina a cikin abubuwan ka wai an kai lefe be gan ni ba

 Wadanan abubuwa ne da suka shafi mata, ba dole sai na fada maka ba, bana son na fada maka wani abu da zai saka ka ji babu dadi shiyasa duk wani jan ragamar auren ma Madam na barwa ita ta yi

Kareem yayi murmushi kamar babu komai bayan kuma ya san can a kasan zuciyarsa yana jin babu dadi.

 Na yi mamakin da Aisha take ta baka goyon baya, ban zata za ta karbi abun salin salin ba babu fada babu daga hankali

Hafiz ya cire hular kansa.

 Ni kaina na yi mamaki, gaskiya Matata yar Aljanna ce Kareem matar nan ta ba ni goyon bayan da duk ake bukata, ita ta saka na ja maganar auren nan ta dauki lokaci haka saboda ta samu damar yin shirye shirye, lefen nan ma ita ta hada ban yi tunanin zan samu haka daga gareta ba, da na fada mata silar auren ma karka so ganin yadda take tausayawa Noor

Kareem yayi jimmmm na dan lokaci jikinsa yayi sanyi, kamar Hafiz ya san abun da yake sakawa a zuciyarsa sai ya ce.

 Ban fada mata alakarka da Safeena ba, ba abu ne mai kyau ba balle na tallata, kuma wannan sirrinka ne da be kamata kowa ya sani ba, Noor din ma da ta zama sila ba zata taba sanin alakarku da Safeena ba, domin ban san me Allah zai yi ba a gaba, idan har zan iya daukar wuka na daba maka na kashe ka Kareem toh Tabbas zan iya fadawa wani sirrin dake tsakaninka da Safeena, ni dai duk abun da na yi kuduri na neman janye ka daga aikata alfasha ne da kuma nema maka farinciki, Ban san ya abun yake ba, domin ni abun da nake so shi na samu mun yi soyayya da Aisha kuma mun auri juna, muna zamantakewar aurenmu cikin amincin da kaunar juna

A sirrance Kareem ya sauke ajiyar zuciya a sirrance domin shi be san wannan dadin ba. Na auren macen da kake so, da kuma be san dadin zaman auren ba, domin be san wani rana daya da suka rayu da Yusura ba cikin soyayya da shaukin juna. Dago kai yayi yana kallon Hafiz dake amayar masa da abun da ke ciki a game da rayuwar Kareem din.

 Indai har yadda soyayya take da tsananin karfi, haka kiyayya take da shi, toh kai abun tausayi ne Kareem, Sabuwar da wadda kake so, ka auri wadda zaku yi zaman aure har ku haihu biyu baka ji kana sonta ba, ita ma bata ji tana sonka ba, lamarinku yana ba ni mamaki Kareem ban tana ganin ma'aurata masu tsananin kiyayyar junansu irinku ba

Kareem ya kwanta jikin kujera yana maida numfashi.

 Daman can kasan ni Yusura bata burge ni, ban taba jin ina son yarinyar nan ba Wallahi tun tana gidanmu, ita ma bata da abokin gaba Irina tana matukar jin haushin tsarin rayuwata, kuma tana da wadda take so amman kaddara ta riga fata, Momy ta ji bata gamsu da tarbiyar Safeena ba bata karbeta a matsayin in-law ba, shiyasa ta musanya min da Yusura ni kuma ba zan iya musa mata ba, Ina son farincikin Mahaifiyata Hafiz, Yusura ma ba zata iya ce mata Aa ba saboda ta bude ido a hannun Momy Momy ta zame mata uwa ta zame mata uba ta mata gatan da yan'uwan mahaifinta suka kasa yi mata, sai take ganin idan ta musawa Momy za a ce saboda ba ita ta haife ta ba ne, kuma Yusura tana da tsakanin Biyayya Ga Momy fiye da Khadija da Momy ta haife da cikinta

 Kun kasa karbar kaddarar ne Kareem kun kasa bude zuciyoyinku kun kasa kallon junanki da Rahama shiyasa har yanzu kuka kasa zaman jindadi

Kareem ya busar da iskar bakinsa.

 Wata kaddarar bata nufin zama har abada Hafiz, idan kiyayya ta yi yawa daya ke tafiya ya bar daya, ko dai na mutu na bar Yusura ta huta ko kuma ita ta rasu ta bar ni na samu salama, domin ba zan taba aikata abun da zai daga hankalin Momy ba, ba zata taba sanin irin zamantakewar da muke ba

 Wata kila tana son sulhu kai ne dai ka ki ka bada kai, domin idan ka hau saukowar abu ne mai wahala Kareem

 Hafiz Yusura bata so na, ta barar da 3rd cikin da ta samu

Hafiz ya kwalo ido yana sakin baki.

 Garin Ya?

 Ra'ayi, watanin baya na ga wasu hallaya da dabi'u a tattare da ita da take idan tana da ciki, kuma ta fada min zata je asibiti, but after that babu cikin nan

 Wata kila dai ba cikin ba ne Kareem ko kuma ya zube a karan kasan ne

Kareem yayi murmushi mai sauti, ya kada kai ya hade hannaye yana kokarin kawar da maganar.

 So yanzu me ya rage a shirye shiryen da kake?

Hafiz ya mike tsaye ya isa gurin da Abokinsa yake zaune ya dafa kafadarsa.

 Kareem ka min alkawari dan Allah ko da ba yanzu ba, nan gaba zaka aure macen da take sonka kake sonta zaka yi aure na farinciki da soyayya ko da bana raye, mu'amala da Safeena ba kaddara bace ganganci ne, kuma ba dalili ba ne

Kareem ya dafa hannun Hafiz dake kan kafadarsa.

 Na maka alkawari, amman Safeena muna wata na bakwai wani abu be shiga tsakanina da ita ba, na aje Safeena a gafe Hafiz

 Ina fatan hakan

Hafiz ya karasa yana bubbuga kafadarsa sannan ya koma gurinsa ya zauna.




NOOR POV.

Duk yadda ake yaba uban lefen da Hafiz ya dankaro min ni babu abun da ya burge ni a ciki. Fargabata da tsoro sun ninku fiye da baya saboda gabatowar auren mutum da babu shi a lissafin masoya na, kuma babu shi a cikin mafarkina. Ko sau daya hannuna be kai cikin kayan na duba ko daya ba balle na jidadi, ko da yake ina jindadin a kyauta ko kyautata ga mutumen da baka so? Ban ji ina son Hafiz ba ko na wuni daya, zan yi biyayya wadda ta zame min dole ba dan zuciya na so ba, ta dayan babin kuma tausayin halin da Zafeer yake ciki ya hana ni tausayawa kaina ya hana ni jindadin abinci ya hana ni sha'awar komai a rayuwata, kusantar kwanakin auren da zan iya kira na kaddara ina jinsa kamar gabatarwar mutuwata.

 Wallahi kin yi dace Noor gaba daya unguwar nan labarin lefenki nan ake

Na dago na kalli Zainab cike da takaici da bakinciki.

 Yabon kawai kika ji ba ki ji ana zagi ba?

Cikin sanyin muryar da raunin fuska ta amsa da cewar.

 Na ji, amman kowa ya san kina son Zafeer shi ma kuma yana sonki, wasu dai suna dora laifin a gurin mahaifinku ne, har ana cewa saboda haka mahaifiyarku ta fita

 Bana son mutumen nan da zan aura, Baba ya dage sai shi, ban san ya zan yi zaman auren ba, ban san ya zan kalli fuskar mutumen da bana kauna na rayu da shi na tsawon lokaci ba, ji nake kamar na gudu

Ina maganar hawaye ya wanke min ido zuciyata ta kara karaya.

 Dan Allah karki yi ki jefa mahaifiyarki a matsala dan dai kin san ta Baba ba ruwansa, da ma dai zai miki lamani ki koma gurin Mama ki zauna kamin auren zaki fi jin sanyi

 Ba zai bari ba, ita kuma ta yi rantsuwa ko mutuwa aka yi ba zata zo daga gidan nan ba, balle kuma aurena, lefen nan ma tace ta yafe ganin ba zai ya zo ba kuma ba sai an kawo mata ba, kuma Baba ya hana mu zuwa gurinta yanzu

 Ki yi hakuri Noor, ni dai zan tafi kar Baba ya dawo ya tararda da ni yayi zaton wani munafurci nake zuwa yi

Ta mike tsaye tana saka Hijab dinta na bita da kallo ina hawaye.

 Amman Zafeer din ya ji sauki?

 Har yanzu dai yana asibiti, idan ma an sallame shi garin zai bari haka na ji Mamansa tana fadawa Ummanmu tace zai koma gurin Yayan mahaifinshi Abuja

Na saka hannuna na share hawayena na mike tsaye na biyo bayanta, har kofar gida na rakata na tsaya ina kallon tafiyar har sai da na daina hangota sannan ya juyo na dawo wasu hawayen suna bin fuskata...

 Ba zan yafe maka ba Kareem, kai ne silar wannan masifar da ta same ni

Na karasa cikin kuka mai karfi har sai da Hana ta fito daga dakin Mama da gudunta.

 Noor Lafiya

Na rike hannayenta ina kuka.

 Hana bana son mutumen nan Wallahi bana sonsa bana son shi ko kadan, Zafeer kawai nake so, yanzu yana asibiti duk saboda ni, tun yana ciwo a gida abun ya kai shi asibiti kuma saboda ni ne, ba zai yafe min ba, Allah ba zai bar ni ba

 Babu wanda ya isa ya hana Baba abun da yayi niya Noor kin sani, kuma aure yanzu sauran sati biyu hakuri kawai zaki yi, Allah ya riga ya kaddara wannan ne mijinki ba Zafeer ba, ba kuma Kareem din ba ma, kuma kin ga ya sama Baba sauki ya ce baya bukatar akai ki da komai, ta ya Baba zai yarda a fasa aurensa ki auri Zafeer

 Amman ni Zafeer nake so

 Baba be san soyayya ba Kudi kawai ya sani, kowa da jarabawarsa mu kuma irin ta mu kenan


Ta rike ni ta mikar da ni tsaye ina kuka. Wata zuciyar na raya min ko dai na gudu kamin aure ko kuma bayan domin ina jin soyayyar Zafeer ba zata bar ni na yi zaman aure ba.





I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne. If you want to subscribe Pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

Or

6484787074
Khadeeja Candy
Moneypoint

And send the evidence of payment to 08036126660

See you>?p? ' #KhadeejaCandy
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*


''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Book 2 - Chapter 2*

Kusan zan iya cewa na saba da kuka a duk lokacin da rai ya bace, balle kuma yanzu da kaddara ta sauya min mu'amala da dabi'u. Kuma ta rufe ni a cikin wani dakin da ban isa na fitar da kaina ba. Idanuwa na saka ina ta kallon yadda ake ta kai da kawo na sha'anin bikin aureni a yayinda bani da wani kuzari na magana ma balle na motsa, kamu, walima da wani event da ake yi na aure ban shirya ko daya ba, Hana ce mai kokarin ganin na yi wasu abubuwa amman ban saurareta ba domin ni kadai ya san yadda nake ji a rayuwata na auren mutumen da ba shi a lissafina.

Ana sauran kwana biyar adaura auren Hafiz ya saka a sallamomi, a lokacin na ci kuka har na sauya kalar idanuwana, sai na fito ina tafiya kamar bana son isa inda yake tsaye. Daga jikin kofar gidanmu na tsaya na rumgume hannyena kaina na kasa domin bana son kallon fuskarsa ma. Daga inda yake jingine jikin mota sanye da kananan kaya ya dago ya karaso kusa da ni kamshin turarensa na kara kusantar hancina. Wayarsa ya ciro daga aljihu ya kunna haske fitilar ya haska fuskata.

 Noor Lafiya kike kuwa?

 Ni ban taba lafiya ba tun da kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login